Tare suka shigo da likitan a hanzarce ya nufi Rukayya da ke kwance.
Cikin mintuna biyu ya gama dubata, kafin ya ja zani ya rufe ta rub.
A rikice Hassan yake magana " Doctor me kake nufi ne?" Don Allah kar ka ce min ita ma ta rasu. Yanzu muka gama magana da ita a kan in kawo mata yaran nan ta gani fa. Me kake nufi da rufetan da ka yi, ka budeta don Allah."
A hankali likitan ya dafa Hassan tare da fadin" Ka yi hakuri abun da ba ka son jin shi ne ya faru da ita. "
"Innalillahi. . .