Skip to content
Part 19 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Aliyu da Sagir abokai ne tun suna yara, ɗaya ba ya taɓa ɓoyewa ɗaya damuwarsa. Hata da karatu tun daga primary tare suke tafiya. Couse ɗaya suka so karanta Allah bai nufa ba. Cikin mintuna ƙasa da goma sai ga shi ya iso.

Yanayin da ya gani a fuskar Aliyu da kuma ƙafafun Alawiyyah da ya gani wadda ke kuka shaɓe-shaɓe ne ya ɗaga hankalinsa. Cikin tashin hankali yake tambayarsa abin da ya faru,

“Da ma ka faɗa mini Sagir ashe ranar nadamata na zuwa!”

“Wai mene ne!?”

Ya faɗa a fusace, bai ɓata lokaci ba ya bayyana masa komai daga farko har ƙarshe. Sagir tun yana tsaye sai ga shi a zaune yana hawaye. Ƙafa ya sa ya yi wa Haj Zali wani mugun duka a ƙugu ai kuwa ta gantsare ta fasa ihu. Aliyu ne ya riƙe shi yana nuna masa ya bari doka ta yi aikinta.

Waya ya ɗauka ya kira abokan aikinsa suka zo suka yi gaba da ita, tare da umartar su kan a tattaro duk wasu abokan hulɗarta gaba ɗaya.

Jiki a sanyaye Aliyu ya ja ƙafa ya matsa kusa da Alawiyyah wadda gaba ɗaya wuta ta ɗaukewa, sai yanzu ne Alawiyyah take gane wasu abubuwan da take kamar ba a hayyacinta ba tamkar umarni kawai take bi.

Ko da wasa ba ta son ɓacin ranta.

“Aliyu ka cuce ni!”

“Na sa ni Alawaiyyah na cuce ki ba ma ɗaya ba, amma taimaki ɗaya za ki wa rayuwarta don zatin Allah kadda ki rabu da ni. Ni kuma na yi miki alƙawari duk runtsi zan rayu dake a yanayin da ki ke ciki!”

“Ƙarya ka ke Aliyu me zaka yi da gurguwa?”
“Ba ƙarya yake ba Alawiyyah ni nasan duk runtsi zai rayu dake a yadda ki ke, domin Aliyu ya san hallaci.”

Idanu ta ƙura masa tana son tabbatar da abin da ya faɗa, yayin da zuciyarta ke son ƙaryatata.

*****
Sai da Saubahn ya warke sarai sannan ya samu ya leƙa Haj Khadija ba ƙaramin mamaki ta yi ba da ya bata labarin abin da ya faru. Faɗa ta dingayi kamar ta ari baki lamarin da ya ba shi mamaki sosai yake jin kamar ita ɗin wani ɓari ne na jikinsa. Bai jima ba ya yi mata salama ya tafi.

*****

Kimanin kwanaki uku kenan tun bayan da Saubahn da ya zo mata da labarin ƙalubalansa da Alawiyyah ta shiga mamaki da tashin hankali. Mace har mace amma kuma babu hali, sosai abin ya ɗaure mata kai.

Wani tunani ne ya ɗarsu a ranta, tun bayan dawowar Fatiman ita take shiga tana kula da jikinta wadda ba ta ga wani cikin danginta ba ko kaɗan, hakan ya sosa ranta ya kuma sake tuna mata da tata rayuwar ta baya. Babban abin da yake ba ta takaici shi ne cin kasin da Samir ɗin yake yi son ransa wai a haka ma yana ganin ƙimarta ne.

Da wannan tunanin ta shirya ta nufi gidan Fatima. Tana fitowa ƙofar gida suka gaisa da Baba maigadi, tana shirin barin wurin Saubahn na ƙarasowa. Har ƙasa ya sunkuya ya gaisheta. Ta amsa cike da murmushi.

“Idonka ke nan Saubahn hadda yi mini kurin za a dinga zuwa dubani. Yau fa kwa biyu ke nan tun zuwanka kan batun Alawiyyah ni ka tafi k bar ni da tunani da tashin hankali.”

“Ki yi haƙuri Mamma, aikin Baba Mal ne akwai yawa.”

“Eh! Gaskiya Mal ba daga nan ba. Ni ma na fito ne zan leƙa yayarka Fatima da jiki kwana biyu ban leƙa ba.”

“Mu je na raka ki Mamma sai na wuce ta can ko?”

“Babu komai mu je Saubahn.”

Tare suka tafi yana riƙe da ledar da ta zubowa Fatima kaya ciki, hira suke sama-sama tana tambayarsa garinsu, tambayar data haifar masa da wata irin kewa,
“Malumfashi shi ne asalin garinmu cikin wani ƙauye, yanzu kuma ahalina na cikin garin Katsina. Amma an ba ni tabbacin mahaifina ɗan garin Maraɗi ne.”

Ya ƙarasa furucin a ƙoƙarinsa na dane wani miki mai girma daga zuciyarsa. Ganin yanayin da yake jiki ne ya sanya ta ƙyaleshi domin ta fahimci kamar akwai wani abu tare da shi. A haka suka ƙarasa shiga farfajiyar gidan Fatima. Daidai lokacin ita kuma ta fito da gudu kamar an jeho ɓera daga rami. Gaba ɗaya jikinta ya yi ruɗu-ruɗu daga ita sai zani ɗaurin ƙirji. Samir ne biye da ita yana huci kamar wani baƙin kumurci.

Kuka take kamar ranta zai fita,
“Don Allah ka yi haƙuri Samir ba zan sake ba, ba zan sake yi maka musu ba.”

Saubahn ido kawai ya zuba masa yana ganin ikon Allah. Haj Khadija kuwa ranta ya yi matuƙar ɓacci, mace da ɗanyen jego a ranar Allah a korota waje ana duka gaban ‘yan aikin gida da masu gadi. Ina mutuntaka ina daraja.

“Kai Samir mene ne haka…”

“Malama ya isheki ai dama ke kike zugamini mata, tsohuwar banza dake don kawai kin ga ina baki girma ke ma daga yau ya…”

Kyakyawan naushin da Saubahn ya sauke masa ne ya hanashi ƙarasa maganarsa. Bai kuma tsaya iya haka ba ya cigaba da libgarsa kamar ya samu kayan wanki. Masu gadi da masu ba fulawa ruwa duk suna kallo aka rasa wanda zai karɓe shi. Fatima kuwa ban da kuka babu abin da take yi. Amma kuma ta ji daɗi, ko ba komai yau ɗaya Samir zai fahimci tana da gata a tsayin rayuwar auren su ta shekara huɗu cif.

Rayuwar da ta gudanar da ita cike da naci da kuma ƙawa zuci. Rayuwar da ta yi ta cike da ƙasƙanci da kuma rashin daraja. Kawai don ta zaɓi ya kasance a tsaginta sai ya zama laifi? Sai yanzu ne take ganin wautarta matuƙa tun farko sai da mahaifinta ya nuna ba zai ba ta Samir ba amma ta nace saboda tana tunƙahon gidan su akwai ‘yanci na duk abin da ka ke ao za ka yi matuƙar baka kaucewa addinni ba. Mahaifin su ɗan boko ne sai dai kuma yana da tsantseni wurin sauke haƙoƙinsu.

Kwaɗayinta na auren Samir ya samo asaline na ganin ya fito daga gidan tarbiya, mahaifinsa babban mutum ne, sai dai ashe kallon kitse takewa rogo shi ɗin furen juji ne. Dalilonsa sai da ta rasa kowa da komai nata. Tunaninta ne ya katse daidai lokacin da Saubahn ya ɗauki Samir ya maka da ƙasa. Hakan ya sanya shi sakin wata ƙara mai ƙarfi.

Daidai lokacin wata mota ta sako hancinta farfajiyar gidan, a tare kuma ƙofofin motar suka buɗe wata mace ta fito, bayanta kuma wani dattijo ne mai cikar kammala. Kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da su ɗin ba su fito gidan da za a raina ba.

Da gudu Fatima ta nufi macen ta rungumeta, kawai sai ta tsaya tana dubanta cike da mamaki. Fuskarta ɗauke da tambayar abin da ke faruwa. Matashin da ya tuƙo su ne ya nufi Saubahn ya ɗaga shi daga kan Samir da niyyar kwaɗa masa mari, sai dai kyam Saubahn ya riƙe hannuwansa,.

“Kadda ka yanke hukunci cikin rashin sani! Ka koma ka dubi jikin baiwar Allahr can da ya yi wa tabbuna kamar kura kafin ka hukunta ni.”

Sai lokacin ya juya yana duban Fatima dake kwance jikin mahaifiyar su. Idanu ya waro cike da mamaki da tashin hankali. Ai kuwa a fusace ya sake damƙar Samir ɗin,

“Ashir kadda ka taɓashi, ƙyale shi hukuma za ta yi aikinta.”

Muryar dattijon ta ratso cike da ba da umarni. Don haka ya sauke shi a hankali kamar ba ya so. Sai lokacin Haj Khadija ta ƙarasa kusa da su. Cikin girmamawa ta gaisa da dattijon wanda ta fahimci mahaifin Fatima ne tunda ta taɓa ganin hotansa.

Mahaifiyarta kuwa sun taɓa haɗuwa sau ɗaya har ta yi mata ƙorafi kan rayuwar da yarinyar take yi amma ta nuna ita ta siya da kuɗinta.

“Maman Fatima kin ga abin da nake ji ko? Tun a baya na yi miki ƙorafi kan rayuwar da yarinyar nan take a gidan nan ki ka nuna ita ta siya da kuɗinta. Sai da na nuna miki ba a biye ta yaro amma ki ka nuna ba haka ba. Yanzu me gari ya waya? Wane irin ƙasƙanci ne da ya wuce a daki matar gida a gaban masu yi mata hidima?”

Ko ba su tambaya ba sun san cewa koma mene ne ba mai daɗi ba ne, sun san rayuwar da ɗiyarsu take yi. Kawai dai suna kawar da kai ne. Sun san cewa ba ta samun farin ciki suna dai hukuntata da abin da ita ta zaɓa. Ta kuma nuna yatsa a kansa tare da saka naci wurin tabbatar da wanzuwarsa a duniyarta.

“Fatima Samir ba yaron da za ki rayu da shi bane!”

“Abba shi nake so”

“Kin san cewa ko aikin yi ba shi da shi, da me zai riƙe ki”

“Abba ba nagartarsa ya kamata ka ƙalubalanta ba, nagartar mahaifinsa!”

Duk ta inda mahaifinta ya ɓulo a lokacin tana da kalaman tare shi. Allah Ya saka masa ƙaunar Fatima sama da kowa cikin yaransa, shi ya sa lokacin da ta nace sai Samir ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba. Tana da kaifin ƙwaƙwalwa, karatun kimiya ya so ta yi amma zugar Samir da muradin auranta suka kangarar da zuciyarta zuwa bigiren da ta ke jin shi ne ya kamaci tunaninta.

“Mama Khadij wallahi na yi iya ƙoƙarina, tun ranar da muka haɗu dake karon farko kika yi mini ƙorafi kan hakan ban sake samun nutsuwa ba, haka kuma Fatina na faɗa mini irin ƙoƙarin da ki ke yi mata sai dai hakan bai sa mahaifinta ya fuskance ni ba saboda laifin da ta aikata tun farko.”

“Ina ga maganar kamar ba ta nan ba ce mai zai hana mu samu wuri mu zauna”

Mahaifin Fatima ya furta ransa a matuƙar ɓace, yayin da zuciyarsa take wani irin suya.
“Za mu zauna Abban Fatima amma ba a gidan wannan mara kunyar ba.”

Mahaifiyarta ta furta,

“A gidan sa za mu zauna Saudatu domin ina san sanin daga inda matsalar ta soma.

Samir dai ya yi tsuru-tsuru yana jin su, gaba ɗaya sai yanzu nadama ta soma luluɓeshi.

Ya sn waye mahaifin Fatima ya kuma san abin da zai iya yi, sam bai san abin da ya hau kansa ba har ta kai su ga haka. Duk abin da yake yi mata ya san ba ta faɗa a gida iya haƙuri tana yi da shi yanzu idan aka raba shi da ita ina ya kama?

“Ka buɗe mana mu shiga idan kana da niyya”
Ashir ya furta kamar zai hamnare shi. Jiki a sanyaye ya buɗe musu gidan, gaba ɗaya suka ɗunguma. Fatima ta wuce ɗaki ta suturta jikinta ta fito har zuwa lokacin shassheƙar kuka take. Bayan sun zauna, mahaifinta ya buɗe taro da addu’a sannan ya soma magana.

“Samir tun bayan dana baka auren Fatima, na sanya muku idanu. Ba kuma wai don bana son ‘ya ta ba ne ina sonta kawai ɓacin rai ne na abin da ta yi min na na sanya doka ita kuma take ta. Sai dai gaba ɗaya kai ɗin baka san zuru ba, duk abin da yake faruwa a gidan nan ina da labarinsa, domin da yawa daga cikin ma’aikatanku yarana ne.

Ban taɓa zaton ka kai haka ba, ban kuma yi tsamanin a tarbiyr gidan ku ba za ka yi abin da ka yi yau wanda ita ma kwɗayin hakan ne ya ja ta ga auranka. Amma ka sani an zo ƙarshe an kuma zo in da nake jin zan iya ɗaukar mataki. Ba zan rabaka da matarka ba domin ba ni na baka ita ba, amma kuma zan bi kadin haƙƙinta.”

Ya juya kan Fatima yana dubanta,

“Tun farko abin da na gudar miki ke nan, amma ki ka saka ƙafa ki ka shure umarnina yanzu mai gari ya waya?”

Karon farko da Fatima ta ji nadama da danasanin biyewa son ranta, ƙiri-ƙiri ta katse karatunta kawai saboda huɗubar da Samir ya yi mata ga sa’anin karatunta nan duk sun kammala wasu suna aiki wasu suna neman kuɗinsau a ɗakin mazajansu asirin su a rufe.

Ita sana’ar ma bai barta ta yi ba.

“Abba ka yi haƙuri, son zuciya ne da rashin sanin ciwon kai ya kai ni, amma a yanzu a shirye nake na bi kowane umarni naka ko da zuwa datse igiyar aure na ne.”

Ɗa da uba sai Allah take ya ji wasu ƙwalla na cika masa idanu, tausayinta ya rufe shi, ya kuma ji zai iya yi mata ko ma mene ne domin tabbatar da ‘yancinta.

“Ba zan kashe miki aure ba Fatima amma kuma zan tafi dake daga nan ko shekara ɗari ne har sai Samir ya tabbata mai nadama akan kuskuren da ya aikata miki. Ni ma kuma ina roƙon afuwarki bisa wofintar da rayuwarki da muka yi. Kuskuren wasu iyayen ke nan, sam ba ma gane cewar ba a gyara kuskure da kuskure.”

Ya ƙarasa yana ƙure kallonsa akan Saubahn da duk kallo ɗaya da zai masa sai gabansa ya yanke ya faɗi tun shigowarsu harabar gidan. Wani abu yake tunawa, wani abu da yake da tabbacin sun rasa shi rashi na har abada. Gaba ɗaya suka miƙe suna sake yi wa Haj Khadija godiya bisa kyautattawarta ga ɗiyarsu. Fatima ta rungumeta tana kuka,
“Mama zan tafi, yau burinki ya cika kin karɓar mun ‘yanci bisa rayuwar da ba ta da alfanu.”

“Tabbas haka ne Fatima, amma ina da sauran buri kin sani.”

“Na sani Mama in sha Allahu burinki zai cika nan da ba ta jimawa ba.”

Duk sai suka ba su tausayi, Saubahn har ƙwala ya shiga sharewa saboda tunawa da nasa ahalin. A hankali mahaifin Fatima ya ƙaraso tare da kama hannunsa,

“Ya sunanka?”

“Sunana Saubahn Tasi’u Umar.”

“Tasi”u Umar?”

Mahaifin Fatima da kuma mahaifiyarta suka yi rige-rigen haɗa baki wurin furucin,

Saubahn ya jinjina kai yana jin wani tsoro na ɗarsuwa a zuciyarsa. Daidai lokacin da mahaifin Fatiman ya ƙaraso ya sa hannu ya ɗaga haɓar Saubahn sai ga wani tambari ya bayyana,

“Saudatu kin ga abin da na gani kuwa.”

Ya faɗa yana ƙure tambarin da idanu,

tambarin da ya kasance a ƙasan haɓarsa. Tambarin da Madu da Abdallah ma na da shi. Tambarin da sai lokacin ya kula da irinsa a ƙasan haɓar Fatima da mahaifinta da kuma mahaifiyarta. Haka kuma tambarin da ya taɓa gani a shafin farko na kundin mahaifinsa. Wanda daga wannan shafin bai sake buɗe kowa ne shafi na cikin kundin ba. Bai manta lokacin da mahaifinsa ya yi musu tambarin ba har faɗa suka yi da Mammansu.

“Abbu Saubahn wannan fa?”

“Maryam kawai ya mun kyau ne, shi ya sa na yi musu. Ba ki su ma ya yi kyau ba kamar nawa?”

Ɓata fuska ta yi,

“Ni dai sam bai mun ba!”

“To ko za ki goge musu ne?”

Ya faɗa yana haɗe rai, sai ta juya kawai ta ƙyale shi ba don ta yarda cewar don ya yi masa kyau ba ne, saboda tambari ne da a fuskarsa kawai ta taɓa ganinsa sai kuma ta Dr Asiya da bangon kundinsa. Tana da yaƙinin tambarin na da alaƙa da wani abu na sa mai muhimmanci. A lokacin t sake jin kewar kuskurent na rashin bibiyar Dr Asiyan.

<< Kuskuren Wasu 18Kuskuren Wasu 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×