Skip to content
Part 23 of 25 in the Series Labarin Asiya by Matar J

Tun da ta shiga office sai ayyukan da taras suka dauke mata hankali, ba ta samu kanta ba sai karfe goma na safe inda ta fito don gabatar da shirin wasa kwakwalwa, wanda ita ce ke jagorantar shirin.

Shiri ne mai farin jini da mutane da yawa kan saurara, shirin na daya daga cikin shirye-shiryen daya kuma sanya sunan Asiya ya yi fice ya watsu a kunnuwa na jahar da ma makwabta, saboda yadda take jan shi cike da kwarewa gami gangariyar hausa.

Akwai masu yo tafiyayya don kawai su ga wacece Asiya Abdallah Baba.

Sannan shirin akan hada shi har da FM din gidan Radion, dalilin da ya sa kenan mutane da yawa ke samun damar saurara har a wayoyinsu na hannu.

Hatta yan makaranta ba a barsu a baya ba, kasancewar weekend ne suma suna manne da radio.

Zuwa karfe goma daidai injjniyan ya sada masu sauraro da shirin da suke dako.

Muryarta mai zaki gami da sanyi ta ratsa akwatin gidan Radion, a daidai lokacin da Hassan ya kamo tashar a karamar wayarsa ya aje gefensa, don shi ma yana daya daga cikin mutanen da ke sauraron shirin, sannan idan dai lafiya baya wuce shi.

“Assalamu Alaikum masu sauraronmu, kamar yadda kuka sani dai sunana Asiya Abdallah Baba, a yau ma cikin Ikon Allah ga shi mun dawo maku dauke da wannan shiri mai farin jini, nishadantarwa gami da fadakarwa.

Kamar yadda kuka sani dai wannan shiri yana da bangare biyu, bangaren muhawara da kuma tambayoyi, akwai kyaututtuka ga duk wadanda suka amsa tambaya daidai. A wannan karon dai zamu fara da sashe muhawara ne mu rufe da tambayoyi, amma kafin sannan bari ku ji wadanda zasu taya mu gabatar da shirin.”

Bayan yan wasanni da tsokanar juna kamar yadda suka saba sannan suka fara gabatar da sunayensu daya bayan daya.

Hakan ya sa Asiya ta fada cikin shirin gadan-gadan.

“Bari mu yaye kallabi shirin da wasikar da muka samo daga Baban Muhsin mijin kan ta ce da ke Zaranda Street”

Duk suka yi dariya saboda jin sunan mai rubuto wasikar, kafin Asiya ta dora.

“Baban Muhsin dai mijin kan ta ce, ya ce yana son a gano mishi a cikin mutanen nan wa ya fi sakarci…”

Ta dan ja numfashi

“Wasu mutane ne ke tafiya don zuwa wata kasuwa da ke makobtaka da garinsu. Bayan sun yi tafiya mai nisa sai barayi suka taresu. Amma barayin nan basu samu wani abun kirki a jikin mutanen nan ba, don haka suka ce su cire masu kayan jikinsu duka.”

Dariyar masu gabatar da shirin ta rasa akwatin Radion.

Hassan ma da ke zaune yana lissafa cinikin da aka yi jiya, ya yi murmushi hade da mayar da hankalinsa sosai don jin yadda za ta kaya.

“To bayan sun tube masu kayan sai suka ci gaba da tafiyarsu. A kan hanyarsu suka tsinci wani akwati, dalilin da ya sanya su komawa gefe suka bude sai kuwa ga kudi tsaba cike da akwatin nan…”

“Toh fah!” wani daga cikin masu taya ta gabatar da shirin ya fada.

Hakan ya sa kananun maganganu ya tashi wanda duk abin dariya ya fi yawa.

Ganin an natsa sai Asiya ta ci gaba.

“Sai suka yi shawara a kan mutum na farko ya debi kudin nan ya shiga kasuwa ya sawo abun da yake so, bayan ya dawo mutum na biyu ma zai diba ya je. Aiko sai mutum na farko ya debi kudi ya nufi kasuwa, zuwa can sai ga shi ya dawo daure da belt a kugunsa, bayan belt din nan fa bai sawo komai ba. Kar ku manta kuma fa babu ko dankanfai a jikinsa “

“lallai wannan ya kai soko.” Hassan ya fada cike da murmushi a kan fuskarshi.

“Mutum na biyu kuma da ya je sai sawo glass ya sanya fuskarsa ya dawo. Na ukun kuma ya sawo agogo ya daura a hannunsa ya dawo. Don haka cikin su uku nan wa ya fi wawanci”

Take fa zauran ya rikice kafin aka natsa Asiya ta kira lambar da za a same su, sannan ta rika bin malaman zauran daya bayan daya tana jin ra’ayinsu. Wanda hakan ya kara nishadantar da mutane.

Masu kira ma sun karawa abun armashi, har zuwa lokacin da Asiya ta rufe shirin da

mutane ke ganin kamar ba a yi awa daya ba saboda yadda suke jin dadinsa.

Misalin sha biyu da rabi ta baro gidan Radion, tun da ta fito zuciyar ta ke raya mata zuwa gida, don kuwa ta yi wajen sati biyu ba ta je ba.

Daga karshe dai zuciyar tata ta fi rinjaya zuwa gidan, shi ya sa kawai ta karkata motar tata zuwa gidan.

A gate din farko ta yi parking, wayarta kawai ta dauka ta kulle motar sannan ta shige gida.

Tun da ta yi sallama sashen Addah ta ji shiru ta san bacci take yi.

Hasashenta kuwa ya yi daidai don kwance ta same ta a kan fankacecen gadonta ga sanyi ac gami da turaren wuta, dole ma mutum ya yi bacci.

A hankali ta fito don kar ta tashe ta, bangaren su Aunty amarya ta wuce, a babban falon ta same su kasancewar lahadi ce, dukkansu suna shigar da mark ne a cikin CA sheet.

Zama ta yi ta gaishesu cikin girmamawa, inda suke fada mata yadda suka ji dadin shirinta na yau, sun dade suna tattaunawa a kan shirin kafin Asiya ta mike don zuwa sashen Hajjah.

“Ga Nono can a fridge Babanki ya kawo jiya, dama ina jiran su Asma’u su dawo islamiya mu ji ko zasu kai miki, tun da kuma ga shi kin zo kin ga shi kenan, nesa ta zo kusa.” Cewar Umma tana kallon Asiya.

Cike da jin dadi ta nufi fridge din, wannan shi ne aikin Baffana nata, nono yana gyara jiki hade da matukar muhimmanci a jikin mutum, musamman su da suke dauke da wannan cutar, shi ya sa Baffa ke sayen lafiyayyan nonon yana aikawa Asiyar.

Godiya ta shiga yi lokacin da ta ciro nonon sannan ta dauki hanyar fita.

Tun da ta bude kofar main falon take jin hayaniyar yara, wannan ya tabbatar mata yaran Jamila sun zo weekend kenan.

Tana shiga kuwa suka yo kanta a guje cike da daukin ganinta, ita din ma sosai ta nuna masu ta ji dadin ganin su.

Gaban laptop ta iske Hajjah, hakan ya sa ta cire dogon hijabin nata ta zauna a gefen ta hade da turawa laptop din ido don ganin me Hajjahn ke yi, a kuma haka suka gama gaisawa hankalin Hajjah a kan laptop din.

Bayan yan sakanni kuma sai Hajjahn ta dago hade da zare gilashin da ke fuskarta (medical glass) “Dazu nake tunaninki, har na fara tunanin tura Zee ta dubo min ku lafiya dai ko?”

Murmushi Asiya ta yi, cike da jin dadin kulawar Hajjahn garesu, lokaci daya kuma ta jawo laptop din zuwa gabanta

“Lafiya ƙalau, ayyukan ne yawa suke min wallahi Hajja, kamar in aje aikin nan” A shagwabe ta karasa maganar.

Ido Hajja ta zuba mata kafin ta ce “A’a! Sam ba maganar aje aiki, yanzu ne fa kike kara gogewa da aikin, yanzu ne sunanki da baiwarki ke bayyana, sai kuma ki ce za ki ajiye, ki cire wannan tunanin gaskiya.”

“Hajjah gidana baya samun kulawata, wani lokaci 5am na fita, daga can zan iya wucewa asibiti sai ki ga wani lokaci har Abban yaran ya rigani komawa gida. Wallahi abun na damuna.”

Shiru Hajjah ta yi kafin ta ce “Kungiyar za ki tsara ma time table, ya zama a sati duka sau biyu ko uku ne za ki gana da marasa lafiya, ko kuma ma dai duk abin da ya shafe ta, bawai kina abu rondamally ba tsari ba.”

Asiya da take kallon Hajjah murmusawa ta yi cike da jin dadin shawararta.

“Wai me ya samu laptop din ta ki na ga komai a rikice?” ta yi maganar hade da janyo laptop din sosai gabanta.

“Uhmm! Ina zan sani, na san dai yaran nan ne, Abdallah ko Zee, amma dukkansu sun ce wai basu ba ne.”

“Ba security ne?” Asiya ta yi tambayar hankalinta a kan laptop din a kokarinta na saita komai.

“Akwai fa. Yara ne kamar mayu wlh, ko na canja sai ki ga sun gano.”

Shiru Asiya ta yi ba tare da ta ce komai ba don so take ta gano matsalar.

Hakan ya sa Hajjah mikewa tana fadin “bari in yi sallah.”

Kai Asiya ta jinjina kawai.

Har Hajjah ta idar da sallah Asiya ba ta daidaita matsalar ba.

Hakan ya sa Hajjah shiga kitchen don zubawa yaran Jamila abinci.

Tsawon awa daya Asiya ta daidaita komai, dalilin da ya sanyata mikewa kenan zuwa toilet ta dauro alwala, Hajjah kam na can na fama da yaran Jamila Bilal da Ammar.

Bayan ta idar da sallahr falon ta fito ita ma ta nemi abinci.

“Na daidaita miki komai, amma ki canja security, ki daina bari yaran nan suna taba miki.”

“To ai na gama duk yan tsince-tsincena na pin wallahi, ban san me zan sanya ba kuma.”

Dariya sosai Asiya ta yi kafin ta ce “Ki kara lalubowa, Babana shiru Hajjah kuma tafiya zan yi.”

“Ina jin har yanzu basu gama taron ba, don na gwada lambarshi ma a kashe, alamar suna dakin taron. Kar ki damu idan ya ji kin zo, gobe za ki iya ganin shi gidanku ai.”

“Zai iya kam wallahi, kuma dadi nake ji sosai idan na gan shi.”

“Haka Jamila ma ta ce.”

“Hajjah tafiya zan yi, na so ganin su Zee kuma na san su da nan sai 6pm idan sun dawo a gaishe su.”

“Zasu ji sha Allah. Ki gaishe da su Afnan din iyayen kiwa.”

“Suna nan kam suna yi, wani lokaci ko Zulaiha basu yarda da ita, idan suna jin rikici.”

Gwalo ido kawai Hajjah ta yi hade da rike baki alamar mamaki.

A daidai lokacin kuma Asiya ke hada tarkacenta don tafiya gida.

“Yarana ku zo mu je ku amshi kudin shan Bobo, ban san kun zo ba, ban zo maku da komai ba, amma idan Zee ta dawo ta sawo maku Bobo da Biscuit na zuwa school.”

Cike da murna kuwa suka bi bayanta, yayin da Hajjah ke murmushin jin dadin ahlin nata.

Sashen Addah ta biya suka gaisa a tsaitsaye, sannan ta nufi inda ta yi parking motarta. 5k ta ciro ta ba su Bilal suka shige ciki a guje suna murna.

Yayin da ta yi wa motarta key ta fice don zuwa gida.

Lokacin da ta isa Nour ce ta bude mata gate, lokaci daya ta dauki tarkacen da Asiya ta shigo dasu, lokacin da suke shiga corridorn ne Asiya ke tambayarta makaranta, ita kuma tana amsa mata da sansanyar muryarta.

Zulaiha ta fito daga kitchen dauke da Affan, da alama girki take yi.

Kan kujera ta zauna hade da dafe kanta, wani irin ciwo yake mata, ba tun yanzu ba, har ta gaji da hadiyar mishi magani.

“Mummy har yanzu kan?” Zulaiha ta tambaya, saboda ita kadai ce ta san Asiya na fama da ciwon kan a cikin yaran.

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “ki bari fa. Musamman yau da na sha hayaniya.”

“Amma kuma Aunty shiriin ya yi dadi, kodayake kullum ma yana dadi” ta karasa maganar cikin dariya.

Asiya ma dariyar ta yi hade da zamewa ta kwanta kan kujerar, tare da fadin “Idan akwai ruwan zafi a dan hada min tea, in sha kafin nan in yi sallah.”

Nour ta nufi kofar kitchen din da sauri, Zulaiha ta bi ta da kallo, sannan ta juyo da kallon nata wurin Asiya tana fadin “Mommy ita za ta hado miki tea din?”

Ta bi hanyar kitchen din da kallo, sannan ta ce “Leave her please, Nour tana son ta ga tana min abu.”

“Za ki sha kwabe.” cewar Zulaiha.

“Ba komai, zan sha haka nan.” Asiya ta amsa lokaci daya kuma tana ta shi zaune, ganin Nour na fotowa daga kitchen.

Lumshe ido ta yi bayan ta kurbi tea din hade ta kamo hannun Nour ta yi kissing sannan ta ce “Thank you Rabin Raina.”

Nour ta yi tsadadden murmushinta hade da kallon Zulaihat.

Zulaihat ma murmushi ta yi hade da wucewa zuwa dakinsu.

Nour da Aunty Zulai ne suka karasa girkin abincin, yayin da Asiya ta wuce dakinta hade da watsa ruwa ma dan zafi.

Misalin karfe takwas ta ji shigowa Hassan, tana jin sa yana ta surutu da su Zulaihat a farfajiyar gidan, a lokacin da suke taya shi shigar da kaya cikin babban store. Wannan ya tabbatar mata kila tallafin da suke jiran isowarshi daga wata kungiya a waje ne ya iso.

Sai 8:45pm ya shigo bedroom din nata, a lokacin kwance take a tsakiyar gadonta, yayin da Afnan ke kwance a gefenta tana barci.

Ta amsa sallamar sa hade da mikewa ta zauna sosai a tsakiyar gadon.

“Kina fushi ne har yanzu?”

Girgiza kai ta yi alamun a’a

“To ba ki ji dawowa ta ba?” ya kuma tambaya idanuwansa a kanta.

“Na ji, kaina ne ke ciwo.”

Wani irin faduwa gabanshi ya yi, da haka Umar ya fara, da yawan wadanda suke rasuwa masu dauke da irin cutarsu, da ciwon kai suke farawa.

Cikin sauri ya matso kusa da ita tare da tambayar “Kin sha magani?”

“Na sha.” ta amsa a sanyaye, haka nan ita ma gabanta ke faduwa, ji take kamar tana bankwana da duniyar.

“Tun yaushe ne?” ya kuma tambaya.

“Na dan jima, kawai dai ban fada ma ba ne.”

“But why?” ya yi saurin tarar numfashinta

“Ba na son in tashi hankalinka ne.”

“Please ki bari mana, Rabin Raina har Sai na fada miki me yawan ciwon kai yake nufi ga masu cuta irin tamu? Ke ce fa kike fada ma wasu, da zarar sun ji ciwon kai mai tsanani su nufi asibiti, ke kuma kina zaune. Please ta shi mu je asibiti yanzu.”

Wayarta da ke gefe ta taba, kafin ta ce” 9:15. Mu hakura zuwa gobe idan Allah Ya kai mu. “

Jikinsa ya janyota cikin kasalallar murya ya ce” Kin san abin da nake tsoro Rabin Raina, ba na son rasa ki, rasa ki yana nufin rasa duk wani kwanciyar hankalina, ban da raina ba a hannuna yake ba, to zan iya ce miki ni ma mutuwa zan yi, saboda rayuwata da ke ne take da armashi. “

Hawaye masu dumi suka gangaro mata, ta kai hannu hade da gogewa sannan ta ce” Ni kuma fatana kullum shi ne in riga ka mutuwa, saboda za ka fi ni kwarin gwiwar ci gaba da rayuwa da kula da yaranmu, koda na mutu Rabin Raina don Allah ka kula min da Nour, tausayinta nake ji. “

A hankali ya dagota daga jikinsa, hannunsa ya kai yana dauke mata hawayen da ke bin kuncinta.

“Stop saying this please, I akwai mutane da yawa, wadanda farin cikinsu yana karkashinki, kungiyarmu tana da membobi sama da hamsin, wadanda kullum bayan ubagijinsu, ke ce ta biyu da suka dogora da ita, suna rayuwa da kwarin gwiwar da kike basu, da yawansu basu sanni ba, basu san su Mukhtar ba, ke suka sani. Ga Nour da har yanzu ba ta sakewa da kowa sai ke, don Allah ki daina irin wannan furucin. “

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta ce” Rabin Raina kullum ina rasa kwarin gwiwata ta dalilin mafarkaina, kullum mafarkaina a kan wadanda suka mutu ne, shi ya sa kullum nake ganin kamar dai ana yi min ishara ne.”

Hannayen du biyu ya rumtse cikin nashi, sannan ya ce” Wannan baya nufin komai sai alkairi, ki je you tube ki yi searching Annahajul huda TV, za ki ga fassarar irin wadannan mafarkan, ki cire damuwa, ina da tabbacin ita ke sanya miki ciwon kai. “

Kai ta jinjina a hankali, yayin da shiru ya ziyarci dakin, ita ce ta katse shirun da fadin” Ka ci abinci ne? “

Kai ya girgiza alamun a’a.

Ita ce ta fara mikewa sannan ta ce” Mu je ka ci, ni ma ban ci ba, amma zan ci yanzu. ” ta karasa maganar hade da kamo hannunshi ya mike tsaye, sannan suka fice.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Labarin Asiya 22Labarin Asiya 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×