Littafi Na Biyu
Juyawa ya yi zai tafi.
“Tunda kin ce na tafi zan tafi’.
Gaba daya ta cafko shi ta kankame shi ta baya, tana wani irin kuka.
“Idan ba ka aure ni ba, da ni da kai za mu mutu, na yi alkawarin haka”.
Mirgino da ita ya yi gabansa, ya kamata ya zaunar a kan gado. Da sauri ya fice, ta bude murya tana wani irin kuka.
Da gudu Abdul da Abbansa suka rugo ciki. Ita kadai suka gani da alama ba su ga fitar Deedat ba. abdul ya rike ta tamau! Tana faman fizge-fizge kamar sabuwar kamu, cikin kuka ta ke shaida musu ba zai aure ta ba.
“Kullum abu daya yake fada, gwara in mutu na huta”.
Ran Abdul ya kara baci, idanun nan sun gama rinewa, alwashi iri-iri ya dinga ci.
‘Za ki kashe kanki a kan soyayyar banza? Son mutumin da bai damu da ke ba?”
“Abba shi nake so, Yaya Deedat nake so, idan bai aure ni ba ba zan rayu ba. abba zan mutu, kada ku bari ya tafi”.
Wani kyakkyawan mari Abdul ya dauke ta da shi yana faman huci.
“To ki mutu mana, wa za ki ma asara? Dube ki ko kunya ba kya ji, shi Deedat din waye shi da ki ke ikirarin kashe rayuwarki a kansa?”
Abbanta ya janye Abdul daga dakin, ya kuma kira likita. Allurar barci aka yi mata.
*** *** ***
“Abba wallahi Deedat ba shi da mutunci, amma zan yi maganinsa, ya bar ganin shi din wani ne, wallahi sai ya raina kansa, in ban da masifa irin ta Nabila da so ya rufe mata ido…”
Da sauri Abbansu ya katse shi, “Ya isa haka, kada in ji wannan maganar ka ji ko?”
Ya yi kwafa ya fita yana faman surutai.
Bai koma gida ba, hotel ya kama daki, kansa ya gama cazuwa, neman mafita yake yi. Wayarsa ta shiga kara, ya mika hannu ya dauka. Kanwata ya gani a rubuce a fuskar wayar, kafin ya kai ga dagawa kiran ya katse. Ya koma ya kwanta, kwakwalwarsa ta hau wani lissafi can daban, zai hakura da Nurat! Ya tsura ma wayar ido, soyayyata da Nurat ta mutu har abada, daga yau ba zan sake tunaninta ba”. Ya furta a bayyane.
‘Zan je gurin Ummita, zan nemi yardarta zan auri Aazeen da Nabila lokaci guda, Aazeen ce wadda ta soni ba tare da sanin waye ni ba, kuma za ta iya ci gaba da sona lokacin da rufaffen sirrina zai bayyana. Zan je mata a yadda ta san ni”.
Wayarsa ta sake shin kara, ya yi saurin karawa a kunne.
“Masoyi”. Ya ji an fada.
Ya yi saurin cire wayar a kunne, ya ji muryar kamar ba tata ba, amma ta dan yi shige da tata. Ya mayar da wayar a kunne.
Ba ta taba kiransa da wannan sunan ba, kodayake hakan zai iya yiwuwa in ya yi la’akari da yadda al’amuransu suka juye a kwanakin nan zuwa soyayya.
“Kanwata”. Ya ce cikin wata shakakkiyar murya, “Ke ce kuwa?”
Ta yi dariya, “Sosai ni ce mana me ka gani?”
Kansa ya sake daurewa, Aazeen dinsa ba ma’abociyar dariya ba ce, to amma me ya sa ta canza haka?
“Masoyi shiru na ji? Yaushe za ka zo gidanmu?”
“Yanzu”. Ya ce.
Ta sake shekewa da dariya.
“Da sauri haka?”
Ya dinga jin anya Aazeen dinsa ce? Aazeen da ya sani ba haka ta ke ba.
“Ba kya son na zo ne?”
“Ah why not? So kai, burina kenan ka zo n a ga kalarka. Allah ya sa ka yi min kamar yadda muryarka ke da dadi. Allah ya sa kai ma mai dadi ne”.
Ras gabanshi ya buga, dadi kuma?
Ta katse shi, “Okey, gaya min yaushe ne za ka zo?”
“Zan zo gobe”.
“Wow! Da gaske?”
“Na yi alkawarin haka”.
“Okey, thanks nawan”.
Ya cire wayar daga kunnensa, gaba daya cikin rashin kuzari yake, bai bar hotel din ba sai da ya yi sallar isha.
“Ummita na amince da auren Nabila, duk lokacin da suke so amma ina da sharadi”.
Murmushin da ke fuskarta ya dauke.
“Sharadi kuma? To fadi in ji”.
Ya dan yi jim zuwa wani lokaci.
“Ni ma ina da tawa zabin, na dade da yi ma wata alkawarin aure. Ke ce kullum ke nusar da ni girman alkawari, kin ga bai kamata in shure alkawarina ba”.
‘Na shiga uku, Babana tozarta ni za ka yi? Wannan ai wulakanci ne”.
“Ki yi hakuri Ummita, ku yi magana da su idan sun amince a sa bikin duk lokacin da ya yi musu”.
Za ta yi magana ya katse ta.
“No Ummita, don Allah kada ki ce komai”.
Ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye, ta ce, “To shi ke nan na ji zan same su”.
*****
“Muryarsa mai dadi, yana magana daya bayan daya kamar wani wayayye. Ban taba tsammanin haka daga gare shi ba, har ma na dokanta da zuwansa. Ban san dalili ba tun kafin na ganshi har ya gama burge ni”.
Ta fada ma Nurat cike da bayyanannen farin ciki.
Dadi ya kama Nurat, “Yaya yadda ki ka ji shi a waya, haka za ki ganshi a fili zai yi miki”.
“Kanwata, kada ki mance sharadina, ko da gobe ya rage in aure shi da zarar na hadu da Ahmad Deedat komai zai sauya”.
“To amma Yaya Aazeen shi kuma ya yi ya ya kenan?”
“Kada ki damu da wannan, da zarar na ba shi hatimin nasara zai mance wata soyayya”.
“A’a Yayata, ki daina cika baki, na san za ki so shi”.
“Uhum ina son kudi fiye da kaina. Ke ni fa zan iya yin komai a kan kudi, idona idon wannan gayen wallahi sai na aure shi ko da zan rasa raina, ko da sama da kasa za su hade”.
“To amma idan kin same shi yana da mata fa?”
“In ta kama zan iya sa wa a kashe ta, ke ni ko da ke yake aure na zabi in rasa ki da a ce na rasa shi. Ki bari ki gani, ba ki san ni ba ne sai ya bayyana zan fito miki da true colour dina”.
Yadda ta ke furta kalaman nata Nurat ta yarda za ta iya aikata komai, ko da ta zo kwanciya kalaman Yayar tata ne suka dinga yi mata kuda a kunne.
Kwance a wani faffadan gado ta yi matashi da kirjinsa, yadda ya dinga bi da ita ta dinga jin wani irin sonsa.
Ya dube ta cikin shafa saman gashinta.
“Da na rasa ki da na mutu, ina tsoron ranar da zan rasa ki”.
Ta yi saurin toshe masa baki da tattausan hannunta.
“Ba za mu rasa juna ba, ka daina fadin haka, kada Allah ya tabbatar”.
“Allah ma ya tabbatar muddin ina numfashi sai na ga bayanku”.
Dago kan da za su yi sai suka hangi Aazeen rike da sharbebiyar wuka.
Wata iriyar kara ta saka, ta mike zaune, ta gama jikewa da gumi.
“Me ya kawo abokin Principal a cikin mafarkina? Na shiga uku”.
A hankali ta dinga jin saukar sonsa a zuciyarta, wani irin mahaukacin so.
Tuni yanayinta ya sauya, ta dinga maida numfashi, me haka ke nufi? Ta maida kallonta ga agogon da ke manne a jikin bango, karfe hudu da rabi, lokacin kiraye-kirayen sallah ya karade ko’ina na unguwar. Gabanta ya buga ta tuno malaminsu ya taba cewa, duk lokacin da mutum ya farka daga cikin mafarkinsa ya ji ana kiran sallah, to abin da ya gani zai iya kasancewa.
A gurguje ta nufi bathroom ta daura alwala, har ta idar da sallar tunanin Deedat ta ke yi. Wani irin farin ciki ya lullube ta, ina ma Allah zai sa haka ta kasance, amma a cire shigowar Aazeen da wuka cikin mafarkin. Tsintar kanta ta yi da son sake ganinsa, Allah ya sa idan ya ganta ya ce yana sonta.
Murmushi ta yi ta rufe fuska da tafin hannunta, kunyar kanta ta ke ji, da alama ta mance batun Zaruk.
Wunin ranar ta yi shi cikin rashin kuzari, lokaci zuwa lokaci ta kan tuna mafarkinta, kawai sai ta yi murmushi. Mutumin da tunda ta ke sau uku ta taba ganinsa, da alama ba a nan yake ba, kawai don sharri ne na mafarki, kila ma har abada ba za ki sake sanya shi a idanunki ba.
Saukar hannu ta ji a jikinta, da sauri ta dago kai suka yi ido biyu da Aazeen, suka sakar wa juna murmushi.
“Da alama kin mance da zuwan mijin da ki ka yi min ko?”
Ta yi dariya, “Ta ya zan mance? Ina nan zaune duk doki ya cika ni”.
Ta koma tana duban Aazeen, “Yayata, ban ga kin yi kwalliya ba”.
Lakuce mata hanci Aazeen ta yi.
“Kin mance ni ne? kina son ne in ba da kaina?”
“No haka ma ya isa, Yayata mai kyau ne fa shi din da gaske”.
Ta rankwashe mata kai, “Ni din ma kyakkyawa ce. Dauko min wayar da Dad ya siya miki ‘yar gata”.
Ta dauko ta mika mata.
“Wow! Haduwa”.
Ta shiga duddubawa, “Waya ta hadu da bagidaya. Babu lambar kowa sai ta Ammi da Daddy, bari in saka miki tawa da ta angon naki”.
‘Angona kuma, waye?”
“Ka ji ‘yar rainin hankali, Zaruk mana”.
Gabanta ya fadi.
“Hum”. Kawai ta ce tana kallo ta loda mata lambobin cikin wayar, ta juya za ta fita. Da sauri Nurat ta ce, “Yayata, kada ki mance duk wayar da muke yi da ke ku ke ui”.
“Okey, kada ki samu damuwa. Bari in leka gurin masu aikin nan in ga sun gama shirya dinning, kada bako ya zo su hau yi mana zarya a ka”.
Karfe biyar da kusan mintuna biyar wayar Aazeen ta dau ruri, wayar na ajiye a kusa da Nurat. Ganin lambar Deedat ta yi saurin daga wayar.
“Allah ya sa na bi kwatancen da ki ka turo min daidai, ga ni a kofar wani get blue”.
“Okey ka zo, bari na turo maka maigadi sai ya shigo da kai ciki ko?”
“Okey, to na gode”.
Ta ajiye wayar a dokance.
Da gudu ta nufi sashin Aazeen inda ta ke tsammanin Aazeen din na can.
“Yaya Aazeen bakonki ya zo fa”.
“Okey, ke Ladi je ki cewa maigadi ya kai shi bangaren baki”.
Ammi ta bi su da kallo a can karkashin zuciyarta addu’a ta ke yi, Allah ya sa mijin aure ne ya zo mata. Kokarin tafiya ta ke yi.
“Yaya Aazeen ina zuwa”. Nurat ta ce da ita, da gudu ta fita har tana tuntube za ta fadi, Ammi ta yi murmushi. Har yanzu akwai kuruciya a tattare da ita, sai ga ta sake dawowa da gudun, kwalbar turare ce a hannunta kawai ta hau feshe jikin Aazeen da shi. Ammi ta gaza hakuri.
“Oh ni Rahma, wannan wane bako ne muka yi mai matsayi haka?”
“Ammi ina zaune Nurat ta…”
Da sauri Nurat ta dinga yi mata magiyar ta yi shiru, bayan ta faki idon Ammi.
“Ammi bara na dawo kada ya yi ta jira”.
Gaba daya suka bar sashin Aazeen ta nufi gurin bako bayan ta sanya wani shegen takalmi mai tsinin tsiya, hadi da cilla cingam a baki.
Tafe ta ke tana rausaya cike da nishadi, ita kam Nurat komawa ta yi bedroom dinta ta yi rigingine a kan gado, ji ta yi gabanta na wani irin bugawa kamar zai faso kirjinta. A fili kuma addu’a ta ke yi, Allah y sa shi din ya yi wa yayar tata.
Kofar sitroom din sashin bakin irin kofar nan ce ta glass. Yana zaune a kan kujera yana faman saka da warwara. Gaba daya ta nitsa cikin tunani lokacin da ta dora idanunta a kanshi kamewa ta yi a gurin. Ba ta taba ganin namiji mai cikar halitta kamarshi ba, wankan tarwada ne, yana da fadi irin su ake kira da giant, irin namijin da ta ke burin ta yi rayuwa da shi, duk inda kyau yake ya kai. Bai kauce ma duk yadda ta ke buri namiji ya kasance ba, gashin girarsa gazar-gazar hadi da zara-zaran gashin ido tamkar na Nurat.
Yanayinsa so cool, duk ta lura da wadannan abubuwan ne cikin minti dayan da ta tsura masa ido. Kut! Ta ce ta dinga ja da baya a hankali gudun kada ya ji motsinta, daga karshe ta kwasa a guje tana haki.
Nurat na tsaye da gudu Aazeen ta rungume ta ta baya.
“Ba ki taba faranta mini irin yau ba, dole ne na ba ki tukwici, kin kawo abokin harka. Nurat gayen mai kyau ne, kyawunsa har ya zarta yadda ki ka kwatanta mini shi”.
Da sauri-da sauri ta ke magana cike da matsanancin farin ciki, ta koma ta sake ta.
“Ina zua, zan sake kaya zan yi kwalliya, zan sanya sarka in kara turare. Amma duk sai na fara goge baki”.
Ta fada tana kokarin barin gurin, Nurat ta ji kamar ta je ta ganshi amma kuma tsoro ta ke yi kada ya gano wani abu. Ta koma ta zauna ita kanta farin cikinta ba ya misaltuwa. Daga hannu ta yi tana gode wa Ubangijin sammai, har ta dokanta Aazeen ta je ta dawo.
Motsin kofar Aazeen ta ji, da sauri ta mike ta yi waje. Arba ta yi da ita sanye da wasu kananan kayan da ba ta santa da su ba. Ta yi matukar kyau, sai dai macen da ta san mutuncin kanta ba za ta iya dosar wanda ba muharraminta ba da wadannan kayan.
“Yayata, kin yi kyau. Amma kayan sun matse ki da yawa”.
“Ke idan ban yi haka ba, ya za a yi na yake shi? Mazan nan fa sai da haka”.
Ta yi saurin ficewa, Nurat kamar ta saka ihu don takaici.
Kas-kas din cingam din bakinta da kwas-kwas din takalminta shi ya janyo hankalinsa, ya yi saurin daga kai idanunsu suka gauraya. Ta sakar masa murmushi, da sauri ya dauke kai yanayinsa ba yabo ba fallasa, shigarta ne ta fara ruguza komai.
A karo na biyu ya ga ta kwalluba da shi, wato ta zauna daf da shi, kansa ya daure.
“Yau ga ni ga masoyi”. Ta ce.
Ras! Gabanshi ya buga, muryarta ta bambanta da ta waya. Ya fada a ransa.
“Aazeen da fatan na same ku lafiya?”
Ta yi murmushi.
“Yau ta tabbata mun hadu, ko yaushe ina burin ganin wannan rana, na yi tunanin lokacin da na yi baje kolin soyayyata ba zan taba siyarwa ba sai da ka zo na tabbatar na yi babban kamu”.
Tana magana tana faman kada ido da karairaya.
Binta kawai yake da kallo, ba ta nuna dabi’unta na waya ko daya a zahiri ba.
Ta katse tunaninsa, “Za ka samu duk abin da ka ke so, jari, farin ciki da komai za ka yi alfahari da ni”.
Ya yi yake, “Haka ne ko? Na ko gode sosai”.
Ta shiga zuba abinci a plate.
“Bismillah ci abinci mana,”
“A’a, na koshi,”
“Idan ba ka ci ba, da kai na zan baka”.
Ya tabbata da gaske ta ke yi, da sauri ya kai ma cokali cafa, ya ci babu shiri, ya dan ci abincin babu laifi ya dan kurbi drinks.
“Ni zan wuce”.
“Da wuri haka?”
“Kada ki damu gobe zan dawo”.
“Yanzu kenan babu yadda za mu dan zaga?”
‘Kada ki damu, na ce zan dawo”.
Ya mike yana kwakkwabe rigarsa, kafin ta ankara ta hange shi a bakin kofa, ta rufa masa baya. Sam ba ta so tafiyarsa ba, gaba daya ta gama haukacewa da wani irin sha’awarshi, sai dai bai kamata ta yi saurin fito da maitarta fili ba.
Har get ta raka shi, sai da ya tada babur lifan ta ga tafiyarsa ukun ta juyo gida.
A can cikin gida Nurat ta kasa zaune sai faman safa da marwa ta ke, tana jiran dawowar Aazeen, ta gama kaguwa.
Tun daga nesa ta jiyo Aazeen na kwala mata kira, ta fito a sukwane suka yi kacibus.
Nurat yana da kyau, yana da kyau matukar kyau, kyawunsa ya sanya kayan jikinsa suka yi masa kyau. Fatar jikinsa luf-luf kamar ba talakan da ki ke ba ni labari ba, komai nasa mai kyau ko magana yake yi kumatunsa na lobawa. Ya burge ni, shi ne namijin farko da ya taba tafiya da imanina. Ban gaji da ganinsa ba ya tafi”.
Nurat ta dinga dariya ta mika mata hannu.
“Ba ni tukwicina”.
“Dole ne wannan kanwata”.