Skip to content
Part 25 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Anwar yana office kansa a duƙi yana duba fayel Hafiz ya shigo kallon shi ya yi cikin mamaki “ikon Allah wata sabon gani yau kai ne a office ɗina?”

Sake haɗe rai Hafiz ya yi Anwar ya yi dariya “to Malam soja taimaka ka zauna.”

Jan kujera ya yi ya zauna “kwana biyu gaba ɗaya ka manta da ni idan na kira ka ba ka ɗagawa na zo office ɗin ka ba ka nan ina fatan dai lafiya ce ta ɓoye ka?”

“Ina cikin uzurika ne shi yasa. Magana na zo za mu yi.”

“To ina saurarin ka Allah dai yasa lafiya.”

Shiru ya yi tare da ɗora hannun shi a goshi.

“ka yi shiru.”

“Uhm! Anwar a kan maganar Zhara ne na rasa yadda zan shawo kanta, ga Dady shi ma ya kafe a kan ba zai ba ni ita ba gaba ke ɗaya kaina ya ƙulle wallahi har na rasa ma me zanyi.”

“Hafiz irin wannan lokacin dama nake gojema ka shi yasa na yi ta ƙoƙarin fahimtar da kai illar hakan amma ka rufe ido ka ƙi fahimta ta.”

Gyara zaman shi ya yi yana ƙwankwasa tebur ɗin gaban shi da ɗan yatsan shi “na sani na riga da nayi kuskure amma ina so na gyara kuskure na sai dai ta ya zan gyara?

Na fahimci a yanzu kamar Zhara hankalin ta ya fi karkata a kan ka, kuma duk laifin ka ne tun kan na fahimci ina sonta kai ka gama fahimtar da son na ta a zuciyata. Me yasa za ka mun hakan?”

Dariya marar sauti Anwar ya yi rungumi hannunsa ya yi a ƙirjin shi yana kallon Hafiz ya ce.

“Saboda kai ne ka ba ni dama sanda nake faɗa ma kar ka yi facali da ita kai ne ka faɗa mini ba ka yi ni na ɗauka ka bar mini shi yasa ni kuma na kafa tawa gwamnatin dan ba zan so na rasa kyakkyawar mace mai nagarta kamar Zh…

“Ya isa hakan! Anwar ban zo nan dan ka ci mutuncina ko ka ci fuskata ba, na zo ne na faɗa ma ka fita sabgar Zhara domin ita ɗin tawa ce domin ni kaɗai a ka yi ta. Matuƙar kana son alaƙa ta da kai ta ci gaba lallai ne ka yi ƙoƙarin barin ta.”

“Hahaha wallahi ka bani dariya haba abokina ka natsu mana yanzu saboda Allah wannan abin kunyar har ina saboda mace za ka bari har a ji kanmu gaskiya ka bani mamaki.”

“Mace ai ta wuce da a kirata saboda Zhara rayuwata ce zan iya rabuwa da ko ma waye in dai a kanta ne. Dan haka ina mai sake gargaɗin ka da ka fita sabgarta!”

Girgiza kai Anwar ya yi nan take fara’ar da take kan fuskar shi ta kau.

“Sanda na so ta har na nemi soyayyarta ita ma kuma ta bani fili a zuciyarta na nemi izinin ka ne?”

Shiru Hafiz ya yi “amsar a’a to dan haka a yanzun ma ba ka isa ka yi mini umurnin na barta ba, kawai ka shiga layin manemanta ai ita allura ce cikin ruwa mai rabo ne kan ɗauka. Sai mu yi takarar neman aurenta wanda ya ke da rabo sai ya ɗauka sai kuma me?”

Ya ƙarasa maganar yana ɗaga masa gira.

“Na fahimci ka wato a shirye dai ka ke da mu sa armakashi mu datsi zumuncin da mukai shekara da shekaru muna yi ko.”

“To mene ne a ciki kanmu farau ne bare har ya zama ƙarau?”

Nuna shi ya yi da ɗan yatsa cikin nuna gargaɗe ya fita office ɗin yana mai yin ƙwafa.

Murmushi Anwar ya yi “ah ka ga mutum da neman rigima ka ce ba ka so wani ya zo yana so kuma sai ka ce ba a isa ba mtsw.”

Husna ta janye Halima tana faɗin “ke wace ce ke kin yi hauka ne kawai za ki zo ki samu yarinya ki hau dukan ta babu gaira ba dalili!”

“Ke kuma karan kaɗa miya mene ne na ki a ciki ke na daka ko kuma ƙanwar uwar… “A hir ɗin ki! Wallahi ki ka ce za ki zageni a wajan nan zan maki shegen duka har sai na fahimtar da ke irin darajar da iyaye suke da ita da dukan da zan ma ki!”

Zhara da take dafi da fuskarta da har ta yi ja ta ce. “Halima me na yi maki da za ki zo har makaranta ki ci mutunci na har hakan? Mari fa.”

“O o mari ba ai wallahi Zhara ba ki ga komai ba abin da ya fi mari ciwo ma sai na yi maki tunda har ki ka zaɓi ki ci amanata ki rasa mijin wa za ki nace wa sai mijina ai baƙin jini ba hauka ba ne ba kuma ni na ɗora ma ki ba bare har ki ce tunda kin rasa mijin aure bari ki aure mini miji!”

Kallon mamaki Husna ta ke yi wa Zhara, ya yin da take ji kamar ƙasa ta buɗe ta faɗa dan kunya, musamman ganin yadda mata da maza suka yi masu ƙawanya suna kallon su.

Kuka ta fashe da shi irin mai cin rai “ban cancanci hakan daga gare ki ba Halima ki fa tuna wace ce ni a gare ki, dama ashe aminci da ƙauna watarana takan rikiɗe ta zama ƙiyayya har hakan?”

“Me kuwa zai hana idan har ta haɗu da wacce cin amana ba komai ne a wajan ta ba.

To bari ki ji wallahi mijina ya fi ƙarfin ki, a je a nemi wani sarkin nawa kam ya yi maki ƙamshin ɗan koli!”

Girgiza kai Zhara ta yi tana murmushin takaici komai ba ta ce ba sai ɗaukar jakarta da ta yi za ta bar wajan Halima ta finciko rigarta ta baya tana faɗin “oh wato ga mahaukaciya ba ina magana za ki tafi ki barni kenan na yi ta haushin ni kadai!”

“Uhmm! Ban san me ki ke so na ce ba Halima, kawai abin da zan iya faɗa ma ki ba ni ya kamata ki yi wa wannan maganar ba mijin ki ya kamata ki fara tunkara domin shi ne ya ke bi na ba wai ni ce nake bin shi ba.”

“Humm yake bin ki ko dai ki ke bin shi ko kin ɗauka ban san irin abin da ki ka je gida ki ka ƙulla ba ne? Ki ji da kyau kurwar mijina tafi ƙarfin ki wallahi!” Khadija ta a ka je a ka faɗa mata ta ƙarasu da sauri ta janye hannun Halima daga jikin Zhara tana masifa.

“Wannan wani irin iskanci ne Halima kawai dan rashin mutunci ki zo har cikin makaranta ki ce za ki ci mutuncin ta saboda kawai kinga ita ɗin ba mai yawan magana ba ce!” Fito da idanu ta yi tana nuna mamaki”

Sabon salo kiran asuba da usur har kina da bakin yin magana a kan Zhara ke mene ne ba kya yi mata na ce wani kalar rashin mutuncin ne ba ki yi mata ba.”

“Ina ruwan ki da duk abin da zan mata naga dai ita ɗin ‘yar’uwata ce ko naman jikin ta ki ka ga ina yanka wa bai shafe ki ba kuma hakan ba yana nufin naga wata banzan bazara ta zo ta ce za ta ci mutuncin ta na zuba mata idanu ba. Maza ki bar nan tun kan ki janyo wa igiyar auren ki ta fara tangal-tangal!”

“Ai wallahi ko wacce ta kawo shi duniya ba ta isa ta ce za ta raba aure na da Hafiz ba bare kuma wata can wai ƙan… Kokuwar da Halima ta kama ta da shi ne ya hana ta ƙarasa maganar suka shiga dukan juna.”

Kar ki nemi ki zagar mana uwa wallahi banga macen da ta isa ba!” Da ƙyar Zhara da wasu suka janye Khadija wasu matan suka janye Halima a ka sa ta mota suna aikawa juna zagi.

“Don Allah Khadija ki yi shiru hakan nan.”

“Dalla can ki zauna baƙin sanyin halin ki ya janyo a illata ki a banza kawai wacce ba komai ba ba ta fi ƙarfin ki ba ta zo tana ma ki rainin wayo har da duka kawai saboda komawa baya ki zuba mata idanu!”

Ta fincike daga riƙon da Zhara ta mata ta bar wajan a zuciye Zhara ta bi ta da idanu tana murmushi haɗe da hawaye har cikin ranta taji daɗin abin da Khadija tayi ba wai faɗan ba a’a yadda ta nuna ta damu da ita hakan ya susa mata zuciya ƙwarai.

Da ƙyar a ka samu Halima ta shiga mota ta bar makarantar a guje kamar za ta tashi sama.

Hannunta Husna ta ja ganin yadda mutane suka sanya masu idanu suna magana ƙasa-ƙasa can baya suka tafi in da babu mutane sosai suka zauna “Zhara faɗa mun me ya faru wace ce ita Halima?” Shiru ta yi ta ka sa magana dafa kafaɗarta ta yi “ki na ji ko ba wai na ce dole sai kin faɗa mini damuwar ki ba kawai na so na ji ne ko da a kwai shawarar da zan iya ba ki. Amma idan har kina ji ban cancanci ki faɗa mini ba babu matsala.”

“Ba hakan ba ne Aunty Husna ban ma san ta ina zan su ma ba ne.” ta dan sihirta tana mayar da numfashi kafin daga bisani ta ba Aunty Husna labarin komai jinjina kai Husna ta yi ciki da al’ajabi.

“Lallai ma yarinyar nan ba ta da kunya yanzu ita duk irin girman cin amanar da ta yi ba ta gani ba sai na ki take kallo saboda rashin kunya!”

“Ni ban taɓa kallon auren su a matsayin cin amana ba tun da har sai bango ya tsage sannan ƙadangare kan samu wajan shiga, ko me ya faru kuskure na ne ni ce na ba ta damar.”

“Idan har kin yarda ke ce ki ka ba Halima dama ba kuma laifin ta ba ne tabbas ya kamata shi ma Hafiz ki yi masa adalci ke ce ki ka ɓata komai tunda bai taɓa zuwa gaban ki ya ce bai son ki ba haka zalika ba shi ne ya fasa auren ki ba ke ce ki ka wargaza auren ki da kan ki. Ni shawarar da zan ba ki wallahi tunda har kina son shi kuma shi ma ya na son ki wallahi kar ki yi wasa da damar ki karo na biyu ki aure abin ki.”

“Ta ya zan iya kishi da Halima ita fa ina yi mata kallo tamkar wacce muka fito ciki ɗaya da ita ne.”

“Za fa ki fara ba ni haushi Zhara ita me yasa duk ba ta duba wannan ba ta yarda ta fara son shi har ta ba shi damar da ya so ta? Sannan duk da wannan kin kawar da kanki kina ƙoƙarin ku yi zumunci ita ba ta duba ƙoƙarin ta ta ci mutuncin ki shi ne har ki ke cewa za ki sadaukar da soyayyar ki saboda wacce bata san darajar ki ba. Wallahi ki aure Hafiz na tabbatar da ba za ki taɓa son wani ɗa namiji ba sama da Hafiz to dan me za ki lalata rayuwar ki a kan wacce ba ta ko san kina yi ba?”

Shiru Zhara tayi tana sauraren Aunty Husna da take ta ba ta shawara da nuna mata illar abin da take shirin yi wa kanta matuƙar ta ce ba za ta aure Hafiz ba. Ita dai sam ta kasa cewa komai ta ma rasa me za ta ce.

Khadija na parking ɗin motar ta Abba da Dady suka fito ciki, bayan ta ɗauki jakarta ta fito ƙarasa wa ta yi gaban su tana murmushi.

“Dady ba ka fita ba ashe”

“Eh yau ba zan fita ba ina gida. Ina ki ka baro mini Mamana?”

“Tana makaranta sai shidda za ta dawo. Ina wuni Abba.”

“Lafiya lau Khadija ashe kina nan shi ne har ina shirin tafiya ban gan ki ba.”

“Wai dama ba ta zo kun gaisa ba? Ke Khadija ba ki san ya zo ba ne?” Susu da kai ta yi tana in da in da “eh na sa sani amma ko da ya zo ba ma nan.”

“Da ku ka dawo kuma fa me ya hana ki zuwa ki gaishe shi?”

“Ƙyaleta Yaya ai ba ga shi yanzu mun haɗu ba, ya karatu.”

“Lafiya lau”

“Kar na sake jin ya zo har ya tafi ba ki fito kun gaisa ba, duk duniyar nan ban da sama da shi ko babu raina ba ku da wani uba da ya wuce shi kin ji na faɗa ma ki ko!?”

“Ka yi haƙuri ba zan sake ba In sha Allah. Ka yi haƙuri Abba na.”

Riƙo hannunta ya yi da murmushi a fuskar shi. “Kar ki damu kin ji ko. Yaushe za ki zo mana ne kin jima rabun ki da wajan mu.”

“Da zarar mun samu hutu zan zo.”

“To Allah ya yarda. Allah ya yi ma ku albarka.”

“Amin.” Suka amsa a tare, tana a wajan har ya shiga mota suka tafi tare da dareba. Tare da Dady suka nufi ciki yana ƙara yi mata faɗa haƙuri kawai take ba shi dan ta gama fahimtar a kan Abba da Zhara tsab za su iya samun matsala da Dady matuƙar ta yi wasa.

“Sannu da hutawa Momy”

Momy da take zaune a kan kujera tana kallo ta amsa mata da fara’a a kan fuskarta. Zama ta yi kusa da Dady da yake waya bayan ya gama wayar ya juyi yana kallonta “ya dai Kadin Dady kamar da magana a bakin ki ko?”

“Humm wallahi kuwa kamar ka sani Dady. Ka san me ya faru yau a makaranta?

“Ina zan sani tun da ban je ba, me ya faru ne?”

“Dady wallahi Halima ce ta je har makaranta ta ci mutuncin Zhara.”

“Wace Halimar!?” Ya yi tambayar cikin tsawa.

“Matar Yaya har da duka da marin ta ta yi, sai ma ka ga yadda ta yi mata wulaƙanci cikin jama’a.”

Komai bai ce ba sai dai kallo ɗaya za ka yi ka ga ɓacin rai a tattare da fuskar shi. Wayar shi ya ɗauka ya kira jim kaɗan a ka ɗaga “hello Dady barka da wuni”

“Kana ina?” Ya masa tambayar ba tare da ya amsa gaisuwar da yake yi masa ba.

“Ina asibiti”

“To ko me ka ke ina so ka bar shi ka ɗauko matar ka ku zo ina son ganin ku!”

“To Dady Allah dai yasa lafiya?” Ya yi tambayar cikin tsoro. “Ina jiran ku” tsinki kiran ya yi ba tare da ya ji me Hafiz ɗin ya ke faɗa ba. “Khadija direban ku yana nan?”

“Eh kamar na gan shi bakin gyet lokacin da na dawo.”

“Ki je ki duba idan yana nan ki ce masa na ce ya je ya ɗauko mini Mamana zan kira ta yanzu na faɗa mata.”

“To” ta amsa tana barin wajan. Taɓi baki Momy tayi tana faɗin ai fa an taɓo ‘yar gwal ga dukan alamo yau idan ba mu yi sa’a ba sai an tashi garin Kano da ɗan ƙaramin yaƙi.”

komai bai ce da ita ba sai ma barin falon da ya yi dan a yadda yake jin ɓacin ran nan idan har ya biye wa Turai komai na iya faruwa.

Khadija na dawowa Momy ta hau yi mata faɗa “to Inna iyani ina ruwan ki da sha’anin su da har za ki wani kwaso ƙafa ki zo jiki na rawa kamar makaɗi ki faɗa masa”

Cikin turo baki ta ce. “To ai na ga abin da ta yi ba ta kyauta ba gara na faɗa dan a yiwa abin tufka.”

“Mtsw! To ke a ka yi wa ko ƙanwar uwar ki!?”

“A’a ba ko ɗaya sai dai ita ɗin ‘yar’uwata ce dole na ji ciwo a duk lokacin da na ga wani ko wata zai ci zarafin ta. Ni fa dama ban da wata matsala da ita kawai dai ke ce ki ke ta ƙoƙarin sai na tsane ta.”

Sakin baki tayi tana kallon ta baki sake “eh a lallai Maryam ta gama da ni ga dukan alama so take duk sai ta ƙwace mini ko ta rabani da ku.”

Tashi ta yi tana tafiya ta ce. “Don Allah dai Momy ki daina irin wannan sam bai da ce ba.”

Sakin baki kawai tayi tana kallonta har ta haura sama. Ajiyar zuciya ta yi “lallai sai na yi da gaske in har ba so na ke Maryam ta sa ni kukan uwar ɗan musa ba.”

Halima tana banɗaki ta jiyo muryar Hafiz yana ƙwalla mata kira ta masa banza har sai da ta gama lalurarta sannan ta fito ta samu zai fita jin motsin fitowar ta yasa shi juyowa.

“Ai na ɗauka ko ba kya ɗakin.”

“Mene ne ka ke mini kiran mafarauta?”

“Humm ya yi kyau wato kiran nawa ne kiran mafarauta, ba komai yanzu dai ba wannan ne ya kawo ni ba ki shirya Dady ne yake kiran mu.”

Zama ta yi gefen gado tana faɗin “to ni miye nawa a ciki ka je sai ka dawo.”

“Amma ai kina jin me na ce ko cewa na yi Dady yana son ganin mu ina nufin har ke.”

“To ai dai kasan ni ɗin ba bagwariya ba ce ko bare har ka ce ban fahimci me ka ke nufi ba.”

Tsayawa ya yi gabanta cikin mamaki ya ce.

“Wai shin dai me ki ke nufi.”

“Ina nufin ba za ni ba dan kai ya haifa kai ne dolen shi ba ni ba.”

“Kin yi hauka ne Halima mahaifina yana kiran ki ki ce ba za ki ba har kina faɗin ke ɗin ba dolen shi ba ce!”

“Ai fa sai ka yi tun da zancen ka ke ji!” Ka sake ya yi yana kallonta har ma ya rasa me zai yi.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 24Kuskuren Waye? 26 >>

2 thoughts on “Kuskuren Waye? 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×