Skip to content
Part 5 of 10 in the Series Launin So by Kabiru Yusuf Fagge

Babi Na Biyar

Ta dade da gama kukan amma ko dan mitsitsin yaro ne ya dube ta, ya kalleta ya san ta yi kuka, kuka mai yawa, kuma kuka kala-kala, kukan zuci, kukan kunci, bakin ciki da na takaici, sai kuma kuka mai fitar da hawaye zafafa.

Zuhra ta yi kokari iyakar iyawar ta don ganin ta rike kukan nan, don kar ta nunawa Abba gazawarta, amma abin ya ci tura, dole kukan ya bayyana gare ta, don babu yadda za ta yi, da da akwai da ta yi, abin ne ya yi mata yawa shege da hauka.

Tarkon da ta dana ya makaleta, haka nan ramin muguntar ta ya afka cif-cif da ita. Sam ta lura ba ta da wata mafita dangane da abin da Abba ya fada, cewar ita da komawa gida sai a darussalam.

A da, a bakin titi suke a zaune, inda ta yi ta kokarin ganin ta tsayar da motoci don samun taimakon gaggawa, amma ba alama, a karshe ma ta fahimci inda suke din guri ne mai hatsari, ta yanayin yanda ta ga mutane na kallonsu. Dole ta saduda, ta nufi can vangaren da Abba ya koma ya zauna, ta jingina da jikin bishiyar da ke kusa da shi, tana kallonsa da idanun tsananin tsana.

Yanayinta abin tausayi, jikinta ya fara sanyi da sakankancewa da mika al’amura cikin saduda. A ranta ta raya ko ta ba shi hakuri, sam ta ga ba za ta iya ba, a ganinta baiwa Abba hakuri a wannan lokacin wulakanta ne da kaskanci, ba za ta iya ba.

Shi kuwa ko kallo ba ta ishe shi ba, ko da ta ke ta kokarin tsayar da motoci da kuma nufowa gare shi bai daga kai ya kalleta ba, bai damu da zubin samuwarta a gurin ba, face yanayinshi da ke nuna yana son faruwar cimma burinshi na salwantar da Zuhra daga duniya kamar yadda ta yi nufi gare shi. A hankali ya ji maganarta a kunnenshi.

‘Kai maida ni gida na ce maka, ko ka ba ni makullin motata, tun da ba na ka ba ne.’ Duk da akwai rauni a muryarta, ba ta gaza ga yin gadara ba a zancen.

Har ta maimaita sau uku hadi da zagin shi, ko kallonta bai yi ba, bare ya amsa mata. Bai ankara ba sai jin ta ya yi ta cakume shi tana kokarin sa hannu a aljihun sa da niyyar dauko mukullin a ganin ta.

Ya sa hannu, ya ture ta, ta fadi ba ta yi kasa a gwiwa ba ta kuma tasowa gare shi, babu zato bare tsammani sai ji ya yi ta kwashe shi da mari, kafin ta mayar da hannun nata, shi ma ya falla mata na sa marin, wanda ya ninka na ta sau biyar da rabi, yatsunsa ya shatu a kuncinta, ta dafe da sauri da hannun da ta yi marin, daman hannun da ya ba da kyautar zuma an ce wata rana zai amshi madaci, bare kuma ya ba da kyautar madacin.

Ta dube shi, kwalla wadace da idanun kallon nata, ba ta kyale ba, don a ganin ta ya yi karya ta kyale shi a matsayin sa na wanda take kallo wulakantacce kuma bawa a gidansu. Ta yi kan shi da raruma, cizo da yakushi, kafin ta dire a jikinshi ya sa kafa ya hankade ta, ta yi can baya sosai ta bugu da bishiyar da suka tarar tsaye a gurin, wadda duk abin da ya faru tana ganin su, za ta iya ware mai gaskiya da mara gaskiya idan da za a tambaye ta.

Daga kwance da take Zuhra ta dago a hankali, jini na zuba ta gefen kunnenta, idanunta makil da kwallar da a yanzu suka fara gangarowa kasa. Ba ta ga alamun tausayi ko sassauci a fuskar Abba ba.

‘Ke da mukullin motar can sai a darussalam, idan ana samu, bare ke na san ba za ki samu ba, saboda bakin halinki.’

Da ya gama maganar sai ya ciro makullin daga aljihunsa, ya kalli can tsallaken titi inda nan ma daji ne, tun karfinsa ya dage, ya yi jifa da makullin, sai da ya tabbatar ya tsallake titin ya yi nisa a cikin dajin, ya fada inda ya san duk iya kokarinta ba za ta je ba, idan da ta je ma ba za ta gan shi ba, sannan ya matsa kadan ya hau kan reshen wata bishiyar tsamiya da ya fado kasa, wanda da alama iska ce ta yo kasa da shi, ya zauna.

Yanzu kukan Zuhra ya kara yawa, ta kuma tabbatar wa kanta abin da Abba ke fada ya aikata shi. Ta dubi yanayin gurin, yamma ta yi, duhu ya fara yi, sai dai da alama garin ba garin Musulmai ba ne, da ta jiyo kiran sallah, zuciyarta ta kara karaya, a nan inda ta ke ta kife, kan ciyayi da dattin kasar gurin, yanzu ta fara rusa kusa.

Tsawon mintuna suna haka, karar fashewar gilasan motar ta su ne ya tattaro hankalansu zuwa gurin da suka ajiye motarsu, mutane ne sanye da bakaken kaya sun kai su bakwai, kewaye da motar, wasun su dauke da bindigogi, wasu kuma adduna ne tare da su, ‘yan fashi ne. Suna ta fadin ina masu motar.

Hankalin su Abba ya tashi, Zuhra ta yi matukar firgita, ba ta san lokacin da ta kurma ihu ba.

Da sauri ‘yan fashin suka juyo zuwa gare su. Abba ya yi saurin sauka daga kan reshen, ya fincike ta, ya yi zaton za ta yi masa gardama, suka zura a guje cikin sarkakiyar dajin nan ba tare da sanin ina suka nufa ba, bare sanin ko me za su riska.

‘Yan fashin nan suka rufa musu baya. Suna yin ihun razanarwa. Babban su yana magana da gurvataccen turanci.

‘Catch hem! Don’t leave them.’ (kamo su, kar ku bar su)

Kamar yadda Abba ke tikar gudu da hakki haka Zuhra ke yi, gumi ne sharkaf lulluve a fuskarsa, idanunsa jawur saboda tsananin gudun da suke yi da kuma kutsawa ta ko ina.

Haka ita ma Zuhrar, sai dai ita bayan tsananin gumin, jan idanun har da hawayen kuka na tsanani da ta ke ciki. Ga duhu ya yi, ya rufa sosai, ga shi ko kadan ba su san ina suka dosa ba, kuma ina suke bi, kawai dai suna gudun ceton rai ne, rai dai aka ce an cirewa fara kai.

Har lokacin suna jin dirin gudun ‘yan fashin nan na biye da su. Sai dai akwai ‘yar tazara a tsakanin su, wannan ya sa Abba tunanin samun guri su voye.

Wani abin mamaki, tun tagwayen harbin da suka ji an yi zuwa sama, ba su kara jin an yi harbi ba, wanda wannan yana da nasaba da ra’ayin ‘yan fashin na kamo su da ransu, don suna ganin hakan zai sa su sami abin da suke nema.

Ketowar alfijir ne ya sa Abba ya tabbatar asuba ta yi, har ta gifta, ya kuma tabbatar da cewa a yanzu wadanda suke biye da su, sun bar su, domin da sun riske su, sun gano inda suke da tuni sun gama kama su, sun kaddamar da hukuncin da suke son yi a garesu.

A hankali ya sa hannu, ya ture ganyayyakin mainar da ke lulluve da su, bai kalli yanayin inda suke ba, ya dubi Zuhra, wadda wadataccen hasken yunkurin ketowar rana ya sa shi ganin ta sosai.

Idanunta biyu, ita ma kallonsa ta ke yi, da idanun tsana, fuskarta fal da alamun jigata da shan wahala. Kayan jikinta kansu sun sha wahala bare ita. A gefen wuyanta akwai ciwo da makalallen jinin da gani ka san wata bishiyar ce ta yage ta, ta mintsine ta.

Abba ya mike, yana duban jikin sa a lokaci guda da yanayin garin da suke. Abin ba a magana, duk kayansa sun yayyage a wasu sassa, yayin da kafarsa ke dauke da ciwuka guda biyu, sai bayansa da ya shafo ya ji jini, sannan kuma kafadarsa da take dauke da wani mawadacin yanka na kayar dundu.

Babu takalma a kafarsa, bai san inda suke ba. Yanayin gurin ya tabbatar masa daji ne, domin babu alamun shuke-shuken da mutane ke yi da ikon Allah, sai dai tsirran da Allah ya halitta a gurin da manyan bishiyun daji.

Da ya dawo da dubansa ga Zuhra, a yanzu ta mike zaune, ita ma wasu guraren na jikin kayanta ya yayyage, sai dai kafarta akwai takalmi, wari daya, daya kafar babu.

Ya dauke kansa daga gare ta, a hankali ya taka zuwa dan nesa da inda take, ya durkusa a gaban wani dan ruwa da ya kwanta ya shiga wanke jikinsa. Tunanin yadda ruwan ya samu a gurin ya ke, ganin alamun cewar ruwan sama ne shi ne ya fi sa shi kara tunanin, domin ya san yanzu ba lokacin damina ba ne. Can kuma sai ya tuna ai a Kudancin Nijeriya ko lokacin damina ne ko ba lokacin damina ba ne, ana yi musu ruwa.

Ya ci gaba da abin da ya ke, ya yi alwala, sannan ya mike, ya koma gurin da ya bar Zuhra.

‘Je ki yi alwala, ki yi ramuwar salloli.’

Ba ta tsaya yin mamakin maganar ba, ta watsa masa amsa.

‘Ba zan yi ba. Ka tafi, ka ba ni guri.’

Ya yi murmushi.

‘Na sani, ba sai kin maimaita ba. Amma batun in tafi ba ki isa ba, nan ba gidanku ba ne, ke zan cewa ki tafi ki ba ni guri.’

Ta mike a fusace, da tsaki, kallon raini da tsana da ta yi masa, ta wuce, ta bi wani guri da take tsammanin hanya ce mai kyau.

Abba ya bi ta da kallo, ba ta vace masa da gani ba, ya yi tsaki, ya dubi sararin samaniya, bai fuskanci ina ne gabas ba, kawai ya tada sallah, yana mai rayawa a ransa inda ya kalla din nan ne alkibla.

Salloli biyar ya rama, Azahar, La’asar, Magariba da Isha’i din jiya, sai kuma asubahin da suka riske shi cikin wani hali.

Wani yanayi ya ji a tare da shi na farin ciki da annashuwa. Ya yi godiya ga Allah, ya kuma tuba a gare shi, tare da fatan ya fitar da shi daga sharrin shaidan da aikata mummunan al’amari na savon Allah.

Yunwa ya ji ta zo masa, sai kuma gajiya da ta riski jikinshi. Ya fara neman abin da ya dace da shi, na abin da ya shafi abin sakawa a baki.

Wata bishiyar kwakwa ya gani a kusa da shi. Ya mike, ya je gare ta, yana tunanin yadda zai tsinka ya ci. Da ya duba gurin bai ga wani abu mai kama da dutse ba, da zai jehota, ko itace, sai kawai ya je ya dafa bishiyar gami da girgiza ta.

Wata dankwaleliyar kwakwa da ta matsu a tavata ta fado ce, wacce ke neman kuka bare an jefe ta da kashin awaki ta rufto zuwa kasa, bai ankara ba kawai sai ji ya yi wani dam a tsakiyar kansa. Da karamin yaro ne ko mace da tuni sun suma, sai dai shi ma din ya ji jiki, ya ganewa kurensa,  gami da galavaita. Don haka da ya nutsu, shi ma ya shiga galavaitar da ita, ya rinka hadata da bishiya har sai da ta vare biyu, sannan ya shiga ci, yana kokarin karar da ita.

Yana gab da gamawa, sam bai damu da tafiyar da Zuhra ta yi ba, ya san dai za ta shiga wani hali, kawai sai jin ihunta ya yi, ya yi hanzarin duban inda ihun ya sudado, sakanni da faruwar hakan ya hango tahowar ta a guje, ta nufo inda yake. Da ya ke ya bar gurin da ta bar shi, sai ba ta gan shi ba, ta zo wucewa ta kusa da shi a guje, idanunta a rufe cikin mummunan hali.

Kawai sai jin ta ta yi a bayan bishiya, ya janye ta, suka voye, yayin da ya samar da rufuwar bakinta don kar ta yi ihu.

Daga haka ba a yi dakiku ashirin ba, wani gawurtaccen mahaukaci, mummuna, garjejen kato, baki wuluk, rike da shafceciyar adda, yana surutai da wani yare da ba Hausa ba, ya wuce ta kusa da su, bai gan su ba, ya nausa inda ya ke tsammanin nan Zuhrar ta bi.

Zuhra ta yi ajiyar zuciyar karaya, idanunta a warwaje, sun yi jajawur. Ta dubi Abba da haushin shi ya sa ta a wannan hali.

Shi kuwa, kwakwar da ke hannunsa ya kalla, sannan ya kai baki, ya lunkuma, ya ci gaba da tauna, yana kallon saman bishiyar kwakwar, da alamun ko zai kara.

*

‘Umma, ni na fi son ki gaya min gaskiyar inda su Umma Maryam suke kawai.’ Abba ya fada ga mahaifiyarsa.

Hajiya Kilishi ta dube shi, duba na kwarai da tsananin jin haushi.

‘Wato karya duk aka gaya maka, da aka ce su da kansu suka bar gidan?’

‘Ni ban ce haka ba. To amma ina suka je ke nan?’

Ta yi ajiyar zuciyar takaici.

‘Sai ka yi kuma.’ Ta shiga fada ‘To wane ne zai san inda suka nufa, ko so ka ke a bi su har inda suka je, in ka zo a gaya maka? Ka manta mahaukaci da yawo, yanzu haka idan aka ce sun dangane da Sin mene ne abin mamaki a ciki.’

Ya mike ‘Ki yi hakuri Umma, zuciyata ba ta gamsu da wadannan kalaman ba. Zan iya tuna lokacin muna yara, akwai tsana da ke da Dadi ku ka yi musu, wadda na ke ganin bai dace ba, kun shiga cikin zarafin su da takurawa…’

Ta kalleshi da mamaki.

‘Ai idan tsanar ce, har da kai…’

‘Babu ni Umma, domin mu yara ne a lokacin ba zamu iya sanin tsana ba, inda ace so da ki ne na kyautatawa da rashin sa, da zan fi yarda. So na yi ki gaya min gaskiya, kamar yadda aka gaya min cewar Abba ne ya dauke Zuhra ya gudu da ita, ku ce kun sa an kama su, to sai in bincika in ga halin da ake ciki, ni zan jagoranci lamarin yadda za a hukunta su, na kuma nemo Abban duk inda yake in hukuntashi. Amma ba a biyo ta wannan hanyar ba.’

‘To ubanmu, sai ka tsara mana abin da ya kamata mu yi.’ Alhaji Masa’udu ne ya furta hakan, tsaye yake a bakin kofar falon daga ciki. Bayan tsit da dakin ya yi, a hankali ya tako kuma a nutse zuwa cikin falon, ya zauna a kan daya daga cikin kujerun falon, bai daina kallon Kabir din ba.

‘Kana so ka nuna mana, yanzu ka zamo babba, mai hankali da hangen nesa fiye da mu ke nan?’

Bai amsa ba, daman shima ba amsar yake nema ba.

‘To bari in gaya maka, alkawarin da su wadanda ka ke karewar suka dauka, idan da kai a ciki ba su ba to zan iya yin maganinku gaba daya. Abin da ba ka sani ba a ciki shi ne. Umma Maryam dai asalin ta matar Yayana ce, tsinanniyar mata ce da kana ganinta haka kamar mahaukaciya to ba mahaukaciya ba ce, ita ce matar da ta yiwa yayana mugun sharri, ta karya shi, da mai kudi ne na kin karawa, hankalin ta bai kwantu ba sai da ta ga ya tsiya ce, karshe ta ga har an kai da garkame shi a kurkuku, hankalin ta ya kwanta, to dukkanin dukiyarsa ta voye, shi ne ba ta kyale mu ba ta vadda-kama ta zo gare ni nima don ta wawashe dukiya ta, ta hanyar da ta daukar wa kanta cewar za ta karar damu daya bayan daya, shi ne ta fara da Zuhra, ta sa danta ya sace ta. To sannu a hankali za ta zo gare ka kai kanka da kake wani jajircewa wai kai mai gaskiya.’

Tun da ya fara maganar kallon sa da jin sa suke yi kowannen su da irin yadda maganar ke ratsa shi, kuma kowanne da abin da zuciyar sa ke raya masa.

Hajiya Kilishi ta san mijinta karya ya yi, kuma sharri ya lafta wa su Umma Maryam, to amma hakan shi ne abin da ta fi so, ta ji dadi da yadda ya yi wa dan na su bayani.

Ga Kabiru kuwa, a wannan karon an sauya masa tunanin sa, domin batun mahaifin nasa ya shige shi sosai, sai yanzu ya ke tunanin lallai fa haka lamarin ya ke, domin idan har ba zai manta ba yana da labarin wan mahaifin nasu, da irin tarin dukiyar sa, shin duk suna ina? Idan ya tuna da fuskar Umma Maryam sai ya ga za ta iya yin abin da mahaifin na sa ya fada, ko tantama babu biri ya so ya yi kama da mutum, idan ko haka ne, to zai dauki matakin gaggawa na hukunta Umma Maryam da diyanta, kuma shi da kansa zai nemo Abba ya karvo kanwar sa, bayan ya hukuntashi.

Bai dire ga tunanin sa ba, Alhaji Masa’ud ya ci gaba da kukkula sharrin da yake ga Umma Maryam da ‘ya’yanta.

Bayan kammala jin dukkanin irin abin da mahaifin nasa ya ke fada, Abba ya dade cikin tunani, daga bisani ya juya, ya fice daga falon, ya bar iyayen nasa jigun-jigum.

*

Kusan awanni shida ana tafka ruwa, kuma duk a kansu, sun yi tsamo-tsamo kamar verayen da suka kwana a ruwan zafi, ita Zuhra ko dago kai ba ta yi bare ta kalli Abba da halin da ya ke ciki, shi ne ma ya ke dan kallon ta jefi-jefi yana ganin matsanancin halin da ta ke ciki.

A gefen hannun ta na hagu akwai ciwo babba da ta ji kafin a fara ruwan, saboda wani maciji da ta gani, wanda ya sa ta firgita, ta rikice shi ne ta yi tuntuve da wani kututturen itace ta fadi.

Tun da take a rayuwarta ba ta tava jin ciwon da ya wuce buguwa ba, amma yau ga ta da wani makeken ciwo, kai ko a mafarki ma ba ta tava yin irin wannan mafarki ba na cewa yau ga ta a wani daji cikin mummunan hali, a ranta ta ce ita ta jawo wa kanta, ta gina ramin mugunta, da alama mai zurfi ta gina.

‘Ba za ka maida ni gida ba, wai me ka ke so da ni?’ Muryar ta da alamar karaya.

Abba ya yi wani abu mai kama da murmushi.

‘Ai ba ni na kawo ki ba.’

Ta ji haushin maganar sa, ko da yake a yanzu idan da sabo ta saba da ire-iren wadannan batu nasa, to me zai hana ta lallava shi, su koma gida, idan ya zo ta sa a rataye shi, ya mutu. Ai kuma da alama ba zai tava yarda da duk wata dabara tata ba, to mene ne abin yi? Ta tambayi zuciyar ta, wani bakin ciki ya kuma tuke ta, take ta raya a ranta gara ta yi masa me dungurugun ta huta, wato ta rabu da shi, idan ya so ko ta mutu, ko kuma ta lalace a hanya hakan zai fiye mata kwanciyar hankali, sai dai ita kanta ta san ta yi asara a rayuwarta, rayuwarta ta shiga muni, ba ta cimma burinta ba.

Zuciya bata da kashi, dukkanin tunane-tunanen da ta yi a zuciyarta da sakawa da warwarewa da ta yi a karshe ta yankewa kanta shawara guda daya, wato ta bar Abba, ta tafi ta rataye kanta, ko ta fita titi ta afkawa mota, ta mutu.

Ta mike daga inda take a zaune, ko kallon Abba ba ta kara yi ba, haka shi ma bai damu da ita din ba. Wata hanya ta bi, ta ci gaba da tafiya a jigace da wani hali mai ban tausayi, kafarta babu takalmi, don haka ta kan ci karo da kaya ta taka, idan karama ce ba ta kula da ita, idan kuma babba ce, ta kan zura hannu ta cire, ta yi kokarin ta danne zubowar hawaye daga idanunta, don tana ganin hakan gazawa ce, sai dai kuma babu yadda ta iya dolenta ta bar hawayen ya ci gaba da zuba abin sa, ita kuma ta ci gaba da tafiya ba tare da sanin inda ta nufa ba, cike da kudirin da ke zuciyarta, mutuwa ko rayuwa.

Ta wuce ta gefen dan wani ruwa mai kama da kogi, a ranta ta raya cewar da ruwan babba ne sosai wanda idan ta fada za ta mutu da ta fada, haka ta ratsa, ta wuce shi, tana kallon ruwan. Ta yi tafiya mai yawa, ba ta tunanin komai face abin da ta kudire a ranta, ba ta tava tsammanin rayuwa za ta yi mata haka ba.

Ta riski daya daga abin da take nema a gefen wata gona, wata igiya ta gani mai dabaibayi da alama ta daure wata dabbar ce, ko ciyawa. Ta dauki igiyar, gajera ce, domin ba ta da tsayi, sai dai da alama za ta yi mata abin da ta ke bukata.

Ta duba gefenta, daga dan nesa ta hango bishiyar da ta ke sa ran za ta yi mata abin da ta ke so, ta tafi a hankali zuwa gurin, ta kalli bishiyar da yadda take, daga bisani ta kama reshen bishiyar mara nisa don hawa, ba ta yi zaton za ta iya hawa ba, to amma da ya ke sa kai ya fi bauta ciwo, sai ta ga ta dare kan bishiyar, haka ta warware igiyar da ke hannunta, ta zarga a jikin wani reshen bishiyar da ya yi can wani vangare da Zuhra ba ta tantance gabas ne, kudu ne, arewa ne ko yamma ba. Bayan ta zarga igiyar a jikin reshen, sai kuma ta yi zarge a daya bakin yadda take bukata, tana kan reshen ta zura kanta a cikin daya zargen.

Abin da ta yi nufi shi ta yi, ta diro kasa, idanunta a rufe don ta rataye kanta ta mutu, domin idan kafafun ta suka yi kasa, to za ta yi gaggawar mutuwa kamar yadda ta ke so.

Ta yo kasa din, ba ta ankara ba sai jin ta ta yi tim a kasa, daga ita har reshen sun yi kasa, reshen ya tizgo ya fado, har sai da ya bugeta a gefen kafada. Wani radadi ya ratsa ta, ta dade a haka cikin tsananin zafi, wuyanta daure da igiya, haka shi ma reshen. Bayan dan lokacin da ta ga ta samu ‘yar nutsuwa, sai ta daga kanta sama tana cike da mamakin yadda reshen ya tizgo haka, alhalin ba ta da nauyin da za ta cizgo shi. Shi kuwa reshen kamar kallon ta cuce shi ya ke yi, domin yana zaman-zaman shi ta zo ta karya shi.

Mamaki ya rufe ta da takaici, haushi da tsana, Abba ne a saman bishiyar, alamu sun nuna shi ya tizgo reshen, ya sa su fadowa, ta yi kokarin yin magana cikin fushi, kafin hakan Abban ya diro, suka dubi juna tsawon lokaci kafin daga bisani ta ce.

‘Ina ruwan ka da ni, da rayuwa ta?’

‘Babu ruwana da ke da wahalalliyar rayuwarki. Sai dai kuma na san so ki ke ki kashe kanki, to wannan ne da ruwana, domin akwai irin mutuwar da ya kamata ki yi ba irin wannan ba. Ke kin fi cancanta da mutuwa mai tattare da tsananin nadama ba wai irin wannan ba. Don haka akwai irin mutuwar da ya kamace ki da ita ba wannan ba.’

Kuka ta ke yi da takaici, ta rasa me ma za ta ce masa, me ya kamata ta ce masa, sai.

‘Allah ya isa tsakanina da kai, babu ruwana da kai, ka rabu da ni, ka kyale ni, ba ni, ba kai.’

Bai kara furta mata komai ba. Haka ita ma, tsawon lokaci, sannan ta cire igiyar da ke wuyanta, ta mike da kyar, har da yin taga-taga, kafin ta tsaya tsam, ta fara tafiya, ba ta dubi inda Abba ya ke ba.

Tafe take, zuciyarta a cushe. Idan bakin ciki ya yi bakin ciki, sai zuciya ta rasa abin yi, haka ta kasance ga Zuhra, wasu baituka ta rinka rerawa a zahiri da amo mai tsuma rai.

Inda farin ciki, ashe akwai bakin kuwa,

In da walwala, ashe a gefe damuwa,

In da akwai fari, ashe akwai bakin bawa,

In da akwai yau ashe gobe na zuwa,

Bayan kyawu, muni ne da yawa.

Ta yi kokarin tuno gida, sai hakan ya haddasa mata juwa, dajin ta ji yana juya mata, yana yi mata ihu a cikin kwakwalwarta, bishiyoyi nata fareti a cikin idanunta, daga bisani dif ta ji.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Launin So 4Launin So 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×