Rayuwa ta ci gaba da mikawa cike da nasori, musamman a bangaren kungiyarsu Asiya, wacce suka bude ta kamar da wasa, Sai ga shi ta kai inda basu taba tunanin zuwanta ba, hatta kungiyoyin wajen kasa sun fara taimaka musu.
A cikin Yan kwanakin ne Allah Ya azurta Kubrah da samun karuwar da namiji a karon farko, Asiya ba ta ji nauyin cikinta ba, suka daukin hanya ana i gobe suna ita da Rukayya.
Suna ya yi armashi musamman da ya kasance an dade ana neman haihuwar ba a samu ba, yaro ya ci sunan Ahmad, bayan suna da kwana. . .