Kashegari da misalin karfe takwas ta fito babban falon cikin shiri, doguwar rigar shadda ce a jikinta fara tas wacce ta Sha zubi, ba kowa falon, kasancewar yaran gidan duk sun tafi makaranta, su Afnan kuma suna dakin Hassan.
Tana kokarin shiga corridorn da zai sada ta da dakin Hassan din ne, ta ji ana buga kofa, dole ta dawo baya hade da nufar kofar
"Waye?" ta tambaya ba tare da ta dakata ba.
Daga ta ji muryar mace tana fadin "Ni ce, Hajiyar na gidan ne?"
A hankali Asiya ta bude kofar bayan ta murza key din, suka zubawa. . .