Skip to content
Part 38 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Tafiya yake kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki, a falo suka haɗu da Khadija tana haurawa sama da Ice cream a hannunta “ina wuni Yaya” kai kawai ya gyaɗa mata ya bi ta gefenta ya ƙarasa saukowa daga matattakalar benen bin bayan shi ta yi da kallo har zai fita ta ƙwalla masa kira “Yaya!”

Juyowa ya yi ya zuba ma ta idanu ba tare da ya ce da ita komai ba. Da sassarfa ta ƙarasu wajan sa “ban dai san me Momy ta faɗa ma ba amma koma dai meye Halima ce Ummul’haba’isi, ta zo gidan nan ta kitsawa Momy ƙarya da gaskiya.”

“Na gode ji ki” ya yi maganar cikin gyaɗa kai tare da ficewa. Ya tarar ba kowa a falon jefar da jakar shi ya yi a kan kujera ya zauna ɗaya kujerar yana mayar da numfashi Zhara ta fito ɗaki tana waya ganin shi zaune yasa ta ce da Mama tana zuwa. “Ashe ka dawo sannu da zuwa.”

“Yawwa sannu” zama tayi a gefen shi tana faɗin “me ya faru naga kayi wani iri kamar ba ka da lafiya.”

“Lafiya lau kawai gajiya ce” riƙo hannunsa ta yi “sannu mu je kayi wanka sai ka ci abinci gajiyar za ta tafi” miƙewa ya yi yana faɗin “bar abincin kawai dai zan yi wankan.” Tunda ya shiga wankan take zaune a gefen gadon shi gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi yanayin sa kaɗai na nuna a kwai damuwa a tare da shi.

Bayan ya kimtsa ya kwanta idanunsa a lumshi tana gefen shi tana yi masa tausa,

“Yaya me yake damun ka ne gaba ɗaya ka yi wani iri” janyota ya yi ta kwanta a jikin shi ya riƙo hannunta yana kallon zanen fulawar da tayi ya kasa cewa da ita komai, itama ɗin bata ce da shi komai ba sai dai zuciyarta da take bugawa. Kamar a mafarki haka ta ji kalmar ta faɗo mata a kunne “ki yi haƙuri tafiyar ki ce ta fasu.”

“Me yasa wani abun ne ya faru kuma?”

“Momy ce ta ce bata yarda ba, na yi ƙoƙarin fahimtar da ita amma hakan ya gagara” shiru ta yi ba ta ce da shi komai ba “kinyi shiru.”

Murmushi ta yi kafin daga bisani ta ce. “Ba komai Allah yasa hakan ne mafi alkhairi.”

ƙoƙarin sanya idanunsa yake cikin na ta amma taƙi yarda sai ma tashi da tayi daga jikin shi tana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon ta ce. “In dai wannan ne yasa ka cikin damuwa Allah ka daina ni har cikin raina na haƙura da tafiyar, ka zo mu je ka ci abinci don Allah.”

Jiki a sanyaye ya biyo bayanta suka je dinning bayan ta zuba masa tuwon shinkafa miyar kuɓewa busassa, ta ce. “Ka kira Halima ko a waya ne ta zo mu ci abincin ko ta ɗibi na ta. ”

“Idan tana da buƙatar ci za ta fito ne ta ɗauka” daga hakan bai sake magana ba ya ci gaba da cin abincin shi. Bayan sun koma ɗakin baccin su suna a kwance a kan gado yana wasa da kitson da yake kanta ya ce.

“Na gode na kuma ji daɗi da ba ki tashi hankalin ki ba, In sha Allah ko bayan na tafi ne zan lallaɓata sai ki biyu ni.”

“Kar ka damu Sweet Babyna fatana dai Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya ya kuma bada sa’ar abinda ka je nema. Tunda har ba ta so kar ka sake tayar mata da zancen kawai na haƙura da tafiyar.”

“Allah ya yi ma ki albarka” ya yi maganar yana ƙara janyota jikin shi.

Soki tafiyar nan ya yi matuƙar yi mata ciwo sai dai ya zama dole ta danni damuwarta ko dan ta ƙarfafa masa dan ya samu ƙwarin gwauwar yi wa mahaifiyarsa biyayya.

Washegari yana wajan wanka kira ya shigo wayar Hafiz a jiye gyaran gadon tayi ta je ta duba tana ganin Momy ce ta fasa ɗauka ta dawo tana ci gaba da gyara gadon. Tana idar da sharar ɗakin ya fito wanka ya je gaban madubi yana sharci ruwan kansa “waye ya ke kiran wayata ne?”

Mai ta ɗauka tana shafa masa a baya ta ce. “Momy ce ta kira”

“Wani abun ta ce ne?”

“A’a ai ban ɗaga kiran ba kasan halin metar Momy ɗagawar sai ta zama tashin hankali.”

Janye hannunta ya yi daga shafin man da take yi masa yana mai zuba mata idanu.

“Yanzu mahaifiyar tawa ce mai meta?” Cikin sanyin murya ta ce. “Ba wai na faɗi hakan ne da wata manufa ba, kawai ina jin tsoron na ɗaga ne kasanta sai ya zama laifi a wajanta.”

Cikin ƙwafa ya ce. “Wato ga masifaffiya ba, tunda ta hana ki tafiya bari a fakaice ki dinga faɗar munanan lafuzza a kanta!” Haushi ya ƙumeta daga magana sai ciwo ya zama ƙari ta masa shiru tsaki ya yi ya ci gaba da shirin sa za ta taimaka masa yasa riga ya ɗaga mata hannu “ba na buƙata maza ki bar mini ɗaki” kallon sa take zuciyarta na mata zafi ji take kamar ta mayar masa da magana ta daure ba ta ce komai ba ta fita.

A ƙofa suka haɗu da Halima za ta shiga dakin shi fuska a haɗe ya ce. “Mene ne?”

“Kamar ya mene ne, ka dawo jiya ba ka neme ni ka ji lafiya ta ba, ina buƙatar wani abun ko ba na buƙata ko oho, yanzu na kawo kaina kuma ka ce wai mene ne.”

“Idan kin gama faɗa ba ni hanya ina da abin yi.”

“Wai me kake nufi ne Hafiz” janyeta ya yi daga gaban shi ya wuce yana tsaki gaba ɗaya nema take ta sure masa a rai mace ba ta da aiki sai ƙoƙarin haɗa shi da mahaifiyar shi. “

Humm ko ma me za kayi kai dai ka sani tafiya dai ce ba ka isa kayi ta da Zhara ba sai dai kowa ya rasa!” Ta shige ɗaki tana meta.

Ta tagar uwar ɗakin ta take kallon shi har ya shiga mota ya bar gidan, kuka ta fashe da shi komawa ta yi gefen gado zuciyarta ba daɗi,

“Shi kenan sai a dake ka a kuma hana ka kuka saboda rashin adalci!” Wayarta ta ɗauka ta kira Mama tana jin muryar Mama ta sake fashewa da kuka “SubhanalilLah Zhara lafiya kike kuka?”

“Na ga ji Mama koyaushe Momy ƙoƙarin ƙuntata mini take, yanzu ta hanani tafiyar nan na daure ban nuna ɓacin raina ba, kawai dan ta kira wayar shi ban ɗaga ba ya tambayi dalili na ce da shi tsoron metar ta nake shi ne fa ya dinga faɗa harda korata daga ɗakin shi wai na raina masa uwa.”

“Mtsw! In banda shashanci Zhara taya za ki ce da shi uwar sa meta ne da ita kuma ki ce ba zai ji ciwo ba! Kar ki sake yin wannan sakarcin duk yadda kike ganin halinta uwa uwa ce duk rashin kirkinta wallahi yana son abar shi duk kuma ɗan kirki ba zai yarda a raina masa uwa ba. Dan haka kar ki sake yarda kiyi wannan kuskuren ki je ki ba shi haƙuri” cikin shagwɓa ta ce. “Amma ai ni ba zaginta na yi ba mita fa kawai na ce.”

“Wai ba kuwa za ki daina ba ko, ke za ki yarda ace da ni hakan ne, kar na sake ji kin ji na faɗa ma ki ko. Sannan maganar tafiya kar ki wani ɓata ranki dama ta yi hakan ne dan ta ɓata ma ki rai to ki nuna ma ta ko a jikin ki domin shi maƙiyi ba ka taɓa nuna masa damuwar ka yi ƙoƙari yaga murmushi da farin ciki a kan fuskar ka shi ne zai sa ka ci shi da yaƙi, matuƙar kika ce ki biye wa halin Turai sai ta raba ki da aurenki ko zaman lafiya a gidan auren ki, kin ga burinta ya cika kenan” sosai tayi mata faɗa da nasiha kafin daga bisani suka yi sallama. Tana a jiye wayar kiran Husna ya shigo ɗaga kiran tayi tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta “tuba nake matar Hafiz na so na zo mu yi bankwana sai dai uzuri yasa ban samu na zo ba”

“Aunty Husna kenan ai tafiya ta fa su.”

“Ban gane ta fa su ba! Ya fasa tafiyar ne gaba ɗaya?” Gyaɗa kai tayi tana faɗin “a’a shi zai tafi ni ce dai na fasa” tambayarta dalili tayi ta faɗa mata bayanin komai “hum-um Allah ya kyauta wannan sarakuwa ta ki sai haƙuri, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi. Don Allah kar wannan abin yasa ki sa damuwa a ranki kamar gobe zai dawo gare ki, sannan daga Maman ta shi har ita kishiyar dama burin su sugan ki da damuwa a dan haka kar ki yarda ki nuna masu hakan, mahaƙurci mawadaci ne.”

“In sha Allah zan yi ƙoƙarin yin hakan na gode sosai Allah ya bar zumunci”

“Amin Ya Allah.” Bayan ta gama wayar ta kwanta tana tunanin wannan ƙiyayyar ta rashin dalili da Momy take yi mata a hakan bacci ya yi awon gaba da ita.

Da dare ta zauna a falo tana jiran dawowar shi dan ba za ta so ya shige dakin shi ko na Halima ba tunda ba girkinta ba ne. Halima ta fito tana cin cingwam tana kallon Zhara ta tintsiri da dariya “oh Allah Lamiɗo wannan shi a ke kira da an ga samu anga rashi a lokaci ɗaya, gaskiya zanen fulawar nan ya yi kyau an sha kyau fa hahaha” kallo ɗaya ta yi mata ta kawar da kanta ba tare da ta tanka mata ba. Zama ta yi a kujerar da take daga wajan ɗakinta tana faɗin “da kina zaton za ki taka ni ne ki wuce lafiya ba tare da kin zame ba?” Tashi Zhara ta yi za ta shiga ɗaki ta ji buɗewar gyet da shigowar motar Hafiz hakan yasa ta koma ta zauna “ko a magantu ko ma kar a magantu na dai san zuciya na nan kamar za ta fashe saboda baƙin cikin ba za a shiga jirgi ba bare har a bi iska zuwa ƙasar masu jajayen kunnuwa. Zama Daram Nageria” murmushi kawai ta yi ji take kamar ta ba ta amsa sai dai kuma tunanin idan har ta biye mata suka yi faɗan ai ta ma ta abin da take so.

“Assalamu alaikum” idanunta ga ƙofar da yake shigowa “Amin alaika Salam sannu da dawowa Sweet Heart”
“Yawwa sannu ku da gida” Halima ta ja tsaki har sai da ya kalleta “ke kuma tsakin na meye?”

“Kawai ra’ayi” gyaɗa kan shi kawai ya yi yana ƙarasa shigowa falon “idan ka gama kimtsawa ina so ganin ka” ta yi maganar ganin ya yi hanyar ɗakin shi. “Kina son ganin sa a kan wani dalili kin manta da yau ɗin ni ce da shi ba ke ba.”

“Tashi ki je zan shigo ɗakin ki idan na gama” ba musu ta yi yanda ya ce Halima ta biyo bayan shi tana masifa “ai sai na ga yadda za a yi ka tafi ɗakin nata bayan ni ce nake da kai” bai ce da ita komai ba ya shiga ɗaki ta biyu shi.

“Ka na fa ji ina ma magana amma kayi kamar ba ka san ina yi ba”
“Kin ga Halima sahun ki a likkafani ki kama hanya ki fitar mini daga ɗaki tun kan a jiyo kanmu” riƙi ƙogo ta yi tana faɗin “hum-um wato korata ma kake saboda ka samu hanyar ba ta dama ta shigo nan ku ci amanata kamar yadda kuka saba ba” a jiye wayar shi da jakarsa ya yi a kan gado yana ajiyar zuciya “kar ki kai ni bango Halima Kinga kin je kin haɗani da mahaifiyata na zuba ma ki idanu bance da ke komai ba ko, to na roƙe ki da ki kama kan ki ba na son rigima tafiya ce a gabana.”

“Wani maƙaryacin ne ko na ce ma munafuki ne ya faɗama na haɗa ka da Mahaifiyar ka.

Kai a je ɗin ma na yi ai ba tsoron ta kefe nake ba, ba kuma haɗin faɗa ne ba gaskiyar da ka ɓoye mata ne ni na je na faɗa ma ta, oh na ma dai gane fushin an hana ka tafiya da ‘yar gaban goshe ne kake so ka sauke a kaina shi yasa kake wani cin magani” ta juya a zuciye tana faɗin “aikin banza ko me za ka yi sai dai ka yi tafiya ce dai yadda ba a yi ta da ni ba wallahi ba a isa a yi da ita ba kowa ya zauna zaman tsoron gida!” Ta rufe masa ƙofa da ƙarfi.

“Mtsw! Sam tunani ya yi mata ƙaranci, mata biyu ko rigima.!”

Zaune ya sameta tana dannar waya shigowar sa yasa ta ajiye wayar gefe zama ya yi a kusa da ita yana faɗin “fatan kin wuni lafiya”
“Lafiya lau sai kewar ka da nake ta yi. Ya aikin?”

“Aiki da godiya, anya kin yi kewata kuwa”
“Da gaske nake” ta ƙarasa maganar tana zamewa daga kujera ta durƙusa gaban shi “don Allah don Annabi ka yi haƙuri a kan abin da na faɗa ɗazun na yi kuskure ba zan sake kamanta hakan ba” tallabota ya yi ya ɗora ta a kan cinyoyinsa yana faɗin “tabbas raina ya ɓaci amma komai ya riga da ya wuce ina kuma fatan za ki dinga kiyaye lafuzzan ki a kan ta”
“In sha Allah ba zan sake ba”
“Koyaushe kina ƙara shiga raina Zharana ki na karɓar kuskuren ki ki gyara a duk sanda ki ka yi. Allah ya yi ma ki albarka”

“Amin mijina abin alfaharina”
“Komai a kwai a sito na saye, abin da duk babu kafin na dawo ku faɗa mini a waya zan sa Anwar ya kawo ma ku. Zan tura maki kuɗi a account ɗin ki ko da da wata buƙatar za ta ta so”
“Mun gode Allah ya ƙara lafiya da yalwar arziƙi, Allah ya kai mana kai lafiya ya dawo da kai lafiya cikin nasara”
“Amin ya Allah. Allah ya yi ma ki albarka”
“Amma har yanzu fa Dady bai san ba tare za mu zo ba so nake sai mun je sai na faɗa masa, ina ƙara ba ki haƙuri” hannunta ta kai a kan fuskarsa tana shafa sajin sa “ka daina ba ni haƙuri ban riƙi komai a raina ba, idan har kun je ka fadawa Dady banda lafiya ne shi yasa na ce ba za ni ba” sumbatar ta ya yi “Allah ya yi ma ki albarka.”

A kwance ya samu Halima tana kuka zama ya yi gefenta “kina so ki dinga sanyawa kan ki damuwa ne Halima, shin me na rage ki da shi daga kulawa da ba ki lokacina soyayyata da sauran al’amuran yau da kullum bayan auren Zhara da za ki sanya karan tsana a kanta ki kuma yi ƙoƙarin sanyo mahaifiyata a ciki?” Tashi ta yi ta zauna tana faɗin “ko wannan tafiyar da kayi niyar yi da ita ai nuna fifiko ne a tsakanin ni da ita!” Murmushi ya yi “ba ki san yadda tafiyar take ba ne shi yasa kike tunanin hakan, shi kenan kiyi haƙuri ai kin nuna matsayin ki tunda ga shi kin sa an fasa tafiyar da ita sai ki godewa Allah, rigima kuma sai ta ƙare. Ki duba na turo ma ki kuɗi ko da a kwai abin da za ki ɓuƙata, sannan ki dinga zuwa awo cikin lokutan da a ka ba ki domin kula da lafiyar ki da abin da ke cikin ki munyi magana da Dr Larai za ta kula da ke yanda ya kamata”

Gyaɗa kanta ta yi tana faɗin “to amma dai ai za mu dinga yin waya ko?”
“Wannan ai dole ne”

“Idan kuma na haihu za ka zo? Kayan barkan fa?” Janyota ya yi jikin shi yana faɗin “In sha Allah zan zo fatana Allah ya sauke ki lafiya, kayan barka kuma ai dai yi mai wuyar a haihu lafiya duk masu sauƙi ne su” murmushi ta yi tana ƙara kwantar da kanta jikin shi.

Tun da ya tafi take a kwance gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikinta sai juye take a kan gado. Hankaɗo ƙofar da a ka yi da ƙarfi yasa ta tashi firgici tana kallon ƙofar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 37Kuskuren Waye? 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×