Skip to content
Part 3 of 25 in the Series Labarin Asiya by Matar J

Turo kofar da ya yi ne bayan ya dawo masallaci, shi ya kuma tayar da Asiya daga nannauyan baccin da take yi a karo na biyu tun bayan kiran sallahr asuba.  

Da hannayenta biyu ta yi tagumi bayan ta ziro kafafunta kasan gadon lokacin da ta mike zaune.  

Mamakin irin baccin da ta yi take yi, kamar ba ta a cikin matsala, kuma har zuwa yanzu da take zaune baccin take ji. 

Da kyar! Ta mike zuwa toilet, yayin da Hassan ya zauna a inda ta tashi, shi ma hannayensa biyun ya zuba tagumi dasu. 

Har ta idar da sallah yana kallonta. Alkur’ani ta janyo, duk da bishi-bishi take gani, daga bisani ma dole ta aje shi hade da kwanciya a wajen, bacci kuwa ya kuma tasa keyarta gaba. 

Misalin goma na safe ta farka, zuwa lokacin kuwa rana ta fito sosai wanda hakan ke nuna za a yi zafi yau sosai. 

Toilet ta kuma shiga ta fito daure da towel bayan ta yi wanka, jakarta ta janyo hade da dakko wayarta. 

Miss called ne a wayar ya tasarma hamsin, sai kuma texts, kiran Mamanta ya fi yawa, sai na abokan aiki, da kuma Zainab wacce take zaman kawa, yar’uwa kuma kanwar maigidanta Hassan uwa daya uba daya. 

Text din ta shiga budewa, a nan ma akwai na mamanta. 

“Lafiya kuwa kuke, na kiraki ba ki dauka ba, kuma kin ce idan kin tashi aiki za ki biyo amma ba ki biyo din ba, ga shi na sanya an yi miki abin da kike so.”

Wannan shi ne sakon mamanta, damuwar da take ciki bai hanata murmusawa ba, sosai take son Mamanta, ba ta son abin zai tayar mata da hankali, za ta iya bayar da ranta don mamanta. 

“Ban tashi da wuri ba, shi ne na wuce gida, aikin gida ya gajiyar da ni na yi bacci, amma zan zo gobe sha Allah don yau sai 12am zan tashi daga aiki, don Allah a kara yi mun Hajja.”

Zama ta yi gefen gadon bayan ta tura sakon. 

Kokarin kiran Zainab take yi, Hassan ya shigo hannunsa dauke da tea flask hade da food flask. 

Kallo daya ta yi masa, ta mayar da hankalinta a kan wayar da ke hannunta. 

Kamshin Kokon (kamu) da yake zubawa ne sanyata saurin kallonsa cike kuma da mamakin ina ya samu gasara, don ita kam ba ta da ita a cikin fridge ba ta gama mamakin ba, ya mika mata cup din da kosai a cikin kula. 

Kallonsa take yi ba tare da ta karba ba, har yanzu mamaki take yi idan ta kallesa, ta kuma tuna suna dauke da cutar Kanjamau, a ina suka sameta? Tambayar da har yanzu ba ta da amsarta. 

“Please take, I’m sorry.” Ya yi maganar cikin marairacewa. 

A wannan karon ma rabin kofin ta sha, hade da cin kosan kadan. 

Shi ne favorite food nata a breakfast, ba ta gajiya da cin kosai haka ma kokon za ta iya wuni tana shan sa. 

Wannan ya nuna mishi sosai tana cikin damuwa. 

Rashin yi mishi magana ma yana damunsa sosai, don kuwa rabon da ya ji muryar Asiyar tun jiya da misalin 5:30pm. 

Da alama kuma ba za ta yi maganar ba, don ko yanzu ma da ta gama shan kokon, komawa ta yi ta kwanta hade da daddanna wayarta. 

Wannan shi ne halinta idan har tana cikin damuwa ko yay mata laifi, yi mishi magana daidai yake da ta yafe masa. Shirunta ya nuna har yanzu mai laifi yake a wajenta. 

“Rabin Raina!” ya ja sunan nata a natse wanda ke nuna yana son su yi magana mai muhimmanci. 

Amma ba ta Kalleshi ba, kamar yadda ba ta amsa ba. 

“Rabin Raina!” ya kuma kiran sunanta a karo na biyu, lokaci daya kuma ya aje gwiwowinsa a kasa, hade da yin amfani da hannunsa ya dafa gadon yana fuskantarta. 

“Na san kina cikin halin ɗimuwa, da kuma damuwa, na san a yanzu babu wanda kika tsani gani ko jin muryarsa kamar ni. Amma ki sani da ace ina da iko, wallahi dana kwashe duk abin da yake damunki tun jiya na maido shi kaina sannan in sawwake miki ki auri wani na. Ki yi rayuwar farin ciki. Sannan zan ci gaba da hukunta kaina na sanyaki a cikin damuwar da na yi na tsawon wuni.”

Wannan karon cikin sauri ta kallesa. 

“Yes! Zan iya yin hakan, idan har za ki yi farin ciki. Zan iya dawwama cikin kunci domin ki kasance a cikin walwala. 

Kwakwalwata a cushe take, na rasa ta ina zan gano wannan bakin zaren. Ina jin kawai mu tafi babban asibiti a kara yi mana wani gwajin.”

“Hmmm!” abin da Asiya ta fada kenan.

“Wallahi!! Asiya ban cuceki ba, idan har ni na sanya miki wannan cutar to ban san ina da ita ba, wallahi ban taba kusantar wata mace ba sai ke.” 

Ya tsagaita hade da kallonta. “Ki ce wani abu don Allah, shirunki na kara daga mun hankali don wannan ke nuna kina fushi da ni sosai.” 

Maimakon ta yi abun da yake so din, baya ta juya mishi, hade da sakin kuka mai sauti, wanda ya kara dagula mishi duk wani lissafinsa. 

Yau Hassan ne a gabanta a kan gwiwowinsa yana rokonta wata alfarma da ta kasa yi mishi, ta fi shi jin dacin hakan, irin abun ne na filin dambe da ake cewa kai ka yi duka kai ka fadi, zuciyarta ta fi ta shi ciwo a yanzu haka, kunci biyu ta hada a zuciyarta, da nata da kuma na halin da take kallonsa a ciki. 

Tana jin kamar ta janyoshi jikinta ta rarrashesa kamar yadda ta saba mishi idan yana a halin damuwa. 

Idan akwai abun da ta tsani gani a duniyarta shi ne damuwa a kan fuskar Hassan, damuwarsa kan hanata sukuni da walwala. 

Amma a wannan karon ba ta jin za ta saurareshi, saboda ya aikata mata ma fi munin laifi. 

Ta yadda da shi dari bisa dari, ta aminta da shi, ta shaideshi, amma kuma daga karshe wannan shi ne sakamakon da ta karba daga gareshi. 

Bayan damuwarta a kan cutar har da tsananin kishi ma ke damunta, na yadda Hassan ya hada shimfida da wata. 

Gaskiyar mata da ke cewa namiji munafiki ne. 

“Da yaushe Hassan ke samun damar kebewa da wata mace?” wannan ita ce tambayar da takewa kanta a ko wane lokaci.

Saboda a tarayyarsu ta saurayi da budurwa ku san ko wane lokaci suna tare, a waya, chat, da kuma text, komai dare za ta iya kiransa haka shi ma.

Yana jin sautin kukanta, na fita wanda ya tabbatar tana jin wani irin kunci ne a zuciyarta, a duk lokacin da take a irin wannan yanayin to tabbas damuwar da take ciki ba karama ba ce. 

Abu ma fi sauki a wajensa shi ne ya daina damunta, har zuwa lokacin da za ta yi masa magana, don kuwa ya san za ta yi hakan komin dadewa. 

Dalilin da ya sa kenan ya mike jiki a mace zuwa falo, don yau kam ba maganar zuwa shago, ba zai iya aikata komai ba. 

Bukatarsa kawai Asiya ta rufe wannan maganar zuwa wani lokaci, kar ta fasata yanzu.

Jin ya fita ne ta kuma kara sautin kukanta, saboda ta san babu abin da yake bukata a yanzu sama da ita, amma kuma ba za ta iya sauraronsa ba, ba za ta iya yi masa abin da yake bukata ba a yanzu, kamar yadda ya fada sosai take jin haushinsa.

*****

Misalin biyar na yamma yana kwance a falo ta fito don zuwa wajen aiki.

Dogon hijab ne fari har kasa, yayin da ta yi amfani da nikabi wajen rufe fuskarta.

Ya san tana son boye damuwar da ke kan fuskarta ne. 

Da sauri ya mike hade da fadin “jira in kai ki” ko kallon inda yake ba ta yi ba, dalilin da ya sa kenan ya bi bayanta.

Ganin motar gidan radion a waje ne ya tabbatar masa da zuwa daukarta a ka yi.

Ya dawo jiki a mace, tambayar kansa yake yi, haka zasu ci gaba da zama ne? Idan kuma zaman zai canja to zuwa yaushe?

Ba zai iya jure irin wannan zaman ba, ya kwammace ya mutu da dai ya rayu da Asiya a haka.

Yunwa yake ji, amma bakinsa ba dandano, empty tea kawai yake iya kurba, shi ya sa shi da kansa yake ji a jikinsa ya rame. 

Kamar wanda aka zungura, ko ya tuna wani abu, radion da ke jikin speakers din da ke manne da kayan kallon da ke falon ya kunna.

Radau kuwa muryar Asiya ta bayyana, babu wanda zai ce akwai damuwa a tare da ita.

Saboda babu abin da ya canja a muryar, tana nan mai taushi, cike da dadin sauraro. Sannan cikin raha da annashuwa.

Ya lumshe ido a daidai lokacin da Asiyar ke gabatar da kanta.

“Assalamu Alaikum masu sauraro, kamar dai yadda kuka sani sunana Asiya A Baba, na karbi abokin aikina Ibrahim Attahir, ni ce zan ci gaba da kasancewa da ku har zuwa lokacin da zamu rufe wannan tasha. Fatan za ku ji dadin kasancewa da ni.”

Waka mai sanyi ta ratsa akwatin radion, bayan da Asiya ta yi shiru.

Har yanzu idonsa a lumshe, yana jin kamar kar a cire wakar. Koma dai sako ne daga Asiyar zuwa wajensa. 

Don sau tari ta kan tura mishi sako ta hanyar waka. 

“Sakon gaisuwa gareki Mamana (Hajja Maryam), Babana ina yi muku fatan alkairi tare da masu sauraronmu irin su….” ta ci gaba da lissafo mutanen cikin raha da mika masu sakon gaisuwa.

Shiru ya kuma ratsawa, a lokacin da Asiyar ta bayar da sanarwar zasu ci gaba da shakatawa har zuwa karfe shidda na yamma, inda Fatima Al’amin za ta shigo da shirin Abu namu

Yau wakokin duk masu sanyi ne, irin masu jefa natsuwa da sanyaya zukatan masoya. Sosai wakokin zasu jefa masoya cikin jazba hade da shaukin junansu. 

Hassan na daga ciki, jikinsa ya mace likis inda Asiya kawai yake son gani a tare da shi, cikin rayuwarsu mai ban sha’awa ta baya. 

Ya yi kokarin kiran layin da Asiyar ta bayar ga masu sauraro don kira su mika sakon gaisuwarsu ga masoyansu, amma hakan bai samu ba.

Saboda busy kawai ake nuna mishi.

Yau kam radio shi ne ya zama abokin hirar Hassan, yayin da wutar kaunar Asiya ke kara ruruwa a zuciyarsa, yau muryarta ta yi masa dadi fiye da ko wane lokaci. Yau kam har kishinta yake ji a ransa. Har zuwa a lokacin da Asiya ta yi sallama da masu sauraro don rufe tashar gidan radion Hassan bai yi bacci ba, kuma yana sauraronta. 

Yana jin karar mota ya san ita ce aka maido, dalilin da ya sanyashi ta shi zaune kenan ya zubawa kofar shigowa ido.

Ba jimawa kuwa ta turo kofar, ba ta yi tsammanin ganinsa a wajen ba, shi ma ya fahimci haka saboda yadda reaction ɗinta ya nuna.

“You’re welcome (sannu da zuwa)” ya fada yana kallonta.

“Thank you” a hankali ta fadi hakan daidai tana wuce sa.

Bayanta ya bi ta hannunsa dauke da Flask da ƙaramin cup.

“Na san kina da bukata, saboda kin yi magana da yawa na san ba komai a cikinki, baby ma yana jin yunwa.”

Kallonsa kawai take a daidai lokacin da ta cire duk kayanta sai zani a kirjinta.

A baya ne wadanan kalaman ke burgeta, amma a yanzu da haihuwar kura da barinta duk a daya. 

“Na gode.” ta kuma fada a karo na biyu, ba don kalamansa sun yi tasiri a kanta ba, sai don halinta ne godiyar komin kankantar abin da aka yi mata.

Shi kuma sai yake ganin lallai ta fara sakkowa, zuwa ko wane lokaci daga yanzu za ta iya saurararsa su yi magana.

Dama ya san ba ta iya fushi mai tsawo da shi.

Kallonta yake yi a lokacin da take shan kunun gyadar a natse.

Bayan ta dire cup din toilet ta shiga, wanka hade da alwala ta yo.

Alkibla ta fuskanta domin mikawa mai duka kukanta, da ya sanyaya mata zuciyarta, idan kuma da gaske ne tana dauke da wannan cutar ya kawo mata sauki, ya ba ta ikon karbar kaddara da jure duk wani kalubale. 

***** 

Misalin karfe goma na safe ta tashi tun bayan da ta yi sallahr asuba. Brush ta yi sannan ta nufi kitchen don yunwa take ji sosai, har kamar za ta yi amai take ji. Hassan ne a kitchen din yana goge-goge, ganinta ya sanyashi dakatawa.

“Kin tashi?”

Kai ta daga alamar Eh.

“Akwai Irish da ƙwai na san kina so.”

Kallonsa take yi cikin ido, so take ta fada mishi ya daina hidima da ita haka, amma kuma ba ta son yin doguwar magana da shi.

Idan kuma har ta ki cin abin da ya yi, nan ma damunta zai yi da surutu, a yanzu kuwa ta tsani yin doguwar magana da shi.

Dalilin da ya sa kenan ta dauki ƙaramin plate kadan ta debi Irish din, sannan ta hada tea ta wuce falo.

Bayan ta gama wanka ta shiga, fitowarta ya yi daidai da shigowar Hassan cikin dakin.

A gabansa ta gama shirinta tsab cikin blue lace mai yarfin farar fulawa.

Hijab blue ta yi amfani da shi hade da daura agogo wanda fatarshi ma ta kasance blue.

Sosai ta yi masa kyau, duk da babu wata kwalliya a kan fuskarta.

Nikabi ta dakko hade da jakarta ta nufi kofa da zummar fita.

Jiya a bayaninta na rufe tasha cewa ta yi sai misalin biyar na yammacin yau za ta kuma kasancewa dasu, “to ina za ta je?”

Ya yi ma kansa tambayar a zuciyarsa, a fili kuma sunanta ya kira.

Ba ta amsa ba kuma ba ta fasa tafiyar ba, dalilin da ya sa kenan ya yi saurin tashi ya cimmata a falo tana kokarin bude kofa.

“Kada ki fita” ya yi maganar da wata irin murya mai nuna alamun rashin wasa.

Ta ci gaba da rike hannun kofar ita ba ta fita ba kuma ba ta dawo ba, sannan ba ta ce mishi kala ba.

Daga inda yake tsaye yake magana.

“Al’amuranki sun isheni haka, me kike so ki zama ne? Why are you treating me like this? (me ya sa kike tafiyar da ni haka?) kina son zuciyata ta fashe ne? Kwana biyu na dakatar da komai just because of you,but see how you treat me like your servant.” ya dan tsagaita yana kallonta.

Har yanzu ko motsi ba ta yi ba.

“Ya kamata ki tsaya mu fahimci juna, ana magance matsala ne kawai bayan an tattaunata, na rasa me ya sa a wannan karon kika ki saurarata. Kina nufin a haka zamu ci gaba da rayuwa?”

Ganin ba ta yi alamar juyowa ba ne ya sa shi yin amfani da hannunsa wajen juyo da ita da karfi. 

Hawaye ne sharkaf a kan fuskarta. 

Ido ya zuba mata jiki a mace, ita ma kallonsa take yi da jikakkun idanunta.

Tsawon lokaci suna a haka ba tare da kowa ya yi magana ba.

Jiki a sanyaye ya ce “Je ki.”

Ita ma jikinta a mace ta juya zuwa kofar fita. 

“Ina za ki je?” ya yi tambayar cikin kasalalliyar murya.

“Gidan Aunty Zee.” Ta ba shi amsa cikin muryar kuka.

Ya fahimci wa take nufi, gidan Zainab kanwarsa. 

“Bana son ta san komai please.”

Ba ta yi magana ba illa ta bude kofar, hade da kokarin sanya nikabin da ke rike a hannunta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Labarin Asiya 2Labarin Asiya 4 >>

1 thought on “Labarin Asiya 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×