Skip to content
Part 22 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

“Mamma!”
Baku nan yaran na ta suka haɗa baki wurin furta sunan cike da tashin hankali. Yayin da Madu ya riƙeta ƙyam a jikinsa kamar zai ƙaceta, sautin ƙararsu ne ya fito da Nuhu da kuma su Afnan dake cikin gidan. Saubahn ya ƙaraso a tsorace yana jijjigata,

“Mamma! Mamma!! Mammah!!!

Lu! Ta yi da idanunta sannan ta buɗe su cike da sa ran mafarki take yi,

“Saubahn!”

“Mammah ki ta shi, Saubahn ɗin ki ne, Mamma kuma ba ni kaɗai ba ga ni ga Mamanki Mamma ga dangin Abbanmu.”

Ai Nuhu ji ya yi kamar zai saki fitsari a wando, Madu kuwa wani irin ɗagowa ya yi a hanzarce yana duban yayan nasu.

“Ƙwarai kuwa Madu tare nake da su, lamarin mai tsayi ne ku shig gida da ita sai mu shigo.”

Kamata suka yi aka shiga ciki, Saubahn kuma ya yi musu jagora zuwa cikin gida. Tuni su Afnan sun shimfiɗa tabarmi tare da kawo ledar pure water guda biyu wadda Abdallah ya shigo da ita. Har zuwa lokacin da aka shigo da mutanan Mamma rarraba idanu kawai take a kan su ji take makar mafarki take yi ko kuma wani abu ne daban yake bibiyarta.

“Maryama ki yafe mini don girman Allah, wallahi ban san abin da ya yi mini shamaki dake ba!”

Ƙuri Mamma ta yi tana kallon Haj Khadija, jinta take kamar a wata duniya ta daban wai yau ita ce take ɗanɗana daɗin mahaifiya kamar yadda su Madu suke ɗanɗana kusanci a tare da ita. Da su ne kaɗai za ta iya gwada misali ko da ba sa cikin yanayi mai daɗi amma akwai wannan kusanci wanda ita take fata tsayin shekara da shekaru. Sai dai ƙaunar da take wa mahaifiyarta abu ne na daban da ba ta jin za ta iya haɗa shi da komai bayan ‘ya’ yanta.

“Mama na yafe miki!”

Ta furta cike da rauni gaba ɗaya wurin aka ɗauki kabara. Nuhu kuwa yana gefe sai rawar jiki yake kamar munafuki. Appah ne ya yi gyaran murya gaba ɗaya hankula suka dawo kansa, muryarsa mai cike da alamun tsufa ya soma magana,

“Duk da kasancewar mun ji wani abu daga bakin yaron mu, za mu so jin cikakken bayani daga bakinki Malama Maryama.”

Murmushi Mamma ta yi, saboda Tasi shi ne yake faɗa mata sunan idan ya so raha. Gyara zamanta ta yi, cikin nutsuwa ta soma ba su labarin rayuwarta tun daga ƙuruciya har zuwa girmanta da rayuwarta gidan Tasi da kuma bayan rasuwarsa har zuwa lokacin da suke zaune. Babu wanda bai zubar da hawaye ba, Nuhu kuwa ban da tagomashin mugun kallo babu abin da yake samu daga ko’ina.

Wasu abubuwan sai a lokacin su Madu suke jin su, ƙauna da tausayin mahaifiyarsu ya sake ratsa su yayin da ƙalubalantar dangogin su guda biyu ya kewaye zuƙatansu. Mamma kuwa sabuwar kewar mijinta ce ta taso mata, sai dai addu’a take masa cikin ranta tare da fatan yana cikin rahamar ubangiji. Ta so ace a gaban su Mama Sumaye aka yi wannan zube ban ƙwaryar, da sun tabbatar ita ɗin ‘yar dangi ce sai dai hakan ma ya yi mata tunda a gaban ɗan koron su ne.

“Mamma yanzu me suka zo yi mana? Duk da ma suna kusa da ke amma muke wanna baƙar rayuwar?”

Madu ya furta yana share hawayen fuskarsa,

“Wallahi ba laifin kowa ba ne Madu laifi na ne, don girman Allah ku yafe mini.”

Yaya Kulu ta furta tana gunjin kuka, gaba ɗaya kanta ya kulle jin rayuwar da Maryam ta yi a baya, hakan ya tabbatar mata tana da kaso mafi girma cikin taɓarɓarewar rayuwarta. Kafin kowa ya sake magana ta soma magana kamar an kuna rediyo.
Tiryan-tiryan ta bayar da labarin yadda ta dinga bi ta da ƙulin zuwa wurin malamak aka cirewa Khadija ƙaunar Maryam da garin da take a ranta. Har ma da mahaifiyarsu da sauran ‘yan uwanta yadda aka saka musu shaunin da kowa zai manta da yarinyar. Hakan kuma duk ya samu ne dalilin kuɗin da Salisu ya dinga tura mata a burinsa na auren Khadijan.

Daga baya kuma matarsa Hajiya Hauwa ita ma ta ɗora na ta saboda da buƙatarta. Ba tare da tasan rayuwar da ƙanwar tata take gudanarwa ta ƙasƙanci a gidan ba. Nan fa wuri ya cika da mamaki da al’ajabi.

“Amma yaya Kulu kin cuce ni sai dai kuma kan ki ki ka cuta da ace kin san rayuwar da na yi ta ƙasƙanci a gidan da baki jagoranci kai ni mahalakata ba. Ko da yake za ki yi abin da ya fi haka ma saboda kuɗi su ne muradinki.”

Haj Khadija ta furta tana gunjin kuka, tausayinta da ɗiyarta na cin zuciyarta da kuma mazauna wurin. Nan ta shiga basu labarin zaman da ta yi a gidan har yadda ta haɗu da Saubahn da kuma sakin da ya yi mata a yammacin jiya kafin zuwansu.

“Shi ke nan ma mun huta kin rabu da ƙaya Kakus domin ko bai sake ki ba ni sai na raba auren na amreki”
Madu ya furta cikin raha, duk da hawayen dake kwance a fuskarsa. Mamma ta kai masa mangari dake yana kusa da ita,
“Ƙaniyarka Madu uwata ce fa” Cewar Mamma.
“Ni kuma matata ce kuma tana son yaro sabon jini”
Gaba ɗaya aka kwashe da dariya, hakan ya yi masa domin yadda yake jin ransa ya tabbata da yawa a wurin suna jin kwatankwacin hakan. Ko babu komai sun sarara. Bayan komai ya lafa ne Saubahn ya basu labarin zuwansa Kaduna da zamansa gidan Mal har zuwa lokacin da ya haɗu da Haj Khadija ya kuma ji a ransa ita ɗin tsaginsa ce. Kowa ya cika da al’ajabi tare da sake yadda da ƙudurar ubangiji. Sai dai ya sakaya labarinsa da Alawiyyah a ganinsa wannan wani babi ne na rayuwarsa da shi ya shafa.
Sai dai Yaya Kulu gaba ɗaya ta shiga hankalinta, ta kuma tsaraka da kanta ta kasa sakewa kwata-kwata. Sai hurwa take tana neman yafiya wurin ‘yan uwanta da kuma mahaifiyarta haka ma Maryam da yaranta. Appah ne ya sa baki har sai da suka yafe mata daga nan wurin ya yi tsit ana jiran abin da zai ce.
Sai dai ga mamakin su sai gani suka yi ya fashe da kuka.
***
“Aliyu kai wa Allah ka ƙyale ni!”
“Alawiyyah ba zan taɓa rabuwa dake ba, zan rayu da ke ko da kin fi haka samun matsala a rayuwarki domin ko mene ne ya faru dake ni ne sila”
Hawaye ta share tana jin wani bango yana haɗewa da wani cikin zuciyarta.
“Ina jin tsoho Aliyu, ina jin tsoron mu kasance maƙiyan juna”
“Ba zai faru ba Alawy ki gasgata ubangiji ki yi yaƙini da kyautata zato. Ni dai burina ki yafe mini”
“Na yafe maka Aliyu, na yafe maka har gaban abada!”
Tun daga wannan lokaci zaman lafiya mai tsafta ya wanzu a tsakanin Aliyu da Alawiyyah, yana iya bakin ƙoƙarinsa wurin kyautata mata. A haka kuma ya ci gaba da neman magani. Kasuwancinsa kuma da yawa ya rage su, wanda suka zama dole ya ɗora ƙannansa akai tare da sauƙaƙawa kansa hidima.
Shi kansa sai yanzu yake jin daɗin kansa, ya kuma tabbatar yana rayuwa yadda ya kamata. Domin yana samun damar halartar ɗaurin aure da kuma jam’i wanda a baya hakan yake masa wahala matuƙa. Sai ya sake godewa Allah Ya godewa ƙaddarar da ta karkato da hankalinsa kan kuskurensa.
Sai dai har gobe yana jin kansa a mai babban laifin da ya gurgunta rayuwar Alawiyyah. Haj Zali kuwa an tarkata su an yanke musu hukunci tare da turasu gidan kaso. Bayan an tarwatsa ƙungiyarsu.
Tun daga wannan rana Aliyu ya zamo tamkar bawa a rayuwa Alawiyyah. Sau tari idan ya yi mata wani abun gani take kamar ba Aliyunta mai izza ba. Hatta danginta sun sha sanar da ita cewar,
“Haƙiƙa Alawiyyah kin yi dace da mijin ƙwarai. Yayin da wasu mazan suke gudun matan su a lokacin lallura ke kuma a lokacin ne yaƙe ƙara ƙaunarki”
Duk lokacin da hakan ta faru murmushi kawai take, murmushin da yake danne duk wani tabo dake ƙasan ruhinta. Ta haƙiƙance wannan ita ce ƙaddarar rayuwarsu. Domin ita da Aliyu kaɗai suka san dalilin sadaukarwarsa sai kuma Sagir.
***
Kukan da Appah yake yi ya sanyaya jikin mazauna wurin, musamman Mammah. Mahaifin Fatima ne ya muskuta tare da yin magana a tausashe,
“Appah don Allah ka yi shiru, kasan kukanka na nufin tashin hankalinmu baki ɗaya”
“Dole na yi kuka Aliyu, na so ace na riski Tasi’u da rai sai dai ƙaddara ta riga fata kamar yadda bai samu ganawa da mahaifinsa ba”
“Don Allah tsoho ka bar kukan nan ka ba mu labarin tushenmu”
Madu ya furta cikin ƙaguwa,
“Madu tushanku dai ba wani ɓoyaye ba ne, mu ɗin fulanin nijar ne kuma mun fito daga tsaftattacen ahali. Sai dai ƙaddarar da ta fito da mahaifin ku zuwa bigirenku ku ƙaddarata a matsayin ƙaddarar rabon haihuwar ku. Don Allah don Annabi ku barta a matsayin rufaffen sirri”
“Rufaffen sirri tsoho? Mahaifinmu fa? Ko dai yana da wani tabo ne da kuke ɓoye mana?”
Saubahn ya yi furucin murya a raunane, Nuhu kuwa kamar an saka shi a aljannah domin ji yake ya samu makamin yaƙar su, sai dai kuma kunnuwansa ne suka jiyo masa abin da ya sa shi nadamar ganin ranar yau.
“Mahaifin ku ba shi da wani tabo, hasalima nagartarsa ce ta sanya aka yi masa kurciya har ya zo gareku. Abu ne da ya taɓa ahalinmu muke kuma fatan mu bunne wannan baƙin cikin har abada. Ba ma san mu sake dasa muku wani tabon bayan wanda yake a zuƙatanku. Amma wallahi wallahi mahaifin ku mutum ne guda har da ƙari”
Rantsuwar tsohon ta karya duk wani ƙuduri na su, don haka Mamma ta fahimci manufar tsohon ta kuma haƙiƙance hakan shi ne mafita garesu. Ƙazantar da ba ka gani ba ta kan iya zama tsafta, bare kuma tana da tabbacin Tasinta ba shi da ƙazantar da ta kamaci ɓoyewa ko iya zamanta da shi ta isa tabbatar da hakan.
“Amma…”
“Madu mana pls, ku sa a ranku ku ɗin tsaftattu ne!”
Mamma ta furta cike da ƙarfin gwiwa.
“Ku godewa Allah da ya bayyana muku dangin mahaifinku ba tare da wata tantama ba, duk wnda ya dubeku ya dube su ya san akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninku. Balantana su da kansu suka gasgata hakan wannan kaɗai ya isa ku godewa ubangiji ku kuma tabbatar da ubangiji yana so da kishinku.
Mutane nawa ne suka rayu babu dangi babu uwa da uba, kuma hakan bai hanasu rayuwa ba. Mutane nawa ne suka rayu, har suka koma ga ubangiji ba za su ɗaga yatsa su nuna wani da sunan shi ɗin ahalinsu ne ba?”

Kuka ya ci ƙarfinta, a hankali Madu da Saubahn da Abdallah da kuma Afnan da Humaiyrah suka ta so suka rungumeta, ta ɗago tana dubansu. Hannuwanta na shafa su,

“Ku duba wannan duk sun tasu saboda ku ne! Duk sun wanzu saboda sanya farinciki bisa tabbatar da dangantaka tsakaninku wannan kaɗai ya isa wanke zuciyarmu. Ko iya haka aka tsaya wallahi mun ci ribar haƙuri”

Gaba ɗaya wurin suka ɗauki kabara. Domin sosai Maryam ta burge su matuƙa. Mal ne ya rufe taron da addu’a. Mama Khadija ta nemi Maryam ta bi ta zuwa gida amma atabau ta nuna ba za ta bita ba. Appah ma ya so ta ba su yaran ta nuna masa ba za ta iya ba, bai ga laifinta ba bai kuma ji zafinta ba. Sai dai sun tafi akan ta yi musu alfarmar ba su yaran duk ƙarshan wata suna zuwa gaishe da su Kaduna.

Hakan ya yi mata ta kuma gamsu za ta iya, haka suka rabu cike da kewar juna bayan Appah ya ba da tabbacin ane musu gida mai kyau za su siya musu. Tare da tabbatar a mayar da yaran gaba ɗayansu makaranta su za su ɗauki nauyin hakan.

Da za su tafi, haka suka dinga yi musu kyautuka na alfarma sai dai ko guda ɗaya Mamma ba ta bari sun karɓa ba, ba wai don ba sa buƙata ba. So take ta nuna musu su ɗin su suke buƙata ba wai abin da yake tattare da su ba.

Sun tabbatar da za su tsaya tsayin daka wurin ganin an kwatarwa Maryam haƙƙinta na game da gonarta, hakan ya yi matuƙar ɗaga hankalin Nuhu don haka ana gama taron ya silale ya nufi tasha ya hau motar Malumfashi.

Lokacin da labari ya riski su Mama Sumaye ba ƙaramin kaɗuwa suka yi ba, nan da nan suka shiga hankalinsu duk wani abu da suka san na Maryam ne sun tattarashi sun fito da shi. Har ma wanda suka siyar sun karɓo su a hannun dilalai.

Haka ya tattara ya dawo gida yana kame-kame. Maryam kwata-kwata ba ta bi ta kansa ba. Haka kuma ta tsawatarwa yaranta kan shiga lamuransa ko ba komai ya ci albarkacin yaransa guda biyu.

*****
Kwanci tashi babu wuya wurin ubangiji, Maryam da yaranta sun yi ƙalau masha Allah. Ba za ka taɓa fuskantar sun yi wata rayuwa ta ƙasƙanci ba. Gidan da aka siya musu yana gab da gidansu Mama Khadija. Hakan ya ƙara mata kusanci sosai da mahaifiyarta. Ya kuma saka shaƙuwa mai girma tsakaninsu.

Tuni Maryam ta gyagije ta koma shar da ita, ganin yadda hankalinta ya kwanta ne ya sanya mahaifiyarta ta dawo mata da ƙudurinta a ranta. Wato muradinta akan karatu. Abin ka kuma d wanda suke a jihar da hakan ba wani abu mai wuya bane, domin jahar Katsina ƙarshe ce in dai a fanin karatu ne. Nan da nan aka yi abin da ya kamata Maryam ta koma makaranta.

Gaba ɗaya yaranta sun koma makaranta, haka kuma dangin mahaifiyarta tsakaninta da su sai sam barka, har ba ta son su haɗu da Yaya Kulu domin kullum cikin neman yafiyrta take ita da mahaifiyarta.

Kullum ita kuma nuna mata take komai ya wuce, yanzu haka ma Kausar ɗiyarta ta tattaro kayanta ta dawo gidanta da zama saboda yadda ta su ta zo ɗaya da ita. Ta kuma himmatu wurin nuna mata aibun shaye-shayen da take yi. Kuma alhamdullilahi tana ɗaukar maganarta. Domin ita uwar da faɗa ta hau ta a farko, wanda ya sake tunzurata har ta soma barin gida. A wani zuwa da ta yi ne tana kuka tana ba Haj Khadija labari tun daga lokacin Mammahn ta soma janta jiki.

Kuma alhamdullilahi ta su ta zo ɗaya da Madu shi ma yana ƙoƙarin nuna mata hanya sosai. Wannan ya ƙara ƙima da martabar Maryam a cikin dangin mahaifiyarta. Sosai suke nuna kulawa a kanta.

*****
Bayan komawar su Fatima da wata ɗaya Samir ya matsa sosai bisa komawarta, sai dai kuma hakan ya faskara saboda mahaifinsa ya yi rantsuwa kan ba zai je yi masa biko ba, haka ma dangin mahaifinsa kaf aka rasa mai zuwar masa. Ba don komai ba sai don kasancewarsa mutum mara kirki ba ya ganin kowa da gashi. Tun yana yi wa abin kallon wasa har ya soma shiga taitayinsa. Domin ko ganinta ba shi da damar yi.

Tuni ya fita hayyacinsa. Ga Fatima kuwa hankalinta ya kwanta sosai ta yi ƙiba, ta samu yancin yin rayuwa cikin ‘yan uwanta babu hantara babu komai hakan ya sa ta yi ɓul da ita. Tunanin komawa makaranta ne ya soma zuwa kanta. Sai dai lokacin da ta tunkari mahaifinta da batun kai tsaye ya nuna mata ta tambayi umarnin mijinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Wasu 21Kuskuren Wasu 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×