Skip to content
Part 5 of 25 in the Series Labarin Asiya by Matar J

A kofar wani katon gida mai keken ya sauke Asiya, bayan ta sallame shi ta fito hannunta rike da basket hade da tura katon gate din, take kuma farfajiyar gidan ta bayyana, wacce take dauke da shuke-shuke itatuwa dangin guava, mangoro, ayaba, lemo, gwanda da sauran fulawoyi masu kyau. 

Kai tsaye ta doshi 2nd gate din 

Gate na biyun kuwa fari ne Kal, kana shiga shi ma babban farfajiya ne mai dauke da interlock sai over head tanks guda hudu manya-manya daga bangaren kudu. 

Daga can gefe kuma teburi ne irin na table tennis, yayin da a bangaren Arewa raga ce aka daura kodai ta bardiminton ko volleyball. 

Tun daga nan kuwa har zuwa cikin gidan da daukacin flat din farin fenti ne tas. 

Flat na farko daga bangaren Kudu shi ne na Alhaji Hamza, shi ne babba a cikin family din. Babban dan siyasa ne yana da mata daya mai suna Maryam, amma duk gidan Addah ake kiranta har yaranta. ita ce kuma ta haifi Hassan wanda abokin haihuwarsa ya rasu tun kafin suna. Shi ne ɗa na biyu a wajenta bayan Aunty Muna da ta kasance ta farko, yana da kanne biyar. 

Idan ka mike yar tafiya kadan za ta kaika flat din su Aunty Kubra da Umma, su kuwa Mata ne ga Alhaji Amadu shi ne ke bin Alhaji Hamza. 

Hamshakin dankasuwa ne Yaransu goma sha uku, uwargida Umma na 8 yayin da Amarya Aunty Kubra na da biyar. 

Idan da ka dawo bangaren arewa flat ne kanana guda biyu, daya na samarin gidan, dayan kuma na baki. 

Daga can gabansu kuma kadan, wani katon flat ne wanda shi ne na Alhaji Abdallah maihaifin Asiya land army ne babba, matarsa daya Hajja (Hadiza) yaranta uku mata biyu, namiji daya, Asiya, Jamila, da kuma Ammar. 

Duk da Hausawa sun ce ko tsakanin harshe da haƙori a kan saba, hakan dai bai taba sanyawa an zo rabon fada a gidan Baba Alhaji ba (Alhaji Hamza) 

Kila hakan na da nasaba da yadda matan suke da ilimi daidai gwargwado. 

Don su Aunty Kubra ita da Umma suna teaching ne. 

Addah ce ke taba kasuwanci. 

Hajjah kuwa ma’aikaciyar gidan talbijin ce ta jaha. 

Idan kana bako za ka dade ba ka tantance ga yaran wannan ga kuma na wannan ba. 

Musamman yadda suke kama, saboda dukkansu tushensu daya daga Alhaji Ali Baba ne. 

 wannan shi ne gidan da Asiya ta tashi tare da mijinta Hassan.

Shiru gidan, dama ta san haka za ta same shi, sai weekend ne kawai yake cika, yanzu kam duk yaran suna makaranta.

Bangaren Addah ta fara shiga.

Daga kitchen ta amsa sallamarta, jimawa kadan ta fito.

Za ta kai shekara hamsin, baka ce, amma baki mai haske, tana da matsakaicin tsawo hade da matsakaicin jiki.

Zamewa kasa Asiya ta yi kanta a kasa tana gaishe ta cike da girmamawa. 

 Ta amsa cike da kulawa, bayan ta zauna a daya daga cikin kayatattun kujerun da suka kayata fankacecen falon nata. 

Shiru ya dan ratsa wurin, kafin Addah ta ce

 “Kuna lafiya ko? Kwana biyu yayan naki shiru, bai zo ba .” 

Asiya ta kuma sunkuyar da kai kasa.

“Lafiya ƙalau, akwai wasu kaya ne da aka kawo musu, shi ya sa ba ya samun zama”

“Haba shi ya sa, idan ba haka ba ai bai kwana biyu bai zo ba, amma a kwanakin wayar sai idan ni ce na kira”

Asiya ba ta yi mamakin maganganun Addah ba, saboda idan har lafiya – lafiya to Hassan kullum sai ya zo gida, wani lokaci ma sau biyu, idan zai tafi kasuwa da kuma bayan ya tashi. 

Asiya ta dan nisa kadan hade da fadin

“Ai da an jima zai zo sha Allah.”

“To ai ke ma kwana biyu bana jin muryar ta ki a gidan radion.”cewar Addah idonta zube a kan Asiya

Wannan karon murmushi ta yi kafin ta ce “Kuma ina fita aiki, kila ba ku kunna radion da yamma”

Ita ma murmushin ta yi, “Ina fa nake samun dama, sannan Babanki ya dawo ga hayaniyar yara, kin san dai yaran gidan nan.”

Asiya ta yi dariya mai sauti, lokaci daya kuma ta dakko flask din da ke a cikin basket ta aje a gaban Addah ba tare da ta ce komai ba

“Ke wai ba ki gajiya ne, kullum za ki zo sai kin kawo mana abu, abin da yar’uwarki ba ta iya ba kenan, sai dai ta, zo hannu na dukan cinya, duk ta zazzagen gado da kwanciya hade tatseni tass sannan ta tafi.”

Wannan karon ma dariya Asiya ta yi sosai ba tare da ta ce komai ba. 

Ganin lokaci daya ta yi hanyar kitchen tana fadin” kin ji abincin can ya fara kauri, makaryatan banza har da cewa wai abinci baya kamewa a tukunyar. “

Murmushi Asiya ta kuma yi, tana fadin” Akwai wadanda basa yi din idan aka dace. “

” Sai idan basu ji wuta ba kam” cewa Addah da ke cikin kitchen.

“Ki je ku gaisa da Maman ta ki ai ina jin ba ta fita ba.” Addah ta kuma fada daga kitchen din

“To.” ta amsa hade da mikewa ta nufi kofar fita

Mamakin yadda Adda ta saki jiki da ita wannan karon take yi.

Da alama yau Addah tana cikin farin ciki, daga yadda suke fira ta fahimci haka, saboda ita din ba ma’abociyar magana ba ce, amma yau suna ta hira abunsu. 

Ko ya za ta ji idan ta fasa wannan gunyar kwan da ke kirjinta oho? Lallai ya kamata ta danne wannan batun ko don farin cikin sauran mutane, ta san daga lokacin da ta fasa wannan kwan, farin ciki zai yi bankwana a cikin zuriyar, kila har zumunci ya samu matsala. 

Da wannan tunanin ta rika takawa a hankali har zuwa madaidaicin falon mai dauke da set din kujeru masu kalar blue, kayan kallo da lallausan center carpet blue shi ma. Akwai center table wanda aka kawata da design me kyau, ba ƙaramin kara haska falon ya yi ba.

Hajja zaune fuskarta fayau, sai siririn farin gilashin da ya kawata fuskarta. 

Gabanta laptop ce, wani rahoto take turawa zuwa sashen labarai na gidan talbijin din.

Abin da Asiya ta so yi kenan Allah bai nufa ba, ba karamin kyau Addah take mata ba, idan aka hasko ta a gidan talbijin tana karanta labarai cikin harshe hausa ko turanci. 

Amma a hakan ma Alhamdulillahi, tana farin ciki da kasancewarta ma’aikaciyar gidan radion jaha. 

A natse ta yi sallama, Hajja ma ta amsa a natse fuskarta dauke da murmushi da ke nuna zallar farin cikin ganin diyar tata.

Ta karaso hade da dukawa dab da ita

“Sannu da gida Hajja, fatan na same ki lafiya?”

Har yanzu murmushi ne a kan fuskarta “Lafiya kalau yarinyata. Fatan ke ma kina lafiya?”

“Alhamdulillahi!” 

Asiya ta amsa hade da mikewa ta zauna kusa da Hajjahn, idonta a kan laptop din ta ce 

“Hajjah ba na samun Babana fa a waya. almost 4days kenan. 

“Kin san yanayin 

aikinsu, ina jin suna wurin da ba network sosai, amma sha Allah suna lafiya. Saboda jiya da dare ma mun yi waya.” 

“Allah Ya amince.” 

“Amin.” Hajjah ta amsa hankalinta a kan laptop din. 

Sannan ta shiga yi wa Asiya bayanin abin da take yi, y yayin da Asiyar ke daga kai alamun tana fahimta. Tare suka kammala hada rahoton sannan Hajja ta tura.

Bayan ta tura ne ta tattara hankalinta a kan Asiya .

” Ina jin dadin yadda kike ta kara wayewa da aikin nan, kullum idonki kara budewa yake yi, ina ji a jikina za ki kai matsayin da ba ki yi tunani ba, saboda kina da mayar da hankali sosai.”

Murmushi Asiya ta yi hade da kwantar da kanta a kafadar Hajja.

“Tun farko kin san wannan shi ne burina Hajjah. “

” Haka ne. Kullum ina kara jaddada miki, ki zama mai gaskiya a kan aikin ki, ki yawaita bincike shi ne zai kara ba ki damar sanin abin da ba ki sani ba” Cewar Hajja.

“In sha Allah!” Cewar Asiya tana murmushi.

” Kwana biyu Yayanki bai zo ba lafiya ko?” Hajjah ta tambayar hankalinta a kan Asiya 

Ta dan nisa kadan, tsakanin Addah da Hajjah ba ta san wa ya fi nunawa Hassan kulawa ba, ta san so ba kamar na uwa ba, amma tabbas Hajjah ma na son Hassan, son da ta san daga kasan zuciyarta ne, ba wai irin na ganin ido ko neman suna ba, ta yadda za ta iya yi mishi komai.

Hassan ku san a dakin Hajjah ya tashi, tana son yan biyu shi ya sa ku san komai na Hassan ita ce ke yin sa. Duk wani abu da ta san zai sa Hassan ya ci gaba shi take yi. 

Hajjah ce ta taimaka masa wajen cika burinsa na zama dan kasuwa, tun da ta fahimci abin da yake so kenan, zuwa yanzu kuwa Hassan na daya daga cikin matasan yan kasuwa da suka yi shura a babbar kasuwa da ke garin nasu. 

“Kina ta kallona. Tunanin me kike yi ne?”

Firgigit Asiya ta dawo cikin hankalinta tana fadin “Mantawa na yi zan turawa Grace (Abokiyar aikinta) wani abu, kuma yana a cikin laptop dina. Ga shi ban zo da laptop din ba. 

Maganar Yaya yana lafiya, ayyuka ne suka mar yawa a kasuwa. “

“To madalla, dama na dauka ko akwai wata matsala ne.” Hajja ta fada hade da tattara kayan aikinta ta mayar bedroom.

Bayan ta fito ne ta zauna kan kujera suka ci gaba da hira,, hirar da ke nuna akwai shakuwa, so da kuma kulawar juna a tsakaninnsu.

Koda wasa ba ta ji za ta sanarwa da Hajjah abin da ke damunta ba, ba za ta yanke mata wannan farin cikin ba. Duk abin da ya shafe ta Hajjah ba ta daukarshi da sauki, barrantana abu mai tayar da hankali irin wannan. Dama Hajjahn na da low BP. 

Shigowarsa ce ta katse masu hirar, tun da ya shigo idonsa a kan Asiya yake, so yake ya fahimci yanayin da take ciki, daga bisani ne ya mayar da hankalinsa a kan Hajjah a daidai lokacin da yake gaishe ta.

Ya sanya hannu a cikin plate din da ke gaban Asiya, dambun kifi ne da ya sha kayan kamshi take ci a hankali.

“Da ban zo ba Hajjah ba zan ci ba?” ya yi maganar cikin marairaicewa.

Murmushi Hajjah ta yi kafin ta ce “Ga naka can a flask, ko ba ku zo ba ma na yi niyyar aika maku da shi”

Hirarsu suke ta yi shi da Hajjah,, yayin da Asiya ta mayar da hankalinta a kan cin dambun kifinta.

Bai fita ba sai da Zainab ta shigo, Zainab dan ce kuma ta ja Asiyar zuwa sassan su Aunty Kubrah.

Sai misalin karfe takwas na dare suka baro gidan, bayan sun ci abincin dare ita da Hassan.

 A kan mashin dinsa ya goyo ta, babu dai wata hira mai armashi a tsakaninsu, amma tabbas hakan ya fi mishi dadi fiye da wancan zaman na baya.

Don ko ba komai yau sun wuni a gida sun yi nishadi sosai, ya ga dariyar Asiya, haka ta saki jiki an yi hira da ita tamkar babu abin da ke damunta.

Bayan sun iso alwala ta yi don yin sallahr shafa’i da wutri, yayin da Hassan ma ya bi bayan ta. 

Shi ne ya fara tashi a kan sallayar bayan da ya rufe Kur’anin da ya gama karantawa.

Sai da ya gama shirin kwanciya ne ya zo dab da ita, hade da karbe Alqur’anin ya ajiye.

“It’s okay. Kalli agogo fa, yanzu lokaci na kwanciya.”

Yana daga kwancen yake kallonta har ta gama shirin baccin ta, kwantawa ta yi gefensa kamar ba ta so.

Ya fahimci motsi mai karfi ma ba ta son yi, sannan ba ta son jikinta ya taba na shi.

Ya sauke numfashi a hankali, hade da janyo ta jikinsa, a cikin kunnen ta ya ce min ” Kyamata kike yi ko?” “

Girgiza kai ta yi alamar a’a

” To menene? ” ya yi tambayar hade da cusa fuskarsa a karkashin wuyanta, humrarta mai kamshi tana ratsa kofofin hancinsa.

Ba ta samu damar ba shi amsa ba, don bakinta ya yi mata nauyi.

Ya kuma janyota sosai ta yadda suke jiyo numfashin juna.

“Ba kin ce komai ya wuce ba? Uhmm!”

Wannan karon ma ba ta yi magana ba, bai damu da hakan ba, saboda ya san dama ba lallai ta yi maganar ba, jikinta ya amsa mishi duk tambayar da ya yi mata.

Cikin sauki ya sauke nauyin da ya tarar mishi, wanda ya fahimci ba shi kawai ba ne yake a yanayin ita din ma tana a ciki kawai miskilanci ne irin nata. 

Alwalla kawai ya iya yi, bacci mai nauyi gami da dadi ya daukesa.

Yayin da bacci ya kaurace ma idanunta, ba ta taba tsammanin za ta kara hada shimfida da Hassan ba, amma kuma sai ga shi ya ci galaba a kanta, tun farko dama hakan ne ke faruwa da ita, soyayyarsa kan hanata hukantashi a bisa wani laifi da ya yi mata.

Idan har za ta bari ya fada, kuma ita ma ta fada to tabbas za ta huce, sometimes ma tana hucewa ne ita kadai ba tare da ya ba ta hakuri a kan laifinsa ba.

A hankali ta mike zaune a tsakiyar gadon, yayin da rayuwarsu ta baya mai dadi, soyayya mai cike da tsabta da kulawar juna ta fado mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Labarin Asiya 4Labarin Asiya 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×