Skip to content
Part 23 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

MURFI
Sai lokacin tunanin Samir ya zo mata domin har ga Allah ta manta da sha’aninsa. Ranar farko da ta kirashi ya nuna mata zai amince matuƙar za ta koma gidansa. Kawai sai ta kashe wayarta. Tun daga lokacin ya shiga yi mata naci tare da turo abokansa.

Msg kuwa tun ba ta buɗewa har ta soma buɗe. Ga shi ta sa wa zuciyarta ƙawazucin karatun shi kuma mahaifinta ta sani baya magana ɗaya dole sai da amincewar Samir. Dola ta sa ta sauko ta soma kulashi har suka daidaita kansu bayan ya yi mata alƙawarurru masu yawa kan sauya ɗabi’unsa.

*****
“Yanzu shi ke nan komai ya ƙare?”

Alawiyyah ta furta yayin da take share hawaye,

“Komai ya ƙare Alawiyyah amma ban da alaƙarmu!”

Murmushi mai ciwo ta yi, tun bayan dawowar Aliyun da ya zo mata da labarin an yankewa su Haj Zali hukunci take kuka. Tabbas sun yi wata rayuwa mara alfanu amma hakan ba ya nufin ba ta jin matar a ranta. Sabo mugun abu ne. Sake share hawayenta ta yi tana shafa ƙasan mararsa. Ɗan ƙaramin cikinta da bai haura wata bakwai ba ne ya yi wata irin harbawa.

Ta runtse ido tana jin wani shauƙi na naushin zuciyarta,

“Ƙaddarar zuwanka ita ta sauya komai”

Wani murmushi ya suɓuce mata, tana jin komai na ficewa daga zuciyarta. Idan ta ce komai tana nufin komai amma ban da wannan ɗan tayin da yake riƙe da duk wani motsi na zuciyarta. So take ta tabbata a matsayin nan da uwa kan ji, so take ta ji shi a ƙirjinta. Ba ta sake tantance soyayyar ɗa ba sai ranar da ta shiga ɗakin scarning. Yadda take kallon yaron a allon magiji na computer, yadda yake motsawa da wani irin karsashi sai da ya sanyata zubar hawaye.

Daga kuma lokacin duk wata motsawa da zai yi ta kan ji tamkar yana motsawa ne da ainihin bugun zuciyarta. Wani irin gudu take yi da yake bata tabbacin kusancin alaƙarsu. Hannunta da Aliyu ya riƙe ne ya sanya tunaninta katsewa.

“Aliyu ni ma zan zama uwa!”

“Kin faɗa min,kin sake faɗa min amma kadda ki manta zamanki uwa ba zai hanani amsa sunan uba ba!”

Dariya ta yi cike da nishaɗi.

Rayuwa suke gwanin sha’awa da kuma sadaukarwa. A farkon lalurarta kawai ta ɗauka Aliyu waƙa yake, ta yi tunanin halin mazan zai aikata mata. Sai dai lokacin da tafiya ta yi nisa sai ta fahinci Aliyu zai iya komai domin samun farin cikinta. Lallai mahaƙurci mawadaci. Da a ce mutum ka iya tariyar baya ya juyo da rayuwarsa ya kuma goge kuskurensa da ta daɗe da yin hakan. Ko don tabbatar da farin ciki a duniyar su.

BAYAN SHEKARA BIYAR

Harabar wurin cike take da manya maza da mata yara da ƙanana da kuma dattawa. Kowa ka duba fuskarsa cike da farin ciki. Wani ƙaton wuri ne da aka lulluɓe gabasa da wani yanki tare da wata ingiya mai ƙyalƙyali. Hawaye ne taf cike a idon Maryam yayin da gefenta hagu Madu ne damanta kuma Saubahn ne, kowa ne sanye da rigar da take tabbatar da matsayins na likita.

Tsakiyar su kuma ita ce ita ma da nata kayan na aikin jinya, tun bayan shekara huɗu kenan da kammala karatunt na Midwife. Karatun da ta yi shi da ƙarfin guiwar ‘ya’ya da kuma danginta na kowane ɓangare.

Dr Asiya da ta zame mata tamkar ƙawa ita ce mace ta farko da ta ɗaga cikar burinta sai kuma mahaifiyarta. Sosai aminci ya ƙulu tsakaninta da Asiyan wadda ta tattara ta dawo Katsinan da zama ta biyo maigidanta duk don saboda Maryam ɗin. Wanda a baya babu yadda bai yi ba kan ta biyo shi taƙi.

Duk wasu shawarwari ita take ɗorata a kai. Haka kuma tana sake nuna mata dangi, sai lokacin ta fahimci ba ƙaramin yawa ne da su ba. Sai dai ta lura Asiyan na da damuwa a kan mahaifiyarta wadda ta kasance mai lalurar taɓin hankali.

“Addah Maryam ku yafe mata, ku yi mata addu’a ƙila ta samu sassauci”
Wasu lokutan kalaman Asiyan na saka mata shakku kamar akwai wani abu bayan tunaninta. Sai dai ta lura kamar Asiyan da kowa ma ba ya so ta fahimta don haka ta ɗauke kanta daga lamarin. Sai dai duk lokacin da za ta taka Kaduna ita ce mai kula da wannan mata mai taɓin hankali tin daga kan wanka zuwa ba ta abinci. Abin da aka rasa mai yi mata kwata-kwata saboda duka da take yi.

Wannan ma ka sanya Asiyar zubar da hawaye a wasu lokutan har sai Appah ya nuna mata ɓacin ransa. Ita kuwa tana ganin komai ta yi wa mahaifiyar Asiya ba ta faɗi ba domin Asiya ta tabbatar mata da za ta iya rayuwa bayan ta mutu.

Da farko ta ɗan fuskanci ƙalubalen rashin gogewar karatu sai kuma Nuhu. Nan ma Asiya ce ta tsaya tsayin daka har ta zama ƙwarrariya yadda ya kamata. Nuhu ya yi barazanarsa ya gama amma ko a jikinta, domin Asiya ta tabbatar mata za ta kashe muradanta ne da takaicin Nuhu. Ƙarshe da ya ga babu mafita da borin kunya da komai ya yi mata saki ɗaya ya tattara ya koma wurin ‘yar uwarsa Mama Sumaye.
Hakan bai wani dameta ba, domin ta san lokacin rabuwarsu ne ya yi, dama Madu na ta wannan ƙoƙarin ita take dakatar dashi.

Godiya kawai ta yi ga ubangiji da ya rabata da ƙaya, sai kuma tausayin yaranta mata da ya kamata domin duk tsiyar Nuhu uba uba ne. Ba ta da wata damuwa karatunta kawai ta sa gaba. Yayin da Appah ya sa aka ɗauki nauyin karatun Subahn zuwa Cairo ɓangaren likitan ƙwaƙwalwa. Madu kuwa gyneacologist ne. Sai Abdallah da ya karanci fanin business yanzu haka yana Kaduna ƙarƙashin company ɗin mahaifin su Fatima.
Babban burinta a duniya shi ne gina asibiti a ƙauyen ƙauran Namoda da kuma makaranta, sai ga shi ubangiji ya cika mata burinta Appah da kansa ya waru wasu kuɗi masu kauri ya ba ta da niyyar cika mata burinta. Su Madu ne suka tsaya tsayin daka wurin gudanar da komai. Har zuwa yau da take tsaye gaban asibitin.

Hannunta na rawa ta yanka yankin da almakashi take sunan,

“ILLA TASI”

Ya bayyana a jikin ƙaton asibitin gaba ɗaya aka ɗauki tafi masu kabara na yi. Bayan buɗe taro da addu’a ta gabatar da maƙasudin buɗe asibitin da sunan mijinta. Ta kuma tabbatar da komai na cikinsa kyauta ne tare tabbatar musu za su samu kulawa ta musamman. Take aka sake ɗaukar kabara.

Hakan shi ne burin da ta daɗe tana fama da shi a ranta, duk da cewar ta samu aiki a general hospital Katsina amma ta yanke wa ranta cewar duk Juma’a da yamma za ta dinga zuwa ƙauran namoɗa ta kwana a nan zuwa ranar Lahadi da yamma ta koma gida. Asabar da Lahadi za su zama lokutan da za ta sadaukarwa da mutanen garin. Wasu tagwayen hawaye ta sake shirewa, gani take kamar Tasi na tsaye yana kallonta.
Wuri ya hautsine da murna. Kamar almara sai ga Nuhu ya bayyana a wurin yana jan ƙafa, duk ya tsofe ga haƙoransa duk sun zube. Murya cike da rauni yake duban Maryam,

“Ban sani ba ko wannan ne haɗuwata dake karo na ƙarshe, sai dai ina roƙonki ki yafe mini domin na cutar dake cuta mafi girma. Ni na kashe mahaifinki, kuma ni na kashe mijinki. Son zuciya da kuma huɗubar shaiɗan yau ga makomata yadda ta kasance.
Duk na yi ne domin kasara rayuwarki ashe ban sani ba matattaka na zame miki zuwa ga tsanin nasararki. Kuma hakan ya faru ne duk a dalilin shawarar wannan muguwar matar Sumaye. Hasalima tare da ita muka murɗe kan mahaifinki. Kaico….”

Bai ƙarasa ba aka ga ya yanke jiki ya faɗi yana murƙususu. Madu kuwa kukan kura ya yi ya damƙoshi sai dai ina rai ya yi halinsa domin sai lokacin suka kula da kwalbar fiya-fiyar dake hannunsa wadda ita ya sha. Nan aka soma Allah wadai da halinsa, Mama Sumaye kuwa take a wurin ta kama hauka ta zauce. Kayanta ta soma wuli da su ta fita a guje, kafin ayi aune wata mota ɗauke da yashi irin tifar nan ta zo wucewa ta bi ta kanta. Ko shurawa ba ta yi ba.

*****
Littafin da ke gabansa ya ƙurawa idanu, wani irin bango ne mai kauri na fata irin wanda ake yi wa alƙur’ani mai girma. Wasu hawaye ya share masu ɗumi da suka jima suna maƙale a kwarmin idanunsa. Ya sani ƙwarai da gaske ya karyawa Appah alƙawarinsa, bai san dalilin da yake jan sa ba har ya kai shi ga buɗe kundin mahaifinsa.
Kundin dake ɗauke da shafuwan ƙaddara masu tsauri.
Kundin dake ɗauke da duk wani sanadi na giɓin rayuwarsu.
Kundin dake ɗauke da laifukan makusanta da suka kamaci afuwa.
Kundin dake ɗauke da wani abu mai girman da ka iya dane duk wani karsashi na fansar rayuwarsu. Lalai dole ne Appah ya yi gargaɗi kan buɗe shi. Dole ne ya hana su tunkarar sabuwar damuwar da za ta rusa kyakyawar alaƙar da suka gina. Sai dai kuma zuciyarsa na kai komo tsakanin ba wa Madu da Mammah da kuma Abdallah kundin domin su karanta abin da ya ƙunsa.
“Wa ya kamata na ba wa?”
Ya yi furucin a fili.

TAMMAT BI HAMDULLAH!

Nan na kawo ƙarshen wannan ɗan taƙaitacen littafi. Ina roƙon ubangiji ya sanya mu amfana da abin da muka saurara.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Wasu 22

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×