Skip to content
Part 21 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Tun bayan da Abba ya fita Mama ta sa Zhara gaba da faɗa “wallahi cire Hafiz a ranki shi ne alkhairi a gare ki idan kuma kika yarda kika biye zuciyar ki da mahaifin ki za ki kai kanki ki baro ne, dan daga shi har uwar ta shi za ki nuna masu kin rasa mai so shi yasa kika nace masa.”

“Mama ki daina ganin laifina ni ai bance auren sa zan yi ba” ta yi maganar cikin kuka, kallonta Mama tayi tana faɗin ai gara na faɗa maki Allah na tuba idan ni ce ke wallahi Hafiz ko autan maza ne shi na barshi har abada, ƙarshen wulaƙanci ya wuce wanda aka sa ranar auren ka da shi ya kewaya ta bayan gida yana cin amanar ki da ƙawar da kika ɗauka tamkar ‘yar-uwa, har a zo gaɓar da za a ɗaura aure ya nuna wa duniya ita ce zaɓin shi ba ke ba. Wallahi kiyi wa kanki faɗa idan kuma zaki biye wa mahaifin ki ne ga mai fili ga mai doki duk abin da ya biyo baya babu ruwana ba hannuna a ciki” shiru Zhara ta yi tasa kai tsakankanin cinyoyinta tana ci gaba da kuka, wani irin abu mai nauyi taji ya tokare mata zuciya ta rasa wani irin kalar tunani za ta yi. Mama ta watsa mata wani kallo ta fice ta barta zaune a wajan tamkar andasa bisshiya.

Da dare tana kwance bacci ya ƙauracewa idanunta sai saƙa da warwara take ta rasa zaren kamawa, ayadda tasan mahaifinta kaifi ɗaya ne baya sauya maganarsa idan ya ce eh tabbas eh din idan ya ce a’a to fa a’a ne, duk da har yau har kuma gobe ba ta tunanin za ta daina son Hafiz kamar yadda take da tabbacin duk wanda za ta aure gangar jikinta ne zai kasance a tare da shi amma zuciyar ta tuni ta binneta a wajan Hafiz, amma hakan ba zai sa tayi farin ciki da hukuncin Abba ba, ba kuma ta fatan tabbatuwar al’amarin domin ta haƙura da Hafiz kamar yadda ɗa idan ya fito cikin mahaifiyar sa ya fito ba komawa to hakan take ji aranta tabar Hafiz. Kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da take kai hannunta tayi ƙasan filo ta lalubo wayar

An ɓoye number hakan yasa ta mayar da wayar ta ajiye har kiran ya tsinki aka sake kira kamar ba za ta ɗaga ba gab da kiran zai tsinki ta ɗaga,

“Hello” ajiyar zuciya taji anyi an kuma yi shiru “idan ba za a yi magana ba zan kashe”

“Ya kika isa gida?” Lumshi idanunta tayi tayi shiru ta kasa motsin kirki tana sauraren yadda bugun zuciyarta ya sauya, “Zhara ba za ki mun magana ba? Na san kina saurare na, ina mai ƙara ba ki haƙuri da abinda ya faru ɗazun”

“Komai ya wuce, Sai anjima” da sauri ya ce. “Kar ki kashe mini waya”

“Ina ce ka riga ka faɗi abin da ka kira ka faɗa ko”

“Humm ba wannan dalilin kaɗai ne yasa ni kiran ki ba, dalilan suna da yawa, sai dai maganar ba za ta yu a waya ba ki jirani gobe karki tafi ko ina zan zo” yamutsa fuska tayi kamar yana gabanta ta ce. “Kar ma kayi wahalar zuwa dan ba ganina za ka yi ba”

“Ni dai ina mai umartar ki da ki jirani zan zo”

“Sannu Babana” ta yi maganar cikin gatsali, zai yi magana ta tsinki kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya ta gyara kwanciyarta idanunta suna zubar da hawaye masu ɗumi “tabbas idan har nayi wasa zan kasa tanƙwasa zuciyata wanda kuma sam ba zan so hakan ba.” Ganin tunani na shirin tarwatsa ƙwaƙwalwarta yasa ta mike ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala tana fitowa ta fara nafila.

“Zhara wannan bacci haka ko ba ki da lafiya ne?” Mama tayi maganar tana shiga ɗakin ta samu har yanzu tana kwance, ƙarasawa ta yi tana tashin ta “Zhara wani irin bacci ne haka goma har ta wuce” buɗe idanunta tayi tana miƙa cikin muryar bacci ta ce. “Lafiya lau Mama bacci ne kawai”

“To ki tashi ki yi wanka in kin shirya ki ɗora girkin rana zan je unguwa” tana miƙa ta tashi zaune tana faɗin “ina za ki tafi?”

“Gidan Yaya Fati, don Allah ki ɗaura girkin da wuri kar su Hasan su dawo babu abinci”

“To Mama yanzu zan tashi.” Bayan fitar Mama ta tashi har ta cire riga maganar Hafiz ta dawo mata a kunne kamar yanzu yake faɗa mata da sauri ta mayar da rigar ta fito ɗaki ta samu Mama har ta fito tana sa Hijab “Mama jiya Yaya Hafiz ya kira ni a waya” turus Mama ta yi idanunta a kan Zhara “ya ce ma ki me?” Shiru tayi “tambayar ki fa nake me ya faɗa maki?”

“Wai zai zo yau” ta yi maganar tana riƙi ƙarfin barandan ƙofar ɗakin “Humm ke kuma wace amsar kika ba shi?”

“Na ce masa kar ma ya zo dan ba zai ganni ba shi ne ya ce sai ya zo” cire hijab din Mama tayi tana faɗin “ni na ma fasa fitar zo ki shirya maza ki bar gidan nan, na fahimci so yake ya mayar da ke tamkar hular kansa ya sa ki a sanda ya so ya cire ki a sanda ya so.”

“Ina kuma zan tafi Mama?” Ta yi tambayar fuskanta ciki da mamaki “gidan ƙanin ubanki za ki tafi!”

“Kiyi haƙuri”

“Matsw! Ki shirya ki tafi gidan Yaya Fatin zan kira ta a waya”

“To” ta bata amsa tana juyawa zuwa ɗaki. Mama ta azalzaleta ta shirya bayan ta shirya ta karɓe wayarta, ba ta samu natsuwa ba har sai da taga Zhara ta bar gidan ta koma ta zauna tana ajiyar zuciya “ai wallahi ya riga da ya yi wasa da damar sa dama can ba son haɗin nake yi ba, tunda har ya bari wancan damar ta suɓuce masa ko ana ha maza ha mata ba zan taɓa bari ayi wannan auren ba.”

Tsaye yake gaban madubi yana fesa turare Halima ta shigo ɗakin kallon sa tayi zuciyata ta ji tana bugawa “wannan kwalliya haka kamar wanda zai je wajan gasar kyau” juyowa ya yi da murmushi a fuskar shi ya ce. “Haba gasar kyau sai kace wani mace”

“Maza ma ai suna yi gasu muna gani” taku ya yi zuwa wajan da take ya riƙo kafaɗunta fuskarsa yalwaci da murmushi ya ce. “su ɗin ma ai rashin abin yi ne, dama kwalliyar taki ce tunda kin yaba kinga sai na ce kwalliya ta biya kuɗin sabulu ko” ta masa fari da idanu tana faɗin “wai da gaske kake, kenan yau ba fita office”

“Uhmm akwai fita gaskiya amma ba jimawa zan yi ba ina dawowa zan zauna ba sake fita” ɓata fuska ta yi cikin shagwaɓa ta ce. “Gaskiya a’a ni fa haka kawai jikina yake bani wani abu”

“Me jikin naki yake baki?”

Sanya idanunta ta yi cikin nashi “kamar wajan wata za ka tafi hakan nake ji” kawar da idanun shi ya yi daga nata yana murmushi a ranshi yana faɗin ‘kai mata abun tsoro ne wallahi’ barin wajan ya yi ya je wajan takalmi yana sakawa a ƙafarsa ya ce. “Wannan tunanin ki ne kawai”

“Humm shi kenan na yarda, za ka je gidan Momy?” Ya na gyaɗa kai “a’a na makara sai dai ko bayan na dawo wataƙila na biya” har cikin ranta ta ji daɗin hakan ko ba komai dai ba zai ga Zhara ba. Cikin farin ciki ta raka shi har mota sai bayan da motar ta bar gidan sannan ta juya zuwa cikin gida.

Mama da Hasana suna zaune tsakar gida suna cin abinci “Hasana idan kin gama cin abincin ki tafi ki kira Husaini na san halin shi idan ya je gidan su Najib ba son rabuwa suke ba sun fi so suyi ta yawon unguwa tare”

“To Mama, amma kin san halin shi idan na matsa masa tsab zai hargaguni”

“Wani lokacin ai har da laifin ki kina faɗa masa ki yi tahowar ki ba sai kin tsaya kin ce sai kin sa shi gaba kun zo ba” za tayi magana a ka ƙwalla sallama “ko Abba ne ya yi baƙo?” Hasana tayi maganar tana kallon Mama, ko ba a faɗa ba tasan Hafiz ne dan ga muryar nan “salamu alaikum”

“Ji ki duba kiga waye” da sauri ta tsame hannunta daga cikin abinci ta nufi suron da gudu “wai yaushe za kiyi hankali ne na hanaki gudun nan ba za ki daina ba!” Ta yi tsaki tare da miƙewa tsaye wajan famfo taje tana wanki hannu Hafiz ya shigo yana riƙi da hannun Hasana, “ina Husaini?”

“Muna dawowa makaranta ya bi abokin shi Najib” ya gyaɗa kai Mama ta juyo da fara’a a fuskarta “maraba da Hafiz wai dama kai ne ka wani tsaya daga waje kamar wani baƙo” key ɗin mota yasa yana susa sumar kan shi ya ce. “A yi haƙuri”

“Haba kai kuwa kai da gidan ku ka tsaya kana sallama a waje. Ƙarasa ɗaki kayi tsaye” ciri takalmin shi ya yi ya hau tabarma yana faɗin “ai nan ɗin ma ya yi .”

“Ina wuni Mama?”

“Lafiya lau Hafiz an zo lafiya, ya mutan gida?”

“Duk suna nan lafiya lau sun ce a gaishe ku” wajan firij ta nufa tana faɗin “madallah muna amsawa.” Ruwan leda ta kawo masa, bayan ta ajiye masa ta je ta kawo masa abinci shinkafa da miyar kefe. Cin abincin yake amma hankalin shi yana kan ɗakin Zhara Mama na kuli da shi ta yi kamar ba ta san me yake ba, sai jan shi da fira take har ya gama cin abinci bai jiyo motsinta ba, wayarsa ya ɗauka ya kira kamar dai sanda yana Kano da ya kira wayar a kashe ajiyar zuciya ya yi ya kai duban sa ga Mama “munyi waya da Abba ya ce ya tafi wajan ɗauren aure”

“Hakan ne amma na san ba jimawa zai dawo in sha Allah”

“Hakan ya ce mun. Ina Husaini ne?”

“Ya fita yanzu nake cewa ma Hasana ta kira shi ganin ka yasa ta yi zamanta. Maza ki je ki kira shi” Hasana na fita ya miƙe tsaye yana faɗin “Mama zan ɗan fita waje kafin Abba ya dawo”

“To shi kenan falon nasa ma a buɗe yake” gyaɗa kansa kawai ya yi tare da miƙewa tsaye ya fita da sauri yana addu’ar Allah yasa ya samu Hasana ba ta tafi ba sai dai kash ta riga da ta tafi, haka ya tsaya gefen motar shi ransa babu daɗi tabbas ya sani saboda shi ne ta kashe wayarta. Yana tsaye a gindin motar yana duban hanya Hasana da Husaini suka dawo cikin sauri ya ƙwalla masu kira da fara’a suka ƙaraso wajan shi “Yaya yaushe ka zo?”

“Na jima da zuwa kana wajan yawo wajan abokai kai ba ka zaman gida ko?”

“A’a” ya yi maganar yana sussuni kai. “Zhara na nan kuwa?” Cikin gyaɗa kai Hasana ta ce. “A’a ta fita unguwa” shiru ya yi kamar mai wani nazari kafin daga bisani ya ce. “Kun san inda ta tafi?”

“Uhm-um mu ma ko da muka dawo makaranta ba mu tarar da ita ba, sai da na tambayi Mama take faɗa mana bata nan”

“Shi kenan kuje” ya yi maganar fuskar shi a haɗe bayan tafiyar su ya ja numfashi ya furzar “wato duk abin da zan yi na yi sai da yarinyar nan ta fita duk da na ce ta jirani har da wani kashe waya!” Ya bude mota a zuciye har ya shiga sai ga Abba ya dawo a kan mashin sam bai kula ba yana tayar da motar ya jiyo muryar Abba “a’a kar dai tafiya za ka yi Hafiz” da sauri ya juyo cikin inda inda ya ce “a’a Abba da zan ɗan fita ne da naji shiru baka dawo ba” ya ƙarasa maganar yana mai fitowa daga cikin motar. “Na haɗu da wani abokina Alhaji Isa ne a wajan ɗaurin auren muka tsaya magana da yake anjima ba a haɗu ba, shi yasa na ɗan jima”

“Allah Sarki, sannu da dawowa”

“Yawwa mu shiga daga ciki.” Bin bayan shi ya yi zuwa cikin falo bayan sun zauna suka gaisa tare da tambayar mutan gida, Abba ya miƙe yana faɗin “bari a kawo mana abinci”

“Ina zuwa naci abinci, wuce wa ma zan yi tunda mun gaisa”

“Tun yanzu ai na ɗauka za ka kwana ne” yana murmushi “Abba ina da aiki na ce ne dai bari na zo ko kai tsaye ne a gaisa”

“Ai ka kyauta Allah ya yi albarka”

“Amin Abba” ya amsa cikin ladabi. “Kun gaisa da Zhara?” Yana gyaɗa kai ya ce. “a’a an ce ta fita unguwa”

“Unguwa kuma? Kun yi magana da ita kuma kafin kazo?”

“Eh to jiya dai da dare na kira na faɗa mata zan zo, yau da safe kuma bayan na tasu na ta kiran wayarta a kashe” ina zuwa jirani” ya yi maganar tare da ficewa daga falon, gyara zamansa ya yi yana addu’ar Allah yasa zai ganta ɗin Allah ya gani a ɗokanci ya zo da muradin ganinta.” Zaune ya samu Mama ɗaki ita da Hasana suna linkin tufafin su Husaini na cin abinci, cikin farin ciki ‘yan biyun suka rungume shi “sannu da zuwa Abba”

“Yawwa sannu ku an dawo makaranta” gyaɗa masa kai kawai suka yi, yana shafa kansu ya ce su tafi ɗakin su zai yi magana da Mamansu bayan fitar su ya tsaya a gabanta idanun shi a kanta ya ce. “Ina Zhara?” Irin kallon da yake mata ƙwarai ya faɗar mata da gaba sai dai tasa a ranta za ta dake ko ma meye ba za ta taɓa faɗar inda Zhara ta tafi ba, “ina tambayar ki kin mini shiru ina Zhara?”

“Ta fita” ta bashi amsa a taƙaici tana ci gaba da linkin kayan. “Na sani ai ta fita ina ta je nake tambaya”

“Nima ban san ina ta je ba kawai dai ta faɗa mini za ta fita” zuba mata idanu ya yi ransa a matuƙar ɓaci ya ce. “Ba gaskiya ba ne kina sani da inda ta je kuma ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba kina sane kika tura ta wani wajan” ajiye rigar hannunta ta yi tana faɗin “wannan zargin ka ne kawai ni ina zan turata kuma akan wani dalili ma da zan turata wani wajan”

“Saboda kin san Hafiz zai zo, sannan kin tambaye ni unguwa me yasa ba ki tafi ba ita ta tafi? Maryam kina ɗaukar maganar Hafiz da Zhara wasa ko, wallahi idan kika yi wasa akan maganar nan zan iya rabuwa da ke! Kallon sa take da tsananin mamaki a fuskarta “rabuwa fa ka ce Abban su?”

“Ƙwarai da gaske, ya zan yanki hukunci akan ‘yata ki nemi ki nuna ban isa da ita ba! Na ba ki minti goma duk inda kika tura mini yarinya ki dawo da ita idan ba hakan ba wallahi hukuncin da zai biyu baya ba zai yi maki kyau ba!!” Zuba masa idanu ta yi tana kallon sa da matuƙar kaɗuwa…

KARKU MANTA A DINGA DANNA MANA TAURARO DA COMMENT, DA KUMA SHIYARIN. NA GODE

Fulani

<< Kuskuren Waye? 20Kuskuren Waye? 22 >>

3 thoughts on “Kuskuren Waye? 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.