Babban kuskuren da Kabir ya jiyewa mahaifinsa, shi ya tafka na kaiwa mutanen nan kudi inda suka bukata ba tare da ya yi taka-tsantsan ba, don haka ya afka cikin tarkonsu.
Misalin karfe biyu na dare, ya je shi kadai da motarsa gurin da suka bukata. Kamar yadda suka gaya masa ya yi. Wato ya kai kudin jikin bankin Jama'a daga baya ya ajiye. Sai kuma ya kewaya gaban bankin zai ga diyar sa ya dauke ta, su tafi.
A tunanin sa haka-siddan din zai yi, ya ajiye kudin ya dauki 'yarsa. Bai yi tunanin komai ba. . .