Skip to content
Part 9 of 10 in the Series Launin So by Kabiru Yusuf Fagge

Babban kuskuren da Kabir ya jiyewa mahaifinsa, shi ya tafka na kaiwa mutanen nan kudi inda suka bukata ba tare da ya yi taka-tsantsan ba, don haka ya afka cikin tarkonsu.

Misalin karfe biyu na dare, ya je shi kadai da motarsa gurin da suka bukata. Kamar yadda suka gaya masa ya yi. Wato ya kai kudin jikin bankin Jama’a daga baya ya ajiye. Sai kuma ya kewaya gaban bankin zai ga diyar sa ya dauke ta, su tafi.

A tunanin sa haka-siddan din zai yi, ya ajiye kudin ya dauki ‘yarsa. Bai yi tunanin komai ba na game da yaudara, ya aikata hakan. Ya ajiye jakar kudin a inda suka so, ya kewaye bayan otal din, gabansa na faduwa na tunanin zai ga Zuhra zaune a kan daya daga cikin kujerun gurin. Amma ko me kama da ita bai gani ba, kai asal ma duk ilahirin kujerun dake gurin maza ne a zazzaune. Da ace ya san ‘yan ta’addan nan ma, to da ya ga daya daga cikinsu a zaune yana kurvar barasarsa.

Ya karade ilahirin gurin, babu mai kama da Zuhra bare ita kanta Zuhrar. Har wurin tarbar baki ya shiga, ya tambaye su, amma babu labari. Ya fito da gudu zuwa inda ya ajiye jakar kudin ita ma babu ita, jifan gafiyar Vaidu kenan.

Bai hakura ba, sai da ya zagaye otel din sau hudu, sannan ya tabbatar an yaudare shi ne, ransa ya yi mummunan vaci, hankalinsa ya tashi. Ya juya zuwa ga motarsa, ba don ya tafi ba. Ya jingina da jikinta yana kallon ginin otel din da ‘yan sheke ayar da ke shige da fice a gurin. Tsawon awa guda, kana ya juyo jikin motar. A lokacin ne ya ga farar takardar like a jikin gilas din motar na gaba. Ya dayo ta, ya fara karantawa.

Sanin ‘yarka ta yi araha a wannan kudin da ka kawo ne ya sa ba mu ba ka ita ba. Don haka ka saurari sako na gaba don a shi ne za ka amshi diyarka.

Sai ka ji mu a sako na gaba.Ka kuma kiyaye barazanar tsomo ma’aikata a cikin wannan lamari. Yin hakan na nufin rasa ‘yarka kenan.

Ya kudundune takardar cikin fushi, har zai jefar da ita sai kuma ya fasa. Ya cusa ta a aljihu, ya zagaya zuwa inda ya ajiye akwatin kudin, ya tarar babu ita, shi kansa ya yi tunanin hakan, a fusace ya koma motarsa.

Su kuwa a nasu vangaren duk wani bilinbituwa da Alhaji Masa’udu ya ke yi, suna ganin sa. Bayan da suka cimma burinsu, na nasarar shirin da suka shirya, sai suka je, suka shigo motarsu, suka wuce gurin ‘yan uwansu.

Sun karasa cikin farin ciki don samun nasarar abin da suka shirya. Suna cike da kalaman murna da za su gayawa abokan fashinsu.

Ba su tarar da kowa ba a wajen gidan da ‘yan uwan nasu suke. Wani gida ne guda daya a ware a cikin dajin, wanda bayan shi babu wani a kusa da shi. Sun yi zaton tarar da daya daga cikin biyun da suka bari. Amma da ba su gani ba, ba su damu ba. Suka shiga cikin gidan, abin da suka riska ya ba su mamaki. ‘Yan uwansu suka gani daddaure a jikin wasu dirakun rumfar da ke tsakar gidan.

Ba su yaudari zuciyoyinsu ba, suka san aikin Abba ne, domin babu su a gidan a wannan lokacin. Dukkanin alamu sun tabbatar musu da guduwarsu.

Suka kwance ‘yan uwansu.

‘Me ya faru?’ Daya ya tambaye su, tun ma kafin ya gama kunce su.

‘Akwai ban mamaki. Yaron yana da matukar dabarun yaudara, he is very wicked.’ (hatsabibi ne)

Daya daga cikin su ya yi hanzarin magana a gaggauce.

‘Ai ba tsayawa za mu yi ba, mu yi sauri mu bi su, ba mamaki mu kamo su.’

Haka kuwa suka yi a gaggauce suka bazama wajen gidan. Sun yi turus ne a lokacin da suka ga but din motar da suka ajiye a bude. Idan suka dawo, sau tari ba su fiye damuwa da cire makullin motar ba, to haka suka yi a wannan lokacin ma.

Wanda ya ajiye motar ya yi hanzarin zuwa bayan motar. Abin da ya je dubawa babu ita. Jakar kudin da suka amso daga gurin Alhaji Masa’udu Naira miliyan ashirin. Gumi ya lulluve shi, ya yi hanzarin duban ‘yan uwansa.

‘Ya sace jakar kudin.’

A tare suka tambaye shi. Tambayar da ba sa bukatar amsa. Babban nasu ne ya ba su umarnin bin su. Ya shige motar da hanzari, su kuma ragowar suka bazama a kafa, wasu suka yi gabas, wasu kudu, sai arewa, domin ba su san inda ya nufa ba. Idanunsu rufe, babban nasu dake cikin mota, ya bi bayan wadanda suka yi arewa da gudu, babu alamar zai tsaya daukar wani daga cikin su.

Sun yi gudu mai yawa a galavaice, kafin su tsaya a daf da wata ‘yar kasuwa dake wani kauye. Abba ne ya tsayar da su a gefen wata bishiyar kwakwa. A da Abba ya yi mamakin yadda Zuhra ta rinka bin shi, tun lokacin da ya kuvutar da su daga gidan ‘yan ta’addan nan, amma daga baya ya tabbatar tana gudun tsira ne, wanda a baya ba ta da wannan kudirin. Ita da take neman mutuwa.

A gareta kuwa Zuhra, a yanzu wani kallo na musamman take yiwa Abba. Ta tuno abin da ya so faruwa, sannan ta tuno irin yadda Abba ya kuvutar da su, ta yi ajiyar zuciya, ta kalli Abba, a zuciyarta kuma ta ci gaba da kallon abin.

Wato suna daure a gidan, daya daga cikin ‘yan fashin ya so yi mata fyade, wanda hankalinta ya yi mummunan tashi. Tabbas wannan ba karamin tashin hankali ba ne, ba karamin muni ba ne, wannan katon ya keta mata mutunci, ya yi mata fyade a gaban Abba.

Abin da ya ba ta mamaki shi ne, yadda ta ga Abba ya fi ta damuwa, ya fita tashin hankali. Wanda daga karshe hankalinsa bai kwanta ba har sai da ya ga ya kuvutar da ita, ya sami nasarar daure su da karfinsa da jarumtarsa cikin taimakon Allah. Har zuwa fitowarsu za su gudu, suka ji karar motar dawowar wadanda suka tafi dauko kudin da mahaifinta zai ba su don su bayar da ita. Inda suka voye a kan bishiya, bayan shigarsu cikin gidan, Abba ya je, ya ciro mukullin motar a gaban motar, ya je but din motar, ya dauko jakar.

Zuhra ta yi ajiyar zuciya, tana kwalla, tana kallon Abba.

‘Ina zamu je, kuma ina za ka kai wannan jakar?’

Abba ya dubeta, sannan ya kalli can cikin kasuwar. ‘Gida zamu je. Jaka kuma ina fatan kin gane ko ta wane ne.’

Ta gyada kai ‘Ta Dadina ce.’

‘To mayar masa zan yi.’ Ya ajiye mata jakar a gabanta. ‘Ina zuwa.’

‘Ina za ka je?’ Ta tambaye shi.

‘Na san kina jin yunwa da kishirwa. Zan samo miki abinci ko ruwa.’

Ba ta iya magana ba. Hawaye kawai ta iya fitarwa na kuka. Har ya tafi. Da ya san me zai faru da bai tafi ba. Domin daga inda Zuhra take zaune tana hango Abba, ya doshi wata rumfa, a ranta, zuciyarta ta wanke Abba kal-kal, ta cire duk wata kiyayyar sa da take yi, ta dauko son shi ta dora, ta dasa. Abin da ba ta tava zato ba, wai yau a wayi gari tana son Abba, babban makiyinta. Lallai so mai launi da yawa, ji ta yi ba wanda idanunta ke son kallo kamar fuskar Abba, tana ji a ranta babu wanda ta ke son ganin farin cikinsa kamar shi. A ranta, tana son idan ya dawo ta nemi gafarar kiyayyar da ta nuna musu, har ta nemi halaka shi. Tana son ta gaya masa duk duniya babu wanda take so, so irin na ‘yan uwantaka, so irin na zuciya da zuciya kamar shi.

Gabanta ya fadi a lokacin da ta tuna abin da zai ce mata. Ai kawai cewa zai yi ‘Ke tafi can, na tsaneki! Na tsaneki!’

Hawaye ne masu zafi suka fito mata daga idanu, ta yi saurin duban inda Abban yake. Ya yi daidai da kuma tsayawar motar ‘yan fashin nan a gurin. Gabanta ya fadi, shi kenan an yanka ta tashi, sun kama Abban. Ta fito cikin kuka, gadan-gadan ta nufi gurin da zummar su hada su biyun su kama.

Lokacin da ‘yan fashin suka doshi sashin rumfar da Abban ya shiga, domin ganin sa da suka yi, shi kuma a lokacin ya hango wata randa a can bayan rumfar, ya isa cikin sauri ya debo ruwan a moda, ya cika wasu ledojin fiya-wata guda biyu da ya tsinta, maimakon ya dawo ta rumfar da ya yi bara aka ba shi sadakar birodi, sai ya bi ta baya don kar mutanen su ce ya dame su da zirga-zirga.

Wannan ya haddasa masa savani da ‘yan fashin nan, su kuma suka mike ga inda suka yi zaton ya dosa.

Abba na kewayowa, ya yi kicivis da Zuhra idanu rufe tana neman kai kanta gurin ‘yan fashi, janyeta ya yi suka bar wajen. Da hanzari suka je bayan wata bukka suka voye. A kan idanunsu ‘yan fashin suka gama karade kasuwar suka koma cikin motarsu, suka hau, suka tafi.

‘Me ya sa ki ka nufi gurinsu?’ Abba ya tambayeta yana kallonta. Ita kanta Zuhra ta fahimci wani irin kallo da Abba ya ke yi mata, akwai wani abu na zuciya da zuciya a tare da kallon.

‘Na yi tsammanin sun kama ka ne, shi ya sa na fito garesu komai ta fanjama-fanjam, ni ma su kama ni.’

Abba ya yi murmushi. Murmushin da Zuhra ba ta tava ganin irin shi ba, gare shi. Murmushi na musamman. Suka yi shiru tsawon lokaci.

‘Me ya sa ba ka dauki kudi a cikin jakar nan ba, ka je ka na bara?’

Abba ya dube ta ‘Na fi son mu mayar masa da kudinsa.’

Hawaye take yi ‘Abba ina son ka!’ Ta fada a ranta. Ji take kamar ta fada masa a zahiri. Shi ma ya yi tunanin kalmar a nasa ran. Amma bai yi tunanin zai iya gaya mata ba. Abin da ya fi daga masa hankali shi ne yadda son Zuhra ya ke neman samuwa, koma ya samu a zuciyarsa.

Suka ci gaba da tafiya, Abba a gaba, Zuhra na biye da shi. Can ta tsaya, ba ta sanar da shi tsayawarta ba. Sai bayan da ya yi tafiya mai tazara, sannan ya ji alamun ta tsaya, shi ma ya ja, ya tsaya, kana ya dube ta. Yana kallon fuskarta, ita ma tana kallon tasa fuskar, a haka ya fara tafiya sannu a hankali zuwa gareta. Ya isa daf da ita ba tare da ya daina kallonta ba, haka ita ma ba ta daina kallonsa ba.

Zuciyarta ce ta tuko mata da abinda ke cin ta a rai, idan ba ta fada ba, za ta iya yin ciwon zuciya. Ta yi ajiyar zuciya. ‘Abba ina son ka.’ Da ta fada sai ta ji kamar an sauke mata wasu tarin kaya da suka yi mata dan banzan nauyi.

Shi ma abin da ya dami Zuhra a zuciya, shi ya dame shi, kwaryar bisa ce ke dukan ta kasa. Bakinshi yana rawa. ‘Nima ina kaunarki Zuhra.’

Suka dubi juna da idanun kuka, suka yi murmushi da fuskar jin dadi.

*****

Gumin da yake tsattsafowa a goshin Alhaji Masa’ud, ya fi fadan da fushin da yake yi bayyanuwa a zahiri. Da ya yi- ya yi, ya kai tukewa sai ya yi shiru. Sannan Hajiya Kilishi ta samu damar fadin wani abu a matsayin kwantar masa da hankali.

‘Ka kwantar da hankalinka Alhaji, na hango wata mafita. Ai ka san akwai mu da samo makirci. Wato abin da na ke ganin za a yi daya ne, bai kai biyu ba. Kamata ya yi ka nemi abokinka, ka gaya masa halin da ake ciki, na tabbatar zai kawo maka mafita…’

Ya katse ta da kallo ‘Wanne abokin nawa ki ke nufi?’

‘Kantafi.’ Ta ce.

Ji ya yi kamar ta kafa masa kusa inci biyu a tsakiyar madiga. ‘Wai kin san ko a kan me raina ya ke a vace, kin san ko a halin da muke ciki ni da Kantafi?’

Murmushi ta yi, kamar ba ta damu ba ‘Ni ko na sani, domin a sanina ma bayan kai, ni ce ta biyu. Ba batun dan nan Kabiru da su Umma Maryam ba ne da suke neman tona maka asiri, suke neman vata shirinka ba?’

Ya gyada kai alamun e, batun kenan. Hajiya Kilishi kuwa ta dora daga inda ta tsaya.

‘Batun Kantafi, ai kun shiga takun saka ne saboda ‘yan abubuwan da ka daina ba shi, yanzu ace ka ci gaba da ba shi din, ko ka yi masa wata lafiyayyiyar kyauta, me ka ke tsammanin zai faru? Ai juya shi za ka rinka yi kamar waina. Su irin su Kantafi ai matsalarsu kudi, idan ka ga ana fada da su, to an hana su, in kuma ka na son ganin shiri da su to fa an ba su. Don haka shawarar da zan ba ka, ka nemi Kantafi, ka share laifinka daga gurinsa, ku zauna, ku fitar da mafitar abin da ka ke ciki. Wannan fa ba yana nufin ka amince masa ba ne, a’a hanya ce ta maganin matsalar ka gami da sanadinsa. Hanya ce ta yin amfani da shi, ta halin da yake da shi. Ko ya ka gani?’

Bai yi magana ba, domin yana tunani, zuwa can da ya gama sai ya dube ta. ‘Kina nufin na yi amfani da Kantafi wajen maganin wadannan karfen kafan kenan?’

‘Ai mugu shi ya san makwantar mugu, abin da nake nufi kenan.’ ta ce da shi.

Ya daga kansa sama, yana kallon wani hoton sa da ya dauko a garin Gusau, ta jihar Zamfara. Ya yi kuri idanunsa ne ke kallon hoton, amma zuciyarsa dansa Kabiru take kallo, wanda ya dage sai ya taimaki su Umma Maryam, yana kokarin tona masa asiri, ya yi ajiyar zuciya, a hankali ya ce.

‘A kan rufin asirina zan iya hakura da kai Kabiru, tun da ba ka ji.’ Ya tuno da ‘yarsa Zuhra, haka kawai ya ji tsoro a ransa. Ga shi a kan danne dukiyar dan uwansa, yana neman rasa ‘ya’yansa guda biyu, wadanda ya mallaka, alhalin yana matukar son su, idanunsa suka yi jawur, a lokacin da ya ke kokarin yin magana, Hajiya Kilishi ta rigaye shi.

‘Tunanin me ka ke yi?’

Ya girgiza kai ‘Ba komai.’

Wayarsa ya zaro, ya shiga laluben lambar Kantafi. Ya amince da shawarar matarsa Hajiya Kilishi.

Daga nasa vangaren, Kantafi ya dauka.

‘Babban kira, daga ji yau ta samu kenan, an tuna da mu kafin mu mu kira.’

Alhaji Masa’ud ya yi tsaki ‘Kai tsiyarka kenan, kullum samu-samu, kudi-kudi. Ba ka la’akari da rashin samun.’

Ya yi dariya ‘Ai mune silar rashin samun, don haka mu samun shi ne a gabanmu.’

Alhaji Masa’ud ya ce ‘To ta samu din, ina son nan da awa daya ka same ni a nan gidana.’

‘A haba, ai tunda ni ka ke son gani, kawai ka sameni a otal din da ka fi sanina da zama, idan ba haka ba, to kawai ka hakura.’

Alhaji Masa’ud ya yi kwafa ‘Shi-kenan, mu hadu a can din gani nan.’ Ya katse layin. Yana duban Kilishi.

‘Zan je in same shi mu tattauna.’

Lokacin da Alhaji Masa’ud ya fita a motarsa don zuwa ya riski Kantafi, ya yi daidai da dawowar Kabir gidan. Allah ya taimaki Kabir din mahaifin nasa bai ganshi ba. Shi ya gan shi, har ya shiga harabar gidan, sai ya yi sha’awar ya bi mahaifin nasa inda za shi, musamman da yake yana son yin magana da shi. Ya juya, ya bi bayansa.

A tsakanin mintuna goma sha bakwai da sha takwas, Alhaji Masa’ud ya isa otal din Madara da Kantafi ya ke. Da ya tsaya da motarsa, ya fito daga ciki da ace zai daga kansa sama da ya hango Alhaji Kantafin, wanda yake hangen duk wani wanda ya iso otel din, a mota, a babur ko a kasa. Don haka yana kallon isowar Alhaji Masa’ud din, ya yi murmushi a zuciyarsa ya ce.

‘Lallai Alhaji ka kagu da gani na, irin wannan hanzari ko awa dayar ba ta cika ba.’ Ya ci gaba da kallonsa, yana nazarin yanayin da yake ciki, yana kuma tunanin abinda ya kawo shi. Fatansa daya Allah ya sa ta fadi da nauyi, ta fadi galala, wato banza ta fadi.

A bakin kofar dakin da Kantafi ya ke, Alhaji Masa’ud ya danna jiniyar sadar da sakon zuwan bako. Kantafi ya tafi sannu a hankali, zuwa wani madanni na bude kofar, ya danna alamun bayar da damar shigowa.

Alhaji Masa’ud ya bude kofar, ya shiga cikin dakin, yana kallon fuskar Kantafi da kirkirarren murmushi. Ko musabiha ba su yi ba, bare gaisawa, suka nemi kujeru, suka zauna, suna duban junansu.

‘Wata kwangila na zo da ita mai sauki, kuma mai tsoka.’ Cewar Alhaji Masa’ud.

‘Da alama ta gagara kenan?’ Tambaya daga Kantafi.

Alhaji Masa’ud ya dube shi ‘Kamar ya ya?’

‘Na san ai, a yanzu ba za a neme ni a bani kwangila in dai ba gagara ta yi ba.’ In ji Kantafi.

‘Kai matsalata da kai kenan, kulafuci, to ka sani ko ba za ka iya kwangilar ba.’

Kantafi ya gurza wata uwar dariya. ‘Ka dai fada ne kawai. Ina sauraron ka, ka yi bayani kawai.’

Alhaji Masa’ud ya hadiye abin da ke cikinsa ya bayyanawa Kantafi dukkanin abin da ke faruwa da abin da ya ke gudun faruwarsa, na tonon asirin sa da kawo karshensu, da kuma abin da ya ke bukata a gurinsa.

Alhaji Kantafi ya mike a hankali, ya taka zuwa bakin taga, ya tsaya, tunanin abin da ya kamata a yi yake, a matsayin sa na kwararre, wanda zai fitar da mafita.

Shi kuwa Alhaji Masa’ud gabansa ne ya ci gaba da faduwa, asirin sa da yake tsoron kar ya tonu, anya ba ya tona shi din ba kuwa? Wai me ya kai shi furta batunsa ga mutumin da ya san ma’illaci ne. Koda yake idanunsa ne a rufe, yana neman mafita, shi kuwa ruwan kashe gobara ba a zave.

A nasa vangaren, Alhaji Kantafi ya samo mafita guda biyu, daya ta shi ce, daya ta Alhaji Masa’ud din. Lokacin da ya juyo din babu murmushi a fuskarsa, yin murmushin na iya vata masa shiri, don haka ya murtuke, ya dawo ainihin kujerar da ya tashi, ya zauna.

‘Gaskiya ne Alhaji, kana bukatar taimako, domin tonon asirinka a wannan lokacin yana nufin wulakanci ga rayuwarka, duk wata hanya da ya kamata ka bi don maganin lamarin to ya kamata ka bi, ni kuma zan taimaka maka da duk iyawa ta. Abu na farko da ya kamata ka yi a shawarce shi ne, magana ce ta dukiya, kadarori da kudi ko? To ka tattara duk wata kadara ka sayar da dukiya, kudade da suke bankuna ka fitar da su, ka hada komai naka a guri guda, ka canji fam na Ingila, ko ka sayi zinar (gwal) ka hada kan iyalanka, ka fita da su wata kasar.

‘Magana ce ta shari’a, ayayin yin shari’ar nan idan aka ga wannan tarin dukiyar, da tarin kudin da kadarorin a kasa, to za a sa maka alamar tambaya, wanda za a yi ta bincike, a karshe kuma ka san abin da zai biyo baya. Amma idan ka tattare komai, ka fita da su babu wani da hankalinsa zai kai kansu, kuma ba za a tada hankalin iyalanka ba.’

Alhaji Masa’ud ya yi shiru. Da alama dabarar ta fara yi masa, yana jin gamsuwa a zuciyarsa, ya dade yana wannan tunani da nazari. Shi ma Kantafi ya kyale shi bai ce masa komai ba, yana yin nashi tunanin. Arziki ne zai zo masa a dare daya, lallai dare daya Allah kan yi bature, mai kera jirage da birane.

Alhaji Masa’ud ya yi ajiyar zuciya, yana girgiza kai na gamsuwa. ‘Shawararka ta yi.’ Ya fada yana duban Kantafi.

Kantafi ya ce “To Alhamdu Lillahi, ai mu din ba na wasa ba ne.’

Ya kamata Alhaji Masa’ud ya yi nazarin wannan hamdala ta Kantafi, amma da yake idanun sa a rufe suke bai tsaya yin hakan ba, ya dauko dubu ashirin ya ajiye masa a gaba.

‘Za mu rinka yin waya duk, abinda ake ciki.’

Alhaji Kantafi da murmushin sa yake duban kudin ‘Ba matsala, ina sauraronka. Wannan na shan ruwa ne kenan?’

‘E mana.’ Cewar Masa’ud.

Suka yi sallama. Alhaji Masa’ud ya tafi.

Kantafi ya rakashi da idanu, har lokacin da ya sauka kasan farfajiyar otel din ya shiga mota, Kantafi yana hangoshi ta tagar dakin otel din. Sai dai da yana da idon gani da ya ga Kabir dake voye a bayan dirowar dakinsa wanda duk abin da ya ji, yake faruwa tsakanin shi Kantafin da Alhaji Masa’ud mahaifinshi. ‘Alhamdu Lillahi dukiya ta zo. Yanzu idan ya yi abin da nake so, ya gama, daukar tsabar kudi na Fam a akwati ko zinare zai fi komai sauki, ni kuma sai in san kasar da na dosa.’ Ya ci gaba da murmushi. ‘Kakata, ta yanke saka.’ Kantafi ya fada.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Launin So 8Launin So 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×