"Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!! Subhanallah! Na shiga uku!" abin da Asiya ta fara fada kenan cikin murya mai rauni bayan da ta karanta sakamakonta, lokaci daya kuma ta mike tsaye hade da kallon Hassan, shi ma ita yake kallo.
Duk da Hassan yana cikin tsananin tashin hankali ta dalilin ganin sakamakonsa, hakan bai hanashi saurin tallafe Asiya da ke shirin faduwa ba, sosai ya kuma rudewa a yayin da ya fahimci babu numfashi a tare da ita.
Ba shi kadai ba, hatta likitocin da ke wurin da patient sun firgita.
Cikin wani daki suka shigar da ita, tare. . .