Skip to content
Part 24 of 25 in the Series Labarin Asiya by Matar J

Kashegari da misalin karfe takwas ta fito babban falon cikin shiri, doguwar rigar shadda ce a jikinta fara tas wacce ta Sha zubi, ba kowa falon, kasancewar yaran gidan duk sun tafi makaranta, su Afnan kuma suna dakin Hassan.

Tana kokarin shiga corridorn da zai sada ta da dakin Hassan din ne, ta ji ana buga kofa, dole ta dawo baya hade da nufar kofar

“Waye?” ta tambaya ba tare da ta dakata ba.

Daga ta ji muryar mace tana fadin “Ni ce, Hajiyar na gidan ne?”

A hankali Asiya ta bude kofar bayan ta murza key din, suka zubawa juna ido, ita da matar kafin matar ta katse kallon kudar da sukewa juna ta, hanyar dukawa tare da fadin “Hajiya ina kwana?”

“Lafiya kalau, ta shi mana” cewar Asiya tana kallon yara biyu mace da namiji da suke tare da matar.

“Don Allah nan ne gidan Hajiya Asiya, wacce ke aiki a gidan radio, kuma tana da wata kungiya ta masu cutar kanjamau?”

“Eh nan ne” Asiya ta kuma amsata fuskarta dauke da murmushi.

“Alhamdulillah” Matar ta fada, har lokacin ba ta tashi daga tsugunnen da take ba.

“Bismillah, ku shigo ciki mana”cewar Asiya a lokacin da take nuna musu hanyar shiga.

Matar ta mike rike da hannayen yaranta guda biyu, har zuwa babban falon da yake dauke da manyan kujeru set biyu, Sai dinning area wanda aka kawata da curtains da kuma fulawoyi masu kyau.

A kan kujerar suka zauna, yayin da Asiya ta nufi dinning ta hada musu tea da bread, kasancewar abin da suka karya da shi ya kare.

Don daga ita har Hassan suna karyawa ne tare da yaran, koda kuwa akwai school.

“Bismillahnku!” ta yi maganar daidai tana ajiye abincin a gaban matar.

“Ni dai na koshi, Sai dai ko yaran”

Ta bi matar da kallo, ba tun yanzu ta fahimci jibgin damuwar da ke shimfide a kan fuskarta ba.

Saman kujerar da ke fuskantar matar ta zauna, bayan ta hanadawa yaran tea ta ba kowannen su. Cike da kulawa ta ce “Ina fatan dai lafiya kike nema na, saboda ni ce Asiyar.”

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta ce “Sunana Suwaiba.”

Jinjina kai Asiya ta yi hade da mayar da hankalinta wajen Zainab lokacin da take dauke hawayen da ke zarya a kan kuncinta.

Cikin murya kuka ta ce “Zuwa na yi ki taimakeni, shekarata goma sha bakwai tare da mijina, na jure duk wata babu ta shi, saboda wlh wani lokaci Idan ya tafi neman kudinshi, Sai mu yi wata ficikarshi ba mu gani ba, ga yara zube ba makaranta, ni ce nake fadi tashin ciyar dasu, iyayena sun so rabamu, amma makomar yarana nake tsoro, musamman da ya kasance dukkansu biyar din mata ne, daya ne kawai namiji.”

Ta dan tsahirta, lokaci daya kuma tana kallon Asiya da ta tattara dukkan hankalinta a kanta.

“Hajiya Ina cikin tashin hankalina ni da yarana, wlh ji nake kamar in kashe kaina in huta saboda bakin ciki, mijina wurin yawace-yawacen shi ya dakko min cuta kanjamau. Karin takaici shi ne ba ni kadai ya gogamawa ba, har da yarana biyun nan, Ya san yana da cutar ya rika kusantata Hajiya… “cikin wani irin kuka mai daci gami da cin zuciya, a daidai kuma lokacin ne Hassan ya fito rike hannayensa rike da Afnan da kuma Affan.

Tun da ya fito yake kallon Asiya da kuma Suwaiba wacce ke ta kuka, kamar ta shiga gasar kuka ta duniya.

Knocking din da aka yi ne, Ya sanya shi nufar kofar.

“Abdallah!” Asiya ta furta lokaci daya kuma tana kallon Abdallahn da yake sanye cikin uniform din makaranta.

“Me ya faru?” Hassan ya tambaye shi lokaci daya kuma yana kare mishi kallo.

“Kudin hoto ne Addah ta ba ni, kuma kudin sun fadi, ga shi yau ne date line na karbar hotunan.” ya yi maganar hade da turo baki.

Asiya da ke can zaune ta ce “Da kyau! Hakan ya yi ma kyau ai. Dama ba karatun kake so ba, kuma karya kake kashe kudin ka yi ba faduwa suka yi ba.”

“Wlh faduwa suka yi?” kamar zai yi kuka ya yi maganar.

“Humm! Fada ma wanda bai sanka ba” Asiya ta kuma fada cike da takaici.

“Nawa ne kudin?”
Hassan ya tambaya idonsa a kan Abdallah.

“500 ne” shi ma amsa a hankali.

“Zo nan Abdallah” cewar Asiya tana kallon shi.

A hankali ya tako har zuwa wajen ta.

Tsaye ta mike hade da zare jakar da ke goye a bayan shi, lokaci daya kuma ta shiga zazzageta, daya bayan daya ta rika bude littafan, har zuwa lokacin da ta ci karo da passport din shi guda 12, cike da takaici ta dago kanta hade da kallon Abdallah wanda hankalin sa ya gama tashi, so yake ya gudu, Sai dai Hassan har yanzu yana bakin kofar.

“Me ye wannan?” ta yi tambayar daga zaunen da take.

Cikin tsawa ta kuma cewa “Na ce me ye wannan?”

Kai karshen maganar tata ya yi daidai da mikewarta tsaye, yayin da Abdallah ya yi saurin ja baya.

Hakan bai hanata daga hannu ta nufi kuncinsa ba, a hanzarce Suwaiba ta rike hannun nata, lokaci daya kuma tana fadin “A yi mishi hakuri, yaran yanzu Sai addu’a ba duka ba.”

Cike da takaici Asiya ke fadin “Me Abdallah ya rasa a rayuwarsa? Komai yana samu, bai rasa komai ba, ci, Sha, suttura, kula da lafiyarsa, ilmin shi, tufafinsa, bai rasa komai ba. Duk wani nauyi na shi mun sauke, amma hakan bai hana shi yin abin da zai bata mana rai ba, kullum cikin daukar magana. “ta kai karshen maganar tata cike da kunar zuciya.

“Zo mu je school din naku?” cewar Hassan yana kallon Abdallah wanda ke manne da gini a tsorace.

Asiya ta tattare tarkacen jakar ta shi, hade da watsa mishi, daidai lokacin da Suwaiba ke fadin “Yaro ka godewa Allah wasu neman irin wannan damar suke ido bude basu samu, kai ka samu kana wasa da ita, a wannan zamanin ba karamin arziki ne Allah Ya hadaka da iyayen da zasu sauke duk wani nauyi na dansu a kansu ba. Yaran nan da ke gabana sun ishe ka misali, da ka kalle su kasan basu sami abin da ka samu ba”

Zuwa lokacin tuni Abdallah ya kai kofa, yayin da Hassan ke fadin “Za mu je asibitin ne?”

“Ina da bakuwa, Idan mun gama da ita zan je, ka je kawai, amma ka tafi da su Affan can gida.” har zuwa lokacin ranta a bace yake

“Please ki tabbatar kin je don Allah.”

“Zan je in Sha Allah.”

A lokacin ne kuma Suwaiba ta gaishe shi cike da girmamawa. Ya amsa ta hade da ficewa daga falon.

Ta juyo kan Asiya wacce har zuwa lokacin ba ta warware ba, cikin sigar lallashi ta ce “Hajiya yara sai hakuri. A yi ta yi mishi addu’a”

Cike da rashin kuzari ta ce “Wlh ina yi mishi addu’a, amma ba ya jin magana, tare yake da wasu yara da sune suke kara bata shi, mun yi-mun yi su ya rabu dasu amma abun ya ci tura.”

“A cikin Unguwa suke yaran ko a makaranta?” Suwaiba ta tambaya a nutse.

“Makarantarsu daya, amma sai a SS-1 ya hadu dasu. Wlh mun yi report din wa hukumar makaranta, amma har yanzu, har class aka canja aka raba musu, amma ki rasa a ina suke haduwa”

Suwaiba ta nisa kadan sannan ta ce “Ai kin san yaran nan, su duk hanyar haduwa da junan zasu nemo ta, mafita kawai ku cire naku yaron daga makarantar.”

“Kuma fa kin kawo shawara, kin ga kuwa shi kenan, dama a school din suke haduwa. Duk da sun kusa rubuta final exam wlh haka nan zan shiga in fita a canja mishi makaranta, sannan zan sa Babansu ya rika zuwa da shi kasuwa, kin ga an yi maganin yawon banza.” cewar Asiya tana kallon Suwaiba.

“Kwarai ma kuwa, ai da an ga yaro ya dakko hanyar lalacewa, to da farko Sai a fara duba daga Ina ake samun barakar, Idan a makaranta Sai a canja mishi makarantar, Idan kuma cikin Unguwa Sai a nema mishi abin da zai zamar da shi busy, ta yadda ba zai samu lokacin haduwa da abokan na shi ba.”

“Wannan gaskiya ne, na kuma gode da shawara. Na ji dadin zuwan ki gidan nan, Sha Allah yau zamu tattauna, zuwa gobe kuma zamu fara daukar mataki.”

“Allah Ya yi jagora”

“Amin.”Asiya ta fada lokaci daya kuma tana gyara zamanta sannan ta ce” Muna magana dazu, kuma sai Abdallah ya yanke mu”

Yanayin fuskar Suwaiba ya canja zuwa bacin rai da damuwa irin dai an fama mata ciwon da ke damunta. Jiki a mace ta ce “Abin da na fada miki ne Hajiya, yanzu haka ni da yaran nan” Ta nuna yaran wadanda hankalinsu ke kan TV) in muna dauke da cutar nan. “

“Ya aka yi kika san kina dauke da cutar, kuma kika dora alhakinta a kan mijinki”Asiya ta yi tambayar idanuwanta a kan Suwaiba.

“Shekaranjiya aka kawo shi babu lafiya, jiya mu ka je asibiti aka tabbatar mana yana da kanjamau, dalilin da ya sa aka gwadamu gabadayanmu har yara, gwaji ya nuna ni da yaran can muna dauke da cutar. Ni kuma da shi kawai na taba hada shimfida.” ta kai karshen maganar tata hade da fashewa da kuka, irin kukan nan da ke nuna lallai mutum na jin zafi sosai.

Sosai take tausayin Suwaiba, hade da jin irin zafin da take ji, ita ma shekarun baya ta tsinci kanta a irin wannan gabar, gabar da ta ji ta fi kaunar mutuwa a kan rayuwarta, har yanzu kuma wani lokaci tana jin dacin abun,bare Suwaiba da aka sako yaranta a ciki

“Ki yi hakuri, za mu je asibiti yanzu ki kara ganin likita, daga nan sai mu ga abin da ya kamata a yi.”

“Hajiya ina son a bi min hakkina, zuwa na yi ki taimakeni in shigar da kara.”

Murmushi Asiya ta yi kafin ta ce “Ba shi ne abu mai muhimmanci ba yanzu Suwaiba, kuma magana ta gaskiya kungiyarmu ba ta da wani link da court, mu kawai muna tallafawa masu cutar ne da magunguna, abinci wa yara kanana, Sai kuma auratayya.”

“Shi kenan yanzu ya cuce ni a banza…” kuka ya sarke ta, wannan ya sa Asiya dawowa kusa da ita hade da dafa kafadarta “Ki daina fadin haka, ko wane bawa da kaddararsa, sannan Allah yana kallon komai, shi ne zai saka miki ta hanyar da ba ki yi tsammani ba, yanzu dai ta shi mu ta fi asibitin.” ta kai karshen maganar tata hade mikewa tsaye tana sanya dogon hijabin ta.

Sai da ta fara shiga store ta duba kayan da Hassan ya ajiye jiya, sannan suka wuce asibiti ita da Suwaiba.

Sai da Asiya ta fara ganin likita a kan lalurarta, Ya kuma tabbatar mata da yawan damuwa ne ke sanya ta ciwon kan, shawarwari kawai ya ba ta, sannan ta gabatar mishi da Suwaiba da kuma yaranta.

Sai da aka yi musu test dukkansu, aka basu magunguna, sannan Asiya ta koma bangaren kungiyarsu, inda ta yi musu register hade da basu kayan abinci.

Har gida ta kai Suwaiba, ta hada su ita da mijin ta basu shawarwari, karshe dai mijin Suwaiba ba ma ya nemi da a sanya sunan shi a kungiyar.

Ba ta dawo gida ba sai 6pm, kusan tare suka shigo da Nour da kuma Zulaiha wadanda suka dawo daga islamiya. Daki ta wuce ta yi wanka, sannan ta yi sallahr magriba. Nour ce ta kawo mata abinci. Tana ci suna hira cikin nishadi, Sai da aka kira sallahr isha’i ne suka ta shi, Asiya kuma ta kabbara sallah.

Kamar ko wane lokaci misalin karfe takwas ba dare Hassan ya dawo, Kai tsaye dakinta ya nufa.

Zaune take cikin doguwar riga rubber material mara nauyi, Sai kamshi mai dadi da ke ta shi a falon.

“Ba ki dakko su Affan ba?” ya yi tambayar bayan amsa gaisuwar da take mishi.

“Ban samu na je gidan ba, I’m so committed wlh.”

“Amma dai ai kin ga likitan?”

“Ba na fada ma”

“Na dauka wasa kike yi”

Sai da ta yi Murmushi sannan ta ce “Da gaske na gan shi, kuma yadda na fada ma a waya dai hakan ya ce min.”

“To Allah Ya kara lafiya, Sai ki rage sanya damuwa don Allah.”

“Zan yi kokari” ta fada hade da mikewa ta nufi bedroom don hada mishi ruwan wanka.

Sai da ya kammala komai har cin abinci, sannan ta ba shi labarin Suwaiba da abin da ya kawo ta.

Sosai ya tausaya hade da alhinin abun.

Ta juya hirar tata a kan Abdallah da fadin “Ina jin kawai a canjawa Baaba makaranta?”

“Saboda me?” ya yi saurin tambaya.

“Saboda kullum rashin jin kara gaba yake.”

“To me ye hikimar yin hakan?”

Gyara zama ta yi sannan ta ce “Hikimar yin hakan shi ne, na farko dai an raba shi da wadannan abokan da sune suke rushe duk wani gini da mu ka yi. Ka ga Idan ya koma sabuwar makarantar zai fara sabuwar rayuwa, kafin ya waye da ita kuma ya gama. Sannan ka rika fita da shi kasuwa don Allah. “

Ya dan yi shiru cikin nazarin kalamanta, kafin ya ce” Amma ya kusa gamawa, just 2 months remain. “

“A wata biyun nan ko, to abubuwa da yawa zasu iya faruwa. “

Kai ya jinjina tare da fadin” To Idan an tafi da shi kasuwar islamiyar fa? “

Murmushin takaici ta yi tare da fadin” Yo zuwa yake yi? Ai ba wata islalamiyar da Abdallah ke zuwa, yawon banzar shi kawai yake tafiya. “

Cike da kunar zuciya Hassan ya ce” Ya subhanallah. Why all this please “

Cikin jimami ta ce” Allah masani, fatanmu dai Allah Ya shirye shi”

“Shi kenan. Ni zan je school din nasu gobe, Idan Allah Ya kai mu, Idan kuma ke za ki je to, sai in wuce kasuwa”

“Gaskiya gobe Ina da Hidimomi da yawa, zan je aiki 12pm zuwa 3pm,zan je wurin masu ginin sabon office namu, sannan zan je gidan Suwaiba, in dan kara duba lamarin mijinta. Kubrah ta ce a ba shi jari, so ina tsoron a ba shi jarin, yana jin ya murmure ya gudu, kamar yadda wasu mutanen ke yi”

Kai ya jinjina alamun yana fahimtarta.

“Ban sani ba ko kun tattauna da Mukhtar, Ya ce kungiya ta dauki nauyin karatun yaran Suwaiba biyu masu cutar”

“Eh tabbas ya kira ni,sai dai na nemi excuse, because I’m too busy at that time, but I will call him tomorrow in Sha Allah.”

“Allah Ya bayar da iko”

“Amin” ya amsa lokaci daya kuma ya mike tsaye hade da nufar gado ya kwanta.

Washegari Hassan da wuri ya fita, saboda zuwa makarantar su Abdallah, Asiya kuma kai tsaye gidan Suwaiba ta nufa a lokacin da ta fita, daga can ta wuce wurin aikinta, bayan ta tashi daga aiki kuma ta wuce wurin masu aikin gini.

Haka rayuwa ta ci gaba da turawa, cikin yanayi mai dadi, musamman a bangaren Asiya, komai ta taso gaba, cikin kudurar ubangiji Sai ta ga ta kammalashi successfully.

Babu abin da za ta ce sai dai Alhamdulillah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Labarin Asiya 23Labarin Asiya 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×