Skip to content
Part 1 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bismillahir-rahmanir-rahim

Lura: Wannan labari kagaggene, ba a yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, idan ka/kin ji sunanki, an yi amfani da shi ne kawai ba don cin zarafi ko ɓatanci ba.

Idan an faɗi wani abu da ya yi kama da halinki/ka arashi ne kawai. Allah ya amfanar damu abin da zamu karanta amin.

Asshi-Fah Clinic

Asiya sanye cikin doguwar riga (abaya) mai kalar ja, kanta nade da ɗankwalin rigar, wanda hakan yaba kyakkyawar fuskarta mai dauke da matsakaiciyar kwalliya damar bayyana.

Kafarta sanye cikin takalmi fari mara tudu, ba komai a hannunta idan ka dauke karamar purser baka. Kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar wayayya ce ta bangaren ilmin zamani da kuma gogewa a cudanya da mutane. Mutane hudu ne kacal zaune a reception (wurin jira) din, hannu ta daga masu alamar gaisuwa suma suka mayar mata kamar yadda ta yi.

“My file no is 853 (lambar fayel dina ita ce 853)” Asiya ta fada bayan ta shiga dakin da ke dauke da file din duk wani mara lafiya da ke zuwa asibitin.

“Health insurance ne?” Nurse din ta tambaya hade da kallon Asiya.

“Eh.” Asiyar ta ba ta amsa a taikace.

Mintuna biyar Nurse din ta dago kai a karo na biyu ta kuma kallon Asiya.

“Ban ga file naki ba, kin tabbatar yana nan kuma?”

Bayan ɗan ƙaramin nazari Asiya ta ce, “Ranar Wednesday na zo awo, kuma sun tura ni lab yin test ban sani ba ko basu dawo da file din ba.”

“Ciki ne?”

“Eh.” Asiya ta kuma bayar da amsa.

“Ok, ki je kika ga Doctor. File din duk su wajensa, idan kin je sai ki fada masa sunanki.”

“Thanks” Ta fada a daidai lokacin da ta nufi hanyar da zai sadata da ofishin likitan.

Mutane uku ta taras a layin ganin likitan, dalilin da ya sa kenan ta fitar da wayarta hade da bude data ta shiga duniyar gizo.

Sosai ta nitsa a binciken da take yi, wanda har layi ya zo kanta ba ta sani ba, sai da ta kusa da ita ta ankarar da ita.

Bayan ta zauna kujerar da ke fuskantar likitan ne, ta amsa tambayar da ya yi mata.

“Asiya A Baba.” ta ba shi amsar tambayarsa.

Wasu files ya janyo, cikin sakanni ya lalubo nata. Lokaci daya kuma ya fara nazari a kansa, har zuwa lokacin da ya jefo mata tambayar.

“Kina da aure?”

“Eh” ta ba shi amsa.

“Kin taɓa haihuwa?”

“A’a”

“Mijinki yana nan?”

“Eh” ta kuma ba shi amsa cike da mamakin tambayoyin nasa.

Shiru ya dan ratsa wajen, yayin da likitan ya zubawa file din nata ido.

“Kun yi test kafin auranku?”

Wannan karon tambayar tasa bayan mamaki har da haushi ta ba ta, wane irin tambayo ne na ya ya uwarka ta haifeka, sun yi ba su yi ba. Ina ruwan biri da gada idan ba shiga uku ba takabar suruki fita da kyar.

Ganin ya zuba mata ido da alama amsarta yake jira ne ta ce, “A’a.” lokaci daya kuma ta kawar da kanta gefe cikin daure fuska.

Yayin da shi kuma ya zuba mata ido hade da karkada biron da ke hannunsa.

Duk da ya fahimci ta gaji da amsa tambayoyin da yake mata hakan bai hanashi kara jefa mata wata tambayar ba.

“To me ya sa ba ku yi ba?”

Wannan karon baki bude da ke nuna alamar mamaki ƙarara lokaci ɗaya kuma ta nutsa kyawawan idanunta a cikin nasa tana masa kallon wai me ye nasa a ciki?

“Haka nan.” cikin zunɓura ba ki ta ba shi amsar

Murmushi kaɗan ya yi, saboda yadda ya ga ta ba shi amsar.

“Result din ki a nan ya nuna kina dauke da kwayar cutar H.I.V koda ma kin sani?” Kaf! Ya tattara hankalinsa a kanta wannan karon.

Jin maganar ta yi yif! Kamar fadowar gini.

“H.I.V! Ƙanjamau fa kenan.” ta yi maganar ita ma hankalinta a kansa. Ganin ya zuba mata ido babu kuma alamar wasa ya sa ta kuma kara cewa,

“Wai kana nufin Ƙanjamau gare ni, anya kuwa file ɗina ne?”

“Na ki ne mana.” Ya yi maganar haɗe da tura mata file din zuwa gabanta.

Karanta abin da ke kan file din ta rika yi har zuwa inda aka rubuta tana dauke da cuta mai karya garkuwa jiki, cikin sauri ta dago ganta, hade da zubawa likitan ido.

Kafin daga bisani ta yi wani irin murmushi mai dauke da ma’anoni masu yawa.

“H.I.V! Ina! Ba zai yiwu ba sam, a ina zan samu wannan cutar? Kai! Karya ne wallahi.”

Duk a zahiri take maganar ba tare da ta sani ba, shi ma likitan bai ce mata komai ba illa kallonta da yake yi.

Shiru ya ratsa wajen, da alama kowa da abin da yake tunani, ita dai Asiya mamaki ne hade da tsoro ke kai kawo a cikin zuciyarta.

“Be patient (bi a Sannu) akwai cututtuka da suka fi wannan cutar hatsari don haka ki natsu zan yi miki wani jawabi.” cewar likitan yana kallon Asiya.

Dalilin da ya sa kenan ta maido da hankalinta kansa, hade da zuba mishi manyan fararen idanunta.

“Jawabi! Jawabin me to? Ni karya kuke ba ni da wannan cutar saboda ban biyo wata hanya da zamu hadu da ita ba, na san kaina haka mijina na san halinsa mutumin kirki ne, ba zai taba dakko wannan cutar ya sanya mun ba.”

“Asiya!” Likitan ya kira sunanta a kokarinsa na san janyo hankalinta ta sauraresa. Saboda ya fahimci yadda kwata-kwata jikinta ya nuna ba ta gamsu ma tana da cutar ba.

Ita kuwa sosai take jin haushinsa, babu wanda ya taba raina mata wayau irinsa, ta yama za a yi ya dubi tsabar idonta ya ce wai tana da kanjamau. Cutar da sai a jikin yan iska marasa daraja ake samunta.

Dalilin da ya sa kenan ba ta amsa kiran da ya yi mata ba, illa dai ta bi shi da idanu, wadanda babu komai a cikinsu sai kallon da ke nuna mishi ya raina mata hankali

“Ita fa wannan cutar ba dole sai a harkar banza ake samunta ba.” Ya ɗan tsagaita yana kallonta gami da nazarin yadda take ɗaukar maganar tasa.

Aiko wani irin kallo take mishi irin na ta raina basirarsa, ko kuma ma dai ba za ta ɓata lokacinta wajen sauraron abun da yake son faɗa mata ba. Taɓe baki ta yi, haɗe da jan dogon tsaki, lokaci ɗaya kuma ta mike tare da dauke file dinta ta yi waje cike da tsanar asibitin.

Yayin da kuma zuciyarta ke cike da fargaba da tsoron kar wannan abu ya kasance gaskiya, wanda kuma ta san ma ba zai taba kasancewa ba.

Saboda babu wata kofa da ta bi, wacce za ta sadata da wannan cutar, kawai likitan ya gama raina mata hankali ne.

A daidai lokacin da take tsaye bakin hanya tana jiran abun hawa ne, ta lalubo wayarta, lokaci daya kuma ta kangata a kunnenta alamun tana kira.

Twins Store

Babbar motar daukar kaya ce, tsaye a bakin store din,, yayin da ma’aikata ke ta sauke lodin da ke cikinta suna shigarwa a babban store din da ke manne da Twins Store din.

A can gefe jikin wata bishiya Hassan ne tsaye tare da wasu mutane uku, da alama abokan kasuwancinsa ne. Za ka fahimci haka ne ta yadda hankalinsu ke kan kayan da ake saukewa, wani lokaci ma su kan taimaka wajen gyara wasu ko kirgawa. Jin karar wayarsa ne ya sanyasa komawa gefe kadan ganin sarauniyar zuciyarsa ce ta kira.

“Rabin Raina!” abin da ya fara fada kenan bayan ya daga kiran.

“Na’am Rabin Raina” daga can bangaren aka ba shi amsa.

“Har kin dawo daga asibitin ne?”

“Eh gani a hanyar gida ma, don Allah ko me kake yi ka bari ka zo mu hadu yanzu.”

“Lafiya, akwai matsala ne?” ya yi saurin jero mata tambayoyin a tare.

“Kai dai kawai ka zo.” Ta karasa maganar hade da katse kiran.

Ya zuba ma wayar ido, cike da tunanin me ya sa Asiya ta ce ya zo gida yanzu.

Tsawon mintuna biyar bai tuno komai ba, hakan ya sa ya juya wajen abokansa hade da rokarsu alfarmar zai je gida ya dawo.

Farin lifan mashin ɗinsa ya hau, wanda koyaushe yake fes saboda kulawar da yake samu.
Tuki yake yi amma ba nutsuwa sosai, iya tunaninsa bai iya tuna matsalar da zai sa Asiya ta ce ya dawo gida ba. Akwai yanayi da ya ji a muryarta da ke ƙara masa fargaba.

Saboda tare suka fita, ya sauke ta a asibiti, shi kuma ya wuce kasuwa saboda zuwan kayansu. Sannan lafiya kalau ya rabu da matarsa, babu wani alamun ciwo ko damuwa a tare da ita.

Amma a yanzu duk da bai ga fuskarta ba, muryarta ta nuna akwai matsala

Tana bude kofar shiga corridor, shi ma ya bude gate din gidan ya shigo da mashin dinsa.

Tun da ya shigo ta zuba mishi ido, jikinsa bai nuna alamar yana dauke da irin wannan cutar ba. Hasalima kara cika yake yi, jikinsa na mulmulewa wanda hakan ke nuna hankalinsa kwance yake ba shi da wata damuwa mai yawa.

Yadda take kallon sa haka shi ma yake kallon ta, so yake ya gano wani canji a fuskarta, amma ya kasa gane hakan har zuwa lokacin da ta gama bude kofar ta shige ciki. Kan kujera ya sameta zaune, yana isa kuwa ko zama bai yi ba ta mika masa file din ba tare da ta ce komai ba.

“Na me ye?” ya tambaya hade da kallon ta cikin son karin bayani.

“Duba mana.” ta ba shi amsa ba tare da ta tsawaita a kallonsa ba.

Bude file din ya yi ya fara karantawa har zuwa inda ya ji kafarsa kamar ba za ta iya daukarsa ba.

Dalilin da ya sa kenan ya rufe file din hade da kallonta a firgice, ita ma shi take kallo.

Shiru ya ratsa wajen, kafin Asiya ta yi karfin halin cewa.

“Ka fahimci result din kuwa?”

“Wane ɗan iskan likita ne ya ba ki wannan abun? Ya haukace ne? H. I. V fa ya ce kina da.”

Ajiyar zuciya Asiya ta yi mai karfi tare da shafa kanta, lokaci daya kuma ta jingina bayanta da kujera hade da lumshe ido. Don ba ta san amsar da za ta ba shi ba.

“Ta shi mu je wurin likitan, sai ya fada mun waye ya ba shi kwangilar bata mun aure. Kanjamau!!! What nonsense? Mtswww! Please let’s go, ba zan taɓa barin wannan ya wuce ba.”

“A ina za ki samu wannan cutar? Sai dai idan result din wata aka ba ki, wai me ya sa likitocin nan basu da hankali ne? Ƙanjamau fa!”

A kan hanyarsa ta fita yake ta maimaita wannan.

Ba ja wai kare ya mutu a saura.  Asiya ta kuma yafa gyalen rigarta ta bi bayansa kamar jela

*****
Tun da suka isa kofar ofishin likitan Hassan ke safa da marwa cike da bacin rai, ya kasa tsaye bare zaune, yawo kawai yake kamar dokin suga, har zuwa lokacin da wanda ke a cikin office din ya fito.

“Kai ne ka ba matata wannan sakamakon, ka fada wai tana da ƙanjamau?” abin da Hassan ya fara fada kenan idonsa a kan likitan bayan da ya shiga ofishin.

Ido likitan ya bi Hassan da shi hade da nazarin fuskarsa, wacce bacin rai da tashin hankali ya bayyana karara a kanta.

“Please have seat.” likitan ya fada a natse hade da nuni da hannunsa na dama. Yana ganin hakan ne kawai zai sanya Hassan din ya dan samu natsuwa su tattauna.

“Kawai ka amsa mun tambayata.” Cewar Hassan jajayen idonsa a kan likitan, ba tare kuma da yayi niyyar zama ba kamar yadda likitan ya bukata.

“Ba ni ba ne.” Likitan ya amsa tambayar hade da sosa saman idonsa a hankali yana duban Hassan

Asiya da mamaki ya kashe ta jin amsar da ya bayar ta yi saurin cewa “To waye?”

“Gwaji ne ya nuna hakan.” likitan ya kuma basu amsa yana kallon su.

Wannan karon Asiya da Hassan saurin kallon juna suka yi da wani irin yanayin da ke nuna kamar likitan na son raina masu hankali.

Lokaci daya kuma suka mayar da kallonsu a kan likitan

“Kai! Ka kalleni da kyau, na fi karfin ka yi wasa da hankalina. Ni ba jahili ba ne, kalleni da kyau, na yi ma kama da mai neman mata? Ko matata ta yi ma kama da irin matan nan marasa kamun kai? Da za ka dauki wani result na banza ka ba ta.” cewar Hassan rai bace.

“Oh God! Shi ya sa na ce ka zauna?” likitan ya fada hade da nuni da kujerar da ke fuskantar sa.

“Ba zan zauna ba, kawai ka fada mun waye ya ba ka kwangilar bata mun aure?”

“Na san lokacin da aka daura auranku ne bare in raba maku shi? Just have a seat let’s talk please.”

“Idan ba ka sani ba, ai shi wanda ya dauki hayarka ya sani…”

“Ka zauna sai mu canja test din a gabanku.” likitan ya yi saurin katse Hassan.

“Ai ko an canja, labarin gizo ba zai wuce ƙoƙi ba. Sai dai ina son ka sani zan canja wuri, idan result din nan ya fita different da naku, I’m telling you and I’m telling you that sai na yi karar asibitin nan.”
Daga fadin haka ya fice daga ofishin.

Asiya da ke tsaye kamar ta kada suruka ta bi bayansa jiki a mace kamar kazar da kwai ya fashema wa.

Likitan ya zubawa kofar da suka fita ido, daga bisani ya tabe baki hade da daga kafadunsa sama. Wayarsa ya da ke aje a kan tebur ya dauka, dakin gwajin ya kira don tabbatar da result din Asiyar ne ko akasi aka samu kamar yadda suke zargi.

Kallon mijin nata kawai take yi, yanayinsa ya canja sosai, idanuwansa sun yi jawur yayin da jijiyoyin jikinsa suka fita raɗa-raɗa, wannan yake nuna sosai yana cikin ɓacin rai.

Ta san halinsa idan yana a irin wannan yanayin baya son magana, dalilin da ya sa kenan ta kame bakinta, duk da ta fahimci ba hanyar gidansu suka nufa ba.

Amma ba ta tambayi ina zasu je, ido kannen kai.

Wani private lab suka je, a gabanta Hassan ya yi masu jawabin komai, aka debi jininsu don yin gwajin kamar yadda suka bukata.

Hassan ya tabbatar masu yana son result din nan da karfe biyar na yamma, inda suka tabbatar masa babu wata matsala a kan hakan.

Shi ya kai ta gida ta yi shirin zuwa aiki, kasancewar tana aiki da gidan radion Jaha ne, kuma ita ce za ta karbi aiki da misalin 12:30pm

Har suka rabu babu hwata maganar kirki da ta shiga tsakaninsu, kowa da abin da yake tunani a zuciyarsa.

A wurin aiki ma Asiya ba ƙaramin kokari ta yi wajen boye damuwarta ba, amma hakan bai hana lokaci zuwa lokaci ta yi shiru alamar tunani.

Don kuwa a cikin abokan aikinta wadanda suka tambayeta ko lafiya sun kai mutum uku.

A bangaren Hassan ma tunani shi ya cinye rabin kasuwancinsa na wunin ranar, zuciyarsa a bace komai baya masa dadi, shi ya sa daga karshe ya koma gefe ya barwa Ashiru (yaronsa mai tayasa zama) kula da kostomomi. Baya son hayaniyar kwastomomin, duk da baya iya tuna komai amma dai kadaicewar ta fi yi masa dadi.

Musamman da kansa ke wani irin ciwo kamar zai fashe.

Yayin da lokaci ba ya mishi gudu, ya kosa biyar ta yi, ya ɗakko Asiya su karbi sakamakonsu.

Tunanin court din da zai maka likitan nan kawai yake yi, idan har ya tabbata basu da wannan cutar.

To a ina zasu sameta, shi dai ya san bai taba kebancewa da wata mace ba face Asiya, kuma ko ba ka son mutum ba za ka ce mazaunansa daya ba, Asiya ba za ta taba mikawa namiji kanta ba.

Kwararren lauya zai ɗauko ta yadda zai yi fata-fata da asibitin daga karshe kuma a kulle asibitin gaba daya.

Ganin zaman da yake yi kamar shi ne ya hana lokacin tafiya da sauri, ɗaukar key ɗin mashin ɗinsa ya yi, ya fice don zuwa daukar Asiya.

Kusan da yawan ma’aikatan gidan radion sun san Hassan don kuwa tun kafin Asiya ta yi aure yana kawo ta, yana kuma zuwa daukarta, sannan kowa ya san irin soyayyar da ke tsakanin su, Asiya ba ta boye soyayyar da take wa Hassan.

Wannan dalilin ne ya sa kowa ya san shi, yanzu zaune yake da biyu daga cikin security din da ke aiki a kofar shiga gidan radion suna hira.

Tun da ta fito ya zuba mata ido. Ta yi fresh da ita,, dirinta ya kara fitowa sosai, fuskarta ta cika gwanin sha’awa.

“Anya likitan nan ba son yarinyar nan yake yi ba?” ya yi ma kansa tambayar a bayyane

Lokaci daya kuma ya mike don tararta.

Ba ko wane lafiyayyen namiji ne zai dora idonsa a kan Asiya ya kuma iya hadiye yawunsa a kanta ba ya wuce.

Ya sha artabu da samari kafin ta zama mallakinsa, ko a wurin aikin ma ta taba yi ma sa complain wani yana damunta, kafin su dauki mataki kuma sai aka kore sa daga aiki. Shikenan kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta.

“Idan har ba sonta yake yi ba, to tabbas akwai wata kasa, don babu wanda zai kalli matarsa ya ce tana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki. Sam jikinta bai nuna tana da alaka da wannan cutar ba.” ya kuma fada a zuciyarsa a daidai lokacin da suka hadu.

Hannunta ta yi amfani da shi a saitin fuskarsa kamar za ta tsone mishi ido.

Dalilin da ya sa kenan ya yi saurin janye idonsa yana kallonta cikin murmushin karfin hali.

Ita ma murmushin karfin halin ta mayar masa.

“Kana ta kallona, har ka sanya na ji kunya.” Ya fadada murmushinsa.
“Ina mamakin yadda lokaci daya kika yi kiba ne, kin zama wata katuwa.”

Ta dan juya idonta kadan wanda ya ba farin bayyana bakin kuma ya buya.

“Ba ka yi mamakin kibarka ba sai ni.” hannunta a kan habarta alamun mamaki ta yi maganar.

“Kin fi ni kiba fa sosai, sai kin ga fuskarki ta wani cika, musamman kumatunki sosai za su yi dadin mari. “

Wannan karon dariya mai sauti ta yi tare da dukar da kanta kasa lokaci daya kuma ta dora hannunta a kan bakinta.

Ba ƙaramin kyau ta yi wa Hassan ba, inda ya kara gyara tsayuwarsa yana kallonta fuskarta dauke da murmushi.

“To Bismillah mana, sai ka mara.”

“Idan mara ni ne zan ci zafin ba ke ba.”

“Wanda aka mara daban mai jin zafi daban.”

“Kina mamakin hakan ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a, sannan ta gyara tsayuwarta, yanayin fuskarta ya canja zuwa damuwa.

“Ina karfin hali ne fa kawai Rabin Raina, amma hankalina yana kan sakamakonmu bamu san me zamu taras ba, sosai abun nan ya rikita mun lissafi, ya bata mun tsawon wunina na yau.”

Lokaci ɗaya fuskar Hassan ma ta canja zuwa damuwa, ya gyara tsayuwarsa, hade da nade hannunsa a kan kirjinsa, cikin kasalalliyar murya ya ce,

“Idan akwai wani abu da ke daure mun kai a yanzun wannan batun ne. Rabin Raina a ina za ki samu H.I.V? Gaskiya kaina kamar zai tarwatse ta dalilin wannan maganar.”

Asiya ma ta sauke ajiyar zuciya mai karfi
“Ni kaina abun na ban mamaki, na rasa irin tunanin da zan yi, koda na zo aiki ma haka nan dai nake magana amma hankalina ba ya jikina.”

“Zuciyata ta fi karfafa mun a kan ba ki da cutar nan, amma kuma na kasa samun natsuwa.” Cewar Hassan a lokacin da yake murza key din mashin dinsa.

“Sha Allah alkairi zamu gani, ina jin hakan a jikina. Don kuwa bamu da wata alaka ta kusa ko ta nesa da wannan cutar.”

Bai yi magana ba, har zuwa lokacin da, ya gyara mashin din nasa ta hau suka fice daga harabar gidan Radion don zuwa karbar result din nasu.

Labarin Asiya 2 >>

2 thoughts on “Labarin Asiya 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×