Skip to content
Part 2 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un!! Subhanallah! Na shiga uku!” abin da Asiya ta fara fada kenan cikin murya mai rauni bayan da ta karanta sakamakonta, lokaci daya kuma ta mike tsaye hade da kallon Hassan, shi ma ita yake kallo.

Duk da Hassan yana cikin tsananin tashin hankali ta dalilin ganin sakamakonsa, hakan bai hanashi saurin tallafe Asiya da ke shirin faduwa ba, sosai ya kuma rudewa a yayin da ya fahimci babu numfashi a tare da ita.

Ba shi kadai ba, hatta likitocin da ke wurin da patient sun firgita.

Cikin wani daki suka shigar da ita, tare da fesa mata ruwa, har zuwa lokacin kuwa tana tallafe a jikin Hassan.

Halin da take ciki ya fi daga mishi hankali fiye da ganin sakamakonsu.

Tsawon mintuna goma ta janyo numfashi mai karfi, kafin daga bisani ta bude idonta a hankali, hade da bin mutanen da ke kanta da kallo daya bayan daya, har ta dire a kan Hassan.

Ta kafe shi da ido, kallon da ya kasa gane ma’anarsa, har sai da ya yi amfani da hannunsa wajen juya wuyanta zuwa wani bangaren.

Don kuwa kallon ya fara wuce hankali, kama yake da na wacce ta zauce.

Kowa sannu yake mata, amma babu wanda ta bude baki ta amsamawa, har zuwa lokacin da ta saki kuka mai sauti, a cikin kukan kuma take fadin.

“Na shiga uku, wayyyo Hajiyata, zan mutu, ni ba yar iska ba, an kwaso cutar yan iska an sanya mun, wallahi ban taba zina ba, wayyyo Allahna, wayyyo Allahna! Allah ka taimakeni, kai ma ka san ban taba zina ba wallahi, ni ba yar iska ba ce.” Ta kai karshen maganar tata cikin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Duk ma’aikatan wajen jikinsu ya mutu, tausayin Asiya ya bayyana karara a kan fuskarsu, yayin da matan wajen masu saurin kuka suka fara kukan tausayawa Asiya.

Tuni Hassan ya muzanta, musamman irin kallon da matan ke yi masa mai kama da na ganin danyen kashi a tsakiyar damuna.

Har zuwa lokacin kuwa Asiya kuka take yi hade da surutan da ba ta san ma tana yin su ba.

“Fita waje please, ina son za mu yi magana da ita” Babban likitan da ke wajen ya fadawa Hassan.

Kamar maciji haka Hassan ya sabe zuwa waje.
Zuciyarsa cunkushe ya rasa kalar tunanin da zai yi, kallon da mutanen wajen suke masa duk bai damesa ba, a kan halin da Asiya take ciki.

Allah kadai ya san yadda yake ji, da ace yana da dama, to daya karbi cutar jikin Asiya ya hada da ta shi, sannan ya sawwakewa Asiyar ta auri wani, shi kuma ya rayu da cutar.

Duk da ba shi da masaniyar ta inda suka sameta. Kamar yadda Asiya take fadar ba ta taba zina ba, shi ma a bangarensa haka ne.

Ruwa mai sanyi likitan ya mikawa Asiya. Girgiza kai ta yi alamar a’a, har zuwa lokacin kuwa kuka take yi sosai.

“Please ki sha.”

Ganin ya matsa mata ne ya sa ta dan kurbi kadan.

“Ki kara kadan, yi hakuri kanwata.”

Ba musu ta kuma kara kurba

“Yauwa ki kalli yadda zan yi, ke ma ki yi haka, sannan ki rika karanta Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un a cikin zuciyarki.”

Kai kawai ta daga mishi.

Ya sa hannu saitin kirjinsa ya dafe, ita ma ta yi hakan.

Ya lumshe idonsa, sannan ya ce “Ke ma ki rufe idonki, ki rika jan numfashi a hankali kina karanta abin da na ce miki, sai na ce ki bude ido sannan ki bude. Oya you can start now. 1, 2, 3…”

Ya ci gaba da kirgan yayin da Asiya take yin abin da ya ce mata.

Kamar mintuna biyar ya umarci ta bude idon.

“Ya kike ji yanzu?”

Numfasawa ta yi kadan ba tare da ta ce komai ba.

A zahiri kam ta ji zuciyarta ta rage nauyin da ta yi mata, sannan ta daina bugawa da sauri kamar baya.

“Asiya!” Likitan ya kirata.

Wannan karon ma ba ta amsa ba, kai kawai ta dago tana kallonsa.

“Ki natsu da kyau ki ji abin da zan fada miki, H. I. V cuta ce amma kuma akwai cututtukan da suka fi ta hatsari, mutane da yawa suna rayuwa da H. I. V sai sun fada miki ne za ki sani. Suna aure suna haihuwa, don haka ya kamata ki dawo cikin hankalinki, cutar ba ta son yawan damuwa, idan kina saka damuwa a ranki shi ne za ta yi tasiri a jikinki.”

Ya tsagaita hade da kallon yadda take ta share hawayen da ke zarya a kan kumatunta, yayin da sautin kukanta ke fita a hankali tamkar amaryar da ake wa fadan zuwa gidan miji.

Ita ba wannan ke damunta ba, ai da ace ma tun farko ta ballagazar da kanta ne ma wani abun ba zai dameta ba, don kuwa an ce amfanin zunubi romo, amma haka kawai ba ta ci nanin ba nanin ta ci ta.

“Idan kina da wannan cutar ba yana nufin rayuwarki ta zo karshe ba, cutar tana yin tasiri ne a jikin mutum idan ba a shan magani a kan lokaci, abinci mai gina jiki da kuma yawan damuwa.”

Har yanzu kukanta take yi, amma da alama tana jin duk abin da yake fada mata. Dalilin da ya sanyashi ci gaba kenan.

“Na yi miki alkawari zan kula da lafiyarki, zan taimakeki da duk abin da kike bukata a fannin lafiyarki, amma ki taimaka ki rage damuwa. Kina jina ko? Don sai kin yi haka ne duk wani kokarina zai yi tasiri a kanki.”

Ta kuma jinjina kai alamar Eh.

“Yanzu ki je gida ki natsu, zuwa gobe ko jibi, ki dawo nan za mu yi magana, zan fada miki yadda za ki kula da kanki. Kin gane?”

A wannan karon ma kan ta kuma daga mishi, hade da mikewa ta nufi hanyar fita.

Hassan da tun da ya fito ya kasa zaune bare tsaye, yawo kawai yake yi kamar macen da aka saki sauran So.
Kwakwalwarshi ta toshe gabadaya, ya rasa a ina suka samu wannan cutar, shi dai ya san bai taba yin zina ba, ita ce dai hanya mafi girma da aka sani mai yada wannan cutar.

“Rabin Raina!” Ya yi saurin kiran sunanta, bayan da ya isa wajenta

Ba ta amsa ba, tashin hankali ne kwance a kwayar idonta da kuma tsananin tsanarsa, sosai kuwa hakan ya kara daga mishi hankali.

Ganin tana kokarin tare mai keke ne, ya sa shi saurin cewa

“Mun zo da mashin fa. Ina kuma za ki je?”

Ko kallonsa ba ta yi ba.

“Rabin Raina! Wallahi ba ni da hannu a wannan al’amarin, ni ma result nawa ya nuna ina dauke da cutar don Allah ki saurareni, zuciyata kamar za ta fashe nake ji, kin san bana son damuwarki.”

A wannan karon ma ba ta kalleshi ba, bare ya sa ran za ta ce wani abu.

“Asiya! Ya kira sunanta cikin muryar da ke nuna yana cikin damuwa sosai.
“Please ki yi mun magana, halin da kike ciki ya fi daga mun hankali fiye da ganin sakamakonmu.”

A daidai lokacin ne kuma wani keke ya tsaya, ba ta bata lokaci ba ta shige.

Hassan ma da sauri ya nufi mashin dinsa hade da bin bayansu.

Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin ta nufi hanyar gidan iyayensu. Tashin hankali wai gobarar gemu.

Tsananin tashin hankalin da Hassan yake ciki ba zai misiltu ba, ji yake tamkar tashin kiyamarsa ne ya tsaya, bai taba tunanin irin wannan ranar za ta riskeshi ba a rayuwarsa.

A cikin kaddarorin da wani lokaci yake tunanin zasu iya samunsa, ko Allah ya jarabceshi babu cutar Kanjamau a ciki.

“Kanjamau!” ita ce kalmar da yake maimaitawa ku san ko wace dakika daya.

Tuki kawai yake yi ba tare da kiyaye wasu ka’idojinsa ba, Allah ne kawai ke tsaresa.

Har yanzu keken da Asiya take ciki yake bi, cike yake da fargabar kar ta je gidansu ta fasa wannan ƙwan, mai matukar wari da tayar hankali gami da sarkakiya.

Ganin keken nasu ya tsaya ne, ya sa shi ma ya yi saurin take burki a gefen hanya ya nufi wurin keken.

“Hajiya yi hakuri ki sauka.” Mai kaken ya fada bayan ya waigo inda take.

“In sauka kuma, ai ba nan na ce ka kawoni ba.” cikin muryar kuka ta yi maganar.

“Na fasa kai ki.”

Kafin ta yi magana Hassan ya iso.

“Me ya faru?” ya tambayi mai keken hade da kallonsa.

“Ba komai, na ce ta sauka ne, saboda ta cika mun kunne da kuka, kar ma a yi zaton sato ta na yi.” cewar mai keken hankalinsa a kan ababen hawan da ke wucewa.

“Ki sauka Hajiya kina ɓata mun lokaci.”

Jakarta hade da laptop dinta ta dakko, wanda Hassan ya yi saurin karbewa.

Shi kuma mai napep din ya ja ba tare da ya karbi ko sisi ba.

“Zo mu je.”

Shiru ta yi, haka ba ta motsa ba daga inda take ba. Sai dai hannunta da yake ta zarya a kan kuncinta alamaun share hawaye.

Ya marairaice, irin marairaicewar da ya san idan har ya yi ta, to tabbas ya kan sauke Asiya daga dukkan wani fushin da take yi da shi.

Amma a wannan karon ko a jikinta, wai an tsunkuni kakkausa. Duk kuwa da idanunta a kan fuskarshi suke.

“Ina cikin tashin hankali, alkalami da takarda ko fatar baki sun yi kadan su fasaltashi. Na rokeki ki taimakeni ki biyoni mu je gida mu yi magana.”

Ya zuba mata idanunshi cikin matsaikaicin hasken da ya gauraye bakin titin.

Hawaye ne kawai ke sauka a idonta, hawayen da Hassan yake jinsu tamkar ana tsaga kirjinsa ne da sabuwar reza.

Ganin ba ta da niyyar magana ya kuma dorawa

“Asiya! Kin manta ke ce kika sha fada mun cewa, idan kowa zai gujeni don wani abu ke za ki kusance ni, idan zan waiga bayana in ga ba kowa to tabbas zan same ki, ba za ki taba juya mun baya ba, komai munin laifina a gareki.”
Ya kuma kallonta don ganin yadda take daukar maganarsa.

“Da haka na sakankance Asiya, na mika miki dukkan ragamata, ki ka kirani da Rabin Ranki, ni ma kika sanya na ji ke ce Rabin Ran nawa, sunan Rabin Rai ya yi tasiri a gareni Asiya,, ina jin ina rayuwa da Rabin Raina ne, yayin da rabin yake a wajenki, kin san yadda tashin hankalinki yake daga mun hankali, please Asiya ki daure ki ba ni dama da kwarin gwiwar warware wannan matsalar.”

Zuwa yanzu jikinta ya fara sanyi, inda sautin kukanta ya canja zuwa tsananin kaunarsa da jin abin da yake ji.

Dalilin da ya sa kenan ya kuma raunana muryarsa

“Ba tun yanzu ba, kin sabar mun tare muke magance matsalolinmu, yayin da wani lokaci nake kwantawa ke ki magance, me ya sa yanzu kike son guduwa a lokacin da nake bukatarki, ina wadancan alkawuran na ba za ki guje ni ba? Asiya ki taimaka ki saurareni please. “

Duk da ba ta yi magana ba, ta juya zuwa wajen mashin din nasa.

Allah ya sani tana son Hassan, shi ne namiji na farko a duniya da ta fara So, ba ta kuma taba hada soyayyarsa da wani ba, ba ta iya jure ganinsa cikin damuwa, ko wane irin laifi zai yi mata muddin za ta ga damuwa a tare da shi, da wuri take yafe masa.

Wannan shi ne ma fi munin laifi da ya taba aikata mata, da ya aureta bayan ya san yana dauke da cuta, bai yi wa So adalci ba. Ba ta jin za ta iya yafe masa wannan.

Har ya ja mashin din Asiya tunanin da take yi kenan.

*****

Suna isa gida kan 3 sitter ta fada yaraf kamar tuwo yay ɗanye.

Bai damu da hakan ba, bedroom ya wuce ya aje mata kayanta inda ya san tana ajiyewa.

Toilet ya shiga, ruwan wanka ya hada mata mai dan zafi, sannan ya kamo hannunnta zuwa toilet din, ya mika mata towel sannan ya ja mata ƙofar.

Duk da irin kunci da rashin jin dadin duniyarta da take ji a wannan lokacin, hakan bai hana ta ji dadin jikinta ba bayan da ta yi wankan, alwala ta yi sannan ta fito.

A bakin gado ta sameshi hannunsa rike da cup, tana zuwa kuwa ya mika mata.

A wannan karon ma ba ta yi musu ba, rabin tea din ta sha, ta aje rabin a kan lokar gado.

A daidai lokacin shi ma ya fito daga toilet bayan ya yi alwala, sai da ya fara duba cup din da ta aje, kafin ya kabbara sallah, magriba isha’i gami da shafa’i da wutri ya yi.

A lokacin kuwa Asiya karatun kur’ani take yi kamar yadda ta saba yi kullum kafin ta kwanta bacci.

Shi ma Kur’anin ya dauka ya fara karantawa.

Yana kallon yadda take hamma, wannan ya tabbatar mishi da maganin baccin da ya sanya mata a cikin tea ya fara aiki.

Sosai baccin ya ci karfinta, dalilin da ya sa kenan ya kama hannunta zuwa gado, shi ya tofa mata addu’a, hade da zama a gefen gadon, tun tana jin yadda yake matsa mata kafafu har bacci mai nauyi ya dauketa.

Ido ya zuba mata yana kallonta sosai tausayi take ba shi, da yana da dama, tabbas da ya kwashe duk damuwarta ya maido kansa, saboda ya san idan har tana cikin farin ciki shi ma zai kasance a ciki.

Rashin son damuwarta ne ya sanya shi sanya mata maganin bacci a cikin tea, sannan ko ba komai yana son ya samu damar yin tunani a kan wannan al’amari mai kama da tatsuniya a nutse, don idan har idonta biyu kara tayar masa da hankali kawai za ta yi da koke-koken ta.

A hankali ya mike hade da goya hannayensa a baya, hakika ya san yana son Asiya, so irin wanda ba zai misiltun nan ba, amma kuma hakan ba zai sanya ya aureta bayan ya san yana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki ba.

Ya kuma nisawa hade da shafa kansa da hannunsa daya.

Maganar gaskiya shi ne bai san yana dauke da wannan cutar ba idan ma shi ne ya sanya mata, saboda bai taba zina ba, shi ya sa ma bai karfafa maganar zuwa yin test kafin aure ba.
Don zina ita ce hanya ma fi kusanci da wannan cutar.

Hatta iyayensa ma basu karfafa maganar test kafin a daura masu aure ba. Kila hakan baya rasa nasaba da ganin tushe daya suka fito shi da Asiya, tarbiyya iri daya aka basu, bugu da kari iyayensu sun yarda dasu.

Ya san yarintar Asiya har zuwa girmanta, kuma tabbas shi ne ya fara saninta diya mace, ba zai manta wannan ranar mai dumbin tarihi ba.

Yayin da ma fi yawan mata kan zubar da darajarsu a waje, musamman wadanda suka yi karatu mai zurfi, ita ta shi matar ta kawo mishi tata darajar har dakinsa, duk kuwa da kasancewar ta yi karatu mai zurfi.

Ya san akwai hanyoyi da yawa da ake kamuwa da wannan cutar, amma wacce mutane suka fi karfafawa ita ce zina.

A dai nan arewa idan har za a samu mutum da wannan cutar to kallon mazinaci ake mishi.

Da wane ido zai kalli mahaifiyar Asiya a yayin da ta ji yarinyarta na dauke da cutar Kanjamau.

Matar da ita ce tsanin da ya taka ya kai inda yake a yanzu, ta nuna mishi so, ta yi mishi halacci, ta hidimta mishi da jikinta, aljihunta, da duk wani abu da take da shi.

A bangare daya tana masifar son Asiya fiye da sauran yaranta, shi shaida ne a kan son da takewa Asiya, duk wani abu da ya shafi Asiya ba ta daukarshi da sauki.

Idan har Asiya za ta nuna tana son abu to kuwa za ta mallaka mata shi muddin bai sabawa addini ko al’ada ba.

Ba mamaki hakan baya rasa nasaba da sai da ta yi miscarriage biyu, da haihuwa biyu duk ba yaran sannan ta samu Asiya.

Ta yarda da shi ta yadda ba zai iya kwatanta girman yardarta gareshi ba.

Yadda ta amince da shi ne ma ya sa ta yi uwa kuma ta yi makarbiya a auransa da Asiya.

Yanzu kam abun kunya ne *kashi jan kare* ya tunkareta da batun Asiya na da ƙanjamau, ba mamaki ma ta fadi sumammiya.

Ya kuma nisawa a karo na ba iyaka, har yanzu kuwa a tsaye yake *kamar ya kada suruka* .

Mahaifiyarsa ya tuna, mace mai alkunya, mai yawan ibada, ta jajirce sosai ganin sun zama na gari, ta yi mishi kyakkyawar shaida, don lukuta da dama ta kan karesa daga wani laifi tun ba ta ji daga bakinsa.

Tun a lokacin da ya mallaki hankalinsa fadan Umma ba ya wuce kan zina, sata da shaye-shaye.

Ta sha fada masu idan dai ɗa nata ne, ita ce ta dauki cikinsa wata tara, ta haifesa ta rainesa har zuwa girmansa, sannan ya je aikata zina Allah ya isa tsakaninta da shi.

“Subhanallah!” ya fada da sauri kuma a bayyane

Ta wace hanyar zai fada mata suna da ƙanjamau? Lallai zama bai gan shi ba, Wai an saci dan ɓarawo.

Dole ya nemo mafita, don babu wanda zai amince tsakanin shi da Asiya wani bai taba zina ba.

Abu daya ya sani shi ne, ko ina sai bayyana cewa a cikakkiyar mace ya samu Asiya.

Kiran sallahr asuba ne ya sanyashi katse tunanin nashi ba don ya zo karshe ba.

Don zai iya karasa rayuwarsa da wannan tunanin hade da nemar mafitar wannan cakwalkwalin caɓindon rikicin ba tare da ya samo mafitar ba.

Har sallar dare ya so yi amma sam baya cikin natsuwar da zai yi sallahr, ko ya kabbarata tunaninshi ne zai rinjaye shi.

Ya zubawa Asiya ido da ke bacci, fuskarta kawai za ka kalla ka fahimci baccin na dole ne, amma hakan shi ne ya fi, ko ba komai idonta zai rage nauyi idan ma zuciyarta ba ta rage ba.

<< Labarin Asiya 1Labarin Asiya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×