Skip to content
Part 23 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Da ihun murna Kande ta rungume ta tana faɗin “Zhara sannu da hanya, kar ki ji irin daɗin da na ji da ganin ki.”

“Aunty Kandala nima hakan ya gidan?”

“Lafiya lau, ya su Mama da ‘yan biyu?”

“Duk suna nan lafiya, sun ce a gaishe ki. Bari na gaida Momy na dawo” jan jakar kayan Zhara tayi tana faɗin “ai ba sa nan yau ni kaɗai ce a gidan” har cikin ranta ta ji daɗin hakan ji take kamar kar ma su dawo dan Allah ya gani a matuƙar tsoraci take. Haurawa ta yi sama Kande na bayanta. Bayan ta a jiye jakar ta juya dan kawo mata abinci Zhara da ta fara cire kaya ta ce. “Aunty Kandala tare mu ki da Abba don Allah haɗa mini abinci kayan nan da suka ishi ne kawai zan cire na zo na kai masa.”

“Allah sarki ashe tare ku ka zo bari to na yi sauri na kai masa daga nan ma sai mu gaisa.”

“Humm to shi kenan yana ɗakin baƙi” kanta kawai ta gyaɗa ta fice da sauri. Wanka Zhara ta shiga dan a gajiye take jinta.

Ta na fesa turare Hafiz ya shigo ɗakin kallon sa ta yi fuska a haɗe ‘yanzu da ba dan Allah ya taimake ni na riga da nasa kaya ba da hakan zai tarar da ni babu sitirar arziƙi, dole ma na yi masa tufka dan na ga alamar shi ɗin ba tunani ne da shi ba.’ ta yi maganar a zuciyarta tana mai janyewa gaban madubi zuwa ta yi ta ɗauki Hijab da darduma Hafiz da ya jingina gefen kafaɗar sa da ƙofa hannunsa rungumi a ƙirjinsa idanunsa na a kanta, ganin ta masa shiru hakan yasa ya bar jikin ƙofar gabanta ya je ya tsaya “ba ki yi farin ciki da ganina ba ne na ga duk kin wani haɗe fuska kamar hadarin da ya haɗi gabas?” Kawar da kanta ta yi gefe “ni gaskiya ba na son abin da ka ke yi mini.”

“To me kuma na yi ma ki daga zuwa na?” Ya yi mata tambayar yana mai kafe ta da idanu “dan me za ka ding shigo mini ɗaki kamar ɗakin ka ko na matar ka, gaskiya hakan ba daidai ba ne.” a Dariya ya yi marar sauti ya koma kan gado ya zauna yana shafa shimfidar gadon “to ai kin riga da kin ba kan ki amsa ɗakin matata ne dan na shigo a sanda na so ba zai zama laifi ba bare har a tuhumi ni kamar ina kuto” murguɗa masa baki ta yi “matar ka na in da ka a jiye ta wannan ɗin ta dai mai rabo ce” ta yi maganar cikin-ciki.

“Me ki ka ce?”

“Sallah zanyi” cikin ɗaga kafaɗa ya ce. “Ki yi sallah ina jiran ki.”

“To ka tafiyar ka mana.”

“Ni na kawo kaina dan haka zan fita a sanda ni na so ba sanda wai a ka umurce ni da na tafi ba” magana take kamar za ta yi kuka “amma dai Yaya Hafiz kasan idan har Momy ta dawo ta tarar da kai ɗakin nan komai ma zai iya faruwa ko?” Janyo filo ya yi ya kwanta rairan idanunsa a lumshi “Momy ba ta nan dan haka ki yi sallar ki a natsi lokaci na tafiya” ba yadda ta iya dan taga alamar maganar yake ji kuma ko me za ta yi ba fitar zai yi ba, kawai ta fuskanci gabas ta kabbarta sallah.

Bayan ta idar da sallah ta kai duban ta ga gadon har yanzu idanunsa a rufe suki hakan yasa kawai ta yi tunanin ta gudu ta bar masa ɗakin. Tashi ta yi cikin sanɗa za ta tafi kawai taji an harɗe ƙafafunta ta yi taga-taga za ta faɗi kai hannunsa ya yi cikin azama ta faɗo ƙirjin shi juyar da ita ya yi ta kwanta a kan gadon ya yi mata rumfa da ƙirjin shi kai bakin shi ya yi saitin bakinta lumshi idanunta ta yi wani irin tsoro ta ji da har yasa numfashinta fita sama-sama zuciyarta ta dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!! Janye bakinsa ya yi daga wajan bakinta ya kai saitin kunnenta yana yi mata magana cikin raɗa “wai da kina tunanin za ki guje mini ne?”

Da ƙyar ta iya tattaro ɗan ƙarfin da take ji tana da ta yunkura dan ta ture shi sai dai ko gizo bai yi ba ganin ta kasa kawai ta koma ta yi laƙwas tana yi masa magiya “Don Allah Yaya ka ɗaga ni kar wani ya shigo ya same mu a hakan” ta ƙarasa maganar kamar za ta yi kuka “matsoraciya kawai na ji zan ɗaga ki amma ki yi mini alƙawarin duk abin da na ce kiyi za ki yi babu musu, kin yarda?” Gyaɗa kanta ta yi cikin sauri alamar ta amince “magana za ki yi tunda dai ba da kurma ki ke magana ba.”

“Eh eh na aminci” mirgina wa ya yi gefe ta tashi da sauri tana mai saukar da ajiyar zuciya ta koma kan kujerar madubi ta zauna tana mayar da numfashi idanunsa alumshi ya ce. “Ki dawo nan ki zauna babu abin da zan ma ki” babu yadda ta iya hakan ta ta so ta zauna gefen sa da ya nuna mata shiru ya yi bai ce da ita komai ba kamar ma ya manta da zaman ta a wajan hakan ya ba ta haushi kamar ta tashi ta yi tafiyarta sai dai kuma tsoron abin da ya faru ɗazun kar ya sake faruwa yasa dole ta haƙura ta ci gaba da zaman.

“Zhara” Kallon gefen da ya ke ta yi da har yanzu a kwance ya ke kuma idanunsa suna nan a yadda suke a lumshin su, “Zhara.”

“Na’am”

“Alfarma nake nema a wajan ki don Allah ki taimake ni kar ki ce za ki yi facali da ita”

“Uhm! Ina jin ka”

Tashi ya yi ya zauna sai dai ya ƙi yarda su haɗa idanu ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “Zhara ina roƙon ki da ki manta da komai da ya faru a baya don Allah.

Sannan kamar yadda na sha faɗa ma ki ban taɓa tsayawa gaban ki na ce ba na sonki ba, hakan kuma har a cikin zuciyata babu ƙiyayyar ki. Kawai na sani KUSKURE NA ɗaya ne da na so ƙawar ki bayan kuma a kwai maganar ki a kaina, wanda idan a ka duba faruwar al’amarin ta wata sigar KUSKUREN ki ne Zhara domin da ba ki bata numbar ta ba da ba ki ba ta damar ta nemi soyayyata ba da ban santa ba da abin da ya faru bai faru ba.”

“Humm ka ga kenan da son rai a ciki dan na ba Halima number ka ai ba shi ne zai ba ka damar cewa kana son na ta ba har ka zaɓe ta sama da ni, dama can da hakan a ranka shi yasa tana zuwa kawai ka karɓe ta a matsayin zaɓin zuciyar ka, dan haka kama daina ganin laifina ko cewa KUSKURE NA ne.”

“To amma da ba ki haɗa mu ba zan san ta ne, sannan sanda na fara son Halima ban san alaƙar da take tsakanin ku da ita ba har sai da sonta ya yi nisa a zuciyata da ba zan iya haƙura da ita ba.” miƙewa ta yi tsaye zuciyarta na dukan uku-uku wani irin azababbin kishi ta ji da har ta kasa ɓoye wa “to sannu romiyu ko sharukan baban soyayya, to dama na ce ne ka haƙura da ita ne da za ka wani zo kana faɗa mini ba za ka iya haƙura da ita ba. Ku je can ku ƙarata ni meye ruwana a ciki me ya shafe ni!”

Juyawa ta yi za ta tafi ya riƙo hannunta fuskar shi ciki da murmushi ya juyo da ita suna kallon juna “kishi nake gani a cikin idanun ki.”

“Kishi a kan me zan yi kishin ka? Ka ma daina wannan tunanin kishi na yana a kan zaɓin zuciyata ba dai kai ba” murmushin da ya ke fuskar sa ya kau ya zaunar da ita gefen shi “idan mu na magana ki daina kawo mini zancen wani, ki kuma yi haƙuri idan har zancen da na yi ya ɓata ma ki rai” shiru ta masa haɗe da kawar da kanta gefe.

Zamewa ya yi daga kan gadon ya durƙusa gabanta yana kallonta da idanunsa da suka yi ja “ki yi haƙuri ba zan sake ba ki manta komai. Na yi wa Dady maganar ki faɗa ya yi sosai na faɗa masa ai da yardar ki na zo na masa mag… Da sauri ta kalle shi “haba Yaya Hafiz ya za ka mini hakan ni yaushe muka yi hakan da kai?”

“Ki yi haƙuri yadda naga Dady ya ɗauki maganar da zafi ne har yana ƙoƙarin fatattaka ta hakan yasa ban da wata mafita da ta wuce na faɗa masa hakan.”

“Gaskiya ni ba ka kyauta mini ba ba kuma ka yi mini adalci ba kawai zan je na faɗa masa gaskiyar ni ban san komai ba” riƙo hannayenta ya yi kamar zai yi kuka ya ce. “Kar ki mini hakan don Allah wai kuwa kin san girman son ki da ya ke cikin zuciyata? Ki bani dama karo na biyu zan gyara KUSKURE na don Allah. Kuma Dady ya ce zai kira ki ya tambaye ki ina roƙon ki dan son Annabi kar ki ce masa a’a don Allah” ya harɗe hannayen sa yana yi mata magiya, hakan sai ya karyar mata da zuciya can kuma ta tuna lokacin da ta gan shi gaban Halima yana yi mata kwantan-kwacin irin wannan magiyar gaba ɗaya sai ta ji ya ba ta haushi wato su dai maza munafukai ne idan sun zo gaban ka suna faɗar kalamai sai ka ji kamar babu yi kamar ka. “Kin yi shiru, don Allah kar ki ce a’a don Allah Zhara.”

Ta buɗe baki za ta yi magana kawai Momy ta faɗo ɗakin firgice ta miƙe tsaye jikinta ya fara kirma kallon Momy take zuciyarta na dukan uku-uku shi kuma ko a jikin shi yana a yadda ya ke sai juyo wa ya yi suna kallon Momy. “Dama ai na sani tunda na ji munafukar yarinyar nan ta dawo na kuma ga motar ka na san kana nan tunda ta je uwarta ta sake yi mata haɗe-haden su da suka saba na bin malamai!”

“Haba Momy abin da ki ke sam ba daidai ba ne, wannan cin fus… Tsawar da ta daka masa ne yasa shi yin shiru fuskar shi na nuna ɓacin rai “wato magana ma za ka faɗa mini saboda ni ɗin sa’ar ka ce ba. Ko da ya ke ai bai kamata ma naga laifin ka ba dan na tabbatar da ba a hayacin ka kake ba Allah kaɗai yasan me suka yi kafin ta dawo!”

Zai yi magana ta ɗaga masa hannu “ba na son jin komai maza ka kama hanya ka bar ɗakin nan tun kan na yi ma ka rashin mutunci!” Tashi ya yi tsaye ya matsa kusa da Zhara da take kuka ƙasa ya yi da murya “mene ne kuma abin kuka, ya kamata ki saba da halin Momy ya daina damun ki.”

Salati tasa tana faɗin “yau ni Turai naga abin da ya ishi ne Hafiz magana nake yi ma ka shi ne ka ke kamar ba da kai nake ba har kake yi mata magana lallai kuwa da aiki babba a gabana, na gane idan har ban yi da gaske ba rabani da kai za su yi” ajiyar zuciya ya yi yana mai ƙara yin ƙasa da murya “don Allah don Annabi idan Dady ya kira ki kar ki ce masa a’a kar ki manta kin mini alƙawarin ko me na ce za ki yi, dan haka ki ce masa da san… “Wai ba za ka wuce ba ne!?” Wani irin huce ya yi ya fice a zuciye “eh dai ko sama za ka tashi kai ka sani sakarai kawai a na nuna ma illar abu kana rintsi idanu ka ƙi ka gani. Ke kuma na dawo kanki!” Zuwa tayi ta tsaya gabanta tana riƙo kunnenta ta murɗe “duk wata tsiyar da kuka ƙulla ke da uwar ki wallahi ɗana ya fi ƙarfin ku, Alhaji ya ce idan har da amincewar ki Hafiz ya dawo da maganar auren ku babu makawa zai ɗaura auren.

To ina mai gargaɗin ki da kar ki kuskura ki ce za ki amince idan har kuma ki ka yi kuskuren amince wa da auren ɗana ki sa a ranki sai kin gwammace rayuwar makabarta a kan auren ɗana!!” Ta hankaɗata ta faɗi ƙasa diɓis har sai da bayanta ya amsa rintsi idanunta ta yi tana ji kamar tasa ihu.

Bayan fitar Momy ta kifi kanta jikin kujerar madubi tana zubar da hawaye zuciyarta a matuƙar tsoraci take ya za ta yi da Hafiz da yake ta yi mata magiya ya kuma sa ta yi masa alƙawari, KUSKUREN ta ne ma da ta masa alƙawari a kan abin da ba ta sani ba, ya za ta yi da son sa da ke barazanar tarwatsa zuciyarta? Ga kuma Momy da ta sanyata a gaba. Wunin ranar ta yi shi ne cikin tashin hankali da damuwa abinci ma ta kasa ci, Kande da ta zo su yi fira taga dai ba ta cikin yanayi mai daɗi dole ta barta ta je wajan aikinta.

“Ya gona fatan komai na tafiya daidai” gyara zaman sa Abba ya yi kafin ya ce. “AlhamdulilLah shinkafa ta fito kuma ta yi kyau sosai da alama ma sai ta fi ta wancan shekarar kyau.”

“Ma sha Allah abu ya yi kyau, In sha Allah zan samu lokaci na zo na yi kewaya.”

“Gaskiya ya kamata. Na yi mamaki da na ji ka ce ba za ka je Abuja wajan rantsar da sabon shugaban ƙasa ba” Dady ya yi murmushi “ka san ni ba ruwana da sha’anin siyasa kawai dai fatan mu Allah yasa sababbin shuwagabannin su zame mana alkhairi ga ƙasa ba ke ɗaya, wadannan matsalolin da ƙasa take ciki Allah ya yaye mana ya kawo mana sauyi mafi alkhairi Alfarmar Annabi SallalLahu Alaihi Wa Alihi WasalLam.”

“SallalLahu Alaihi Wa Alihi WasalLam. Amin Yaya shi ne kawai addu’ar da ya kamata duk ɗan ƙasa ya yi Allah ya yi mana mai kyau. Yawwa Yaya ina so mu yi magana da kai ne a kan Hafiz da Zhara.”

“Humm dama na sani ai tunda na ji ka ce kai ne za ka dawo da ita na san Hafiz ne ya sa ka gaba da zancen.”

“Hahaha ba hakan ba ne magana ta gaskiya dama fasa auren daga ni har kai ba wai ya yi mana daɗi ba ne kawai dai abin da Allah ya nufa bawa bai isa ya sauya shi ba. Tunda har ya dawo ya ce yana so ina ga kawai sai a yi domin ƙara ƙarfafa zumuncin mu.”

wayar Dady ta yi ƙara ya ɗaga kiran sai bayan da ya gama wayar sannan ya ajiye ya mayar da hankalin shi a kan Abba “kawai saboda ya mayar da mu sa’o’in sa sai ya dinga juyar da mu tamkar waina a cikin tanda ko? Ya ce bai so an ba shi zaɓin shi yanzu kuma ya dawo ya ce yana so kawai sai a ba shi anya a kwai adalci a cikin maganar nan ta ku daga kai har ɗan na ka? Ita kenan Mamana ba ta da zaɓinta sai yadda ya yi da ita?”

“Ba hakan ba ne Yaya na san itama ai ba wai tana ƙin shi ba ne kawai dan al’amarin ya zo ne ba a yadda a ka zata ba, na tabbatar da za ta yi farin ciki da wannan hukuncin” girgiza kai Dady ya yi yana faɗin “ni ba zan yarda da wannan hukuncin ba, zan kira ta na tambaye ta idan har ta amince shi kenan, idan kuma ta ce a’a tabbas ba za a yi wannan auren ba duk wanda take so shi zan aura mata. Kowa a barshi da zaɓin shi shi ne adalci.”

“Am… “Na riga da na gama magana. Ka zo mu ci abinci idan mun gama zan kira ta a tambaye ta, shi ma Hafiz ɗin yana hanya na ce ya zo” shiru kawai Abba ya yi dan ba yadda ya iya.

Kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci a ruɗe take ga Dady ya zuba mata idanu yana jiran jin amsar ta, ga Momy a gefen shi wacce a hanyar su ta zuwa falon Dady sai da ta sake yi mata gargaɗi da kausasan kalamai, ga Hafiz zaune a gefen Abba da ya kira ta a waya yana yi mata magiya kamar zai yi kuka a kan ta amince da auren shi da tunatar da ita alkawarin da ta masa, ga Abba da tun a mota yake ƙara jajjada mata lallai ba ya da farin cikin da ya wuce ya ga auren ta da ɗan ɗan’uwan shi. “Mamana kin yi shiru, ina so ki sani ba za mu taɓa yi ma ki dole ba matuƙar ba kya son Hafiz anan wajan anan take zan fatattaki maganar ba kuma za a sake yin ta ba” sunkuyar da kanta ta yi zuciyarta na halwabawa da sauri da sauri.

Fulani

<< Kuskuren Waye? 22Kuskuren Waye? 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×