Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Laifin Wa? by Mustapha Abbas

Tun daga soron farko za ka gane talauci ya jima da samun gindin zama a cikin gidan, duba da yadda daɓen tsohon siminti da bangwayen da suka kewaye gidan ke ta farfashewa ana watsi da su. Sai dai a cikin gidan akwai wani ɗaki guda ɗaya tal da kowa a gidan yake fatan a ce mallakinsa ne, ɗakin ya fi ko wane ɗaki tsaruwa, an malale shi da tiles, anyi masa fentin zamani mai tsada, nau’in kayan alatu ba komai za ka nema ka rasa ba a ɗakin Ladidi.

Ladidi ba kowa ba ce, itama ‘ya ce a gidan, sai dai ta fi duk ‘yan gidan hasken fata, ado da kyau, me yiyuwa saboda sabulun da take wanka da shi da man shafawar da take amfani da su na musamman ne, suttura kuwa abar banza ce a wajen Ladidi. Ta fi Mahaifinta da yayyunta da suke aikin ƙwadago suna samun na ɓatarwa samun kuɗi.

Rabon da ta ci abinci a gidan har abin ya zama tarihi, a duk lokacin da take jin yunwa za ta aika Restaurant a siyo mata abinci mai rai da motsi ta ci, ba ta fiye zama ba, idan ka ganta a gida to za ta wuni ne a ɗaki cur tana barci, da yamma kuma ta yi wanka ta caɓa ado ta fice, ba za ta dawo ba sai cikin dare, a wasu tsirarin kwanakin ma ba ta kwana a gidan.

Sau babu adadi Mahaifiyarta ta kan tsaya a ƙofar ɗakinta tayi ‘yar murya,
“Ladidi jiya da ba kya nan na aika yara Kanti sun amso bashin kayan abinci don Allah ki bada kuɗin a kai musu.” Idan ta ga dama ta bayar, idan kuwa ‘yan mutuncin basa kanta ta kan ce, “Ba ni da su Mama.”

“Ladidi taimaka ki ɗebarwa Jummai (ƙanwarta) ɗan man shafawar nan naki ta murza ko itama ta samu ta ɗan washe kwana biyu ta yi dilim da ita kin san nata ya ƙare, gashi bani da kuɗin da zan bata ta siya.” Shima idan ta ga dama ta kan ce, “To ta kawo roba in sammata.” Ko kuma ta bata wani ragowar nata tunda ita tana da su da yawa. Idan ko ba tayi ra’ayi ba sai tace “Dole ne sai ta shafa man? Ta haƙura man.”

“Ladidi ɗan taimaka ki bawa Jafar (ƙaninta) aron sabulunki zai yi wanka, na mu ya ƙare tuntuni.” Sai ta ce, “Mama in dai wannan yaron ne Allah sai dai in kar yayi wankan, rannan ƙiri-ƙiri na aike shi ya ƙi zuwa.”
“Don Allah ba don halinsa ba.”
“Zan dai iya ba shi naira ashirin ya siyo Kilin ƙazamin banza.”
“To kawo ashirin ɗin.”
Haka Yayyen Ladidi Maza ma idan gari ya kulle musu sukan zo su nemi tallafinta.

Mahaifin Ladidi ba ya iya taɓuka musu komai saboda yanayin sana’arshi wataran a samu wataran a rasa, yau akwai gobe da jibi babu, wannan ya tilasta masa gazawa da ɗawainiyar su, don haka yana ganin duk abinda yake faruwa a gidansa amma ba shi da ikon yin magana, ba shi da ikon hanawa, saboda ba zai iya ciyarwa ba, ba zai iya shayarwa ba bare tufatarwa.

A wani lokaci da ya shuɗe, sa’ar da ƴa fara fahimtar irin rayuwar da ‘yarsa take yi yayi ƙoƙarin gyara komai duk da cewa ba shi da tabbacin komai ɗin zai gyaru, amma sai Matarsa ta hayayyaƙo masa, ta nuna masa lallai kar ya shiga layin ‘yan sa idon unguwa da ba sa iya gani su ƙƴale kuma basa so su ga wani ya ci gaba. Shima daga ƙarshe sai ya miƙa wuya aka haɗu da shi ana dangwalar arziƙin Ladidi.

***
Wasu ‘yan tsirarin shekaru suka shuɗe, Idan ka shigo gidan babu abinda zai fara yi maka iso face tarin da Ladidi take yi daga cikin ɗakinta kuf kuf kuf, Idan ka leƙa ɗakin tana yashe a kan tabarma guda daya tal da ta rage mata cikin kayanta, an kaɗar da komai an siyar wajen nema mata magani, hatta tiles ɗin dake malale a ƙasan ɗakin da ace zai siyu da tuni an ɓamɓare shima an sayar da shi.

Ta kaɗe ta yamushe ta zama kamar ƙwarangwal, tayi ba haya a kwance a zo a kwashe, tayi fitsari a zo a share a goge kamar jaririya. Duk mazajen nan da suka yi ta rububinta a baya yanzu babu ko ɗaya, gudun ta suke yi, Ladidi ta gane cewa dama ƙuruciyarta kawai suke so. Tayi da na sani tayi kuka har hawayen idanunta sun tasamma ƙarewa.

Mahaifin Ladidi yana sonta, mahaifiyarta ta fi sonta kaf cikin ‘ya’yanta, Yayyenta da ƙannenta ba sa so su rasa ta, amma ba za su iya yin komai ba domin su dawo mata da rayuwarta ta baya, ba za su iya maido mata da muhimman abubuwan da ta rasa ba, daga ciki kuwa har da lafiyarta. Ladidi tana so ta samu lafiya ko don ta gyara kusa-kurenta na baya.

Wata rana ko da sau ɗaya ne a rayuwarta kafin ta koma ga Allah tana so ta tashi tayi alwala tayi Sallah, tayi Sujjada ta roƙi Ubangiji Ya yafe mata laifukanta, amma ba za ta iya koda tashi zaune ba, saboda ciwo ya gama cin ƙarfinta, abinda kawai ya rage mata shine hawayen da suke iya tsiyayowa daga kwarmin idanunta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.6 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

5 thoughts on “Laifin Wa? 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×