A kofar wani katon gida mai keken ya sauke Asiya, bayan ta sallame shi ta fito hannunta rike da basket hade da tura katon gate din, take kuma farfajiyar gidan ta bayyana, wacce take dauke da shuke-shuke itatuwa dangin guava, mangoro, ayaba, lemo, gwanda da sauran fulawoyi masu kyau.
Kai tsaye ta doshi 2nd gate din
Gate na biyun kuwa fari ne Kal, kana shiga shi ma babban farfajiya ne mai dauke da interlock sai over head tanks guda hudu manya-manya daga bangaren kudu.
Daga can gefe kuma teburi ne irin na table tennis, yayin. . .