Skip to content
Part 15 of 25 in the Series Labarin Asiya by Matar J

Kasancewar yau Lahadi kuma ba ta da aiki shi ya sa ta dukufa gyaran gida, zuwa 11am gidan ya fita tsab.

Sai a lokacin ne ta dakko wayarta don ganin wadanda suka kirata, daman ta san dole akwai kiran Aunty Zee, da Hajja, sune kuma ta fara kira, daga bisani ta kira abokan aikin da ta san muhimmin abu ne ya sa su kiranta.

Tashin Zee daga bacci ne ya sanyata rufe data hade da mayar da hankalinta a kan Zee din.

A hankali ta tako zuwa wajenta, don kuwa yanzu babu inda ba ta zuwa, da ace ma shayar da ita take da tuni ta yaye ta.

Sallamar Jamila hade ta turo kofa ne ya sanya Asiya mayar da hankalinta a kofar shigowar.

Yan’matan gidansu ne su biyar, Jamila, Rukayya, Aysha, Sadiya da kuma kulu.

“Da na san za ku zo ba zan yi aikin nan ba wallahi, na yi tunanin ma kiranku, na san halinku, yaron birni ne ku, ba kuya ba biyan bukata. Za kui ta fada min gaku nan in ji shiru.”

Gabadaya suka yi dariya daidai suna zama a kan kujera yayin da Rukayya ta dauki Zee.

“Yanzu ma fa kasuwa za mu je, muka biyo nan.” Cewar Sadiya bayan ta jinginar da kanta a jikin kujera.

“To ya mutanen gidan?” Asiya ta tambaya tana dubansu.

“Duk suna lafiya”

“Aunty wai me ya samu Zee ne, na ga sai bata rai take yi?” Rukayya ta tambaya lokaci daya kuma tana kallon Zee.

“A bacci ta tashi, yunwa take ji. Dakko mata kununta na nan a kitchen cikin flask.”

“Aunty ina bakonku na ranar can, ko har ya tafi.” Jamila ta tambaya fuskarta dauke da murmushi.

Haba Asiya ta rike “Amma abu wajen sati biyu, shi ne kuma ace har yanzu yana nan.”

“Tambaya fa na yi Aunty.”

“To ya tafi.”

“Sai yaushe kuma zai dawo” Jamila ta kuma tambaya

“Na shiga ukuna, wai me zai miki ne?”

“Aunty Wallahi gayen ya hadu ne.”

Dariya su Kulu suka yi, yayin da Asiya ta mike tsaye hade da nufar hanyar kitchen “Allah ya kyauta Jamila wannan rashin kunyar har ina.”

“Ai Aunty tun ranar take damunmu da hirarsa.” cewar Kulu cikin dariya

Bayan ta Jamilar ta bi cikin dariya “Kin san Allah Aunty ya hadu.”

“Ya tafi da zuciyarki kenan?”

Dariya Jamila ta yi kafin ta ce “Ni ma na san na tafi da tashi.”

Suka dan yi gajeruwar dariya.

Shiru Jamila ta yi kafin ta ce “Aunty wai dan wane gari ne?”

“Ki bar ni in mutu maza su kai ni ba mata ba Jamila.”

“Aunty!!” Jamila ta kira sunan cikin marairaicewa.

“Kina sonshi ne?” Kai tsaye Asiya ta jeho mata tambayar.

Shiru Jamila ta yi illa murmushin da take yi.

“Hmmmm! To ki jefar da wannan tunanin don kuwa nan da wata daya Mukhtar na tare da matarsa.”

Ido jamila ta fitar waje ba tare da ta yi magana ba.

“Kwarai ma kuwa.” Asiya ta fada hade da ficewa daga kitchen din.

Wannan shi ne son ma so wani.

Tun ranar da ta dora idonta a kansa ba ta kara samun sukuni ba, fuskarsa ta ki bace mata, kallon da yake mata ta dauka na so ne, ashe ita ce ta mayar da shi na so din, shi a wurin sa kallo ne da yake ma kowa ba kebabben kallo ne irin na musamman wa mutane na musamman ba.

Sosai kishinsa ya taba zuciyarta, tana jin wani irin daci.

“Kuka kike yi.?” Asiya ta katse mata tunani da tambayarta

“A’a.” Jamila ta ba ta amsa hade da girgiza kai.

“To wannan hawayen fa?”

Da sauri Jamila ta kai hannunta a kan fuskarta jin ruwan hawayen da ta taba ne ya sa ta kuma jin wasu sabbin hawayen sun fito.

Murmushi Asiya ta yi mai dauke da ma’anoni masu yawa kafin ta ce “Na dauka wasa kike yi, ashe gaske kike yi.

Tabbas Mukhtar yana sonki, amma kuma ba zai yiwu ya aureki ba.”

“Me ya sa Aunty?” cikin sauri Jamila ta yi tambayar

“Saboda ba shi da lafiya, yana da irin cutarmu kin ga kuwa ba zai yiwu ya aureki ba.”

Wani irin kallo Jamila ta bi Asiya da shi.

“Gaskiyar kenan, ban so kuma na fada miki ba, amma kila hakan zai sanya ki yi saurin cire shi a ranki.”

Ta dan nisa kadan

“Maganar auransa kuma sha Allah shi ma muna sanya ran nan da wata biyu ayi in sha Allah, saboda duk wani bincike da wasu sharruda muna ta kokarin ganin mun cika su. Ki yi hakuri sha Allah za ki samu wanda ya fishi.”

Shigowar Kulu kitchen din ne ya hana Jamila magana

“Ki zo mu tafi ” Cewar Kulu ba tare da ta kula da halin da Jamila take ciki ba.

“Aunty zan tafi da Zee, Haidar ya damu a kai ta.” Jamila ta fada cikin kokarin boye damuwarta.

“Allah ya kiyaye maku hanya.”

Har gate Asiya ta rakasu bayan ta basu dubu biyu kudin mashin.

Zee kuwa ko a jikinta don ta saba dasu ba kuma yau ne suka fara tafiya da ita ba.

Sosai Asiya ta ji ba dadi da halin da kanwarta take ciki, tabbas da ace Mukhtar kalau yake za ta bi ko wace hanya ganin Jamila ta mallake shi muddin akwai alkairi a ciki.

Saboda kome za ta yi wa Jamila ba ta biyata ba yadda take dawainiya da kuma kula da Haidar.

Haka kuma take kula da Zee idan ta kai ta gidan.

Daidai da dakika ba ta taba kyamatarsu ba.

To me zai sa ita ma ba za ta hidimta mata ba. Sannan ta yi bakin rai bakin fama wajen samar mata duk wani abu da take so muddin bai sabawa shari’a ko al’ada ba.

Tsakaninta da duk ‘yan’ uwanta sai addu’a, don kuwa su din kamar wani bango ne a gare ta, sun tsaya mata a lokacin da take tunanin zasu guje ta .

Basu kyamace ta ba ita da yaranta.

Musamman Haidar suna kula da komanshi, misalin reza, clipper yin aski, shan maganinsa, soson wankansa abincinsa da kuma karatunsa.

Shi ya sa ba mai kallonsa ya ce yana da wata cuta a tare da shi.

Alhamdulillahi kawai za ta iya cewa tare da rokon Allah ya ba ta abin da za ta yi masu ita ma

Haka rayuwa ta ci gaba da turawa, tare da nasarori da kuma akasinsu, a cikin hakan ne Allah ya kara azurta Asiya da ciki, In da ta samu Abdallah, sunan mahaifinta, shi ya sa suke kiransa da Baba, kamar dai Zee shi ma Abdallah lafiya aka haifesa cikin ikon Allah da kuma kulawar likitoci,

A hankali ta turo kofar hade da sallama, sabe take da Abdallah (Baba)

Nusaiba ce rike da Alqur’ani hizif goma, yayin da Haidar ke gefenta idonsa a rufe yana karanto surutul-Ahkaf. Wannan ya nuna mata hadda yake bayarwa, saboda a cikin satin nan zasu je musabaka ta jaha, kuma shi ne zai wakilci makarantarsu a musabakar dalibai yan shekara bakwai.

Tun da sunansa ya fita a matsayin wanda zai kare karamar hukumarsu ya zamana ba shi da wani aiki ko wane lokaci sai na karatu musamman da satin musabakar ya kama.

Wani farin ciki ne ya lullube ta, kaunar yaron ta kuma ratsa ko wane bangare na jikinta, tana yi wa Allah godiya da ya ba ta Haidar a matsayin ɗa, tana alfahari da hakan a bangaren karatun addini kam Haidar yana da kwanya sosai, a bangaren boko ne yake da matsala musamman a bangaren lissafi.

Ta karaso cikin falon a hankali ta tsaya gabansa, kasancewar idonsa a rufe yake kuma hankalinsa na kan karatun da yake bai ji alamun an tsaya kusa da shi ba, don haka bai bude idon ba, har sai da ya kai karshen surar.

A lokacin kuwa Asiya hawayen farin ciki take yi, dukawa ta yi gabansa bayan ta aje Baba a kasa hade da dora hannayenta a kan guiwoyinsa.

Shi kuwa kallonta kawai yake yi fuskarsa dauke da wani yanayin da ba zai fassaru ba, amma kam tabbas ba zai wuce damuwa da kuma mamakin halin da mamarsa take ciki ba.

“Haidar!” ta kira sunanshi a hankali, ba ta jira ya amsa ba ta ci gaba da cewa

“Kukan farin ciki nake yi, wace uwa ce ba za ta yi alfahari da samunka a matsayin ɗa ba, ban damu da rashin kokarinka amfanin boko ba, saboda ka maye gurbin sa da wani ilmin da ba kowa ke samun shi ba sai zababbe a wajen Allah. A shekarunka bakwai a duniya kana da haddar hizif goma ni a wurina ba ƙaramin abun farin ciki ba ne Haidar.”

Shiru ya yi yana kallonta da alama ba shi da hausar maganar da zai fada mata wata magana da za ta ji dadi.

“Na yi Alkawari idan har karamar hukamar nan ta zo na daya a bangaren masu shekarunka zan yi maka duk wani abu da kake so in sha Allah.”

Yanzu kam an zo wurin da zai iya bayar da amsa don haka cikin doki ya yi saurin cewa “Momy digital Qur’an za ki saya min irin na malaminmu, wacce babban mutum ke koyawa wani yaro karatu.”

Murmushi Asiya ta yi hade da share hawayenta lokaci daya kuma ta rike hannayensa biyu.

“Na yi ma alkawari yarona, sai kuma me?”

“Sai Alqur’ani hizif sittin irin mai pieces din nan na cikin kwali”

“Zan saya ma, bayan nan fa?”

Ya yi shiru alamun tunani “Ba komai.”

Shigowar Jamila rike da hannun Zee ne ya hanata magana.

Da gudu kuwa Zee ta karaso hade da mamutse Asiya ta baya tana dariya.

“Lafiya kuwa Aunty na ga kamar kin yi kuka.”
Jamila ta jefa mata tambayar hade da zuba mata ido.

“Lafiya kalau, kukan farin ciki ne, yaronki yana matukar kokari haddar hizif goma a shekarunsa akwai abun farin ciki”

Jamila ta fadada murmushinta “Shi ne kuma abun kuka?”

Asiya ta mike hade da yin dariya “Ba za ki gane ba.”

“Yarona ba ka ganni ba ne?” Jamila ta yi maganar hade da kallon Haidar.

Murmushi ya yi hade da mikewa ya rungumeta.

Da kyar ta daga shi sama, tana fadin “Wayyo Allahna! Yarona ya kara nauyi fa.”

Dariya suka tuntsire da ita har da Haidar da yake kokarin sauka kasa.

“Wallahi sai kin bude hakarkari, Haidar yanzu ai ya yi girma da a daga shi irin haka, shekara bakwai fa.”

Asiya ta yi maganar hade da nufar kofar da za ta sada ta da falon Hajja.

“Ba ki ganin yadda kika kashe mishi jiki, shi ya sa nake son mantar da shi.” Jamila ta ba ta amsa a lokacin da take bin bayanta.

Tare suka shiga falon Hajja da ke zaune tana shirya kayan guga ta yi saurin dagowa hade da fadada murmushinta.

“Sannunku da zuwa, ban ji shigowarku ba. Ina Zee din?”

“Tana tare da su Nusaiba” Jamila ta ba ta amsa hade da zama.

Hannu Hajja ta sanya hade da daukar Baba (Abdallah) tana fadin “Har kin gama da can din ne?”

Asiya ta cire gyalenta hade da aje ahi gefe “Eh na gama, kin gama duk wata shaida a nan sun ba ni.” ta yi maganar hade da janyo wasu takardu da ke cikin jakarta ta mikawa Hajja

A natse Hajja ke karantawa har ta zo karshe.

“Ma sha Allah! Allah ya taimaka. To yanzu me ye ya rage kuma?”

“Babu komai, na yi masu duk wani bayani da suke bukata kuma sun yaba sosai da yunkurinmu”

Jamila da ke gefe tana sauraron hirar tasu ta katse su da fadin “Wai me ake kullawa ne ba a sanya damu ba.”

Duk suka yi gajeruwar dariya kafin Hajja ta ce “Auntynki ce tare da hadin gwiwar su Mukhtar da matarsa Kubrah ke son bude wata kungiya da za ta rika wayar da kan masu cuta irin tasu hade da tallafa masu da abubuwan bukata.”

Kai Jamila ta jinjina cike da gamsuwa”Gaskiya wannan yunkuri ne mai kyau. “

“Haka ne. Sannan za mu rika hada masu cutar aure ta hanyar amfani da kwararrun likitoci, za kuma mu rika ba wa yaran da aka haifa madara kyauta, da magungunnansu. Kin ga hakan zai taimaka kwarai” cewar Asiya tana kallon Jamila.

“Wannan gaskiya ne, Allah ya saka maku da mafificin alkairi ya dafa maku, ni kaina zan so in shiga cikin wannan taimako, amma Aunty yaushe aka fara wannan shirya wannan kabakin arzikin ni ban sani ba, abu har ya zo karshe.” cewar Jamila lokacin da take duba takardun da Asiya ta ajiye.

Murmushi Asiya ta yi hade da fadin” Tun bayan auran Mukhtar da Kubra na fara tunanin, musamman yadda na ga komai ya ta fi successfully, sai na ga me zai hana mu bude wata cibiya da ta shafi masu wannan cutar, shi ne muka tattauna da su Mukhtar kuma suka amince, yanzu haka dai kungiyar ta hada komai da ake bukata, sai ta fara aiki aikace.”

“Kai ma Sha Allah. Allah Ya taimaka, wannan tunani ne mai kyau. Allah ya sanya albarka a ciki.”

“Amin.” in Asiya ta amsa, hade da mayar da hankalinta kan Hajja tana fadin “Hajjah yaronki yana kokari sosai”

“Wane yaro?” Hajja ta tambaya hankalinta a kan Asiya

“Haidar mana”

“Au Malam, kin san mu yanzu haka muke ce masa ai”

Dukkansu suka yi murmushi

“Ni kaina ina mamakin kokarin Haidar,, kin ga dai a hizif goman nan zai wahala ki ci shi gyara, ranar ina jin su da Jamil tana gwada shi, amma duk ayar da ya jawo sai ki ji ya karasa ta ya dauki ta gabanta, a jikina nake jin tabbas Haidar zai yi nasara saboda yana da mayar da hankali sosai. “

“Allah ya yarda.”

“Amin ya Rabbb ” Hajja da Jamila suka fada.

“Ni kam Hajja me ke samun kanwata ne? Ko ni kadaice nake ganin ramarta? ” Asiya ta kuma tambaya hankalinta a kan Hajja

Tabe baki Hajja ta yi cike da takaici.” Abun jiya ne dai ya, dawo, idan kana da ‘ya’ ya mata sai a hankali, yau wannan matsalar gobe wannan. Sai mu rika tunanin da mun aurar dasu mun gama da matsalarsu, sai kuma ki ga wata ta kunno kai, shi ya sa aka ce mai yaya mata baya rude kofa.”

Asiya dai kallon Hajja kawai take yi hade da sauraronta.

“kan dai maganar Kabir ce, kin san basu rabo da matsala, na ce ta hakura da shi a mayar mishi da kayanshi ta ki.”

Asiya ta yi sauran zaro ido “a mayar kuma Hajjah “

“Kwarai ma kuwa, su samar mishi mata a dangin nashi tun da abin da suke so kenan, Amma ni na gaji. Shekaranjiya wata ta kirata tana mata barazana, wai ta raba kanta da auran Kabir idan tana son kwanciyar hankali”

“Hajjah don wannan kawai kike son raba su, don Allah kar ki bari su sami abin da suke so mana?” Asiya ta fada cike da kunar zuciya

“Asiya irin wadannan fa wasu da gaske suke yi, manganin kada a yi kawai kada a fara, amma ni na gaji da matsalolin Kabir.”

“Irin wannan auran ya fi albarka ai.”

Tabe baki Hajjah ta yi ba tare da ta ce komai ba.

“To bari in tashi, wai ciwo ya ji dare.” fadar Asiya daidai tana mikewa tsaye

“Ya ce idan bai kashe ba, ai ya hana bacci” Hajja ta karasa mata karin maganar.

“Don mugun abu” Jamila ta fada cikin dariya.

Su ma dariyar suka yi.

“Bari in je in gaishe da su Umma in dauki Baba mu wuce gida.” cewar Asiya a lokacin da take tattara takardunta da ke kan kujera.

“Idan kina bukatar wani abu ki fada min kar ki damu Hajja tun da dai yanzu ba aiki take yi ba.” Cewar Asiya tana kallon Jamila

Kai Jamilar ta gyada daidai Asiya na ficewa daga falon.

Bangaren su Umma ta nufa bayan ta gaishesu ne suke fada mata Baba na wajen Adda don ta dawo.

Kai tsaye can ta nufa, cike da girmamawa ta gaishe da Addah bayan gajeruwar hira ta mike tana kiran Haidar ya kawo mata Baba.

Ya fito dauke da Baba yana fadin “Tafiya za ku yi?”

“Eh ko za ka bi mu?”

Ya yi murmushi hade da makale kafada.

Suka yi siririyar dariya ita da Addah, don ta san dama ban bin ta zai yi ba.

“Momy gida za ki tafi?” Zee ta tambaya a lokacin da ta shigo

“Eh. Za ki je ne ki gaishe da Dady”

Ita ma dariya ta yi kawai hade da wasa da hannayenta.

“Za ki je?” Addah ta kuma tambayarta tana kallon ta.

“A’a.” ta ba ta amsa hade da rufe idonta da hannayenta.

Asiya ta yi dariya hade da daukar Baba “Mun tafi gida.”

“To Allah ya tashe mu lafiya, ya kuma tsare hanya.”

“Amin” fadar Asiya daidai da fitarta.

Tamfatsetsen lace ne a jikinta mai ruwan madara, wanda aka kawata shi da adon duwatsu a ko ina.

Dinkin doguwar riga ne irin ta manyan mata, kallo daya za ka yi wa lace din ka tabbatar ko nawa aka ce an saye shi ya cancanta

Dambareriyar sarka ta dakko mai kalar ruwan gold ta daura a wuyanta sai kwalliyar ta kara fitowa sosai, tana fara daura agogo shi ma mai ruwan gold din bayan da ta daura dankwalinta ture ka ga tsiya, a daidai lokacin ne kuma wayarta da ke kan gado ta fara kara alamun kira.

Kubrah ce matar Mukhtar “Kin tafi ne?”

Abin da Kubrah ta fara tambaya kenan bayan ta daga kiran.

“Tukun na dai, ina shiri.”

“Kar fa ki manta da yi mun recording”

Dariya Asiya ta yi kafin ta ce “Kin fada ya fi sau 70 fa”

“Eh ai don kar ki manta”

“Ba zan manta ba.”

“Allah ya bayar da sa a.”

“Amin” Asiya ta fada daidai da katse kiran Kubrahr

Hira za a yi da ita yau a kan kungiyarsu mai sunan *Save life* so suke kungiyar ta bazu kowa ya santa tun da sun riga sun kammala mata komai na register.

Daidai tana sanya zobenta Hassan ya shigo sabe da Baba, shi ne ya shirya shi yau.

Fuskarta dauke da murmushi ta ce “Ka fa iya shirya yaro wallahi, yaron nan nawa ba dai kyau ba.”

“Shi kawai kika gani ban da ni.”

Ta mayar da hankalinta a kansa tana dariya, sanye yake da shadda mai ruwan Zuma, dinkin buba, sosai ya yi kyau, musamman yadda jikinsa ya cika dama ga shi da tsawo sai ya zama wani ingarma wanda ba za a gaji da kallon sa ba

“Wow! Ka yi kyau, bari mu yi hoto”

Hotuna suka yi masu yawa kala-kala.

Sannan suka fice a motar Hassan, a gate a ya aje ta sannan ya wuce da Baba cikin gida, shi kuma ya wuce kasuwa.

Misalin karfe goma kuwa a ka fara shirin mai taken *Mu gudu tare* har a gidan tv za a haska kai tsaye, da yake Asiya ba bukuwar abun ba ce, sai ba ta wani damu ba ko rawar murya wajen amsa tambayoyin da masu shirya shirin suke jeho mata.

“kamar yadda muka sanar maku, yau dai dakan daka, shikar daka tankaden bakin gado za mu yi, saboda yau bakuwar ta gida ce, amma bari ku ji daga bakinta yadda wakar za ta fi dadi” Jibril ya karasa maganar cikin murmushi hade da kallon Asiya da ita ma sautin murmushinta ya rika fita a akwatin radio da kuma na masu kallon talbijin.

“Ni dai sunana Asiya A Baba, na san sunan da muryar duka ba bakonku ba ne, muddin kuna sauraron wannan gidan radio. A takaice dai kamar yadda maigabatarwa ya umarta da in bayar da takaicitaccen tarihina, to ai ban ma yi tarihin ba, saboda ban yi komai da zan bayar da tarihin a kansa ba.” ta kai karshen zancen nata cikin dariya, ba ita kadai masu gabatar da shirin ma da yan kallo da masu sauraro sun dara.

Hakan ya sa ta ci gaba” Ni dai haifaffiyar wannan jaha ce, a nan na yi karatuna har matakin degree, sannan akwai certificate sosai dana samu a kwasa-kwasai da dama a bangaren aikin jarida, ina kuma aiki a gidan wannan radio a matsayin mai tace labarai da gabatar da shirye-shirye, ina da aure da yara uku.”

“Ma sha Allah! Tarihi kam ya kammala ke ce kike da abun fada. Ya sunan wannan kungiya taku da kuma kudirinta ko aikinta? “

Asiya ta gyara zama hade da siririyar gyaran maurya 1

“Wannan kungiya dai tamu sunanta *Save life*… “

“Ban tar bi numfashinki ba. Me ya sa aka sanya wannan kungiya wannan suna? “

“Abin da ya sa muka zabar mata kungiya wannan suna shi ne, saboda muna san mu tsaya a taren ne domin magance ma kanmu wasu matsaloli hade da wayar da kanmu a kan wani abu da bamu da masaniya a kansa, wannan kudiri shi muka dunkule ya zama ceton rayuwa.”

“To da kyau. Wannan kungiya ta su waye ne maza, ko mata ?” Jibril ya kuma tambaya hankalinsa a kan Asiya

“Wannan kungiya an kafata ne don masu cutar kanjamau wato HIV, ba kuma iya mata ba, ta kowa da kowa ce.”

“To babbar magana. Me ya ja hankalinki har kika samar da wannan kungiya”

“Abin da ya ja hankalina shi ne yadda masu cutar suke tsorata da ita a duk lokacin da suka kamu da ita, sannan suke ganin kamar rayuwarsu ta zo karshe, bayan kuma zasu iya rayuwa kamar kowa.”

Ta dan ja numfashi hade da kallon Jibril don ganin yadda yake daukar bayanan nata.
Daga nan kuma sai ta ci gaba

“Mu wayar da masu wannan cuta kai a kan zasu iya rayuwa su yi aure kuma su haihu muddin sun bi matakan da likitoci suka dorasu.”

“Lallai wannan yunkuri ne mai kyau. To wane bangare wannan kungiya za tafi mayar da hankali wajen ayyukanta?”

“Wannan kungiya za ta fi mayar da hankali ne wajen nuna masu cutar muhimmancin shan magani da, zuwa asibiti maimakon boye kansu, zamu rika hada auren masu cutar bisa shawarwarin kwararrun likitoci, sannan akwai tallafi da za mu rika ba masu cutar na jari da kuma nemar masu ayyuka in sha Allah. Akwai madara da muka tanada wacce zamu rika ba masu shayarwarmu, saboda ka san masu cutar basu cika shayar da yaransu ba kamar sauran masu lafiya.”

Gyada kai Jibril ya yi cike da gamsuwa “A bayanan ki a baya na ji kin yi maganar likitoci, kungiyar nada likitoci ne?”

“Eh muna da likitoci kwararru a wannan fanni da zamu tura marasa lafiyarmu wajensu.”

“Wannan kungiya kokarinki ne ke kadai ko akwai hada hannu da gwamnati ko wani kamfani?”

Murmushi Asiya ta yi “Ba ni kadai ba ce mu hudu ne, ciki kuwa har da mijina, sannan akwai wasu ma mata da mijin da suka kasance kawaye ne a tare damu, dasu muka hada hannu.”

“Ma sha Allah. Gaskiyar wannan kungiya zamu iya cewa kamar ba a taba samar da irinta ba duba da yadda za ta tafiyar da aikinta a wannan yanki. Kafin mu ba masu sauraro damar bugo mana waya da daukar sakonninsu, taya masu wannan cuta zasu samu su amfana da wannan kungiya taku?”

“Ta hanyar zuwa wajenmu kai tsaye ta wannan adireshi da zamu bayar da kuma wannan No, za a iya turo mana sako ko kira kai tsaye.”

Asiya ta rufe maganar tata da bayar da adireshin hade da lambar wayar

Sannan kuma Jibril ya bude layin waya inda mutane suka yi ta yabawa Asiya a kan wannan kokari hade da tambayoyi da sanya albarka.

Inda Asiya ta rika amsa tambayoyin a natse kuma cike da gamsar da mai tambayar.

Misalin 11am suka fito daga shirin inda suka ci gaba da tattaunawa da yaba masu kan wannan yunkuri har zuwa lokacin da Asiya ta shiga office don amsar abokin aikinta, inda ta dora da gabatar da shirye-shiryen rana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Labarin Asiya 14Labarin Asiya 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×