Skip to content
Part 32 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Har Zhara ta shige ɗaki ta kasa ko da motsi bare har ta furta ko da kalma ɗaya, ture filet ɗin wainar tayi ta miƙe tsaye a zuciye ta nufi ɗakin Zhara sai dai kash ta samu ta rufe da key ƙwafa tayi tana faɗin “da ki tsaya wallahi da sai na canza maki kamanni!!”
“Hahaha ke kin san ko tsayawa na yi babu abinda za ki ɗauka a jikina dan na fi ƙarfin ki, sai dai kiji jiki, ba kuma zan biye maki ba ko ba komai ina son Babyn Baby ya fito duniya lafiya!!” Zage na fitar hankali ta dinga ɗuɗdura mata sai dai ko motsin Zhara ba ta yi ba bare har tasa rai da za ta tanka mata.

Tsaye take a kichen tana haɗa ƙullun wainar sumo da za tayi Halima ta shigo ta tsaya mata a kai “bani waje zan yi aiki.”

“Amma dai kinga aiki nake ko, Sannan duk faɗin kichin ɗin nan ki rasa wajan da za ki yi na ki aikin sai inda nake saboda neman fitina.”

“Nan naga dama yi kuma ba ki isa ki hani yi ba” shiru ta mata ta ci gaba da aikinta, bangajeta ta yi cikin tsautsayi ƙullun ya zube Zhara ta kalle ƙullun ta kalleta “dubi abin da ki ka janyo wannan ai rashin hankali ne.”

“Yanzu kuwa zan nuna maki rashin hankalin nawa dan ki daɗa tabbatarwa!” Cin kular Zhara tayi daidai nan Hafiz ya shigo kichin ɗin “ke meye haka!?”

“Mahaukaciya ta tace dani shi ne nake so na nuna mata haukan nawa” janyeta ya yi daga riƙon da ta yi wa Zhara “ke Zhara me yasa za ki ce da ita mahaukaciya?” Ajiyar zuciya tayi tana ciza laɓɓa “aiki ta tarar ina yi shi ne babu inda za ta yi nata aikin sai inda nake yi, dan na yi magana shi ne fa tayi cikina har hakan ya janyo zubewar ƙullun” kallon Halima yayi tsaki tayi tana faɗin “naga ai gidan ba ita kaɗai take da iko a kan shi ba bare har ta ce dole sai ta zaɓa mini wajan da zan aikina.”

“Ai ba ita kika yi wa asara ba ni ki kai wa da nasa kuɗi na saya” juyawa ya yi yana tafiya ya ce. “Ku sameni a falo.”

Bayan fitar shi Halima ta ce. “Wallahi yarinya ba za ta zo ta sameni a gida ta ce za ta nuna mini isa ba” murmushin tura haushi Zhara ta mata ta bi ta gefenta ta fita ai kuwa ta shaƙa wato ga mahaukaciya ma.

“Shin yaushe kuka raba girki ne ban sani ba?”
“Sai dai ka tambaye ta ni dai ban sani ba” jiyowa yayi yana kallon ta sai cika take tana batsewa “faɗa mini yaushe a ka raba girki ni ban sani ba.”

“Ai ba sai ka raba ba, ni dai kasan ba zan taɓa cin girkinta ba dan ban san me za ta barbaɗa a ciki ba, ko cikin nan nawa baƙin cikinsa take na san duk yadda za tayi dan ganin ta illata ni yi za ta yi, ka ga kuwa ai dole na kiyaye.”

“To ikon Allah! Haha Halima na sa maki magani na ji me to? Kin dai faɗa ne saboda rashin abin faɗa amma kin fi kowa sanin ban ko san hanyar malamai ba bare har na je. Sannan dan me zan maki baƙin ciki da abin da ba ni na baki ba.”

“Dan na san halin ki ada shi ke nuna a yanzun ma hakan kike ko ba za ki sauya ba? Ai mugu bai da kama kuma mutum mugun icce ne” riƙi kansa yayi cikin takaici ya ce. “Iri-irin waɗan-nan abubuwan ne na so na guje masu shi yasa na so na raba maku gida amma sam kika ƙi amincewa, yanzu saboda Allah ita Zhara ce za ta sa maki magani a abinci in banda son tada zaune tsaye mtsw!” Miƙewa tayi riƙi ƙogu tayi tana faɗin “ai kuma sai kayi girkinta ne dai ba zanci ba!”

“Ki koma ki zauna!” Tsawar da yayi mata ne yasa ta zama babu shiru sai harare-harare take “yau saura kwana biyu Zhara ta cika sati ɗaya da zuwa a ranar ne kuma girki zai dawo hannunki, dan haka daga yau in dai girki ba na mutum ba ne to kar na ji ko nagan shi a cikin kichin, ko waccen ku tana da firij a ɗakinta komai akwai a ciki bare ki ce za ki neman wani abu.”

“Ni fa Hafiz ba zanci girkinta ba sai dai ka raba mana girki.”

“Ni kuma na ce ba zan taɓa rabawa ba tunda har kuna gida ɗaya dole ne girkin ya zama a haɗe wacce ta ji za ta iya ci ta ci wacce taji ba za ta iya ci ba ta bari banda haƙƙin kowa a kaina!” Fau ta tashi ta bar falon ranta a matuƙar ɓaci. Zhara ta riƙo hannunsa tana murzawa ahankali “kayi haƙuri.”

“Ki daina bani haƙuri ai ba ke ce ki ka mini laifin ba, kawai dai zan ja kunnenki ko me za ta yi maki karki sake biye mata ki faɗa mini zanyi wa abun tufka.”

“Uhm In sha Allah ba zan sake ba, amma me zai hana ka yarda a raba girkin tunda ita tafi son hakan” meƙewa yayi yana faɗin “yadda na ce babu canji hakan za a yi, dan ni nake aurenta ba ita ce take aurena ba da koyaushe za ta zo da wani tsirko ta ce shi za a yi” ganin babu fuska yasa ta yin shiru ba dan ranta ya so ba dan ita kanta ta fi son a raba girkin domin ta tsorata da maganar Halima ko sharri za ta iya yi mata gami da maganin da take faɗa. Dama wayar shi ya manta ya dawo ɗauka ya tarar da wannan rigimar yana ɗauka ya fita bayan ya sake ja masu kunne.

Ranar da ya koma ɗakinta ta karɓe shi kamar ba abin da ya faru hakan ya sanya shi farin ciki da addu’ar Allah yasa a ɗore wa hakan. Duk yadda Halima take taƙulu rigima Zhara ba ta kulata. Tsaye take a gaban madubi ta ɗauki turare za ta fesa Hafiz ya shigo ɗakin kallonsa tayi da murmushi a kan fuskarta “har ka rigani shiri duk saurin nan da nake yi” tsayawa yayi ta bayanta ya rungumota jikinsa suna kallon juna ta cikin madubi “dama ai shirin mata da namu ba ɗaya ba ko sai kun tsaya wani ƙawa sa wannan goge wannan.”

Hannunta ta ɗora akan hannayesa tana murmushi “ni da ba ma wata kwalliyar da nayi” juyo da ita yayi suna kallon juna “anya kuwa kin dai san na faɗa maki ko fauda ban yarda ki shafa ba ko?”

“Lah bayan mai babu abinda na shafa.”

“Shi kuma wannan ɗin me za a yi da shi?” Ya yi tambayar yana karɓar turaren da yake ɗaya hannun “zan sa ne” fito da idanunsa ya yi “kai makaranta fa za ki je shi ne har wani sa turare za ki yi wasu mazan su juyo ƙamshin matata” karɓar turaren ta yi ta ajiye a kan madubi “to na ajiye kuma ba zan sake tunanin yin hakan ba” haɗe fuskokinsu ya yi yana goga hancinsa a kan nata “baby mu tafi kar na makara kuma kasan dai yau ba ni ce da kai ba.”

“Mata kuna da matsala ni koyaushe ina da hurumin kasancewa da ko waccen ku ba tare da shamaki ba komai nake akan ilimi nake yinsa.”

“Uhm ni in… “Dama jikina ya bani cin amanata ake shi yasa na zo dan na tabbatarwa da kaina gaskiya” Zhara ta janye jikinta da sauri kanta a ƙasa ta ɗauki Hijab da yake a kan gado tana warware wa, “yanzu ke me kika ga anyi da zai sa ki faɗin anci amanar ki?”

“Yanzu me na tarar kuna yi?”

“Kin samu tana jikina amma ai ban san hakan laifi ba ne saboda duk ranar girkinta idan na shiga ɗakin ki na kanyi maki kwatankwacin hakan, amma ba ki taɓa faɗa mun laifi ne yin hakan ba” kwaɓi fuska tayi tana turo baki gaba ta ce. “Amma dai ai bayan wannan babu wani abun da yake shiga tsakanin mu.”

“Ita kuma wani abun ki ka samu ina yi ko?” Shiru ta yi “tambayar ki nake ki bani amsa”
“Ni ba ruwana ai da hakan ake komai, ni kawai dan tana ‘yar’uwar ka sai ku taru kuna cin duduniyata” tsaki ya yi ya ce da Zhara ta fito su tafi, takalmi tasa ta bi bayan shi Halima ta biyo su tana masifa “ta fito ku tafi ina?”

“Zan kaita makaranta ko kina da matsala da hakan ne?”

“Ni kuwa nake da matsala da hakan dan babu dalilin da zai sa ku fita tare da ita bayan girkina ne, wa ma ya sani ko ba makarantar za ta tafi ba wani wajan za ku tafi tun da a gida dai ansan ba zan yarda aci amanata ba.”

“Kina da matsala Halima sai ki dinga yin abu kamar wata bagidajiyar da bata taɓa shiga aji ba, to ko ma me za ki faɗa sai ki faɗa fita ce dai sai mun yi” Zhara da take tsaye a kusa da shi ta ce. “Ka bari na shiga a-dai-daita-sahu sai kayi tafiyar ka wajan aikin”

“Munafuncin banza ni za ki nunawa kisa nasan komai, dan haka riƙi wata kisar taki ni ce fa kar ce ta san kan a tsakanina da ke!” Ta yi maganar tana hararar Zhara “idan na sake jin kinyi maganar shiga motar kasuwa in ranki ya yi dubu sai ya ɓaci! Ma za ki zo mu tafi” da sauri tayi gaba ba tare da ta ce da shi komai ba ganin yadda yake yi mata magana cikin faɗa “wallahi in har a ka yi wani abun Allah ya isa! Dan ba zan taɓa yafewa ba” kallonta kawai yayi ya gyaɗa kansa tafiyarsa yayi ba tare da ya ce da ita komai ba. Zama tayi akan kujera da ƙarfi tana huci “za ki dawo ne dan ubanki wallahi sai kin san kin shiga gonar da ba a fita Lafiya!”

Da dare suna zaune a ƙaramin falonta ta yi filo da cinyoyinsa yana duba abu a laptop ɗin sa ya ce. “Ya kamata ki fara zuwa awo cikin ki yanzu yayi wata huɗu” gyara kwanciyarta tayi kafin ta ce. “Ba za a bari sai wata mai fita ba, ni yawon asibitin nan ne ba zan iya ba.”

“A’a ki shirya gobe idan zan tafi asibiti sai mu fita tare, sannan mene ne wahalar ke da ba a ƙafa za ki je ba sannan ba jira za ki yi ba da mun je za a yi duk abin da ya dace ne ki dawo gida.”

“Shi kenan Allah ya kaimu.”

“Amin” tashi ta yi ta zauna ta ɗora kanta a kafaɗar sa tana faɗin “ina so za mu yi magana.”

“Ina saurarenki” janye hannunsa ta yi daga laptop ɗin ta juyo da fuskar shi suna kallon juna “yawwa kaga yanzu ai sai kafi fahimta ta amma ina magana hankalin ka ba ya a kaina.”

“Kin ganki wani abun ne fa nake dubawa, to ina jinki mene ne” ta yi shiru kamar ba za ta ce komai ba ta ɗan yi gyaran murya kafin ta ce. “Dama zancen karatu ne ina so zan koma makaranta.”

Murmushi ya yi kafin ya daga bisani ya ce. “A da ai ba kya ra’ayin hakan me ya sauya ma ki tunani yanzu?”

“Kawai dai yanzu na ji ina so, kuma ka san ko a baya ai na yi ma maganar zan koma.”

“Halima banda ra’ayin hakan kin kuma sani, ko Zhara saboda da karatun na aure ta, sannan kafin auren Dady ya ta jajjada mini lallai na barta ta ƙarasa karatun ta, wannan dalilin ne yasa ki ka ga na barta tana zuwa” sakin hannunsa ta yi ta janye jikinta daga jikinsa tana faɗin “dama na san hakan za ka ce ai, a komai dai sai ka nuna mini ni bare ce a a wajan ka ita ce jinin ka.”

“Ya salam! Yanzu saboda Allah me kuma na yi maki da yake nuna fifiko ko nuna ita ɗin jinina ce? Ki daina kawo wannan tunanin a ranki Halima, dukan ku matsayin ku ɗaya ne a wajena, don Allah ki bari mu zauna lafiya.”

“Ba ka so a zauna lafiya ba idan har ka so hakan kawai ka barni nayi karatuna ko kuma ita ma ta zauna gida babu karatun kamar dai ni.”

“Ko ɗaya ba zan yi ba sai kuma me” miƙewa tayi tsaye “sai ka taro masifa da tashin hankali matuƙar ba ka yi ɗaya daga cikin abin da na faɗa ba!” Ba ta jira jin me zai faɗa ba ta shige uwar ɗaki. “Allah ya kyauta, ita dai in har ba ta taƙalo rikici ba hankalin ta ba zai taɓa kwanciya ba, shiyasa yake girmama Zhara ba za ka taɓa jin ta ambaci ko da sunan Halima ba a duk sanda suke tare bare har tayi maganar ta” tsaki ya yi ya janyo laptop ɗin shi yana ci gaba da binciken wani magani da yake yi.

Kwance ya sameta lulluɓe da bargo kasancewar anyi ruwan safe sanyi ya sauka, duba agogon wayarsa ya yi ƙarfe tara da mintuta, zama yayi gefen kanta yana shafa kitson da yake kanta “Sweet Baby kin manta yau Monday kike bacci ko yau ba zuwa makaranta ne?” Juye ta yi cikin magagin bacci ta ɗora kanta a kan cinyoyinsa “um sai ƙarfe biyu zan shiga mu fito 6.”

“To ai shikenan a sha bacci lafiya, dreba zai zo ya ɗauke ki tunda tsoro ya hana ki tuƙa taki motar” tashi ta yi ta zauna a jikin shi “wai ƙarfe nawa ne Baby?”

“Goma ta kusa” buɗe idanunta ta yi da sauri “kai ashe rana ta yi, bari na tashi na shirya, ka faɗa masa ya zo 11 ya ɗaukeni ya kaini gida daga can zan tafi makaranta.”

“Wani gidan?”

“Ka manta na faɗa ma zan je na gaida Momy?”

“Oh sam na manta, amma ki bari sai zuwa jibi tunda gobe Dady zai dawo jibi sai na kai ki da kaina ki gaishe su” ba yadda ta iya sai to kawai ta ce da shi ba ta san me yasa ba duk sanda ta masa maganar zuwa gidan Momy sai ya san yadda ya gaucewa tafiyar, kwantar da ita ya yi yana lulluɓeta “ki koma baccin ki sai na dawo, idan har babu aiki sosai ba mamaki na zo na kai ki da kaina” idanunta a kansa ta masa addu’a ya fice bayan ya manna mata kiss a goshi.

Tana fitowa banɗaki kira na shigowa wayarta da sauri ta ƙarasa wajan da tasa cajin wayar ta ciro ta da murmushi a fuskarta ta ɗaga “duk amarcin ne yasa ba a ɗaga kiran na mu ne Mrs Hafiz.”

“Kai Aunty Husna Allah ba hakan ba ne, ina banɗaki ko da kika kira.”

“Hahaha to ai ba laifi bane ma ko angon ne ya hana a daga, dama na fito ne na ce bari na ji ko za ki shigo.”

“Eh har ma na shirya zan yi sallah yanzu sai na fito.”

“Allah ya kawo ki lafiya.”

“Amin” ta faɗa tana tsinki kiran. a fito cikin shiri tana gyara sa niƙab turus tayi lokacin da tayi tozali da ita zuciyarta ta dinga dukan uku-uku.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 31Kuskuren Waye? 33 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 32”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×