Skip to content
Part 21 of 25 in the Series Labarin Asiya by Matar J

Rayuwa ta ci gaba da mikawa cike da nasori, musamman a bangaren kungiyarsu Asiya, wacce suka bude ta kamar da wasa, Sai ga shi ta kai inda basu taba tunanin zuwanta ba, hatta kungiyoyin wajen kasa sun fara taimaka musu.

A cikin Yan kwanakin ne Allah Ya azurta Kubrah da samun karuwar da namiji a karon farko, Asiya ba ta ji nauyin cikinta ba, suka daukin hanya ana i gobe suna ita da Rukayya.

Suna ya yi armashi musamman da ya kasance an dade ana neman haihuwar ba a samu ba, yaro ya ci sunan Ahmad, bayan suna da kwana daya suka juyo gida.

Bayan dawowarsu ne kuma ta rubuta Maternity leave, shi ya sa yau ta yi shirin zuwa wuni gida, musamman ta yi a gida.

Dambun nama ta yi da ya sha kayan kamshi za ta kaiwa mahaifinta, dasu Addah. Idan har da sunan yawo za ta je gidan ba biyawa daukar yaranta ko aje su ba, to ba ta iya tafiya hannu biyu,, dole sai ta rike wani abun.

Yanzu kuma da mahaifinta ya kasance a gida dalilin ritayarsa, sai ta kuma zage dantse wajen ganin ta yi mishi abubuwan da zai yi alfahari da samun su, a matsayin yayanshi.

Wannan shi ne karo na farko da suka samu damar zama da mahaifin nasu, saboda yanayin aikinsa, za ta iya cewa basu sabu da shi kamar yadda sauran yara ke sabuwa da iyayensu. Kullum kamar bako haka yake a wajensu.

Doguwar riga ce ta sanya wadatacciya wacce a sake take, babu inda ta kamata.

Duk da haka cikin nata ya fita sosai a cikin rigar . Sai da ta rufe ko ina hade da kashe kayan wuta sannan ta fita.

A kan hanya ne kafin ta samu abun hawa ta kira Rukayya, inda take shaida mata fitarta, hade ba ta sallahun idan Nour ta dawo makaranta, ita ba ta dawo ba, to Nour din ta taho wurin ta.

Yanke wayar ta yi hade da dariya jin amsar da Rukayyar ta ba ta.

A hankali ta tura gate din gidan hannunta rike da basket din da ta zubo food flask guda uku.

Kamar ko wane lokaci bangaren Addah ta fara shiga, don mika mata gaisuwa.

Cike da kulawa Addah ke kallon Asiyar

“Har kina iya fita? wannan cikin naki a wannan karon girmanshi na ba ni mamaki. Ga shi duk kin kumbura.”

Murmushi Asiya ta yi, ita kanta cikin ya isheta, ko don ta rabu da haihuwar shi ya sa take jin gabadaya a takure take.

Ko bacci a wahale take yin shi.

” Na gaji da zaman gidan ne, shiru ba inda nake zuwa”

“To ina Nour din?”

“Tana makaranta, zasu tsaya lesson sai 4pm zasu tashi.”

“To wannan kumburin ba dai wata matsala ko?” Addah ta kuma tambaya cike da kulawa

“Babu dai suka ce, har B.P sun yi min kuma lafiya kalau.”

Asiya ta yi maganar tana kallon jikin nata, musamman kafarta sosai ta dan tasa.

“Kodayake dama ke haka kike cikinki da kumburi”. Cewar Adda hankalinta na kan food flask din da Asiyar ke aje mata a gabanta.

“Kawarki ta damu wai za ta dawo gida gabadaya, wai ana ta yin abubuwa ba da ita ba.” ta canja salon hirar tasu

Murmushi Asiya ta kuma yi “Zee ta rasa wajen zama fa, kodayake tana da gaskiya, yau tana can gobe tana can. Koda yake tana da gaskiya, ana yin abubuwa ba da ita ba kam, kamar ni sai in yi abubuwa goma ba tare dana tuno sunanta ba. Na san kuwa da muna tare hakan ba zai yiwu ba.”

“wallahi kuwa ba ke kadai ba, ni kaina na kan manta da ita a wasu al’amuran.”

Cewar Addah daidai lokacin da take bude flask din da Asiya ta mika mata mai dauke da dambun nama da ya sha kayan hadi.

“Ba kya gajiya dai, mun gode Allah ya saka maku da alkairi ya buda maku ya kuma sa a sauka lafiya .”

“Amin ya Rabbb.” Cewar Asiya daidai lokacin da ta yunkura da kyar ta tashi.

“Baaba ba a dawo ba?”

“Bai dawo ba, dan jakar uba, wannan yaro da shi ne da sunan marigayi da rashin jin da zai yi bamu san iyakarsa ba. Sam ba ya ji” cewar Adda tana dariya.

Ita ma Asiya dariyar take yi a daidai lokacin da take fita, ita kanta ta san Abdallah akwai rashin ji, idan ya je wajenta da sunan wuni to ita ma wuni take da ciwon kai saboda rashin jin sa, Nour kuwa har baccin dole take yi saboda kwadar da yake mata.

Shi ko irin baccin rana na yara ba ya yi, shi ya sa basa shiri da Hajjah, da ya shiga bangarenta za ta koro shi, ta ce wai hannun biri gare shi, baya zama ba aiki.

Bangaren su Aunty ta shiga, nan ma ta mika masu nasu flask din, su kai ta godiya hade da magana a kan girman cikin nata.

Daga nan bangarensu ta nufa, dakin Alhaji Abdallah ta fara nufa.

Zaune yake cikin riga yar shara ta maza, irin ta shan iska, kamshi mai dadi na fita a cikin dakin. Yayin da hankalinsa ke kan laptop din shi da alama yana yin wani abu ne mai muhimmanci.

Shigowar Asiyar ne ya sanya shi mayar da hankalinsa a kanta.

Shi kansa wani irin dadi da nishadi yake ji, karon farko da yake kasancewa a cikin iyalansa, yana kallon dukkan wani motsinsu, sabanin baya da yake zuwar masu kamar bako.

Bai san haka magidanta ke jin dadi da farin ciki ba, idan suna tare da iyalansu. Sai yanzu yake jin lallai ya yi missing din abubuwa da yawa game da iyalansa, ina ma ace yana zaune dasu yana kallon shirme da kirinyar yarintarsu.

Yanzu sai dai su Zee ke debe shi kewar wannan.

Wata irin kunya da nauyin mahaifin nata ya rufeta, ban da dole ba ta son ya ganta da wannan turtsetsen cikin.

Dole ta yi saurin dukawa daga bakin kofar kanta a kasa tana gaisheshi.

Murmushi yake hankalinsa kaf a kanta, bayan ya gama amsa gaisuwar

“Ya jikin naki? Jamila ta ce ba kya jin dadi.”

“Eh na ji sauki sosai ai” kanta a kasa ta ba shi amsa

“To ma sha Allah. Akwai wata matsalar ne?”

Girgiza kai ta yi alamun babu.

“Komai yana tafiya daidai,, ba kya jin wani sauyi a jikinki da ba ki yarda da shi ba.”

Kuma girgiza kai ta yi alamun babu.

“To Alhamdulillahi”

Ta mike da kyar zuwa dab da shi ta aje mishi food flask din mai dauke da dambun nama.

Godiya ya shiga yi hade da sanya mata albarka, a can kasan zuciyarsa yake jin wani dadi gami da farin ciki, kaunar yaran na kara shiga cikin bargonsa.

A bedroom ta cimma Hajja tana tattare tarkacen Zee tana fada ita kadai “Yarinya sai girma take, girman dankatakore girma ba hankali, ita idan za ta dauki abu daya sai ta fitar da kaya duka, kuma ba ta san ta mayar ba. Kai Allah ya jikan Aliyu, duk ban san wannan shirmen ba a tare shi wallahi.”

Murmushi Asiya ke yi mara sauti, har zuwa lokacin da Hajjar ta juyo rrungume da kayan a kirjinta.

Sai kuma ta ware ido a kan Asiya tana fadin” kin ba ni tsoro”

Ta tuntsire da dariya sosai hade da fadin “Kai Hajja! Don dai abun tsoro ba shi da wahala.”
Karasawa ta yi sosai cikin dakin ta zauna gefen gadon hade da cire hijabinta da take ji kamar an daureta da shi.

“To ba dole in ji tsoro ba, ni dai na san ni kadai ce, na juyo naga abu kamar rumfa a kaina.”

Bata rai ta yi cikin shagwaba ta ce “Ni wallahi na gaji da cikin nan, tun can dama ni ban shirya mishi ba, ga shi nan ko ina na shiga ai ta kallona”

“Ke ni wasa nake miki, kuma dama ai haka kike yin cikinki kato kamar kin kunshe yara goma”

“Amma Hajjah wannan daban fa.”

Ta dago daga adana shirya kayan Zee din tana kallon Asiya. “Gaskiya dai wannan cikin ya yi girma sosai, koda yake kin ce an ce biyu ne, fatanmu dai Allah ya raba lafiya koma guda dayan ne”

“Amin” cewar Asiya a lokacin da ta kwanta sosai saman gadon.

“Ina bindin ta ki?”

Dariya sosai ta yi kafin ta ce “Tana school, sai 4pm zasu taso suna da lesson ne”

“Wannan yarinyar kin bata ta, sam ba ki iya raino ba. Yarinya duk a shagwabe, idan ta zo nan sai ta wuni bakinta bai bude ta yi magana ba, ko abu take so sai dai ki ga tana kuka. Yarinya kullum kamar a ranar aka cire ta a bakin nono”

“Kai Hajjah!” cewar Asiya a marairaice

“Allah kin batata, sai a ki fadin gaskiya.”

“Hajjah me Nour take yi da ya wuce rashin maganar? Kuma haka take, amma bayan nan Nour ai ba ta damuwa.”

“Ba wani nan,, yarinyar da abinci ma ba ko wanne take ci ba. I don’t want eat this one- i don’t want eat this one, i want eat this one- i want eat this one, aikinta kenan fa, haba ranar na ce a kira ubanta ya zo ya kaita gida,, don ba aikinta nake yi ba, da za tai ta sanya ni wahala.”

Sosai Asiya ke dariya.

Ta san halin Nour kam, ba ta cika sakin jiki da mutane ba, sannan ba ko wane abu take ciki ba, shi ya sa ma ba ta cika turo ta wajen Hajjahn ba, ita ma Nour din ba ta son zuwa. Kuka sosai take yi Idan ta ji an ce za aje gidan Hajja.

Ba wurin Hajja kawai ba, ko wurin Rukayya aka ce ta je to da kuka take tafiya, shi ya sa tana zuwa sai Rukayyar ta koro ta, idan kuwa Asiyar ba ta nan to wuni Rukayyar ke yi fada hade da kiran Asiya tana fadin ta yi sauri ta dawo.

Ba wannan ne ya fi ba Asiya dariya ba, sai idan ta kira Rukayya ta fada mata ga Nour nan zuwa, Sai Rukayyar ta ce ta taho da abincinta wai ita ba za ta iya wahala da ita ba. Cikin dariya ta ce

“Ku ne dai baku fahimci Nour ba, amma ni na fahimci kayata, yarinya ma mai hakuri irinta. Can ma Rukayya haka take mun korafi, ko cewa na yi zan turo ta zuwan gidan zan je wani wuri, sai ta ce wai ta zo da abincinta. Ki ji fa, wai ta zo da abincinta, ita ba za ta iya da wahalarta ba. “

Hajjah ta rike haba “To kin ga laifinta, ko ni ma na kusa fara yin hakan ai, ashe ba ni kawai take sanyawa ciwon kai ba. Ai ni bana son ma ta zo”

“Kai Hajja a gabana kike fadar haka?” Asiya ta yi maganar daidai tana tashi daga kwancen hannunta a kan habarta

“Idan na fada a bayan idonki to me kanan na yi, tun da wacce na yi maganar don ita ba ta ji ba.”

Dariya Asiya ta yi kafin ta ce “Ku sha kuruminku, indai Nour ce sai kun neme ta da kanku watarana.”

“Allah ya kai mu wataranar?”

“Hajjah wai da gaske mutanen basu barin Aliyu ya zo nan?” Asiya ta canja salon hirar tasu

“To da bai zo ba me ya same ni Asiya? Barkana ba shi ne kawai jikana ba, ni fa saboda yana da sunan marigayi ne ma nake kulafuci a kansa. Yana can wurin kakarsa.”

“Ikon Allah! To duk tsiyarsu dai mune dangin uwarsa, kuma dole muna da rana.”

“To kare ma ya yi rana bare dan Adam.”

Cikin hirarsun ne bacci ya dauke Asiya, ba ta tashi ba sai karfe biyu, ta yi sallah sannan ta ci faten doya da waken da Hajjah ta girka, sannan ta kuma komawa bangaren Addah.

A can ta yi la’asar, tana kan sallayar ne ba ta ta shi ba kiran Hassan ya shigo.

“Kin koma gida ne?” ya fara tambaya bayan amsa sallamar tata

“A’a” ta ba shi amsa.

“Ina jin kawai zan kai Umar asibiti mu kara ganin likita.”

“Har yanzu jikin nashi?” ta yi saurin tambaya.

“Eh amma ba sosai ba.”

“To shi kenan sai kun dawo. Allah ya ba shi lafiya.”

“Amin” ya fada hade da yanke kiran.

“Waye ba lafiya kuma?” Adda ta tambaya bayan Asiya ta dire wayar.

“Umar ne.”

“Subhanallah! Allah ya ba shi lafiya, mutumin kirki yaron nan kamar ni na haife shi, ko ido baya son ka hada da shi akwai kunya.”

Murmushi jin dadi Asiya ta yi, haka nan take jin dadi idan ana yabon Umar, ita kanta tana jin kaunarsa saboda kyawawan halayensa, rikon gaskiya da kuma amana.

“Amin” ta fada bayan kai karshen tunaninta.

“Matar ma kamar ciki gareta, kwanaki da ta biyo nan ta ɗashe sosai”

“Eh amma karami ne.” cewar Asiya.

“Ma sha Allah. Allah ya raba lafiya, ga Jamila nan ma da nata.”

Hira su kai ta yi har magriba.

A lokacin kuwa tuni Nour ta dawo tana bangaren Hajja. Don ta kira mai daukarta a kan ya kawo ta family house din su

Sai da ta ci abinci sannan tabar sashen Addah ta nufi sashensu don yin sallama da Hajja su tafi gida.

Shigarta ke da wuya kiran Hassan ya kuma shigowa wayar tata.

” Ki samu keke ku tafi gida, ba zan samu damar zuwa daukarku ba, don an bamu gado ne, ba zan samu damar zuwa daukar ki ba.” ” abin da ya fada kenan bayan amsa sallamar

“Subhanallah! Har abun ya kai haka?”

“Eh amma Alhamdulillahi akwai sauki sosai,, jini ne zasu kara mishi leda daya.”

“To shi kenan zan biyo ta asibitin na duba shi.”

A gurguje ta yi sallama da Alhaji Abdallah da Hajjah ta tasa Nour zuwa asibitin. Don gabadaya hankalinta ya tafi asibitin

Hassan ne ya shigar dasu dakin da aka kwantar da Umar hannunshi rike da Nour.

Rukayya na kan kujera a kusa da shi, yayin da Umar din ganin su Asiya ya tashi zaune hade da jingina bayanshi da bango yana kallon su Asiya fuskar dauke da murmushi.

Nour ce ta dan duka cikin muryarta mai sanyi ta gaishe shi hade da yi mishi sannu.

Ya amsa cike da jin dadi, kullum ya kalli Nour wani farin ciki ne baibaye ilahirin kirjinsa, yarinyar kamar ba tashi ba, ta taso cikin kulawa ilmin zamani dana addini sabaninshi da ya taso cikin gararamba a kan tit hade da aikin wahala don rufawa kansa asiri.

A ko wace sallah idan ya yi, addu’arsa a kan su Asiya dabance, ta yi masa komai a rayuwa da babu wani abu da zai biyasu da shi face addu’ar.

Ta gyara mishi rayuwa, ta cika mishi burinshi, sannan ta rike mishi yarshi kwalli daya a duniya, bai san komai nata ba, ci, sha, kudin makaranta, magani suttura.

Tun yana ba Asiyar wani abu game da Nour har ya daina, sai dai kawai idan ya samu dama ya kan dinke yaran ko saya masu kaya masu tsada ita da Zee ya basu.

Ya dauke idonsa daga kan Nour ds har yanzu hannunta na a cikin na Hassan ya mayar da hankalinsa kan sannu da Asiya ke masa.

“Sannu Baban Nour, abu har da su karin jini, Allah ya sa kaffara ne ya ba ka lafe.”

“Amin Aunty. Jikin ma ai da sauki, na gode sosai da dawainiya” ya yi maganar yana kallon Asiya.

“Kai dai kullum sai godiya, godiyar kam ba ta karewa ne, na fada ma godiyar ta isa haka.” Cewar Hassan ranshi a dan bace.

Duk dakin murmushi suke yi har da Umar da har sautin dariyarsa ya fito fili.

“To ai yaba kyauta tukuici Yallaboi, ai godiya ma ina furtawa ne saboda ban san wata kalma da ta fi godiyar ba, da zan yi amfani da ita a, kanku. Ku kalli fa yadda kuka gyara mun rayuwata, komai ya daidaita, kuka cika mun buruna, ko yau na mutu ba ni da fargaba game da iyalina.”

“To har sau nawa ne za ka fadin hakan Umar? Ina ka fada, ka kuma ka fada, kullum ma sai ka fada. Tsawon zamanmu da kai ba zan ce ga kuskurenka garemu ba, ka daukemu tamkar iyayenka, ba ka taba ha’intarmu ko cin amanarmu ba. Burinka a rayuwa shi ne ka samu gudan jini, ka samu matata ta karbe maimakon ta bar ma kullum kana kallonta, kuma ka yi hakuri ba ka taba nuna damuwarka a kai ba, daga kai har matarka, don haka wannan ma kadai ma wani karamci ne da kyauta ka bamu.” Cewar Hassan fuskarsa a kan ta Umar.

” Kai haba, duk su waye sanadin samuwar Nour kam ba ku ba, babu fa wani abu da na yi da zai zama ya maye gurbin alkairanku gare ni. “

” Idan jinin ya kare za a sallame ku ne? ” Asiya ta canja salon hirar, don kuwa idan za a kwana ana yi Umar ba zai hakura ba, haka yake kullum sai idan ba a zauna da shi ba.

Rukayya ta sauke numfashi” anya kuwa, ina jin sai da zuwa safe”

“To Allah ya kai mu ya kuma ba shi lafiya.”

“Amin” suka hada baki dukkansu.

Hassan ne ya fita ya yo masu take away, suka ci sannan suka shiga hira har da Umar.

Sai goma na dare suka baro asibitin, Hassan ya so Rukayya ta taho shi ya kwana, amma Rukayyar ta ce a’a za ta kwana kawai, tun da jikin akwai sauki sallama kawai suke jira.

Umar din ma ya dakko Nour da ta yi bacci ya kwantar da ita a seat din baya, sannan suka yi sallama, Hassan ya fice daga asibitin cike da farin cikin ganin yadda Umar din ya yi kyau.

Sai dai me, misalin sha biyun dare Rukayya ta kira lambar Asiya a kan ta fadawa Hassan jikin Umar ya tashi sosai aman jini yake yi.

A rikice Asiya ta tashi Hassan da ke gefenta yana bacci, ta fada mishi sakon Rukayya.

Shi din ma rikicewar ya yi, cikin sauri ya zura jallabiya hade da daukar key din motarsa, Asiya da ta manta akwai ciki a jikinta ta bi bayansa cikin sauri

“Ina za ki je?” ya tambayeta a lokacin da yake dakatawa daga bude kofar da yake son yi.

“Zan bi ka ne, ina son ganin jikin nasa.”

“To ki bar Nour da wa? Ki jira kawai in dawo,, ki yi masa addu’a.”

Jiki a mace ta yi tsaye a wajen har ya bude kofar ya fice.

Ta dade a tsaye ba tare da ta san me take ciki ba, daga karshe ta ja kafafunta zuwa kan kujera ta zauna cike da addu’ar Allah ya ba Umar lafiya.

Duk kiran da take yi wa Hassan bai daga kiran nata ba, Rukayya ma sau daya ta daga daga nan ma idan ta kira wayar sai ace a kashe.

Bacci ya kauracewa idonta har zuwa lokacin da aka fara kiraye-kirayen sallahr asuba.

A sanyaye ta yi sallahr asuba, daga nan ta tashi Nour ita ma ta yi sallah, kaya ta canja wa Nour din, ta dauki flask mai dauke da ruwan zafi hade da kayan tea sai bread da dama basu rabo da shi.

Ta dan jima a bakin titi kafin ta samu keke kasancewar ko shidda na safe ba ta yi ba

Misalin shidda da kwata ta shiga asibitin, a baranda da za ta sada ta da dakin da Umar suka ci karo da Hassan.

Ko ba ta tambaya ba, fuskarsa kawai ta shaida mata yanayin tashin hankalin da yake ciki.

Don haka sauri ta karasa wajen da suke tsaye da wasu Nurse maza suna magana.

Ganin ta ya sanyasu mayar da hankalinsu a kanta.

Jiki a mace ta ce “Ya jikin Umar din ne?”

Ya zuba mata ido, hade da karantar yanayinta, daga bisani ya sauke ajiyar zuciya.

“Sai dai mu bi Umar da addu’a, amma Allah ya karbi abinsa Rabin Raina.”

Gabadaya ta ji komai ya tsaya mata, yayin da ta zubawa Hassan ido ba tare da ta iya furta ko wace kalma ba.

Kallonsu kawai take, a hankali kuma taga suna canja mata kala, yayin da take kallon komai na wajen yana juya mata.

Sai kuma ta nemi ganin nata ta rasa.
Sosai Hassan ya kara dimaucewa ganin halin da Asiya take ciki, domin kuwa ba rai Nurse suka dauketa zuwa dakin tiyata, don yi mata aikin gaggawa.

Yayin da gawar Umar ke shimfide a gado, ga kuma Rukayya kwance da ba ta san inda kanta yake ba, saboda tun lokacin da ta fahimci ran mijinta ya yi nisa da gangar jikinsa, ta yanke jiki ta fadi jini ya balle mata, kuma har zuwa lokacin jinin bai tsaya ba, iyakar bakin kokarinsu likitocin ke yi amma jinin bai tsaya ba.

Misalin takwas na safe asibitin ya cika da yan’uwan Rukayya, da kuma su Asiya.

Sai misalin tara na safe aka fita da gawar Umar zuwa gidan Hassan don yi masa suttura a kai shi makwancinsa na karshe.

Duk da hankalin Hassan yana kan Asiya wacce aka tabbatar mai a lokacin ake mata aiki hakan bai hana shi halartar sallahr jana’iza Umar ba.

Da hannunsa ya saka gawar Umar a cikin makwancinsa yayin da idonsa ya kasa tsayar da hawayen da ke kwaranya a idonsa.

Allah ya sani yana jin Umar kamar wani bangare na jikinsa, shi ne abokinsa, amininsa, abokin shawararsa, abokin dariyarsa.

Tun lokacin da Umar ya dauki niyyar watsar da makamansa a kan mummunar dabi’arsa, bai taba kama shi da wani laifi mummuna ba.

Yana shirye-shirye bude masa katon shago a unguwar Allah ya dauki ransa.

Har ya iso gida bai iya tsayar da hawayensa ba, haka yaba mutane hakuri a kan zai koma asibiti don ganin halin da Asiya da kuma Rukayya suke ciki.

A lokacin da ya isa asibitin ku san duk ‘yan’ uwansa na wurin.

Aunty Muna ce ta tare shi da labarin an yi wa Asiya aiki an cire yara biyu mace da namiji kuma duk suna cikin koshin lafiya sai dai jikin Rukayya ne sai a hankali.

Ko yaran bai nemi gani ba, ya nufi dakin da Rukayya ke kwance.

Jini ake sanya mata, idonta a rufe kamar mai bacci, tsaye ya yi a kanta yana kallonta cike da tausayawa, lallai Allah kadai ya san soyayyar da ke tsakanin mata da miji, sai ya kara jin tausayin mace da mijinta ta rasu, Allah kadai ya san halin kuncin da suke tsintar kansu a ciki.

Ya dade a tsaye kanta, kafin ya juya da niyyar fita don duba jikin Asiya.

Daidai kofar fita ta kira sunansa a hankali “Uncle”

Ya juyo da sauri hade da karasowa kusa da ita. Yana fadin “Sannu ya jikin naki?”

“Akwai sauki.” ta fada a hankali

“Da gaske Baban Nour ya rasu kodai doguwar suma ya yi?” ta yi mishi tambayar idanuwansa a kanta.

Shiru ya yi yana kallonta, ya rasa kalar amsar da zai ba ta

Shirun da ta taga ya yi ne, ta fara kokarin tashi.

Cikin sauri ya dakatar da ita. “Koma ki kwanta don Allah ba sai kin tashi ba.”

A hankali ta koma ta kwanta, ita kadai ta san ya take ji a zuciyarta, lallai mutuwar miji akwai tashin hankali, musamman miji irin Umar mai kokarin faranta ran iyalansa, a zamansu ba za ta iya cewa ga laifinsa ba, mutum ne shi mai kokarin ibada, ta sha ce masa yau dai ka kwanta ka yi baccinka, tun da ba samun bacci kake yi da rana ba, in ya so gobe sai ka tashi sallahr.

Ya kan yi murmushi ya ce ” ina da tarin laifuka a wajen Ubangijina, wanda har nake jin idan zan kare ko wace rana tawa wajen neman afuwarsa kamar ba zai dube ni ba.”

Ta rasa wane irin laifuka ne haka ya aikata, iyakar saninta shu mutum ne mai kyautatawa, iya mu’amala,, yawan ibada, rikon amana da kuma tsayawa a kan gaskiya.

A ina za ta samu miji kamar Umar, don kuwa shirun Hassan ya tabbatar mata da Umar ya rasu.

Wasu hawaye masu dumi suka zubo mata, yayin da shiru ya ziyarci dakin.

“Asiya ta haihu, an samu yan biyu mace da namiji” ya fada a hankali yana ganin kamar hakan zai dan faranta mata ranta.

Kamar yadda ya yi tsammani kuwa hakan ne ya faru, murmushi ta yi da ke nuna irin dadin da ta ji.

“Ma sha Allah! Alhamdulillahi! Duk suna lafiya?”

“Ban dai sani ba, saboda har yanzu ban gansu ba”

“Don Allah je ka dubosu, sannan ka kawo mun su in gansu ni ba zan iya zuwa ba.”

Sosai yake kallon farin ciki a fuskarta lokacin da take maganar kamar ta manta da maganar mutuwar mijinta.

Hakan ya ba shi kwarin gwiwar zuwa dakin da Asiya ke kwance bayan gama mata aikin.

A kwance ya same ta fuskarta na duban sama, ba kowa dakin idan ka dauke fankar da ke juyawa a hankali.

Shigarsa ke da wuya kuwa ta bude idonta hade da zuba mishi su har ya karaso.

“Sannu Rabin Raina, ya kike jin jikin naki yanzu?” a lokacin da ya janyo kujera ya zauna kusa da ita yake maganar.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke

“Da gaske Umar ya rasu?” ta jefo mishi tambayar ba tare da ta amsa ta shi tambayar ba.

Hannunta daya ya kamo yana murzawa a hankali alamar lallashi

“Ko wace rai sai ta dandani mutuwa, shi da ya tafi bai yi sauri ba, mu da muka rage ba mu yi jinkiri ba. Mutuwa na kan kowa, koda ciwo ko ba ciwo. Saboda haka Umar lokacinsa ya yi fatanmu Allah ya kyautata makwancinsa, ya gafarta mishi dukkan kura-kuransa, muma kuma Allah ya kyautata namu karshen.”

Ba ta damu da hawayen da ke gangarowa daga idonta zuwa kan filon ba.

Sosai ta ji mutuwar Umar, ta kan manta da duk wani munanan ayyukansa, da ku san idan har zasu kadaice da shi sai ya tuna ya kuma ce yana nadamar aikatasu.

Ya sha fada mata yana jin dadin rayuwarsa ta yanzu, ko wane lokaci yana jin sa a cikakken mutum sabanin baya can da kome yake sai ya rika jin wani kunci a ranshi.

“Rabin Raina!” Hassan ya kira sunanta a hankali ganin yadda hawaye suke ci gaba da kwaranya daga idanunta.

Waigowa ta yi tana kallonsa.

“Ki yi hakuri, hade da yi masa addu’a ba kuka ba.” wannan karon ma ba ta yi magana ba.

Suka kuma dauke tsawon lokaci kafin ta ce “Ina Rukayya?”

Wata ajiyar zuciya ya ajiye kafin ya ce “Rukayya ma sun ba ta gado ne, da alama ta samu miscarriage, amma ta yi farin ciki sosai da ta ji kin haihu, kuma kin haifi abin da suke miki fata. Yanzu haka ma ta ce in kai mata yaran.”

Murmushi Asiya ta yi hade da sharce hawayenta.
Tun lokacin da cikin nan ya samu daga Umar har Rukayya uwar biyu suke kiranta, basu da magana sai na cikin, lokacin da aka yi mata scanning aka ce yan biyu ne shiru ta yi ba ta fada masu ba.

Ina ma ace Umar na da rai tabbas da Allah kadai ya san farin cikin da zai yi.

“Ina Nour?” ta kuma tambaya.

“Nour tana gida wajen su Aunty.”

“Ta san abin da ya faru ne?”

“Ban sani ba gaskiya.”

Shigowar Hajjah da Aunty Muna ne ya katse masu hirar.

Aunty Muna ce ta kanga mata yaran

“Ma sha Allah! Kin ga twins naki manya, sai ka ce ba biyu ba.”

Ta dan zuba ma yaran ido, da suke sanye da kayan sanyi overall pink da white color.

“Wacece macen a cikinsu?” ta tambaya a hankali.

“Wannan mai pink din kayan” cewar Aunty Muna.

“To wannan namijin sunanshi Umar”

“Allah ya raya mana shi bisa sunnah”

Hajjah ta fada a karon farko tun Shigowar ta dakin.

“Aunty akaiwa Rukayya su ta gani, ta ce tana son ganinsu.” cewar Asiya tana kallon Aunty Muna

Hassan ne ya dauki namijin Aunty Muna ta dauki macen suka nufi dakin da Rukayya ke kwance.

“Da alama ta samu bacci ma.” cewar Aunty Muna tana kallon fuskar Rukayya da idanuwanta ke lumshe.

Ido Hassan ya tsura mata cike da fargaba, yayin da bugun zuciyarsa ya karu.

Bai yi magana ba ya fice daga dakin sabe da yaron.

Matar JāœšŸ»

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Labarin Asiya 20Labarin Asiya 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
Ɨ