Skip to content
Part 53 of 55 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

How sad to miss someone, who you know doesn’t miss you…

No.86, Garki 2, Abuja…

RABI POV.

Tun da ta tashi sallahr asuba bata koma bacci ba. Amma da Mishal da ba ta samu bacci jiya da daddrae ba ta koma baccin. Sai Rhoda a bata farka ba. Gyaran gidan ta shiga yi. Bayan ta gama kuma ta ɗora girki, bayan nasu wanda za suci, har da na su Zaid ta girka, ta juye musu nasu a cikin was warmers masu kyau, ta saka a basket ta aje.

Nasu kuna ta kai kan danning ta jera. Ɗakinta ta koma, ta je ta taso Mishal da Rhoda, tace musu su tashi su yi wanka. Ita kuma ta fice ta shiga ɗakin Zaid. A can ta yi wanka, ta ɗauki ɗaya daga cikin kayanta da suke can ta saka, ta fito.

Sanda ta koma ɗakin nata, Mishal ce a banɗakin tana wanka, ita kuma Rhoda ta yi wanka tana shafa mai.

“Rhoda kaya na kuwa zai miki?”

Ta tambaya tana buɗe lokokinta. Rhoda ta juyo ta kalleta.

“Ai ba zai iyu na saka kayanki ba ma, yau za mu shiga kotu, dan haka kayan aiki ya kamata na saka, so ba sai na sauya kaya ba,zan tafi da wannan, daga can kuma sai na wuce Kaura”

Cike da gamsuwa Rabi ta rufe lokarta, bayan da ta ɗaukowa Mishal wata doguwar rigar atamafa da take da tabbacin za ta mata dai-dai, dan kansu ɗaya da wadda ta bata ta saka jiya.

Zama ta yi a bakin gadonta,tana buɗewa wayarta dan kiran Zaid, sai de kuma wayar har ta yi ringing ta katse bai ɗaga ba. Sai kawai ta aje wayar, don ta san da ma balalle ya ɗaga ɗin ba.

A lokacin Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta ɗaure da towel.

“Ga kaya, sai ki sauya”

Rabi’a ta faɗi tana mata nuni da doguwar rigar atamfar dake aje a kan gado, Mishal ta kalli kayan, sannan ta ƙaraso ta ɗauka, ta koma banɗakin dan sakawa.

Cike da jin tausayinta Rabi ta girgiza kai, idanunwata ba ƙaramin kumbura suka yi ba, saboda tsabar kuka.Wayar Rhoda ce ta yi ringing, hakan ya sa ta ɗaga wayar tana fita waje, dan kiran daga headquarter su ne.

Bayan wani lokaci, Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta sanye da doguwar rigar. Ba tare da ta saka komai a jikinta ba ta zauna a kusa da Rabi. Fuskar nan cike da damuwa, kana ganinta za ka san cewa tana cikin tashin hankali, idonta ya jeme, fuskar nan ta yi jajir.

“Ga hijabi ki saka”

Kallon hijabin ta yi, kafin ta karɓa tana miƙewa tsaye.

“Mu je mu ci abincin to”

Rabi ta faɗi tana dafata, bayan da ta gama saka hijabin. A falo suka haɗu da Rhoda, wadda ta gama wayar da ta tafi yi, daga nan suka wuce danning suka ci abinci. Kafin suka shirya fita daga gidan.

Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja.

KULIYA POV.

Zaune yake daga bakin gadon marasa lafiyar dake dakin da aka kwantar da shi. Ya zuro ƙafafunsa ƙasan gadon. Jikinsa sanye da kayan marasa kafiya da ake bawa pertinent ɗin asibitin. Hannunsa na dama, sanye cikin arm sling. Daga gefen damansa kuma, Zaid ne zaune yake kallonsa ta gefen ido, dan jinsa yake kamar wani baƙo a gurinsa.

A ɗazu bayan da ya dawo daga masallacin sallahr asuba, ya tarar da Aliyun ya buɗe idonsa, amma kuma yana kwance a kan gadon, hakan ya sa ko ɗakin ma bai ƙarasa shiga ba ya juya da sauri ya tafi kiran nurses. Tare da nurses guda uku suka dawo, su suka dakatar da shi a waje, su kuma suka shiga ɗakin. Jim kaɗan ɗaya daga cikinsu ta fito, bayan ɗan wani lokaci kuma sai gata ta dawo ita da likitan da ya duba Aliyun. Sun jima sosai a ɗakin, dan har sai da ya ƙagu.

Sai ga su sun fito, da sauri ya shiga tambayar likitan jikin Aliyun. Likitan ya sanar masa da komai lafiya, dan har sun saka masa arm sling, gudun kada ya cika yawan motsa hannun. Amma kuma sun masa wata allura, wadda ta sa ya koma bacci, amma daga lokacin zuwa ƙarfe bakwai na safe zai iya farkawa. Da haka hankalinsa ya kwanta, har ya dawo ɗakin ya zauna ya ci gaba da gadinsa, har zuwa lokacin da ya farka.

“Ya… Ya kake?”

Cewar Kuliya, dan be ma san me ya kamata ya tambayi ɗan uwansa ba, wanda Allah ya haɗasu bayan shuɗewar shekaru masu yawa da rabuwarsu. A ɗazun da ya farka cewa ya yi Zaid ɗin ya ara masa wayarsa, akwai wanda zai kira. Bayan da Zaid din ya ba shi wayar, sai ya kira Anna ya sanar mata halin da yake ciki. Kuma tun bayan wannan maganar, wata magana bata ƙara shiga tsakaninsu ba.

Zaid ya juyo ya kalleshi, me makon ya amsa tambayar da ya masa, sai ya ja ɗan uwan nasa ya rungumeshi. Duk cikinsu babu wanda be zubar da ƙwalla ba, dan faɗar kalar kewar juna da suka yi ma ɓata baki ne.

“Wannan ne abun da ya kamata ace ka tambayi yayanka bayan kun haɗu?!”

Cewar Zaid yana shafa kansa bayan da suka saki juna. Kuliya ya share hawaye.

“Ban… Ban san me ya kamata na ce ba ne?”

“Dama kai kana rasa abun faɗe ne?”

Sai suka yi dariya.

“Ina Mishal?”

“Wa? Ko matarka ?”

Sai Aliyu ya sunkuyar da kansa yana faɗin.

“Eh ita”

“Suna gidana, ɗazu na ga kiran matata, na san nan da anjima za ka sun iso…”

Daga nan kuma sai aka buɗe babin hira, suka shiga bawa juna labaran abubuwan da suka faru a rayuwarsu bayan rabuwarsu, daga Zaid har Aliyun, Allah ne kaɗai ya san kalar farin cikin da suke ciki, bayan shuɗewar tarin shekaru, yau sai ga su a tare da juna,me ya fi wannan daɗi?. Ba su ɓoye juna komai ba, wani zancen su yi dariya, wani kuma su matse ƙwalla. Kuma cikin hirar tasu ne, Zaid yake sanarwa da Aliyu cewar ya haɗu da dangin Momma, kuma su ne ma suka aura masa matarsa, dan ita ce ‘yar anti Maryam da Momma ke basu labarinta. Sosai suka tattauna kan matsalolin da suka faru da su, da kuma nasarorin da ko wannensu ya yi a rayuwa.

“Ni da ma na san baka mutu ba, dan ce mana aka yi ka gudu, ba cewa aka yi ka mutu ba… Kawai de na haƙura na fawallawa Allah ne, fon na san ko ba daɗe, ko ba jima idan har Allah ya hukunta haɗuwar mu da juna za mu haɗu…”

Zaid ya ci gaba da kallon ƙanin nasa cike da alfahari. Ji yake kamar ya buɗe cikinsa ya saka shi ya kulle, gudun kada wani abu ya ƙara zuwa ya shiga tsakaninsu.

Ƙofar ɗakin aka turo, Mishal da Rabi suka bayyana a bayan ƙofar. Daga Zaid ɗin har Aliyu suka juyo suna kallon bakin ƙofar. Mishal na arba da Kuliya, zaune da rai, wata ƙwalla ta silalo daga idonta. Ba ta san ya ka yi ba, amma ita de ta san kowa dake ɗakin ya ɓace a idonta, ba ta ganin kowa sai Aliyuj da ke zaune a bakin gado, sanye cikin wasu bluen riga da wando, hannunsa na dama saƙale cikin arm sling, ya kafeta da idamuwansa ya na kallo. Dan haka ta taka da gudu ta yi kansa, kuma tana zuwa kusa da shi ta faɗa jikinsa ta rungume mijinta.

Kuliya ya ɗan cije lips ɗinsa na ƙasa, saboda zafin famun da Mishal ta masa, amma haka ya ɗago da hannunsa na hagu, ya ɗora avkan gashinta dake cikin hijabi.

“Abu Aswad… Abu Aswad ɗina… Abu Aswad… Da ma na san ba za ka mutu ka barni ba…”

Faɗi take tana ƙara ƙanƙameshi. Hakan ya sa Zaid miƙewa daga bakin gadon ya ja hannun Rabi zuwa waje, tare da rufo musu ƙofar.

Mishal ta ɗago da kanta daga ƙirjin Kuliya, ta shiga dudduba jikinsa, hawaye ya jiƙa mata fuska. Hannunsa ya ɗago ya kama fuskarta.

“Abu Aswad ɗina!”

“My Teddy Bear”

Kuliya ya furta a hankali yana share mata hawayen.

“Da ma ai na faɗa maka cewar ba za ka mutu ka barni ba…”

Fuskarsa ya kara da tata ya na faɗin.

“I love you Mishallyn Aliyu, i love you to the moon and back… I love you my Boo, my last love, my babe, my other half, my treasure, my honey bun…”

Kafin a hankali, ya haɗe bakinsa da nata, suka shiga musayar yawu. Sakinta ya yi yana zaunar da ita a gefensa. Sai kuma ya kalleta sosai. Idonta har wani ƙyallin murna yake na ganin ya samu sauƙi.

”Kin yi kyau, wa ya baki hijabi kika saka?”

Sai ta kalli hijabin jikin nata tana faɗin.

“Anti Adawiyya ce ta bani”

“Ya miki kyau sosai”

Matsawa ta yi kusa da shi, kamar me shirin komawa cikinsa, ta maƙalƙale hannunsa na hagu.

“Abu Aswad! Jiya fa na ɗauka cewar ka mutu. Na yi tunanin ka mutu ka barni.Na ɗauka cewar wani maraicin zan sake shiga”

Kuliya ya yi murmushi ya na sumbatar kanta.

“Insha-Allah zan ci gaba da zama da ke, har zuwa lokacin da zaki kawo mana babynmu!”

Sai ta ɗago da kanta ta kalli fuskarsa.

“Kenan zan samu baby?”

Sai ya yi dariya.

“Haka nake zato, ina da yaƙinin cewa mun kusa samun baby soon”

Sai ita ma ta yi dariya tana kwantar da kanta a kafaɗarsa.

“Ka san suna wa za’a sa masa?”

Dariya shi ma ya yi, har jikinsu na jinjiga a tare.

“Wai an tabbatar ne?”

Ta ɗago tana fadin.

“Me ɗin?”

“Babyn mana. An tabbatar kina ɗauke da shi?”

Nan take ta haɗe rai tana kai masa duka a damtsen hannunsa.

“Auuchhh! Teddy Bear irin wannan duka haka?”

Ta turo baki gaba tana faɗin.

“To ba kai ka ce min na samu baby ba, kuma sai ka dawo kana min wani ƙauli da ba’adi”

Ta faɗi idonta na ciccikowa da ƙwalla, dan ita har ga Allah ta riga da ta yadda da cewar ta kusa samun babyn, ya riga da ya sa mata rai, kuma sai ya zo yace ba haka ba?.

“Wasa fa nake miki, amma idan kina so sai an ƙara!…”

Ta san me yake nufi da sai an ƙara ɗin, dan haka ta ƙara ɗaka masa wani dukan, wannan karon a cinyarsa, ya dafe wurin yana dariya.

“Ki yi haƙuri, kin ga fa ba ni da lafiya, ya kamata ace an raga min ai”

Mishal ta share ƙwallar da ta silalo mata, dan ita ta mamanta da ba shi da lafiyar.

“To ka yi haƙuri”

“Ke!”

Ta kalleshi.

“Me ya sa kika yi laushi ne?. Abu kaɗan sai ki masa kuka, bayan na san da ba haka kike ba”

Ya tambaya jin a ɗazun da ta yi magana murmuyarta ya fito a raunane.

“To ba girma nake ba!”

“Iyeee, lalle girma, su Mishallyn Aliyu an fara girma”

Sai ta yi dariya tana rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shi ma sai ya yi dariyar. A lokacin kuma aka turo ƙofar ɗakin. Anna ta shigo, hakan ya sa su duka suka kalleta.

<< Labarinsu 52Labarinsu 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×