Skip to content
Part 2 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Tarko

Tunda motar da ta ɗaukota ta direta a bakin shigo-shigo ɗin wajen gyaran gashin mai ɗauke da tambarin Marwakh ta ke jin idanun matan da ke tattare a wajen a kanta. Ba yau hakan ta saba faruwa gareta ba, musamman idan aka yi la’akari da yanayin motar da ta kawota da kuma suturar da take jikinta. Hakan ba baƙon al’amari ba ne gareta, sai dai maimakon ta ji ɗaɗin yadda idanu ke shawagi a kanta akasin hakane.

Taune gefan bakinta ta yi har sai da ta ji gishiri-gishiri yana bin tsakanin haƙoranta wanda ba ta tantama da cewar jini ne. Ɗauke idanunta ta yi daga kansa akaro na barkatai, ta tura murfin motar da zumar fita. Rafar kuɗi ƴan ɗari-ɗari ya ɗora mata kan cinyarta.

“Na san za ki shiga gida, a gaida min su kafin na dawo ɗaukarki.”

Ɗauke kai ta yi tana ƙoƙarin maida ƙwallar da ta ke ƙoƙarin samun muhali a kuncinta, ta girgiza kai tare da tura murfin ba tare da ta ɗauki kuɗin ba, lokaci guda ta furta,

“za su ji.”

“Alawiyyah…!”

Ya kirata murya can ƙasan maƙoshi, saii dai yadda ta ɗauki ɗumi tasan tsaf za ta biye masa su kwashi ‘yan kallo. Don haka ba ta jira cewarsa ba ta wuce, tana jin lokacin da ya yi ƙwafa ya bawa motarsa wuta.

A Hakan sam bai dameta ba, hasalima ya rage kaso mafi tsoka daga cikin nauyin da ya asassawa ƙirjinta. ba ta daina mamaki yadda idanun tsarorinta mata ke yawo a kanta ba, tana da yaƙinin ayyana samun kwatankwacin rayuwarta suke yi a ƙarƙashin ransu. Murmushi mai sauti ta saki tana tunanin kowace dai da irin nata ƙalubalan.

A hankali ta sami matsuguni a cikin wajen da aka tanada saboda irinsu. Wadda su ka saba sossai a wajen, ta nufota da kazarniyarta tana dariya,

“Hajiyarmu yau ma kin iso ashe? Lallai yau jakata a cike take da maƙuɗan kuɗaɗɗe.”

Dariya ta yi mai sauti, “daɗina da ke akwai ban dariya Hassana yau ban ga injilahbba.”

Ta furta tana ba za idanunta alamun nema. Matashiyar budurwa ce siririya kamar a busheta ta faɗi ta ƙaraso wajen, kallo ɗaya za ka yi mata ka sakata a sahun masu iyayi.

Ɗan ƙaramin hancinta ta sosa tana faɗi,

“Ga ni nan ai tunda na hango Alhajinki ya ajiyeki naketa nishaɗi.”

Wannan karon ba ta tanka ba, ta ajiye murmushi mai sauti tare da miƙa musu kum da kibiyarta. Nan da nan su ka soma yi mata abin da su ka san ta fi buƙata. Suna yi suna jan ta da hira tana biye su ko ba komai sun rage mata kewar abin da ya ke cin ranta.

Wani ƙamshi ne ya yi musu sallama, gaba ɗaya su ka ɗaga idanunsu ba dan sun shirya wa hakan ba.

“Tubarkallah.”

Injilah ta furta a ranta daga nan ta maida kanta kan abin da take yi. Ita ma da ake wa tsifar daga kallo ɗaya ba ta kuma maida kanta sashin ba. Sai dai wani sashi na zuciyarta na mintsininta kan sake kallon sashin musamman yadda ƙamshin matar ya dinga haifar mata da wata irin kasala da nutsuwar da ba ta san dalilinta ba. Ƙarar takalma ɗas-ɗas ya ja hankalinta, kafin ta gama tantancewa ta ji mutum a mafi kusancinta, murmushin tsakiyar laɓɓa ta sakar mata tare da furta,

“Sannu”

“Yauwa sannunmu” ta maida mata amsa a yangance. Ta ci gaba da tauna cingum ɗinta, ƙas-ƙas-ƙas-ƙararras! Karo na barkatai ta ɗora idanunta akanta. Gabanta ya yi mummunar faɗuwa. Ta sakar mata murmushin da ya ƙarasa kashe gaɓan jikinta,

“Ku ɗan bamu waje!”

Ta furta tana sauke idanunta akan matasan ƴan matan, zuciyarta cike da farin cikin samun alamun nasara, akaro na wanda ba ta san adadinsa ba na hallartarta wajen dominta kawai. Hannunta ta damƙa, take wani sanyi ya ziyarceta, ta ɗan murza shi a hankali tare da furta, “ko zaki min alfarma mu zama ƙawaye?”

Kai ta jinjina mata, tana mai jikin kamar ta yi wani ƙaton kuskure da ba za ta iya gyarashi ba.

Zaune take yayinda ta sa hannuwa biy-biyu ta buga tagumi tun bayan dawowarta gidan Fatima. Babu abin da ya ke bijiro mata a rai sama da ɗiyarta tilo da ta bari. Shin wace rayuwa take? A kintacenta za su yi sa’ani da Fatima. Ras! Gabanta ya faɗi yayinda wata zuciyar ta raɗa mata,

‘Kenan ita ma ta yi aure! Wa take aure? A wane matsayin rayuwa take?’

Ba ta ankara ba ƙwalla su ka soma zarya a kuncinta. Yayinda wani duhu ya gilmawa tunaninta. Numfashinta ya soma yin sama da ƙasa. Ba ta ankara da shigowar maigidantaba tsabar fitar hayyaci.

Ya kai mintuna huɗu da shigowa ɗakin amma ba ta sani ba, idanu ya tsura mata cike da takaici, ba wai dan ganin halin da take ciki ba sai dan ɓata masa lokacin da ta yi yana ta magana babu amsa. Ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu tsabar baƙin ciki. Doka stool ɗin mudubi ya yi da ƙarfi. Firgigit ta juya,

“Alhaji sannu..Kai ne..? Ban san…”

“Dakata Khadija, ba uzurunki nake buƙata ba.”

“Wallahi ban san ka dawo….”

Sake katseta ya yi a tsawace, ke ki ka sani, ni ba damuwata bace. Na shigo ne na faɗa miki za mu tafi Saudiyya hutu gobe ni da Hajiya Hauwa da yara so abin da ki ke buƙata ki yi magana.”

Wannan karon ba ƙwalla ba ce kaɗai, kuka ne ya ke shirin taho mata. Yayinda wani miki ya shiga famuwa a tsokar dake tsakanin a wazunta. Wai sai yaushe za ta zama kamar kowa ce mace mai cikakken iko a gidan mijinta? Shekaru goma sha takwas tana zaman bauta amma tamkar an shuka dusa.

Ta sani cewa kuskurenta ya isa girbar fiye da abubuwan da take riska, amma ba ta yi tsamani za a samu naci wajen zamansa a gurbin rayuwarta ba. Duka kuskuren nata ne, amma girbar laifukan da ba ita ce tushan dasa su ba.

Ta lura tsaf rayuwarta neman zama turken kare take yi, shi wanda take yi dominsa baya ta tata yayinda a idanun ƴan uwanta yake nuna babu ya ita har suna ganin ita ce mowar gida. Wawwan tsakin da ya ja ne ya juyo da hankalinta amma kafin ta farga ya wula mata damin kuɗi ya fi ce fuu!

Kallon su ta yi tare da ɗauka ta yi wurgi da su ta fashe da kuma kamar ƙaramar yarinya. Ba sune muradinta ba, ba su ne za su ba ta abin da take ganin ya yi wa rayuwarta giɓi na har abada ba. Yau ɗaya tana jin kewar giɓin da ba ta da tabbacin cikeshi. Tana jin kamar ba ta cancanci girbar wannan shukar ba. Ba nomanta bane, akwai girbin da ahali ke gadarwa da makusanci shi bisa kaifi irin na alƙalamin ƙaddara.

Ta jima anan zaune tana jin hayaniya da karakainar mutanen gidan amma ba ta jin fitowarta za ta haifar da alfanu dan haka ta zauna tana jan istigifari. Ba ita ta fito ba sai magarba bayan ta idar da sallah saboda yadd take jin ranta ya yi sanyi. Gaba ɗaya mutanen gidan suna fallo, kowa da abinda yake yi.

Mashiɗa tana gam a laptop ɗinta tana haɗawa da cin ƴaƴan itacen da ta sa aka tanadar mata. Tun fitowar Mama Khadijan ta kalleta sheƙeƙe kamar wata sa’arta ta watsar. Karima ce ta taho da ɗan gudunta. Ta turo baki gaba,

“Mama tun ɗazu nake zuba ido ban ganki ba, ga shi gobe zamu yi tafiya ba mu yi hirar da zan dinga tunaki ba.”

Kalaman yarinyar sun ɗauke kaso tamanin na damuwarta. Aranta ta ji ashe ita ma uwa ce..Sai dai ƙarfin tsakin da Hajiya Hauwa ta saki ya ankarar da ita mafarki take yi.

“Wallahi Karima sai na buge bakinki ya yi taɓon da duk ranar da wannan matar tabar gidan nan zaki dinga tuna ita ce sila! Dan anamimmanci ita uwarki ce?”

Rau ta yi da idanu, kamar za ta yi magana sai ta juya da gudu ta shige ɗakin su. Ji ta yi ƙafaffunta sun ƙara nauyi kamar ba za su ɗauketa ba. Zuciyarta na matsewa da wani irin tashin hankali da ba sabo ne a duniyarta ba.

Tabbas ta zauna da abokan zama masu baƙin jahilin kishi irin na matan ƙauye amma ba ta taɓa gamo da muguwa kuma makirar mace kamar Hajiya Hauwa ba. Wankakiya ce fes a idanun danginta saɓanin cikin rayuwar auranta.

Sallamar Baba maigadi ce ta katse mata tunani, ta amsa masa da hanzari sanin babu wanda yake da ƙimar yin hakan duk cikar fallon.

“Hajiya Mama wai ga shi daga gidan barrister…”

Kafin ya ƙarasa Mashida ta kwashe da dariya,

“An dai yi girman kwabo. Gemai-gemai ana bin gidan matasan yara abin hadda ƙwaɗayi”

Saroro ta yi tan dubanta daga ita har Baba maigadin. A haife ta haifeta hasalima ita ce mutum na farko da ta yi mata wanka tana jinjira amma saboda ƙasƙanci ita ce ta ke mata wannan furucin. Ɗauke kai ta yi ta karɓi saƙon kamar ba ta ji ta ba. Hakan ɗabi’arta ce ta ji, amma kuma ta nuna kamar ba ta jin ba. Ta gani amma sai ta zama makauniya duk dan a zauna lafiya.

Tana hango tausayinta a idanun tsohon ya girgiza kai ya fita. A ransa yana jinjina rashin tarbiya irin na yaran gidan da mahaifiyarsu ta zamo tsani. Shi kansa be tsira a wajensu ba amma yana mamakin yadda take shanye duk wani abu daga faninsu.

Tsayin shekaru ashirin yana aiki agidan, a lokuta mabanbanta alaƙar mutunka ta sha haɗa su tun kafin ta zamo ƙarƙashin ikon maigidan har zuwa matakin da su ka zamo inuwa guda. Sai dai ba zai iya cewa ga rana guda ta ya tsinkayi murmushi a saman nutsattsiyar fuskarta ba wanda bana yaƙe ba. Tabbas cikin mutane ma irinta ƙayadaddu ne.

Da sassarfa ta wuce ɗakinta ko buɗe saƙon ba ta tsaya yi ba, tana jiyo shewarsu tare da mahaifiyarsu har zuwa lokacin da ta jiyo sautin mahaifinsu suna murna. Idanunta gaba ɗaya sun rufe mafita kawai take nema. Kai tsaye ta ɗauki wayarta ta kira layin babbar yayarsu. Bugu biyu ana uku ta ɗaga,

“Ka ga matan many..”

Aka faɗa daga ɗaya ɓangaren, sai da ba ta kai ga ƙarasawa ba ta katse a zafaffe. Karon farko da ta tunkari yayar ta su da irin wannan zafin da ya sakata ɗaurewar mara.
“Dakata Yaya Kulu, wallahi na kira ne in shaida miki yau na gaji da cin kashin da Yaya da matarsa suke min. Abu har kan ƴaƴan da acikina na haife su. Tabbas ku shirya gani na a gida ko da wane lokaci.

Kadda ki yi min barazana da cewar Baba za ta tsine min, ko tsireni zai yi wannan karon na kai maƙura. Da girmana da komai na zama ƙasƙantaciyar baiwa. Kuma ku sani daga ranar dana dawo zan nemo ɗiya ta duk inda take zan gyara kuskurena wannan a rubuce yake. Tabbas zan nemo Mar….”

Ga mamakinta ta kasa ƙarasawa. Sunan ya tokare mata maƙoshi tana jin yadda take kokawa da numfashinta. Ba wannan ne karon farko ba duk lokacin da taso furta abin da ya shafi rayuwar ɗiyartat ta hakane yake faruwa da ita. Wayar ta suɓuce a hannunta ba tare da ta sani ba.

Sunkuyawa ta yi hannunta a wuyanta da ta shaƙe da tunanin hakan ne zai kawo mata sassucin raɗaɗin da yake neman fasa mata maƙoshinta. Daidai lokacin Karima ta shigo da zumar ba ta haƙurin abin da ya faru a fallo.

Halin da ta ganta ya sanya ta shigo da gudu da ƙyar ta ɓamɓare hannuwanta a wuyanta. Suna maida numfashi tare. Kallonta ta yi a ruɗe sai huci take yi yayinda ƙwalla suke sunturi kan kumatunta.

Wayar ta ɗauka tare da datse kiran da har lokacin yake a kunne. Ba tare da ta jira cewarta ba ta shige bedroom ɗinta ta bar Karimar a zaune.

A can ɓangaren yaya Kulu kuwa tsabar kaɗuwa da mamaki ne ya daskarar da ita har ta kashe wayar ba ta san amsar da za ta ba ta ba. Babu abin da ya soma faɗo mata a rai sai gargaɗin da aka yi mata kan ta kiyayi asara da durƙushewar rayuwa duk ranar da Khadija ta sa ɗan bar neman ɗiyarta.

Musamman akan dukiyar da ta mallaka a sillar auren ita Khadijan. Don haka hankali ta she ta hau lallubar wata lamba a wayarta. Sai dai kafin ta dana kira wata lamba ta shigo a wayarta ta, ta ɗaga da faɗuwar gaba.

“Madam miliyan huɗun da aka haɗa za a kai banki ƴan fashin sun shigo ɗazu sun karɓeta ba jimawa.”

Yaraf! Ta faɗi ƙasa ba ta motsi.

*****

Kaico!

“Alawiyya akwai tafiyar da za mu yi yau don haka me kike buƙata?”

Sai da ta haɗiyi wani kakkauran miyau sannan ta furta,

“Bana buƙatar komai ma, kuma ma mene ne abin gagawa ba anjima za ka dawo gidan ba?”

“No ba zan dawo ba daga office zan wuce, dawowar ba ta da wani muhimmanci”
‘Muhimmanci?”

Zuciyarta ta yi mata raɗar kalmar a kunnuwanta. Wani abu ta ji ya daki ƙirjinta, girmnsa har ya shallake tunaninta. Murɗawar da mararta ta yi ya tuna mata tarin abubuwan da ta yi ta ɗirkawa kanta saboda tana yaƙinin daren yau zau iya zama tsaraba gareta.
Shekaran jiya ya dawo, kuma yana ba ta tabbacin yau zai koma. Ba wannan ne takaicinta ba, inda zai tafin ya fi yi mata ciwo fiye da wofintar da ita da yake yi,

“Ba ki ce komai ba!”

“Abin cewar ne babu”

Ƙit ta kashe wayar tare da dannawa Haj Zali waya.

“Kina gida?”

“Ina gidan ko kuma kango?”

“Bana san shirme Zali ina san ganinki!”

“Baki da matsala ke tawa ce zan yi komai domin farin cikinki”

Wani matsuguni mai girma kalaman nata su ka samu a zuciyarta. Hakan ya ɗarsa mata mamaki, a duniya babu mutumin da yake yi mata kwatankwacin kalaman ta ji sun tafi da duniyarta sama da Aliyunta amma mene ne yake shirin faruwa da ita?

Cikin hanzari ta shirya ta ɗauki mota ta fita. Har ta isa gidan nata ba ta daina mamaki ba, tana da yaƙinin amincewarta na zama ƙawaye ne mafari. Amma ko alamu ba ta jin danasanin faruwar alaƙar.

Sai yanzu ta ke jin dama tun asali wannan rayuwar ce ta kamaci mai matsala irin tata. Sai dai a wasu lokutan takan ji an ya ba ta tafka kuskure ba? A haka ta gangara da motarta layin gidan. Maigadi ya buɗe mata ta shiga.

Ɗaya bayan ɗaya take kallon mutanen da suke cikin gidan, yayinda zuciyarta take kisima mata akwai waɗanda irin tata rayuwar ce ta kawo su gidan. A babban fallon gidan ta samu masauki, amma sai ta samu umarni daga Hajiya Zali na cewar a kaita ɗakinta na musamman.

Haka ta miƙe tabi yarinyar kamar raƙumi da akala. A ranta tana ƙara ya ba tsaruwar gidan duk da ba shi ne shigowarta ta farko ba. Suna shiga yarinyar ta juya. Idanunta ta janye daga bakin ƙofar ta ɗora su kan Hajiya Zali. Take ta sake jin wani karsashi na ɗaukarta. Hannuwanta ta ware mata, babu musu ta miƙe kan duga-duganta cike da sassarfa ta isa gareta.

Lumshe idanunta ta yi, wani sasshi na zuciyarta ya kwaɗaitar da ita,

‘ina ma Aliyu ne!’

Dum! Wani sauti ya ziyarci masarafar sautinta, ɓurɓushin murmushin dake tsakiyar laɓɓanta ya soma zangwayewa yana gushewa zuwa bigiren da ya saba zama a irin yanayi.

Hannunwan Haj Zali da su ka sami matsuguni a wasu sassa na jikinta su ka soma saukar mata da wani irin hucin da ya tilasta mata hanzarta barin jikinta. Da ido ta dinga binta, ta taɓe baki tana taunar cingum ɗinta a nishaɗan ce,

“Ke dai Alawiyyah kin ji ɓutur wallahi, ki zauna ɗa namiji ya dinga watangaririya da rayuwarki kamar ɗiyarsa. Kin gani nan ba ni da ƙulafuci kan namiji tunda na gano wajen ragema kaina zafi. Tsakanina da ɗa namiji abu biyu ne, shi ɗin waigi ne ga rayuwata, sai kuma kadaran-kadahan idan ya ce kulle in ce cas!

Ga inda zan je ana mararina ana tattashina kawai ta tsaya ina ɓatawa kaina lokaci. Ke fa bama irin namu ki ke ba, an yi anyi a gwada miki kina dojewa to mene ne matsala a harka irin taki? Abu ne fa na sirri daga ke har shi kun sauƙaƙawa juna ba tare da shi ya fuskanta ba. Kawai dai zai wayi gari kin zama irin yadda yake so, kin sakarmasa mara ya yi fitsari ke kuma kina nan kina sha’aninki!”

Ƙarasowa ta yi kusa da ita tana rangwaɗa, yayinda ta sassauta murya da wata irin ƙaramar murya me haɗe da wani irin maganaɗisun da suke jan hankalin abokan harkar su. Hannunta ta shiga murzawa da wani irin sallo na ban mamaki,

“Please ki yi wani abu dan Allah. Ki ba ni dama ko ban baki farin ciki ba zan zamo tsani”
Kallon da ta yi mata ba iya kashe jiki bane kawai, akwai wani abu. Wani abu da taso mata wanda yake kwance tsayin shekaru a ƙirjinta. Binta ta yi da idanu, sai kuma ta gyaɗa kai tana kasa kowane harafi na ta a mazaunin da ya dace a ƙasan ruhinta.

Take zuciyarta ta amince da abin da ta faɗa. Dan haka ta shiga sakin murmushi tana jin duniyarta sabuwa. Shewa wasu ƴan mata biyu su ka saki, suna shigowa maƙale da juna. Kauda idanunta ta yi akan su tana jin za ta amince da shirin Hajiya Zali na samun farin ciki amma ba za ta iya irin rayuwar da suke yi ba.

<< Kuskuren Wasu 1Kuskuren Wasu 3 >>

6 thoughts on “Kuskuren Wasu 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×