Fursuna, kasuwar mazaje, kowa ya gama cin tasa gida zai koma. Wa'adin Alhaji Yusuf ya cika na zama a gidan yarin, shi da wadanda kiyasin lokacin su ya yi daidai, an sallame su, su bakwai ne suka fito a tare, yanayin garin ne ya fara zame musu wani iri kamar bako, za ka fuskanci hakan ta yadda wasu daga cikin su suke kalle-kalle dangane da yanayin garin, wasu ma har da kare fuskar su daga hasken rana, wanda hakan ke nuna sun dade a cikin wurin da babu rana, ko kuma ta yi karanci.
Mutane hudu daga cikin. . .