Skip to content
Part 20 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Zhara ta na haɗa kayanta a jaka Kande ta shigo ɗakin fuskarta da damuwa ta zaune ta na taya ta haɗa kayan “ya dai Aunty Kandala me ya ke damun ki ne?” Ta yi maganar ta na kallon Kande “uhm! Sai murna ki ke za ki tafi gida, ni kuma har na fara jin kewa shi kenan zan zauna ni kaɗai babu abokiyar fira” dariya ta yi ta na dafa kafaɗar ta “haba ke kuwa sai ka ce wacce ba za ta dawo ba. Sati ɗaya kawai Dady ya ba ni ba jima wa zan yi ba zan dawo, ki yi haƙuri” za ta yi magana Hafiz ya shigo ɗakin hakan ya sa ta yi shiru tare da miƙewa tsaye, Zhara ta yi saurin jan bargo ta rufe jikinta kasancewar fitowar ta wanka kenan tawol kaɗai ne a jikinta ta tsaya haɗa kayan ta sannan ta shirya ranta ya ɓaci sosai ta yi ƙasa da kanta.

“Ina kwana?”

“Lafiya lau Kande” ya amsa ya na janyo kujerar madubi ya zauna, bayan fitar Kande ya kalleta “kin kyauta kenan za ki tafi gida ba za ki faɗa mini ba sai dai na ji a bakin Anwar kenan ya fini a wajan ki ko?”

“Amma Yaya bai kamata ka shigo kai tsaye ba tare da ka neman izinin shigowa ba.”

“Tambayar da nake yi ma ki daban amsar da ki ke ba ni daban. Me ya sa ba ki faɗa mini za ki tafi ba?” Kawar da kanta ta yi gefe “ok na gane ki na ƙulacci da ni shi ya sa tun da ki ka zo sam babu ruwan ki da ni ba kya shiga sha’ani na wato bare ya fi ni matsayi a wajan ki sai dai komai da ya shafi ki na ji a wajan sa.”

“Sai kai ta ce wa na ƙullace ka da ka yi mini me zan ƙullace ka? Kai ne ka riƙi abin a ranka ni waccan lamarin tuni na manta da shi na ɗauki lamarin tamkar abun da ya faru a mafarki a na farkawa kuma ya wuce” miƙewa ya yi tsaye fuskarsa babu annuri ya ce. “na ji koma dai me ye ina ƙasa ina jiran ki idan kin shirya ni zan kai ki.”

“A’a na gode, tare da Yaya Anwar za mu tafi.”

“Na ce ni zan mayar da ke zan jira ki a ƙasa”

“Ko Dady fa ya sa ni har zai ce dreba ya kai ne na faɗa masa Yaya Anwar ya ce shi zai kai ne” a zuciye ya fincikota ƙiris ya rage tawol ɗin jikinta ya faɗi tayi saurin riƙiwa ta yi ƙasa da kanta idanunta na zubar da hawaye magana ya ke cikin tsawa “idan na sake jin sunan nan a bakin ki sai na cire ma ki haƙora! Zan jira ki a waje!” Ya ingiza ta ta faɗa kan gado ya juyo a zuciye su ka yi ido biyu da Momy da sam bai ji shigowar ta ba. Ya bi ta gefenta zai wuce ta dalla masa harara “uwar me ka ke yi a ɗakin nan!?” Shiru ya yi “oh ba ka da abin faɗa kenan?” Gyaɗa kanta ta yi ta nufi kan Zhara ta hau kanta da duka hakali tashi Hafiz ya je ya na ƙoƙarin riƙi Momy “wallahi Hafiz idan ka sake ka taɓani zan yi ma abin da ba ka tunani!”

Tsayawa ya yi cak “shi kenan ki yi haƙuri ki daina dukanta ba laifinta ba ne wallahi ba ta ma san zan shigo ɗakin ba.”

“Munafuka ki faɗa mini uwar me ki ka yi masa, wato lalata mini yaro za ki yi, ke ga ki tsohuwar kilaki da ga ke sai tawol a jiki kin kira shi ki nuna masa jikin ki tun da auren ya fi ƙarfin ki bari ki ba shi kan ki ba!” Kuka ta ke cikin ƙoƙarin kare dukan ta ce. “Abin da ki ke tunani ba hakan ba ne shi n… Marin da ta yi ma ta ne ya sa ta haɗiye sauran zancen tare da dafi kuncinta dan sosai marin ya shige ta ta sake kai mata wani marin da ya haifar mata da zubar jini ta hanci hankali tashe ya janye Zhara da ga riƙon da Momy ta yi mata ta koma bayan shi ta na kuka “ba daidai ba ne hakan sam ba daidai ba ne, ko wani irin hukunci za ki ni ya kamata ki yi wa ni ne na shigo ɗakin sannan Momy abin da ki ke tunani sam ba hakan ba ne magana ce kawai fa mu ka yi.”

“Ai ban san ba daidai na yi ba har sai idan ka zo ka rama mata dukan a sannan ne zan san ban yi daidai ba!!” Shiru ya yi ya na huci “maza ki tattara ina ki ina ki ki bar mini gida ai tunda na ga kunyi kucingwailar da ki ka dawo gidan nan da zama na san a kwai tsiyar da ku ka ƙulla ke da uwar ki, to ta Allah ba ta ku ba. Ban shirya karɓar jika a matsayin shige ba, dan haka zaman ki ya ƙare a gidan nan wallahi sai dai a bi wani sarkin wannan dai ya fi ƙarfin ku!’ ta nufi wajan gado “gidan uwar wa za ki je!?”

“Zan ɗauki rigata ne na sa” ta ba ta amsa ta na nuna kayan da ta fitar za ta sa a kan gado ” ingiza ƙiyarta ta yi zuwa waje “a hakan za ki tafi dama ba tallar jikin ki ki ke ba, tunda a nan ba ki yi kasuwa ba ba mamaki a hanya kya yi kasuwa”
“Don Allah ki yi haƙuri na sa kayana don Allah” ta yi maganar ciki da magiya “oh wasa ki ke ɗaukar maganar tawa kenan za kuwa ki tabbata” ganin da gaske Momy ta ke a hakan ta ke so Zhara ta fita ransa ya ɓace a zuciye ya fincikota da ga hannun Momy “ba in da za ta tafi a hakan dole ta suturta jikinta” marin shi ta yi ta na huce ta ce. “Ni ka ke faɗa wa magana Hafiz!” Ciwon duka da wannan cin zarafin da ta yi wa Zhara ya fi ƙona zuciyar shi a kan marin da ta yi masa hakan yasa bai ce da ita komai ba ya ja Zhara zuwa wajan gado ya ba ta kayan ta “ki yi haƙuri karɓi kisa” jikinta na rawa ta karɓa cikin tsoro tasa tare da ɗaukar hijab ɗinta, janyo jakarta ta yi ta bi ta gefen Momy da mamakin Hafiz yasa ta ƙame a wajan bin bayan Zhara ya yi sun kai ƙofa ya jiyo muryar Momy cikin tsawa ta na faɗin.

“Wallahi idan har ka ce za ka kaita gida ban yafe ma ka ba!!” Dukan su sun biyun su ka tsaya tare da juyowa su na kallonta “don Allah ki yi haƙuri ki barni na kaita.”

“Wallahi Hafiz in har ka kaita ba da yawo na ba ba zan taɓa yafe ma ka ba” numfashi ya ja ya furzar da ƙarfi kafin ya ce. “shi kenan amma ki barni mu je asibiti na dubata kin ga hancin ta sai jini ya ke zubar wa.”

“Hafiz za ka sa na tsine ma ka a kan maganar yarinyar nan wallahi Allah!!” Zhara ta buɗe ƙofa ta fita da gudu ta na kuka jingina jikinsa ya yi da ƙofa idanunsa sun yi ja sai numfashi ya ke fitar wa ciki da huce “ba ni hanya na wuce!” Janye wa ya yi ya tsaya da ga gefe har ta fita babu wanda ya yi magana.

Wayarsa ya ciro cikin aljihu ya kira wani abokin shi da gida ɗaya ne kawai ya raba su ya ba jin ya daga ya yi ajiyar zuciya “Muhusin ka na gida?”

“Eh ina gida ina shirin zan fita ne.”

“Don Allah Muhusin ka taimaka ka kuma yi mini alfarma ƙanwata Zhara ta na fitowa yanzu ka ɗauke ta ka kaita asibiti a duba ta. Idan har ba ka da wani uzuri don Allah ka kai mini ita gida. Idan kuma ka na da uzuri ko tasha ne kai kaita don Allah.”

“Kar ka damu Hafiz dama yau ban da aiki zan shiga gari ne zan kaita In Sha Allah.”

“Na gode sosai Allah ya bar zumunci”

“Amin kar ka damu.”

“Yawwa ka na ji ko na san ta da kafiya za ta iya ƙin yarda ta bi ka don Allah ka lallaɓata duk yadda za ka yi ta yarda ta bi ka.”

“In Sha Allah zan yi hakan” tsinki kiran ya yi ya fita ɗakin a falo ya same ta zaune ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya bi ta gabanta zai wuce ta kira shi ya dawo “zama za ka yi idan ka ga ka bar gidan nan dare ne ya yi na tabbatar zuwa lokacin ta bar garin” murmushin takaici ya yi kafin daga bisani ya ce. “Momy ni ɗa ne da nake fatan na gama da iyayena lafiya, tunda har ki ka ce kar na yi ba zan taɓa yi ba domin ko da wasa ba na fatan na yi abin da zai sa ki mini baki. Amma idan har ba ki yarda ba zan zauna ɗin”

“A sauka lafiya” ta yi maganar fuska a ɗaure. Komai bai ce da ita ba ya fice. Ƙasan Hijab tasa ta na goge jinin da ya ke hancinta babu ko sisi a hannunta sam ta manta da ƙaramar jakarta ba kuma za ta iya komawa ta ɗauko ba hakan ta nusa ta na tafiya ta na tunanin yadda za ta yi har wayarta ta na a kan madubi ta manta ta yi nisa sosai da gida ta jiyo hon a bayanta ta ta ɗan juyo ta kuma yi gaba abinta a ka saki danna mata hon da ƙoƙarin tsayar da motar kusa da ita hakan yasa ta tsaya saukar da gilas ɗin ya yi “Zhara shigo mu tafi.”

Girgiza kanta ta yi alamar a’a tare da yin gaba buɗe motar ya yi ya biyo bayanta “ki zo mu tafi Hafiz ne ya ce na zo na ɗauke ki.”

“Ka yi haƙuri Yaya Muhusin ni ba zan shiga ba”
“Me ya sa?”

“Hakan kawai” ta faɗa ta na tafiya ya biyo bayanta ya na faɗin “koma dai me ye ni ki mini alfarma ki zo mu tafi saboda darajar Manzon Allah (S.A.W)”
“(S.A.W) shi kenan mu je” karɓar kayan hannunta ya yi yasa a mota ta zagaya ta zauna gefen mai zaman banza ya zauna gefen dreba, bayan sun hau hanya ya ɗan kalleta “me ya same ki fuskarki ta yi haushi haka ga jini a hancin ki.”

“Na ɗan bugu ne” ta ba shi amsa a taƙaici “Allah ya tsare gaba. Bari na kira Hafiz na ji asibitin shi za mu tafi ko kuwa.”

“Kar ka kira shi ba asibitin da zan je ni gida kawai za ka kai ni.”

“Amma ya ce da ni mu je asibiti ga kuma fuskar ki ta nuna buƙatar zuwa asibitin.”

“Wallahi Yaya ba za ni asibiti ba idan kuma lallai sai mun tafi sai dai na sauka motar nan.”

“Shi kenan Allah ya sawwaƙa” ‘dole a kwai abin da ya ke faruwa sai dai faɗan cikin gida ba na tsananta bincike ba’ ya yi maganar a zuciyar shi ya na kunna rediyo. Hafiz da ya tsayar da motar shi nesa da su ya na kallon badaƙalar da su ke kafin ta yarda ta shiga sai da ya ga tashin motar su sannan ya juya zuwa gidan shi.

Ya na zuwa gida ya kwanta a falo Halima ta fito ɗaki ta same shi kwance a kan kujera idanun shi a rufe ‘to me kuma ya dawo da shi da ga fitar shi?’ ƙara sawa ta yi gaban shi ta tsaya ta na faɗin “Baby mantuwa ka yi ne na ga ba ka jima da fita ba ka dawo” buɗe idanunsa ya yi da su ka yi ja sosai ya na faɗin “ba na jin daɗi ne.”

“Ayya sannu me ya ke damun ka” miƙewa ya yi tsaye ya na faɗin “ni kaina ban sa ni ba” ɗakin shi ya tafi ta taɓi baki “dama a na ciwo ne ba tare da an san ina ne ya ke ciwo ba” zama ta yi a in da ya tashi ta na chat.

Su na isa a na sallah la’asar ta na fitowa mota Hassana da dawowarta kenan da ga aika ta rugu da gudu “oyoyo Aunty Zhara” rungome ta ta yi fuskarta ciki da murmushi “Hassana kin ƙara girma me Mama ta ke ba ki ne haka. Ina Hassaini?”

“Ya na gidan Kawo Habibu” ta ba ta amsa ta na dariya, kallon Muhusin ta yi da ya fito motar ya na miƙa “mu je da alama ma Abba na nan naga ɗakin shi a buɗe.”

“Ya na nan bai jima da dawowa ba. Ina wuni.”

“Lafiya lau ‘yan biyu kyautar Allah” dukan su suka yi murmushi ɗakin Abba su ka nufa ya na duba littafi ya jiyo muryar ta ta na sallama “kamar muryar Mamana nake ji.”

“Ni ce Abba” ta faɗa su na ƙarasa shiga da fara’a ya tarbe su. Bayan sun gaisa ta shiga ciki tabar shi su na gaisa wa da Muhusin. Mama ta fito kichen su ka yi ido huɗu da juna ta yi turus fuskarta ciki da mamaki “Zhara” rungume ta Zhara ta yi ta fashe da kuka “mene ne kuma abin kuka ko duk farin cikin ne?” Ta yi maganar ta na ɗago fuskarta zuba mata idanu ta yi “shacin hannu nake gani a fuskarki ga busasshen jini a hancin ki me ya faru?” Shige wa ta yi jikin Mama ta na ƙara fashewa da kuka Abba ya shigo ya na faɗin “a ba Hassana abinci ta kaiwa baƙo na ce ya bari sai gobe ya tafi ya kafe yau za… Shiru ya yi ya na kallon su “me ya faru kuma?”

“Ni ma tambayar da nake kenan Abban su.”

“Uhm! A kai masa abincin ko meye ma yi maganar da ga baya.”

“To” ta yi maganar jiki a sanyaye tare da janye Zhara da ga jikinta “ki je ki yi sallah ki ci abinci” kai kawai ta gyaɗa.

Da dare su na zaune a falo Mama ta sa ta gaba da faɗa “tun da ki ka zo sai kuka ki ke kin ƙi cin abinci ki faɗi abin da a ka yi kuma kin ƙi” Abba ya shigo ya zauna gefen Zhara ya na faɗin “Mamana ki yi haƙuri Hafiz ya kira ya na ba da haƙuri ya faɗa mini duk abin da ya faru” ɗora kanta ta yi jikin Abba ta na zubar da hawaye ta ce. “Abba ba dukan ne ya ke ƙona mini rai da saka ni kuka ba cewa fa ta yi da ni wai ni kilaki ce sannan na gama zaman gidan dan ba za ta shirya ɗaukar shige a matsayin jika ba.”

“Wai me ya faru ne kun bar ni a duhu” cikin kuka ta yi wa Mama bayanin komai shiru Mama ta yi ta na huce shi kan shi Abba shiru ya yi kasancewar ba komai Hafiz ya faɗa masa ba “na gaji da yin shiru Abban su dama kai ne ka ke hanani magana sannan zuwan ta gidan ma fin ƙarfi na ka yi shi ya sa kawai na yi shiru. Yanzu kam tura ta kai bango Zhara har abada ba ita ba gidan Turai kuma wallahi sai an bi mata haƙkin ta a kan dukan da ta yi ma ta ai ba jaka na haifa mata ba da za ta yi mata duka irin haka bayan nan kuma har da ƙage da sharri.”

“Koma dai me ye ya riga da ya faru kuma ba ta kyauta ba amma hakan ba zai sa a biye mata ba gida ba na ta ba ne hukuncin ta na banza ne idan har Yaya ya buƙaci Zhara ta koma tabbas za ta koma” zuba masa idanu dukan su ka yi cin ɓacin rai ta ce. “kenan ka ba ta damar ci gaba da ci mata mutunci da ƙagi to ni wallahi ba zan yarda ba” miƙewa ya yi tsaye ya na faɗin “shi cin mutuncin ko ƙagin zai manne ne a jikinta? Sannan ke ko ita Turai wa ya isa ya yanki zumunci na da Yayana ko raba kan ‘ya’yan mu?”

Kai duban sa ya yi ga Zhara “ki na ji ko Mamana ko me za ta yi ma ki ki zama mai kawar da kai uwa ce a gare ki, sannan ko da zaman ki a gidan a yanzu na ce eh ba za ki zauna ba a gaba ai ba zan hana ba tunda ƙaddarar ki a cikin tsatsunta ta ke.”

“Me ka ke nufi da hakan?” Ta yi tambayar cikin mamaki da tsoro. “Hafiz ya zo har nan ya na ba da haƙuri tare da neman yardar na sake ba shi auren Zhara.”

“Ka ce masa me?”


“Me ki ke tunanin zan ce da shi bayan na yarda ko zan ƙi shi ne na bai wa bare? Maganar Anwar ki ma cire shi a ran ki Hafiz ne mijin ki” numfashin ta ne ya dinga yin sama Mama ta miƙe a zuciye ta ce. “Wace irin zuciya ce ne da kai? Ka manta tozarcin da ya yi mana ne? A na gobe ɗauren aure kowa ya taru ya fasa aurenta ya ce ƙawarta aminiyarta ce zaɓin shi a fasa da ita a ba shi zaɓin shi shi ne yanzu saboda bai da ta ido ya kuma mayar damu binan ka tafi zai zo mana da zancen banza har ka goya masa baya. To wallahi in dai ina raye ba zan taɓa yarda da wannan auren ba!”

“Ke ce dai ki ka manta Hafiz bai fasa aurenta ba bai kuma taɓa furta kalmar ƙi a gare ta ba ita ce da kanta ta rusa komai sannan duk abin da ya faru a sanadin KUSKUREN TA NE ko me ya faru. Dan haka aure da Hafiz babu fashi”

“To wallahi ba zan yarda da wannan auren ba in dai ina raye Zhara ba za taɓa auren sa ba haba sai ka ce wacce ta rasa mijin aure ai wannan neman sayar mata da mutunci ne ka ke da sa Turai ta ji a ranta lallai nace wa ɗan na ta a ka yi kamar yadda ta ke faɗa.”

“Sai na ga ni idan ke ce za ki ba da auren na ta ai.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 19Kuskuren Waye? 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×