Littafi Na Biyu
Juyawa ya yi zai tafi.
“Tunda kin ce na tafi zan tafi’.
Gaba daya ta cafko shi ta kankame shi ta baya, tana wani irin kuka.
“Idan ba ka aure ni ba, da ni da kai za mu mutu, na yi alkawarin haka”.
Mirgino da ita ya yi gabansa, ya kamata ya zaunar a kan gado. Da sauri ya fice, ta bude murya tana wani irin kuka.
Da gudu Abdul da Abbansa suka rugo ciki. Ita kadai suka gani da alama ba su ga fitar Deedat ba. abdul ya rike ta. . .