Kasancewar yau Lahadi kuma ba ta da aiki shi ya sa ta dukufa gyaran gida, zuwa 11am gidan ya fita tsab.
Sai a lokacin ne ta dakko wayarta don ganin wadanda suka kirata, daman ta san dole akwai kiran Aunty Zee, da Hajja, sune kuma ta fara kira, daga bisani ta kira abokan aikin da ta san muhimmin abu ne ya sa su kiranta.
Tashin Zee daga bacci ne ya sanyata rufe data hade da mayar da hankalinta a kan Zee din.
A hankali ta tako zuwa wajenta, don kuwa yanzu babu inda ba ta zuwa, da ace ma shayar. . .