Skip to content
Part 15 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Murmushi Zhara ta yi ba tare da tace da ita komai ba ta juya ta fita, tsaki Halima tayi ta koma ta zauna a kan kujera zuciyarta na mata zafi sam ba ta son abinda zai sa mijinta ya kiɓanta da Zhara.

Zhara na fita ta yi ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta yalwanta fuskarta da murmushi. A hanya ya tsaya ya yi mata take away yana shigowa mota ya miƙa mata karɓa ta yi tana faɗin, “Na meye ne?” Bai ce da ita komai ba har sai da ya hau kan hanya “kiyi haƙuri ba ta jin daɗi ne shi yasa ba ta samu ta yi girki ba, idan kin je gida sai ki ci.”

“Da ka faɗa mini da ba za ka sayo komai ba, tunda gida zan tafi. Allah ya bata lafiya” ta yi maganar fuskarta ɗauki da murmushi tare da kawar da kanta daga kansa tana kallon hanya.

Bakin gyet ya ajiyeta ya juya har yanzu ransa a ɓace yake da abinda Halima ta masa. Tana shiga gida ta tarar da Momy a falo tana dannar waya.

“Ina wuni”

“Ina kika tsaya?”

Ta mata tambayar tana mai kafeta da idanu, kanta a ƙasa ta ce. “Gidan Yaya Hafiz na tsaya sai da ya taso wajan aiki sannan ya je ya ɗauko ni.”

Harararta Momy ta yi tana faɗin “munafunci ne ya kai ki gidan ba komai ba, bari ya zo na ji dalilin da yasa ya kai ki gidansa saboda neman fitina. Bani ledar hannunki!” Jiki a sanyaye ta je ta bata ledar fizgar ledar ya yi ta buɗe tana dubawa,

“Lallai wato har da kuɗi ya kashe maki saboda sangarta duk abincin gidan nan da makulashin gidan nan ba zai ishe ki ba har sai kin haɗa da roƙonsa ko, to ba za ki ci ba maza ɓace mini da gani” sumai-sumai Zhara ta wuce ta shiga ciki zuciyarta na mata zafi Momy ta raka ta da harara.

Ta na shiga ta cire Hijab ta kwanta a kan katifa tana mayar da numfashi maganganun Halima suna dawo mata a ƙwaƙwalwarta tamkar a yanzu take faɗa mata su, mamaki take sosai ko a mafarki ba ta taɓa tsammanin Halima za ta yi mata hakan ba bare kuma a zahiri ‘lallai mutum mugun icce’ shigowar Kande ne ya katse mata zancen zucin da take.

“Maman masu gida ashe kin dawo” tashi ta yi ta zauna tana faɗin ‘eh dawowa ta kenan. Ya gidan”
“Lafiya lau, bari na kawo maki abincin ki”
“Da kuwa kin kyauta mini dan na kwasu yunwa” bayan fitar Kande ta tashi ta shiga banɗakin tana fitowa Kande na dawowa da kolar abinci tana ajiye wa ta ce.

“Hajiya ta ce da kin gama ki fito ki wanke mata banɗaki ki kuma yi harrama ɗora girki.”

“Uhm! To shi kenan” ta faɗa tana zama a kan kafet “bari na je na ɗora girkin daren sai ki ji da wanki banɗakin kawai” kallonta ta yi tana faɗin “yi zaman ki kar ki janyo wa kanki faɗa.”

“Ba wani faɗa yanzu na barta za ta fita unguwa, na kuwa san kafin ta dawo na gama.”

“To bari dai na kama maki mu yi tare ni ma ai ba son zama ba aiki na ke ba, kuma kema ɗin kina buƙatar hutu” ficewa Kande ta yi ba tare da tace da ita komai ba. Ta suma cin abincin.

Nabila tana zaune ƙasa tana daddana wa Mama ƙafa “Nabila Hashim ya matsa mini da maganar ki ya ce ba kya ɗaga wayarsa idan kuma ya zo ba kya wani kula shi me yasa ki ke yi masa haka? Ba a wulaƙanta masoyi fa Nabila.”

“Ni fa Mama bai yi mini ba shi yasa, ina ta ƙoƙarin yi masa hannunka mai sanda amma shi sam ya kasa fahimta” kallonta tayi tana faɗin “mene ne makusar shi yana da kirki kuma yana da aikin yi, kuma ɗan’uwanki ne da na ke da tabbacin zai ba ki kulawa” ta ɗan yamutsa fuska tana faɗin “ai ba shi ne matsalar ba matarsa ce kin san halin Aunty Umma kishin masifa ne da ita komai ma za ta iya yi in dai a kan Yaya Hashim ne”

Fatima da ta ke gefensu ta na tsifan kai ta ce. “Ba wani matsalar Aunty Umma ke dai kawai ba kya son shi, Mama ita fa Yaya Hafiz ta ke so har yanzu ta kasa cire shi a ranta ko ranar na ga ta…

Filo ta jefa mata hakan yasa ta yi shiru ta na turo baki “Mama kin ganta ko”

“Yarinyar nan kema kin raina ni ko” Mama ta zuba wa Nabila idanu kafin daga bisani ta ce. “Wato dai ba za ki cire Hafiz a ranki ba ko? Na faɗa ma ki ba ko wani abu ka ke so ka same shi ba. Ya kamata ki daina ba wa kan ki wahala a kan wanda bai ko san kina yi ba, ki yi ƙoƙarin sanya wani a ranki ki cire son wanda ba kya gabansa”

idanunta suka ciko da hawaye cikin rawar murya ta ce. “Ni ma ina so na manta da shi ina so na cire shi a zuciyata ko zan samu salama a zuciyata amma na kasa. Mama ki taya ni da addu’a ina ji kamar son sa ne zai zama aja… Muryarta ta yi rauni sosai kuka ya zo ma ta ta bar wajan da sauri ta shiga ɗaki. Mama tabi ta da kallo tausayin ta ya cika mata zuciya har ta rasa wani tunanin ya kamata ta yi.

Tana moping ya shigo gidan sam ba ta ji shigowar sa ba har ya zauna a kan kujera, idanunsa a kanta a ransa ya ce ita wannan ko a gidan ma sai an zauna da Hijab. Haka kawai ta ji kamar ana kallonta hakan yasa ta juyo suka yi ido huɗu zuciyarta ta bada dum! Ƙasa ta yi da kanta.

“ina kwana”

“Lafiya lau. Ina Kande ne ki ke aikin da kan ki”
“Ta na ɗaki” Kande ta fito ta na faɗin “Barka da shigowa an tashi lafiya?”

“Lafiya lau. Ya ki ka bar Zhara ta na aiki?” Kallon Zhara ta yi tana faɗin “Haji … Saurin katseta Zhara ta yi ta ce. “Ni ce na ce zan yi na ga ji da zaman” shiru ya yi har cikin ransa bai gamsu da abin da ta faɗa ba musanman hana Kande ƙara sa maganar ta da ta yi. Tashi ya yi ya haura sama Kande ta zuba mata idanu ta na faɗin “me yasa ki ka hanani faɗa masa gaskiya?”

Murmushi Zhara ta yi kafin daga bisani ta ce. “Babu amfanin faɗa masa mahaifiyarsa ce fa zai hana ta yin abin da ta so ne ko kuma zai mata faɗa ne, ba ko ɗaya da zai faru sai dai ma ransa ya ɓace idan har ya ɓacin ma. Kuma ni wallahi sam ban damu da duk aikin da ta ke saka ni ba tunda ko a gida na saba ni na ke aiki gida. Ko ba yau ba don Allah kar ki ce za ki faɗa masa”

“Insha’allah ba zan faɗa ba.”

“Me yasa a ke sa Zhara aiki Momy?”

“Idan ba a sa ta aiki ba me ka ke so ne a sata iye?”

“Momy na ga ita ma kamar ‘yar gida ce yadda Khadija ta ke ‘ya a gidan nan” tana harararsa ta ce. “Ai sai ka cire kama ɗin, kai ni fa na rasa dalilin da yasa ka damu da yarinyar na
“Haba Momy ita ɗin ƙanwata ce fa”

“Kasan Allah Hafiz zan ce ka daina zuwa gidan nan in har ba za ka fita sabgar yarinyar nan ba”

Zajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “Ni fa babu wani abun a zuciyata gami da Zhara ya kamata ki yarda da ni kawai ita ɗin ƙanwata ce dole na damu da ita kamar yadda zan damu da Khadija am…

“Hafiz tashi ka ba ni waje, na ce ka tashi ka tafi” miƙewa tsaye ya yi jiki a sanyaye ya ce. “Allah ya ba ki haƙuri” ya fice ta raka shi da tsaki “yaron nan sai na yi da gaske in har ya na zuwa gidan nan ya na ganin yarinyar nan komai ma na iya faruwa” zumut ta yi ta mike ta fito ɗakin.

Kichen ta samu Zhara tana gyara nama, “ke kun haɗu da Hafiz!?” Gabanta ya bada dum! “Ba kallona na ce ki yi ba mai zubin munafukai tambayar ki na ke ki bani amsa!” Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa “eh mun haɗu”

“Me ya faɗa ma ki?”

“Gaisawa kawai mu ka yi” ta na harararta ta ce.

“Komai me ku ka yi da ga yau idan har ki ka ji ya zo kar ki sake fitowa har sai ya fita, sam ba na buƙatar ya ganki dan ban san surƙullen da uwarki ta haɗu ki da shi ba!”

Wani irin abu ta ji mai nauyi ya tukare mata a zuciya ta kasa cewa uffan. Momy ta kai ƙofa ta juyo ta na faɗin,

“kin dai ji me na ce ko?”

“Eh” ta amsa cikin sarƙewar murya. Hawaye masu zafi suka zubo mata ta rasa dalilin wannan tsana da Momy ta ke yi masu, da ta san yadda Mama ta tsani aurenta da Yaya Hafiz tun farko da ba ta ba kanta wahala wajan tunani da zargin Mama za ta yi wani abin domin Hafiz ba.

Ajiyar zuciya ta yi tare da share hawayen da su ka zubo mata ta juya ta cigaba da aikinta tana zancen zuci ‘son Yaya Hafiz abu ne da ba zai taɓa shafiwa a zuciyata ba, sai dai kuma hakan ba ya na nufin wai har yanzu ina da burin auren shi ba, har abada na barshi kamar yadda na bar cikin mahaifiyata ko da shi ne kaɗai ya yi saura a mazan duniyar nan’ ta yi murmushin takaici haɗi da zubar da hawaye ta na ci gaba da zancen zuci.

‘Haba sai ka ce ni ce sarkin mararsa zuciya ya ƙini ya so ƙawata sannan na kasa haƙura da shi sai ka ce an bawa kare zuciyata ya canye.!’

Zaune ya ke falo a ƙasan kafet laptop ce a gabansa ya na duba wa, Halima ta fito sanye cikin kayan bacci rigar ko cinyoyinta ba ta ƙarasa rufe wa ba, ta zauna dab da shi har jikinsu na gogan juna. “Ba ka sha lipton ɗin ba har ya fara hucewa” ajiye laptop ɗin ya yi ya na kallonta ya ce. “Ina wani bincike ne yanzu zan sha” janyo ta ya yi jikinsa ya na shafa fuskarta “kin ƙara kyau kin yi fis da ke meye sirrin” ta ɗora hannunta a kan hannunsa da ya ke fuskarta da murmushi a fuskarta,

“Kai ne sirrin Baby”

“Faɗa mini dai ko dai na yi ajiye a wajan nan ne” Ya faɗa ya na shafa ƙasan cikinta ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa tana dariya ƙasa-ƙasa “Kai ko”

“Ba wani kai ko kuman ki ya sauya kamar mace mai juna biyu”

“Ni ba wani juna biyu da na ke da shi.”

“Shi kenan ki ka ce dai na ƙara ba da himma kenan” ta fito da idanu ta na kai masa duka a ƙirjinsa rungumeta ya yi ya na dariya. “Albishirin ki” ta ɗago su na kallon juna ta ce. “Goro fari ƙal”

“Ki shirya ranar asabar jibi kenan za mu tafi mu gaida su Mama” Tsalle tayi ta rungume shi ta na ta murna sai kallonta ya ke ya na murmushi, can kuma ya ga ta tsaya cak fuskarta na nuna damuwa, “Ya dai me ya faru?”

“Ina tsoron haɗuwata da Mama ne har yanzu fa fushi ta ke da ni, ko na kira ba ta ɗaga kirana” riƙo hannayenta ya yi ya na mai karfafa mata gwauwa ya ce.

“Ki daina damuwa ina ji a jikina Insha’allah zuwan mu zai sa ta haƙura kin ji ko. Ko na sa Zhara ta shirya mu tafi tare sai ta taya mu ba ta haƙuri?”

Da sauri ta gyaɗa kanta ta na faɗin “A’a ba sai mun ɗauki wata ba, kawai mu tafi ba lallai sai da ita ba.”

Murmushi ya yi kawai a ransa ya na jinjina kishi irin na mata Zhara ba ta ji haushin ta ba sai ita da ta samu ta ke jin haushin ta.

“Shi kenan Allah ya kaimu. Idan mun dawo da sati ɗaya zuwa lokaci vizar ki ta fito za mu tafi Australia idan na gama abinda ya kai ne za mu tafi mu yi umura.” Fito da idanu ta yi farin ciki ya cika ta “Ina sonka Baby, wayyo daɗi” ta rungume shi tana kissing na shi.

Ta fito cikin shiri ta samu ba kowa falo ta haura sama duk su na bacci ba su tashi ba, hakan yasa ta sauko ƙasa ta samu Kande ta fito kichen ta ce. “Yawwa Aunty Kandala idan Momy ta fito ki faɗa mata na tafi makaranta.”

“Kin dai mayar da ni Kandala ko Maman masu gida, to shi kenan zan faɗa mata” ta na dariya ta ce. “Sunan bai yi daɗi ba ne.”

“Ai tun da a bakin ki ne daɗi rangaɗau” Zhara ta fice ta na dariya. Ta samu Dreba tare da mai gadi suna fira, “barkan ku da safiya”

“Yawwa mai babban suna an tashi lafiya”

“Lafiya lau. Malam Abba na fito mu je ka kai ni.”

Kasa ya yi da kansa cikin sanyin murya ya ce. “Ki yi haƙuri jiya da dare Khadija ta ce ƙarfe tara zan kaita makaranta kar na je ko ina na jira ta. Shi ne na ke faɗa mata kema za ki tafi ƙarfe takwas, Hajiya ta ce ba sai na kai ki ba” Murmushi ta yi “to shi kenan.”

“Ki yi haƙuri don Allah.”

“Haba kar ka damu ba komai.” Bayan fitar ta Abba ya yi ajiyar zuciya “wallahi sam ban ji daɗin hukuncin da su ka yi ba, ina jin nauyin Zhara ta na da kirki da girmama na gaba da ita ba kamar Khadija ba.”

“Kai kuwa ina za ka haɗa halin su, ita Zhara da Alhaji da Hafiz duk halinsu ɗaya wajan mutunta ɗan’adam. Amma ka ga Khadija da Hajiya sai dai kawai mutum ya yi shiru.”

“Allah dai ya kyauta kawai”

“Amin Ya Allah.”

Ta na tafiya kira ya shigo wayarta ta na duba wa ta ga Yaya Mahamod ne ta ɗan yi tsaki ‘ya fiya damuwa wallahi mtsw!’ gab da kiran zai tsinki ta ɗaga ajiyar zuciya ta ji ya yi kafin daga bisani ya ce.

“Har na fidda rai da za ki ɗaga.”

“Ayya zan ɗaga mana an tashi lafiya?”

“Lafiya lau. Fatan ki na lafiya.”

“Lafiya lau”

“Jiya mu na magana ki ka tsinki kiran, na kuma kira daga baya ba ki ɗaga ba me ya faru?”

“Momy ce ta kira ni shi yasa”

“Ok. Ki na hanya ne?”

“Eh zan je makaranta ne”

“To ba damuwa idan kin dawo sai mu yi magana.

Ƙarfe nawa za ki dawo dan na san lokacin da ya kamata na kira ki dan na san ko dawowa ki ka yi ba kira za ki yi ba” ta ɗanyi murmushi kafin ta ce.

“Haba dai zan kira mana” ya mayar mata da martanin murmushin ya na faɗin “ba wani nan ai nasan halin, faɗa mini yaushe za ki dawo?”

“Ƙarfe huɗu Insha’Allah”

“Allah ya kaimu. Ki kular mini da kan ki.”

“Amin na gode” ta tsinki kiran ta na tsaki a ranta.

Ta tsaya gefen hanya ta na duba agogon hannunta “oh Allah ka taimakeni na samu abin hawa har 7:30 ta yi” hon ta ji kamar zai kashe mata dodon kunnenta da sauri ta yi baya ta na mai kai idanunta wajan da ta ke jiyo hon ɗin, daidai sanda ya saukar da gilas su ka yi ido huɗu da shi murmushi su ka sakarwa juna, Hajiya Zhara ina zuwa da sassafen nan?”

“Wallahi makaranta zan tafi Yaya Anwar.”

“Ok shi go mu tafi.” Sun hau hanya ta ke gaishe shi bayan ya amsa ya ce. “Ya na ga kin fito neman abin hawa babu Dreba ne?”

“Eh an sa shi aiki ne kuma ina sauri kar na makara shi yasa” gyaɗa kansa kawai yayi, “yau shigowar safe a ka yi wa unguwar tamu.”

“Na kowa saƙo ne gidan Baffana da ya ke nan ƙasan ku. Kin zama ‘yar Kano ko” tana murmushi ta amsa masa da “ai kuwa dai karatu ya cillo mu garin Kano” ya karya kwana ya hau babban titi ya ɗan kalleta kafin daga bisani ya mayar da dubansa ga hanya ya na faɗin “ya ki ka ga garin da daɗi ko”

“Uhmm! To ba na ce ba, tunda ni daga gida sai makaranta ba in da na sani, ai ka ga ba na ƙaras da daɗin garin ba ko.”

“Ah laifin Hafiz ne da bai fito da ke ki ka ga ta dabo tumbin Giwa ko da me ka zo an fika.”

“Oh Allah ko fa kanawa a kwai koɗa kai, kar fa na zo na ga saɓanin hakan.”

“Haba ina babu wannan maganar, ai na tabbatar ke da kan ki sai kin tabbatar da Kanon mu ta wuce duk yadda a ke faɗar ta. Ranar da duk babu makaranta zan zo na kai ki ki ga gari.”

“To shi kenan Yaya Anwar sai mun fita sai na tabbatar.”

“Za kuwa ki sha kallo ko ƙasar waje albarka.” Su na tafe su na fira har su ka isa, su na zuwa ya karɓi numberta sannan su ka yi sallama.

Bayan isha ta na zaune gefen katifa tana duba littafi ta ji an mata tsaye a ka ta ɗago suka yi ido huɗu zuciyarta ta yi wata irin bugawa dum.!

<< Kuskuren Waye 14Kuskuren Waye? 16 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.