Skip to content
Part 22 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tare suka shigo da likitan a hanzarce ya nufi Rukayya da ke kwance.

Cikin mintuna biyu ya gama dubata, kafin ya ja zani ya rufe ta rub.

A rikice Hassan yake magana ” Doctor me kake nufi ne?” Don Allah kar ka ce min ita ma ta rasu. Yanzu muka gama magana da ita a kan in kawo mata yaran nan ta gani fa. Me kake nufi da rufetan da ka yi, ka budeta don Allah.”

A hankali likitan ya dafa Hassan tare da fadin” Ka yi hakuri abun da ba ka son jin shi ne ya faru da ita. “

“Innalillahi Wa’inna Ilairhir-Raj’uun! Kana nufin ita ma ta rasu? Ta bi Umar kenan? Sun barmu a nan, Rukayya ma ta rasu.”

A hankali Aunty Muna ta karbe yaron da ke hannun Hassan ta kwantar da shi gefen Rukayya.

Saboda ko wane lokaci Hassan zai iya mantawa da me ke hannunsa, sosai ta ga rudewa da rikicewa hade da tashin hankali a kwayar idonsa.

Kamar jira yake yi ta amshi yaron, da sauri ya karasa gadon da Rukayyar ke kwance.

Dafa gadon ya yi da hannayensa biyu, yayin da ya kasa controlling kansa, sautin kukansa ya rika fita a hankali, wanda ya kara tsorata Aunty Muna da ba za ta iya tuna rana ta karshe da taga hawayenshi ba, bare sautin kukansa.

Daga shi sai Allahn da ya halicce shi ne kawai yasan irin yadda yake ji a zuciyarsa, a rana daya ya rasa wasu mutane masu muhimmanci a rayuwarsa, ba zai iya gwada matsayin Umar a zuciyarsa ba, haka ma Rukayya sun dauke shi tamkar mahaifi, yayin da shi kuma yake jin sa tamkar wasu kannensa ma fi kusanci da shakuwa da shi.

Bai san sun yi nisa a zuciyarsa ba sai yanzu da yake jin ya rasasu.

Kafin Umar ya rasu ya yi ta nanatawa “Idan ba ni Rukayya za ta shiga damuwa Oga, tausayinta nake ji, don Allah ka kula min da ita ka tsaya mata kamar yadda ka tsaya mata a baya.” wa’annan sune kalaman da Umar ya rika furtawa a lokacin da ransa ke kokarin fita gare shi.

Tun a lokacin zuciyarsa ta kuduri zai yi bakin rai bakin fama don ba Rukayya farin ciki, sai dai kuma ita ga shi ita ma ta bi mijin nata, ba tare da ta fada mishi nata damuwar ba.

Dandandanan dakin ya cika da koke musamman mata na daga yan’uwan Rukayya da kuma bangaren Asiya.

Hassan ma kuka yake tamkar mace, ya Kasa jurewa, Hakan ya sa kowa ya fahimci mutuwar ta taba shi sosai.

Asalin gidanta aka wuce da gawarta, a can aka yi mata suttura hade da sallah aka kaita makwancinta.

Duk yadda ya so komawa asibitin bai samu damar yin hakan ba, saboda yawan mutane, amma hankalinsa kaf yana asibitin, musamman yadda yake samun labarin yanayin da Asiya take ciki, ta koma kamar mai aljanu sakamakon jin mutuwar Rukayya, kuka dai ta yi har ta gaji, tun ana ba ta hak’uri har kowa ya zuba mata ido.

Ranar da aka yi addu’ar uku, da misalin karfe 11am ya nufi asibitin.

Sosai yake mamakin irin ramar da Asiya ke yi, kullum ya zo sai ya ga gara jiya da yau, ta zama fiyot a kan gadon.

Ya san akwai shakuwa ta musamman tsakaninta da Rukayya amma bai yi tunanin za ta dauki abun da zafi haka ba.

Kujerar da ke gabanta gadon ya gyara sosai ya zauna, yana kallon yadda take sauke numfashi a hankali.

A cikin baccin take jin kamar akwai mutum a kanta, a hankali ta bude idonta hade da diresu a kanshi.

Kasa dauke idonta ta yi a kansa, cikin kwanaki ukun shi ma ya zube sosai hade da yin baki wannan ya tabbatar mata da lallai mutuwar ta shige shi sosai.

“Ya jikknki?” ya furta a hankali bayan ya sauke ajiyar zuciya.

“Alhamdulillahi!” ta furta a hankali.

“Ya karin hak’urinmu?” ya kuma fada a hankali.

Sai da ta share hawayen da ya gangaro mata kafin ta ce “Alhamdulillahi”

“Ban ga kowa a waje ba” ya canja salon hirar kamar bai ga hawayen nata ba.

“Dama Jamila ce kawai, kuma ta je dakko min Nour ina son ganinta”

“Su Hajjahn fa?”

“Duk suna gidan rasuwar ai, ko zasu dawo sai zuwa an jima. “

“Oh! Ca nake ma sun dawo ai, sau daya kawai na hadu dasu”

Shiru ya ziyarci wurin kafin ta ce.

“Rukayya da Umar basu bar ma wata wasiyya ba ko game da Nour?” ta yi maganar daidai tana ta shi daga kwanciyar da take.

“kina kuwa cin abinci Rabin Raina? Kin ga zamanki kuwa?”

Guntun murmushi ta yi mai cike da nuna damawar da take ciki “Hala kai ma ba ka duba madubi ne, ko don ni ban tambaye ka ba? Ai ramarka ta fi tawa Rabin Raina har tsoro ka ba ni”

Shi ma irin murmushintan ya yi kafin ya yi magana Jamila ta turo kofa hannunta rike da Nour

Zubawa Nour ido Asiya ta yi tana kallon yadda yarinyar ke canja mata kala zuwa siffar Rukayya da kuma Umar, abin da ba ta taba gani ba sai yau.

Jikin Asiya ta fada hade da sake kuka a hankali.

Dago kanta Asiyar ta yi hade da share ma ta hawayen tare da fadin

“Yarinyata menene kuma ya faru? Hajjah ce hala tai ta tsangwamarki?”

Girgiza kai ta yi alamar a’a

“To me ye na kukan?”

“Ban ganki ba ne” cikin kuka ta ba ta amsa

“To yanzu ba ga shi kin ganni ba? Sai kuma me?”

“Mutane suna ta cewa wai Ummana da Abbana sun rasu Momy”

Asiya ta kai kallonta a kan Hassan da dama su yake kallo cike da tausayi, sannan ta dire a kan Jamila.

Kafin ta yi wani yunkuri Hassan ya janyo Nour jikinsa cikin sigar lallashi yake magana

“Ko ba Umma da Abba Nour ai akwai Momy sannan ga ni Dady duk abin da kike bukata za mu yi miki kin ji. “

Kai ta jinjina alamar gamsuwa lokaci daya kuma tana share hawayenta sabbi da suke sauka alamar dai ta ji mutuwar duk kuwa da kasancewarta yarinya.

Iyaye daban ne ai, komin rashin kusancinka dasu ko duk yadda kake ganin kana dawainiya dasu saboda tsufansu ko wata matsala tasu duk ranar da basu sai ka ji ka koma kamar kai kadai ne a duniya sai ka ji ko ina ya maka fadi.

“Momy ina Babyn naki, was Aunty Jamila ta ce kin samu baby guda biyu?” cewar Nour lokacin da ta dawo jikin Asiya.

“Je ki Auntynki ta kai ki wajen su, ki gan su.”

Ba musu kuwa ta bi bayan Jamila suka fi ce.

“kin tambaye ni dazu game da batun Nour ko?”

Kai ta daga sama alamar Eh.

“Babu wata wasiyya maganarsu kaf a kan matarsa ne, da alama ya fi tausaya mata fiye da Nour din.”

Kai ta kuma jinjinawa ba tare da ta ce komai ba ta koma ta kwanta.
Kamar mafarki take jin abun, wai ba Rukayya ba Umar.

Shi ma Hassan din fita ya yi don gano yan biyunsa.

Addu’ar bakwai kuwa gidan Umar cika ya yi taf da mutane, kasancewar har yan’uwansa na kauye sun halarta. Haka ma Mukhtar da Kubrah sun zo.

Ranar ne kuma yaran Asiya suka ci sunan Umar da Rukayya inda ake kiransu da (Affan da Afnan)ba a yi taron suna ba.

Wanshekare kuma su Mukhtar da Kubrah suka wuce gida.

Sai bayan komai ya natsa ne Hassan ya kira dangin Rukayya da Umar ma fi kusanci dasu.

Dukiyar Umar ya gabatar masu gami da zancen Nour, don bai sani ba ko su ce suna bukatar yar dan’uwansu.

“Alhamdulillahi! Na yi farin ciki kwarai da gaske kasancewarku a nan, dama ba wani abu ne ya sanya ni cewa ina son ganinku ba, sai don in sanar maku da abin da ke tsakanina da dan’uwanku Umar. Allah ya sani rabona da jin mutuwar da ta shige ni irin wannan tun rasuwar yarona Haidar. Umar mutumin kirki ne, tsawon zamana da shi ba zan ce ga wani abu na rashin gaskiya da ya min ba. Na kan yi shawara da shi kamar yadda shi ma yake yi da ni. Na san duk wasu al’amura na shi da ya kamata in sani shi ya sa nake san sanar daku. “

Hassan ya dan ja numfashi yana kallonsu, inda fuskarshi ke nuna halin daci da zuciyarsa take ciki.

Ganin basu yi magana ba sai ya ci gaba

“Umar ya sayi fili har an fara gini, ginin ma ya yi nisa, don ya sanar min yana son matarsa ta haihu a ciki ne. Sannan akwai kudi dubu dari bakwai da hamsin wanda ya zuba a shagona. Yanzu haka na ware cinikinsa dubu dari hudu da hamsin, sannan akwai sauran kaya na dubu dari uku da 70. Sannan akwai kudin ajiyarsa da zai sayi tiles dasu dubu dari da hamsin. A akwai kuma adashe da ake yi, a wannan karshen watan shi ne zai kwasa, zai kwashi dubu dari biyar. “

Ya zuba masu ido, inda suke jinjina kai cike da gamsuwa da bayanin sa.

“kun ga dubu dari hudu da hamsin a hada da dari da hamsin. Ya zama dubu dari shidda kenan. Sai kuma kudin a dashe dubu dari biyar kun ga miliyan daya da dubu dari kenan. Sune tsabar kudi da Umar ya bari”

Baffa Adamu da ya kasance kane a wajen Baban Umar shi ne ya fara nisawa cike da jimami yake magana

“Allah ya jikan Umar da matarshi, ya kyautata makwancinsu, mu kuma Allah ya kyautata namu karshen.”

“Amin” duk mazauna wajen suka fada a kasalance.

“Kai ma Allah ya saka maka da alkairi kai da matarka da irin rikon da ka yi wa Umar, lallai na dade ban ga mutum mai kyakkyawar zuciya irin ka ba. Maganar kudi kuma ai ba huruminmu ba ne, ni tun da yana da yarinya, da dai ba shi da ‘ya ne.” 1 cewa Baffa Adamu yana kallon sauran mutanen wajen.

“Wannan gaskiya ne… ” Yayan Rukayya Musbahu ya yi saurin fada, bayan ya nisa ya ci gaba…

“Maganar Baffa gaskiya ce, Umar da Rukayya suna da mai gadonsu, don haka mu dai daga bangarenmu bamu da wata matsala idan an bar kudin nan a hannunka ka ci gaba da juyasu ga wannan yarinya da Umar ya rike. sai dai bamu sani ba ko dangin maihaifinta na da bukatar daukarta su rike a wajensu?” ya karasa maganar gami da kallonsu Baffa da suke aje kai a kasa alamun tunani.

Murmushi Baffa ya yi kafin ya ce” A’a! Ba zamu dauki Asiya zuwa ko ina ba, tun asali ma an ce ai a wurin shi Alhajin take. Don haka har yanzu dai ga amanarta nan a hannunsa muna fatan Allah ya ba shi ikon riƙewa.”

Sun tattauna sosai, inda daga karshe dai aka cimma matsaya, Hassan zai ci gaba da rikon Nour, sannan za a karasa ginin da Umar ya fara a zuba yan haya. Sannan Hassan ya ci gaba da juya kayan Umar da ke shagon don yiwa Nour wasu hidimomi.

Ya amsa dai to kawai, amma ya dauki alkawarin ko me Nour take bukata zai yi mata shi ne da aljihunsa in sha Allah.

A haka taron nasu ya tashi cike da addu’o’i ga Umar da fatan alkairi wa ahlin Hassan.

*******

Zuwa yanzu komai ya koma daidai sai dai mutuwa irin wannan takan dade tana nukurkusar mutum, kamar yadda Hassan kullum ya fita shago ya kan tuna da Umar yadda suke gudanar da harkokinsu, irin ayyukan da yake gudanarwa don ci gaban su.

A bangaren Asiya ma haka ne, kasancewar Rukayya kan taimaka mata sosai da ayyukan kungiya, yanzu da ba ta sai komai yay mata yawa, ga zuwa aiki, ga hidimar kungiya, don ku san kullum sai sun sami sabbin members da kuma masu son yin aure.

Ga rainon yan biyu wanda sam ba sauki, sannan ga hidimar gida.

Su Addah da Hajja shekaru sun ja, don tuni Hajja ta yi ritaya, hakan ya sa rainon zai zamar masu aiki, a can din ma Zee ce ke taimaka ma Hajja da wasu ayyukan musamman girki.

Wani lokaci sai ta ji kamar ta aje aikin, sai Hassan ne ke karfafa mata gwiwa.

Maman su Rukayya ce ta kawo mata kanwar Rukayyar mai suna Zulaiha.

Zulaiha ta girma sosai, saboda a lokacin tana ajin karshe a secondary .

Sosai Asiya ke jin dadin zama da ita, ba karamin taimako take mata a bangaren ayyukan gida ba har ma dana kungiya.

Sam-sam Zulaiha ba ta da son jiki, za ta wuni tana aiki ba ta gajiya, ga tsabta, wani lokaci Asiya har cewa take anya ba aljanun shara ne a kan Zulaiha ba, don wuni take abu guda, idan dai ka ji shiru to ba ta gidan ne.

Shi ya sa ko wane lokaci gidan Kal cikin kamshi, haka ma su Nour dasu Afnan suke kasancewa.

Idan kuwa aka yi baki to Zulaiha ba zama, wai an saci dan barawo, ta yi ta faman gyare-gyare kenan.

Ita ko bakin ma ba ta so a yi, wai bata gida suke yi.

*******

Sanye take cikin bakar doguwar riga, irin yadin nan mai santsi da daukar idon daga nesa. An yiwa gaban rigar ado da jajayen fulowi. Hannun rigar kuma da kasan rigar an dora masu bakin lace ja, hakan ya kara fitar da riga sosai, kallo daya za ka yi mata ka fahimci madinkin ya kware sosai.

ta yi rolling din jan mayafi mai dauke da adon duwatsu.

Sosai ta yi kyau, musamman da yanzu ta kara zama babbar mace, ta cika ta ko ina, ba mai kallonta ya ce tana da kwayar cutar HIV.

Fatarta ta yi fresh babu wani kirji ko tabo saboda maganin da take sha yana taimakawa sosai wajen gyara fata.

Turo kofar falon da aka yi ne ya sanyata juyawa hade da janye hannunta da ke kan laptop dinta.

Ta zuba masu idon hade da murmushi, lokaci daya kuma ta hade hannayenta tana tafawa alamar wasa.

Hakan yasa Affan yin zillo hade da washe baki yana son fadowa jikinta.

Zulaiha ma dariya take yi hade da dora mata Affan din a kan cinya, dama ya kosa ya ji shi a kan cinyar Asiyar.

“Wallahi kin yi kyau Aunty.” Zulaiha ta yi maganar tana kallon Asiya cike da sha’awa.

Asiya da hankalinta ke kan Affan da ya sha gayun shi sai kamshi yake yi mai dadi ta ce “Ko kina son rigar ne?”

Dariya Zulaiha ta yi sosai kafin ta ce “Kai Aunty.”

“To ai na san halinki ne, idan har zan biye miki zan yi yawo tsirara ne, saboda komai na sanya mai kyau ne a wajenki, sannan kuma in ba ki.”

Dariya Zulaiha ta kuma yi “Ayyah! Aunty! Ayyah Aunty!” a shagwabe ta karasa maganar.

“To na yi karya ne?” Ta tambayi Zulaiha lokacin da take kokarin aje Affan kasa don yana zama.

“Na isa ne Aunty. Amma idan kin banin ma ai ina so.”

Tare suka saki dariya da ke nuna suna cikin nishadi.

Lokaci daya kuma Asiya ta mayar da hankalinta a kan laptop din cikin kwarewa take sarrarfata, har zuwa lokacin da Zulaiha ta ce ” A kawo abinci ne Aunty?”

Ba tare da ta kalle ta ba ta ce

“Me kika Kwaɓa?”

“Kwaɓawa dai Aunty, wai har yanzu ban iya girkin ba?” cikin shagwaba Zulaiha ke maganar.

Har yanzu hankalinta a kan laptop din, sai siririn murmushi a kan fuskarta

“Kawo min amma kadan, kar kuma ki cika min sugar a tea.”

“Zo ki dauki yaron nan, kin san ya fara jan duwawunshi, yanzu zai raba min hankali biyu.”

Ba musu Zulaiha ta dawo ta dauki Affan.

Ba jimawa kuma sai ga ta dauke da faranti ta aje gaban Asiyar.

“Wai Afnan da Nour basu tashi ba ne har yanzu?”

“Wace Nour din kuma Aunty? Nour fa tana islamiya tun 7am na raka ta.”

Ido Asiya ta waro alamun mamaki lokacin da take kurbar tea din

“Ga ni nake fa kamar yau Monday, ashe Saturday ne.”

“Saboda ku kullum cikin aiki kuke ai shi ya sa.”

Murmushi Asiya ta yi lokacin da ta ke daukar soyayyan Irish din tana ci.

“Ki duba store ki ga madara nawa ce ta rage. Sannan da an jima zan turo Lawalli ki rubuta mishi kayan kunun Dr Brown zai je kasuwa ya sawo. Idan ya kawo ki debi iya wanda za a yi wa su Afnan sauran kuma zai kai gidan uwar biyu ta hada kamar yadda ta saba. Don rage ma kanki aiki za ki iya hada mata da rabobin duk sai ta zubo a ciki.”

Kai Zulaiha ta jinjina cike da gamsuwa.

Har zuwa lokacin Asiya abincinta take ci a natse

“Akwai wata matsalar ne bangarenki ko bangaren yara?”

Kai Zulaiha ta girgiza alamar babu.

Kafin su kara magana Hassan ya shigo, da alama fita zai yi, saboda sanye yake cikin boyel ja, da aka yi wa ado da blue din yadi, dinkin zamani ne da ya zauna a jikinsa ya cika shi ko ina.

Kamshinsa mai dadi ya garwaye falon, Zulaiha raba shi ta wuce bayan ta gaishe shi.

Bai zauna ba sai da ya dauki Affan da ke ta daga hannu alamun yana son ya dauke shi.

Kiss ya manna mishi a kumatu bayan ya daga shi kafin ya ce “Yau asubanci ya buga ne wannan malamin?”

“Ka san halinshi ai, kiran sallah farko a kunnensa.”

Zama ya yi a kusa da ita jikinsu na gogar juna”Kila limami masallacin Abuja ne.”

Suka yi murmushi tare, lokaci daya kuma ya gyarawa Affan zama a jikinsa. Cup din hannunta ya amsa hade da kai wa baki, lokaci daya kuma ya mika mata

“Ke sai kina shan abu kamar magani, wai ba sugar ne a gidan?”

“Akwai mana, ni fa tun daga cikin su Affan shi kenan bana iya sha ko cin abu da sugar sosai.”

Tabe baki ya yi “Ina jin yunwa madam”

A hankali ta Mike zuwa kitchen ta hado mishi breakfast din a babban tire ta aje gaban sa.

A lokacin tea yake ba Affan.

“Madam kin yi kyau fa.”

Sai da ta juya ido wanda ke nuna jin dadin maganarsa kafin ta ce “Na gode. Kai ma haka ka yi kyau. Kullum kara murjewa kake zuwa babban mutum mai cikar zati da kamala.”

Murmushi ya yi hade da kika hannu ya karbi tea din da take muka mishi ya kurba a hankali.

“Haka dai kowa ke cewa.”

Baki ta bude da ke nuna alamun mamaki

“Kowa fa ka ce? Su waye kowa din?”

Dariyar da yake ta boyewa ce ta sarke shi don haka ya aje tea din yana tare a hankali.

“Sorry!” ta fada a hankali.

“Thank you” ya fada hade da yin dariya mai dan sauti.

Ita kuma ta hade rai kamar ba ta a wajen.

Hakan ya sa ya ci gaba da cin abincinsa hankali kwance hade da wasa da Affan. Lokaci zuwa lokaci kuma ya kan kai kallonsa a kan Asiya da ke tsugunne gabansa ta juya kanta gefe.

Tun da ta hada mishi tea din ta Mika masa take tsugunne, ya kuma san a kan maganar da ya fada ce.

Asiya na da mugun kishi, irin kishin nan da ba ta iya boyewa, ko ya ne sai an gan shi a kan Fuskarta.

Tissue ya sanya hade da goge hannunsa ga mi da bakinsa, ya mike tsaye hade da fadin “Alhamdulillahi! Kin shirya fita ne? Ni zan wuce.”

Ba ta yi magana ba, sai dai ta mike hade da tattara duk wasu kaya da za ta bukata, rungumesu ta yi a kirjinta hade da raba shi za ta wuce.

“ki koma ki saka hijab.”

Ba ta yi magana ba ma a wannan karon, komawa ta yi cikin bedroom ta dakko Hijabin mai ruwan toka ta sanya, har kasa ya sakko mata sannan ta saka hannun hijabin hade da rungume takarcenta ta kuma raba shi ta fice.

Murmushi ya yi saboda ya san ta shaka, fushinta shi ne rashin maganarta.

Fita ya yi sabe da Affan, ya fara kwallawa Zulaiha kira.

Ta amsa cikin sauri kuma ta nufo inda yake, yayin da Asiya ke bin bayan ta sabe da Afnan da ta tashi bacci.

Mika mata Affan ya yi bayan ya kama hannun Afnan ya girgiza alamar wasa sannan ya fice.

Ba jimawa Asiya ta biyo bayanshi.

A lokacin tsaye yake gaban motarsa yana waya, dalilin da ya sa kenan ta nufi inda ta ta motar take.

Zulaiha ce ta kuma fitowa ta bude masu gate. Ganin ta tsaya alamun tana jira su fita ta rufe sai Hassan yay mata nuni da ta koma gida kawai zai rufe.

AAsiya tuni ta nufi gate da motarta, yana kallo ta fice, shi dariya ma take ba shi.

Yana mamakin irin kishin ta.

Kuma lalurarshi ce kawai za ta hana shi aje mata biyu, bayan haka kam bai jin zai rayu da mace daya.

<< Labarin Asiya 21Labarin Asiya 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×