MURFISai lokacin tunanin Samir ya zo mata domin har ga Allah ta manta da sha'aninsa. Ranar farko da ta kirashi ya nuna mata zai amince matuƙar za ta koma gidansa. Kawai sai ta kashe wayarta. Tun daga lokacin ya shiga yi mata naci tare da turo abokansa.
Msg kuwa tun ba ta buɗewa har ta soma buɗe. Ga shi ta sa wa zuciyarta ƙawazucin karatun shi kuma mahaifinta ta sani baya magana ɗaya dole sai da amincewar Samir. Dola ta sa ta sauko ta soma kulashi har suka daidaita kansu bayan ya yi mata alƙawarurru. . .