Skip to content
Part 7 of 10 in the Series Launin So by Kabiru Yusuf Fagge

Fursuna, kasuwar mazaje, kowa ya gama cin tasa gida zai koma. Wa’adin Alhaji Yusuf ya cika na zama a gidan yarin, shi da wadanda kiyasin lokacin su ya yi daidai, an sallame su, su bakwai ne suka fito a tare, yanayin garin ne ya fara zame musu wani iri kamar bako, za ka fuskanci hakan ta yadda wasu daga cikin su suke kalle-kalle dangane da yanayin garin, wasu ma har da kare fuskar su daga hasken rana, wanda hakan ke nuna sun dade a cikin wurin da babu rana, ko kuma ta yi karanci.

Mutane hudu daga cikin bakwan da suka fito suka yi vangaren dama, zuwa gurin wasu mutane da ke nuna tabbacin ‘yan uwansu ne suka zo taryen su, to haka suma biyun suka yi hagu gurin nasu ‘yan uwan cikin murna.

Alhaji Yusuf shi babu nasa ‘yan uwan, don haka, babu farin ciki a tare da shi, yanayinsa bai nuna ya yi murna da fitowarsa ba, wani tunani da ya fado masa a rai ne ya sa shi tsayuwa kyam a gurin, cikin matsananciyar damuwa. Tunanin matarsa da ‘ya’yansa ya fara yi, tunanin ko sun mutu.

Yanzu ne ya fara ganin ya kamata ya san halin da matarsa da ‘ya’yansa suke ciki, idan sun mutu to shi ma kam tashi ta kare, bai ga yanda daki zai ta shi ya bar jinka ba.

Kamanninsu da yanayinsu da irin kallonsu da maganganunsu ne suka fara zayyana a kwakwalwarshi.

Umma Maryam matarsa, Samir, Samira da Abba ‘ya’ya a gare shi, daya bayan daya suke zuwa da dukkanin yanaye-yanayensu su wuce ta cikin ransa.

‘Suna ina?’ Ya tambayi kansa. Bai samu amsa ba face hawaye da ya biyo kan kumatunsa.

‘A ina suke?’ Ya maimaita, kamar tavavve, kana ya mike zumbur, ya bi hannun dama da saurinsa, da alama ya tuno inda suke, Allah ya sa dai ba tavuwa ya yi ba.

Tafiya ya ke yi, babu abin da ya dame shi kuma bai damu da kowa ba, akwai inda ya ke son zuwa. Sai ya je hankalinsa zai kwanta a ganinshi. Sauri ya rinka yi, kamar ya manta gurin kamar bai manta ba, kamar tunanin sa zai hargitse, sai ya yi kokarin daidaita shi.

A haka, a haka har ya karasa bakin kasuwar, ya isa gurin da yake son zuwa, ba wani waje ba ne face gurin da ya tava komawa da iyalinsa suka rakuve lokacin da sharrin Alhaji Masa’ud ya fara bibiyar sa.

Da ya isa gurin bai ga wadanda ya je nema ba, daman tsammanin ganin su ya yi, to kuma ga shi bai gansu din ba. Lamarin ya sake dagule mi shi, bai manta da cewar matambayi baya vata ba, ya matsa gurin wani bawan Allah mai bakar goro, da alamu a gurin ya ke kasuwancinsa, ya yi masa sallama, sannan.

‘Don Allah wata tambaya gare ni.’

Mai bakar goron ya dan dube shi ‘Ina jin ka.’

‘Akwai wata mata da ‘ya’yanta uku da na sa ran ganinsu anan, ko ka gan ta?’

Mai bakar ya yi murmushi ‘Me take sayar wa a nan din?’

Alhaji Yusuf ya girgiza kai ‘Ba komai.’

‘Babu wani kwatance da za ka yi da za a gane ta.’ Ya tuntuve shi, domin ya lura yana bukatar taimakon sanin inda matar ta ke.

‘E to a zahiri kusan sama da shekaru ashirin da wani abu ta zauna a nan din da mijinta…’

Mai bakar ya yi galala ‘Babbar magana, to ai ni kaina na fi shekarun da ka lissafa ina sana’a anan, kuma ba na ce na san ta ba….’

Suka dubi juna tsawon lokaci, sannan Alhaji Yusuf ya yi ajiyar zuciya ‘Na gode.’ Ya juya, ya tafi.

Mai bakar ya bi shi da kallo, har ya yi nisa sai kuma ya kwalla masa kira ta hanyar fadin ‘Malam-malam.’ Alhaji Yusuf ya tsaya cak, gami da hanzarin juyowa kafin mai bakar ya gama yafito shi, har ya nufo gare shi. Suka kuma duban juna. Alhaji Yusuf ya juya kawai ya fara tafiya yana tunanin mai mutumin yake nufi? Iyalinsa sun kau daga doron kasa kenan?

Kafin ya samu amsa, ya ji yunwa ta addabe shi.

*****

Zuhra ta kawar da kanta daga kallon kyawawan korayen tsirran da suka yi luf-luf a kan tantagaryar kasa ta Ubangijin tsirrai, tsirran gwanin sha’awa amma a gurin Zuhra takaici suka sa ta. A yanzu ta gamsu da cewar ta vacewa Abba, wanda ta kira hatsari a rayuwarta, ita ta kara tsanar shi, mutumin da ya ke abokin gabarta, makiyinta, ya zame mata makale-mata, kiri-kiri tana son hallaka kanta wai ya hanata, da tuni ta rabu da duniya ta huta da bakin cikinsa.

Kwakwalwarta ta gama cushewa, zuciyarta ta yi duhu, babu abin da take kullacewa a ranta da ya wuce ta mutu a wannan lokacin. Don haka duk wani tunani nata bai wuce ta hallaka kanta ba.

Allah sarkin halitta, da ace ta san dandanon mutuwa to da ba ta neme ta ba, da ace ta san me za ta tarar a inda mutuwar za ta kai ta da ba ta yi gaggawa ba, ‘yar rayuwar ta da kuruciyarta da lallavata ta yi idan da nisan kwana ta sami rabo daga bauta ga mahaliccin ta nan gaba.

Ta mike a hankali, ta fara tafiya, inda ta dosa din gurin wani maciji ne da ya taho daga cikin yala-yalan ciyayi, ganin ta ya sashi tsayawa cak, ya kuma fasa kanshi tare da tattara makaman yakin sa. Shi kam ba komai ba ne ya sa shi yin hakan ba, face ganin ta tsare masa ainihin inda raminsa yake.

Baiwar Allah kuwa mai neman kuka ce bare an jefeta da kashin awaki, mai neman mutuwa ta ga dillalinta, sai ta nufi gare shi, tana da masaniyar irin zafin kisan macijin amman hakan shi ne burinta. Gara dafin maciji a jikinta da dafin kiyayyar Abba da ke ranta.

Tana tafe daf da macijin, abin mamaki shi da kansa macijin ya rinka jan jiki, yana yin baya-baya, yana tunanin wacce irin halitta ce wannan. Ya kuma yi tunanin ya zambada da gudu ya yi ta kansa, sai ya ga yin hakan ya yi kama da gudun da ba kuvuta a shi, gara kwanciya, domin yarinyar da ta doso shi yana kallon ta tana kallonshi idan ya gudu ma ba sha zai yi ba, za ta kamo shi ne ta kashe shi, don haka kawai ya tsaya ya kwaci kanshi.

Wani irin mugun tashi ya yo, gaba dayansa da saran sa zuwa kan fuskarta, da yunkurin kwatar kai ko da za a yi kare jini biri jini, ko mutuwar kasko.

Allah bai ba shi sa’a ba, domin saukar wani makeken itace a kanshi ta riga shi zafin nama, can gefe ya fadi, ya birgima sau biyu, ya mace ba tare da shurawa ba.

Abba da ya doki macijin yana tsaye rike da itacen, kallon Zuhrar ya ke yi wacce ke tsaye kamar busashen itacen kalgo, a tunaninta ta mutu, faduwa ne kawai ba ta yi ba, sai da ta yi mintuna masu dan yawa, kana ta lura ba ta mutu ba, kuma idanunta a yanzu fuskar Abba suke kallo, yana wani abu mai kama da murmushin mugunta.

Ajiyar zuciya ta yi da hawaye a tare da suka zubo, halin da take ciki ya munana, zuciyarta ta kuntata, kunar rai mai yawa ga Abba, a karo na farko cikin muryar kuka.

‘Don Allah ka kyaleni in mutu in huta da bakar rayuwarka. Ka kyale rayuwa ta, tunda da akwai bambanci tsakanin ta da ta ka, ka fita daga lamurana ka san babu ni babu kai.’

Dariyar takaici ‘Haka ne, rayuwarki daban, tawa daban, sai dai ke ki ka shigo tawa rayuwar…’

Ta katse shi da fushi ‘To na fita ka kyale ni mana, na ce na fita! Na fita!!’

‘Haba yarinya za ki fita din amma ba yanzu ba, kowa ya shiga gonar wani ya san ya yi ganganci, bare ke da ki ka shiga gonar abokin gabarki, sai a hankali, kin san duk dan da ya hana uwarshi barci, to shi ma ba zai runtsa ba.’

Ta fashe da kuka mai sauti.

‘To ka kashe ni mana ka huta.’ Muryarta cike da abin tausayi.

‘Allah shi ne mai kashewa ba ni ba, sai dai sanadi, kuma ni ba na cikin masu kudirin sanadi, kuma ba na fata in zama. Ke dai da ki ke ciki sai ki ta kokarin sanadin ta ki rayuwar, tun da kin kasa sana’ar tawa.’

‘To ka kyale ni.’

Ya kalli wata ungulu da ta gifta tana yi musu kallon mushe.

‘Lokaci ne bai yi ba, ki dai ci gaba da kokari ita mutuwar wulakanci guzirinta wulakanci, haka tana tanade da masaukin wulakanci. Kaico da mummunan karshe, wulakantacciyar makoma, sinadaran wahala…’

Ya wuce, ya bar ta anan ko dubanta bai yi ba. Maganganunsa suka rinka yi mata amsa-kuwwa, kamar za su tarwatsa dodon kunnenta, ji ta yi ana yi mata kara a kunne, ta yi hanzarin tuna kurumcewa, tabbas alamun sa ne ta ji a kunnenta.

Ta zabura da gudu, ta yi kan wata bishiya, ta gwaru da ita, ta dawo da baya ta fadi, kanta ya fashe daf da kunnenta. Ba ta daddara ba ta kuma mikewa, ta zabga da gudu, kananan tsirrai da itatuwa da take yin karo da su tafiyar ruwa take da su. Dutse da ‘yan kayoyi kuwa duk sun fasa mata kafafuwa, amma ba ta damu ba. Wasu sassa na kayan jikin ta ya yayyage, wasu guraren kayoyi, dangin su karangiya sun kassara su har da yagar naman jikinta. Ta kiririce.

Gudun da ta ke, irin kananan namun dajin da suke dajin kan sasu ranta a na kare, su ba ta wuri, ba ta tsaya ba sai da ta kai ga wani tafki mai gudana, nan ta yunkura tun karfinta ta fanjama cikin ruwan nan, a lokaci guda kuma ta saki gavvan jikinta, ta yadda kai tsaye za ta mutu da wuri.

Sa’ilin da ruwan ya fara tsiyaya cikin kunnuwa da sauran kafofin baki, hanci ne ta ji an yi gefe da ita, cikin hanzari kuma aka fitar da ruwan da ta fara sha ta hanyar danna cikinta.

Idanu da ta yi da fuskar Abba, ta san shi ya ceto rayuwar ta, wannan ya sa ta kwalla ihu da karfi, hakan ya sa ta ji wani gungurungun a kanta, ta cikin kunnuwan ta suka cushe.

‘Sai ki tashi, ba irin wannan mutuwar za ki yi ba.’

Garara-garara ta ji maganar tashi, kuma ba sosai ba. Ta yi kokarin mayar masa da amsa sai ta ji ta kasa furuci, tana ta motsa baki. Wayyo Allah, ta bebence ta kurumce!

Ta bi fuskar Abba da kallo, shi ma a yanzu kallon nata yake a nutse, wani hawaye na vari guda ne ya biyo kan fuskarsa.

Ba su daina kallon junan ba, har lokacin da dorinar ruwa ta biyo wata tsohuwar kada suka wuce ta tsakiyarsu. Hankulansu sun tafi.

*****

Maganganunta sun tsuma shi matuka, ta yadda har sai da hawaye ya zo idanunsa, ya tausaya musu matuka, kuma ya yi alkawarin kawo karshen al’amarin ko da ba zai yi masa dadi ba.

Ya kuma nutsuwa tsaf yana tuna wata rayuwa ta can-can baya da ta shude, shekara da shekaru. A karshe ya dire a tunanin yadda sakamakon ya kasance, akwai matsala ace yanzu Umma Maryam tana kurkuku, kamar yadda yayan mahaifinsu Alhaji Yusuf ya kwashe shekaru a can, ga kuma barazanar salwantar da su Samir, Abba da Zuhra, duk ta sanadiyyar iyayensa.

‘Sam bai kamata haka ta faru ba.’ Ya fada a ransa.

Yanzu ga shi duk abubuwan can sun faru, idan har mahaifinsa ya zamo butulu, ya ki jinin dan uwansa da iyalansa, to shi ga soyayya ta kullo zuciyarsa zuwa ga Samira, haka nan ga son da Samir ke yi ga kanwarsa Zuhra.

‘Kar ki damu Samira, lamari ne na rudin duniya da sharrin shaidan, idan Allah ya yarda komai zai zo karshe, zan so ki yi min wata alfarma. Alfarmar kar ki ki ni, kar ki ki iyaye na da ‘yar uwata, domin ke ma iyayenki ne, kuma ‘yan uwanki ne mu din, abinda ya faru sharri ne na zuciya, wanda Allah zai kawo mana karshen sa.’

Samira ta dube shi kawai, zuciyarta ta yaba da tunanin sa, ya yi namijin kokari matuka wajen kokarin tsayawa akan gaskiya a ganinta, ta yaba da halayensa.

To amma ta ya ya zai iya yin maganin abinda mahaifansa suka kudiri aniyar kawar da su daga doron duniya? A matsayin shi daya, kuma da a gare su.

Yanzu ne ta fara fahimtar akwai wata makarkashiya da Alhaji Masa’ud ya shirya gare su (iyayen ta da ‘yan uwanta). Ta fara tunanin cewar su din ‘yan uwansu, dalilan da ba ta sani ba na zamansu a gidan nan a matsayin barori, wulakantattu masu bara yanzu ta na neman daukar haske.

Koda yake an sauya ainihin dansandan mai alaka da kes din Umma Maryam a matsayin matar da ake zargin ta hada baki da danta ya sace Zuhra, hakan bai hana Kabir bincikar wanda ya kamata ya yi bibiya gami da binciko fayel din ba, da kuma wanda aka mika wa kes din.

Ya taki sa’a, Sifiritanda Inuwa Lambu, mutum ne mai kirki, mai kokarin yin aikin sa saboda Allah da gujewa sava masa, fari, dogo, cikakkiyar siffa irin ta Hausawa.

‘Me ma ka ce ra’ayin ka game da kes din?’

‘Ban yarda da cewar an yi adalci ba a cikin sa, akwai kura-kurai da dama.’

‘Kamar yadda ya tabbata ba ka nan aka aiwatar da al’amarin, sannan idan ba yaron ne ya sace ta ba, to ina ya tafi da ita?’ In ji Sifiritanda Inuwa Lambu.

‘Yauwa.’ Cewar Abba, ‘Na farko ban yarda saceta ya yi ba, sai dai ya tafi da ita din kamar yadda ka ce, za ka yarda da ni idan ka yi la’akari da abin da binciken ka ya kawo maka, da kuma abin da na fada maka, domin shi ma yaron ba shi da ikon tava mota a gidan ko da wanki ne, to bare ya sami makulli ya shiga, ita ma ta shiga ya sace ta, haka ne?

‘Sannan akwai maigadi a gidan nan, kamar yadda ya fada salin alin suka fita, ba banke shi ko banke kofa suka yi suka fita ba, bare zargi ya shiga tsakani….’

‘Ba ka tunanin wata dama ya samu ya yi amfani da ita.’ Sifiritanda Inuwa Lambu ya tari numfashin sa.

‘Yauwa. Ka ga batun sacewa ya kau kenan, ko ba haka ba? Don haka nake nuna maka idan ka yi la’akari da jawabin (statement) din ‘yansanda za ka tarar akwai kuskure a ciki da aka yi amfani da shi aka zalunci daya vangaren…’

A yanzu kallon Kabir, Sifiritanda Inuwa Lambu yake yi da mamaki.

‘Kana ba ni mamaki, shin ita wannan yarinyar da aka sace, ba kanwarka bace? Sanna kuma ba iyayenka ba ne suka sa aka kama ita matar da ka ke ganin sharri aka yi mata…’

‘Haka ne, kanwata ce Zuhra, kuma iyayena ne, sai dai ni ina magana ne akan gaskiya ba zalunci ba, wanda babu bi ko biyayya a yayin savawa mahalicci ga kowa…’

Sifiritanda Lambu ya yi shiru, yana kallonsa, ya lura a zahiri maganarsa gaskiya ce, akwai bukatar a bibiyi kes din a fitar da a’i daga rogo, ya yi ajiyar zuciya.

‘Haka ne, mu bari zuwa gobe, mu ci gaba da tattaunawa, zan yi wani dan tunani.’

Kabir da Sifiritanda Lambu, ba su yi kasa a gwiwa ba wajen haduwa a kan lokacin da suka sanya, haka kuma suka fara bibiyar lamarin a tsanake, kafin daga bisani su bazama inda ya dace wato kotun da ta yanke wa Umma Maryam hukunci. Suka ga alkali, wanda a lokacin an sauya anihin alkalin da ya yi shari’ar.

Alkalin da suka samu din ya saurare su, ya kuma gamsu da hujjojin da suka je masa da su. Da taimakonsa aka samo bakin zaren kes din, tare da nazarin irin tufka da warwarar da aka sha a yayin kukkulla zaren al’amarin.

Duk abin da ake ciki mahaifin Kabir ba shi da masaniya da tuni ya lalata shirin dan nasa, yana can, yana kulla na shi shirin akan yadda za a gano masa ‘yarsa, sai kuma matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya, wato matsalar Kantafi, wanda ya mayar da shi saniyar tatsa.

*****

Umma Maryam ta kalleshi sosai.

‘Kabir ne wannan?’ Tana bukata ga ‘yarta Samira, wadda take cikin matukar murna da farin ciki tun fitowar mahaifiyar tata daga kurkuku, wadda Kabir ya taimaka hakan ta samu.

Umma Maryam ta yi ajiyar zuciya.

‘Ba ni labarin abin da ya ke faruwa. Sannan ki sanar da ni halin da ‘yan uwanki suke ciki. Ya ya kuma labarin mahaifinki?’

Samira ta girgiza kai. Ta zayyane mata labarin dawowar Kabir kasar nan, abin da ya riska a gidan su, haduwarta da shi da kuma kokarin sa na ganin fitowar ta da bayyanar da gaskiya.

‘Amma har yanzu babu labari dangane da vatan Abba da Zuhra, shi ma Samir ban san takamaiman inda yake ba, sai dai kwanaki wani dansanda yana gaya min cewar ya tava ganin shi a gidan dambe. Baba ma babu labarin shi.’

Kallon ta kawai Umma Maryam ke yi, kafin ta nisa.

‘Amma lokacin fitowarsa ya yi.’ Ta mike daga zaunen da take, suma suka mike ‘Ku zo mu je.’ Ta gaya musu a lokacin da ta yi gaba alamar tafiya. Kabir ne ya dakatar da ita.

‘Akwai mota sai mu je duk inda zamu je a ciki.’

Ta dubeshi sosai, sannan ta dubi motar. Ta girgiza kai ‘Ba na bukatar hawa mota.’ Ta ci gaba da tafiya.

Kabir ya kalli Samira.

Samira ta gyada masa kai alamar su bi ta. Haka suka yi, suka bi ta.

Nufin Umma Maryam shi ne, ta je ainihin kurkukun Gidan Sarki ta binciki halin da mijinta yake, kuma kamar yadda ta fada, ko da kurkukun ta fita daga garin Kano, to fa ba za ta hau mota ba, musamman ta gidan Alhaji Masa’ud.

Tana gaba suna biye da ita, Kabir bai saba da tafiyar kafa ba, amma dalili ya sa yana ganin zai iya jure zuwa duk inda za a din.

Barin su inda suke babu zango dogo, daga can vangaren Alhaji Yusuf ne cikin sauri ya zo wucewa, iyalinsa za shi nema, ba don yana daya varin ba da sun yi kicivis da su Umma Maryam din, haka suma su Umma Maryam da sun yi gamo da shi da suka tafi nema. Wani iko na Allah, Kabir ne kawai a cikinsu ya hango shi, domin yanayinsa da yadda yake tafiya ne ya ja hankalin sa, har ya kalle shi din, ya kuma tausaya masa. Bai tsaya ba, domin bai san ko wane ne ba, ya ci gaba da bin su Umma Maryam.

Sun yi doguwar tafiya tsakanin giftawar su da Alhaji Yusuf, kawai sai Kabir ya tsaya tare da fadin.

‘Umma, Samira ku tsaya.’

Suka tsaya din. Sannan ya juya, ya kalli baya, bai hango dalilin tsayawar tasu ba, wato mutumin da ya gani, cikin ladabi ya kalli Umma Maryam.

‘Kamar na ga wanda zamu je nema ya wuce ta can vangaren.’ Yana nuna tsallaken, gami da mikewa ga nuna inda ya nufa, zuciyarsa ta ba shi hakan.

Umma Maryam ta kura masa idanu, kamar za ta yi magana, ba ta yi ba, ita kuwa Samira mahaifiyarta take kallo. Can Umma Maryam ta nisa, kawai sai ta juya zuwa inda Kabir ya nuna, suka rufa mata baya.

Alhaji Yusuf ya tsaya cak, da tafiyar da yake, kamar mai tuna wani abu da ya manta, kamar mota sai ya juya, ya tsallako titi da gudu, ya biyo hanyar da su Umma Maryam suka bi, idan ka gan shi babu maraba da mahaukaci. Da su Umma Maryam da Alhaji Yusuf, ba su debi lokaci ba sai ga su sun hadu, Umma Maryam da Alhaji Yusuf suka kalli juna da idanun kwalla, Samira fashewa ta yi da kuka, saboda ganin mahaifinta. Kabir kallon su ya ke yi daya bayan daya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Launin So 6Launin So 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×