Duk yadda Ziyada take rusa ihun kuka tana turjewa su Rukayya basu sarara wajen jan ta da ƙarfi ba. Duk yadda zukatansu ke cike da tausayin ƴar’uwarsu, cika umarnin mahaifiyarsu shi ne gaba da komai a rayuwarsu. Sosai suke cike da tsoro da fargaban inda Ummanmu za ta mayar da Ziyada a halin yanzu, amma ba su da yadda za suyi, ko kaɗan ba su da ƙwarin gwuiwar tambayar inda za’a kai ta.
Kasancewar safiya ce, mutane ɗaiɗaiku ne ke zirga-zirga a cikin layi. Ganin wannan baƙon al’amari da bai taɓa faruwa akan Ummanmu da ƴaƴanta ba sai aka tsaya kallo, fuskokin manya da yara cike da mamaki. Duk inda suka wuce sai a bi su ɗuuuu don ganin inda suka nufa. Duk yadda fuskar Hajiyarmu ke ɗaure tamau idanunta sunyi jajur masu ƙarfin hali sai da suka tare ta da tambayar lafiya? Me yake faruwa haka?
Kamar wacce aka ɗinke ma baki. Bata samu zarafin amsa ma ko mutum ɗaya daga cikin masu tambayarta ba har suka ƙarasa ƙofar gidansu Khamis.
Anan ne ta tsaya cak, ta waiga baya tana hango su Rukayya. Izuwa yanzu da Ziyada ta tabbatar ga inda za’a kai ta sai kawai ta ƙara ƙarfin turjewarta, dambe take neman yi da yayyinta. Da gaske nema take ta ƙwace a hannunsu ta gudu, ta gwammace ta gudu zuwa ko ina ne da dai a shiga da ita gidansu Khamis a tona asirin abinda suka aikata ita da shi a ɓoye, ba tare da sanin kowa ba.
“Ku sake ta!”
Muryar Ummanmu ya ratsa dodon kunnuwansu ba tare da sun san sa’adda ta ƙarasa gurin ba.
Sakinta suka yi kamar yadda ta umarce su. Ita kuma ganin ta samu damar da take buƙata sai ta yunƙura da dukkan ƙarfinta za ta zura a guje. Wani irin fisga da bala’in ƙarfi Ummanmu tayi mata, ko kafin ta dawo cikin hayyacinta Ummanmu ta dunƙule hannu ta kai mata wani naushi a kumatu. Nan take ta kife a ƙasa, fuskarta ya daki ƙasa, bakinta ya fashe, goshi da hancinta suka yi wani bala’in daujewa. Tsananin azaba da raɗaɗi yasa Ziyada ta kasa kuka, sai wani irin gurnani take yi kamar mai naƙuda tana malelekuwa a ƙasa.
“Wa kika ɗauka sa’an wasanki anan gurin? Tashi mu tafi!”
Ummanmu ta bata umarni cikin tsawa da ɗaga murya.
Sau huɗu tana yunƙurin miƙewa sai ta sake kifewa a ƙasa, a na biyar ɗin ne ta yunƙura daƙyar tana cije baki, idanunta na ganin hurhuɗu ta miƙe tsaye a wahalce tana tangaɗi.
Da ƙarfin gaske Ummanmu ta fisgi hannunta zuwa ƙofar gidansu Khamis. Wani irin duka tayi ma ƙofar gidan da ƙarfi nan take ƙofar ta buɗe, daman sun zare sakata ta ciki saboda wayewar gari.
Ummanmu na shiga cikin gidan riƙe da hannun Ziyada da take jaye da ita Rukayya da Kareema suka bi bayanta. Sauran jama’a ma da suke biye da su don ba idanunsu abinci take suka rufa musu baya zuwa cikin gidan.
Alhaji Abubakar da Yusuf na zaune kan kujerun roba a tsakar gidan suna shan iskar safiya. Daga can gefe ɗaya kuma Khamis ne sanye da singileti fara kar da gajeren wando iya gwuiwa, brush ne a hannunsa na dama yana goge baki, a hannunsa na hagu kuma ledar pure water ne guda ɗaya.
Hajiya Hauwa tana kicin tana aikace-aikacen abin karyawa. Kasancewar babu tazara sosai tsakanin kicin da inda su Alhaji Abubakar ke zaune daga cikin kicin ɗin suke hira da maigidanta, lokaci bayan lokaci ƴaƴan ke tsoma musu baki.
Ummanmu tana isa tsakar gidan ta tura Ziyada da ƙarfi gaban su Alhaji Abubakar, ta tafi taga-taga saboda rashin ƙarfin jiki ta zube a ƙasa. Sai a lokacin ta samu ƙwarin gwuiwar fashewa da wani marayan kuka.
“Subhanallahi! Assha!! Hajiya menene kike yi haka?”
Alhajin ya tambayeta hankalinsa a tashe bayan sun miƙe tsaye shi da Yusuf. Fuskarsu akan Ziyada da take kuka da daujajjen fuska.
Kafin Ummanmu ta amsa mishi karaf idanunta suka faɗa kan Khamis da yake tsaye yana kallon Ziyada da take yashe a ƙasa. Da wani irin zafin nama da zafin zuciya ta ƙarasa inda yake ta fincikosa zuwa kusa da Uban. A haukace kuma cikin rufewar idanu ta ɗaga hannunta ta fara zabga mishi mari. Cikin ƙasa da mintuna biyu a jejjere tayi mishi mari shidda. Yana tsaye ƙiƙam ko gezau baiyi ba, sai idanunshi da suka kaɗa suka yi jaaa, shatin yatsunta sun fito ƙarara a fuskarsa.
Ta ɗaga hannu za ta sake zabga mishi mari a bazata taji an riƙe hannunta, aka wankalar da hannun. Hajiya Hauwa ce, cikin bala’i da masifa ta ɗaga hannu za ta zabga ma Ummanmu mari da saurin gaske Rukayya ta riƙe mata hannu, Kareema ma tayi saurin ƙarasawa ta riƙe ɗaya hannun. Jikinsu babu inda ba ya rawa ganin ana neman keta alfarmar mahaifiyarsu a bainan nasi.
Hajiya Hauwa ta buɗe baki za ta fara zazzaga ruwan bala’i Ummanmu ta dakatar da ita ta hanyar sanya ƴar yatsarta manuniya a kan laɓɓanta.
“Shhhhhhhh! Ki rufe min wannan ɗaɗɗoyan bakin naki. Ki saurara ki ji abinda ke tafe da ni kafin ki buɗe ruɓaɓɓen bakinki ki fara kawo min zantukanki na ƙarya da son zuciya.”
Sai ta mayar da idanunta kan Khamis da har lokacin yake tsaye ƙiƙam, idanunshi na kan Ziyada. Ko ƙiftawa baya yi.
“Kai! Tantirin yaro Khamis kalle ni nan!”
Ta faɗa cikin tsawa bayan ta ɗago haɓarshi ta dawo da fuskarshi saitin nata. Wani irin kallo suke aika ma junansu su biyun, ƙarara kallon da Ummanmu ke masa babu abinda yake baiyanawa sai matsananciyar tsanar da take masa.
Shi kuwa nashi kallon babu tsana a ciki. Saboda ita ɗin mahaifiyar yarinyar da yake matuƙar so ce. Amma kallo ne mai bayyana jin haushi, haushin ita tafi taka muhimmiyar rawa wajen tare gaba da baya don hana shi mallakar abinda yake so.
Wani dogon tsaki Ummanmu taja, ta tsartar da miyaun bakinta gefe ɗaya. Ta nuna Ziyada da yatsarta manuniya ta ce
“Likita ya auna jini da fitsarinta sannan ya tabbatar mana tana ɗauke da ƙaramin ciki…”
“Nawa ne!!”
Khamis ya katse ta da amsar cikin kai tsaye ba tare da kunyar Ummanmu, ko tsoron iyayensa, ko shakkar idanun jama’ar da suke tsaye cirko-cirko a tsakar gidan ba.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!!”
Bakunan jama’a da dama ciki har da iyayensa suka ja salatin suka sauke cikin tashin hankali.
“Eh! Ciki nawa ne. Kuma ina son abina, kashaidi na farko kuma na ƙarshe shi ne kar wanda yayi gigin taɓa min ciki. Ina rantsuwa da Allah duk wanda ya ce zai taɓa min cikin jikin Ziyada sai nayi shari’a das…”
“Tas! Tas!! Tas!!!”
Ƙaran saukar ƙarfafan maruka uku da Yayanshi Yusuf ya sauke mishi a jere.
Alhaji Abubakar da Hajiya Hauwa kuwa babu wanda yasan sa’adda suka sulale zuwa ƙasa. Kawai ganinsu aka yi daɓar zaune a ƙasa sunyi zaman ƴan bori, da hannayensu biyu ɗore a kawunansu. Hajiya Hauwa da take ta nishi cikin masifa tana son sauke kwando-kwando na rashin mutunci ga Ummanmu sai ga ta tayi laƙwas, idanu warwaje baki buɗe take kallon Auta Khamis, ɗa da take mutuwarso fiye da Yayanshi. Lokaci ɗaya wasu zafafan hawaye suka fara ambaliya a fuskarta.
Ganin hawayen da take yi yasa Ummanmu sakin wata dariya mai ciwo. Ta taka a hankali ta tsuguna gabanta
“Kin ji da kunnuwanki ko? Uhmmm! Dama kin adana hawayenki Hajiya Hauwa, da sauran kukanki a gaba. Wallahi in dai wannan ɗan naku ne da kuka sakarwa mara yana tsula tsiyatakun da yake so a cikin gari da unguwa baki ma fara kuka ba, wannan ai somin taɓi ne. Me aka yi da maza Hajjaju? Uhmmmm! Muje zuwa dai.”
Ta matsa kusa da Alhaji Abubakar ta ce
“Alhaji ka ga tufkar da nasoi muyi ma hanci tun kafin afkuwarsa ko? Amma da yake kai ɗin ma tara da goma ne tsakanin kai da sususun matarka sai kuka sa ƙafa kuka shure maganganun da nazo muku da shi a wancan lokacin. Kuka rufe idanunku, ƙiri-ƙiri kuka ƙi fahimtar gaskiyar da nazo da ita. Har sai kuna nuna min ma kamar Ziyada ita ce ta maƙale ma ɗanku ɗan so shalele. To ga ta nan, kun samu ƙarin ƴa. Na rantse da girman Allah Ziyada baza ta taɓa zama a gidana da cikin shege a jikinta ba.
Idan kun so ku riƙe ta da shegen jikanku a jikinta. Idan baku so ba ku haɗa ita da Uban shegen cikinta ku kora su duniya. Abu ɗaya da nake so ku sani shi ne, duk sadda zuciyar tausayi irin na uwa ta waiwayi ƴarta babu inda zan fara nema sai anan gurinku. Ta inda aka hau ta nan za’a sauka. Na barku lafiya!!!”
Tsam ta miƙe tsaye ba tare da ta saurari ko za su ce wani abu ba ta damƙi hannun Kareematu da Rukayya taja su suka kama hanyar ficewa daga gidan.
“Ummanmu, wayyo Allah Ummanmu. Na tuba na bi Allah na bi ki Ummanmu. Don girman Allah ki yafe min. Kar ki tafi ki barni a inda ban san kowa ba Ummanmu. Wayyo, Wayyo Allah na… Wayyo jama’a ku taimaka min ku ba ta haƙuri..”
Sambatun da Ziyada take yi kenan cikin ihun kuka tana zabura a haukace za ta ruga ta bi bayan uwa da ƴan’uwanta.
“Ziyada, Na rantse da girman Allah daga yau matuƙar ba ni ce na neme ki ba kika tako min gida BAN YAFE MIKI BA.”
Wannan magana da Ummanmu tayi, shi yai sanadiyyar tsayawar bugun numfashin Ziyada. Da fari wani irin sanyi jikinta yayi, ta tsaya cak a inda take, sai kuma ta tafi a slow motion za ta faɗi ƙasa. Da ihu mai baiyana matsanancin tashin hankali Khamis ya ƙwalla mata kira, cikin zafin nama ya ƙarasa da gudu ya tare ta ta faɗa a jikinsa, a lokacin da take daf da kifewa a ƙasa.
Wani irin ƙwaƙƙwaran bugawa zuciyar Ummanmu tayi, daga jin yanayin kiran da yayi cikin ihu, da kuma ƙarar takun ƙafa da taji alamun gudu, ta san babu lafiya ga Autarta. A ruɗe su Rukayya suka waiwaya baya don ganin abinda yake faruwa, hankali tashe suka motsa hannayensu da nufin ƙwacewa sai ta sake riƙe su ƙam. Tsawon daƙiƙu sha biyar Ummanmu na tsaye tana mayar da nauyayan numfashi, zuciyarta tayi wani irin nauyi, sai suya da zugi take mata. Su Rukayya na rusa kuka haka taja hannunsu suka fice daga gidan.
******
Duniya juyi-juyi wai kwaɗo ya faɗa a ruwan zafi. Haka zalika kowane bawa na tafe ne a bisa doron ƙaddarar da tun tale-tale aka rubuta zai faru a rayuwarsa. Cikin ƙasa da kwanaki biyu labarin abinda yake faruwa tsakanin ahalin biyu ya karaɗe unguwar.
Mutane da ba’a raba su da tsegumi da son ganin ƙwaf, wasu masu ƙarfin hali har da iya shiga gidajen biyu da sunan jaje. Amma fa a zahirin gaskiya kaso biyu da rabi cikin uku na masu shiga gidajen suna shiga ne da son ganin ƙwal uwar daka da kuma neman cikakken ƙarin bayani kan abinda ya faru, ta ina aka faro, ta ina aka kwana, ta ina aka haihu a ragaya? Amma kamar haɗin baki tsakanin gidan Ummanmu da gidansu Khamis shiru ne, babu wani sabon magana da yake fita.
Ummanmu sam ba ta ma bari a ganta. Sai dai aga su Rukayya, su kuwa daga gaisuwa fuska a ɗaure tamau suke amsa jajen da ake musu. Acan ɓangaren gidansu Khamis kuma wani irin ɓoye Hajiya Hauwa take ma Ziyada. Duk masu jelangiyar shiga gidan babu wacce ko wanda ya taɓa tozali da ita. Daga bisani ma sai suka tsiri ɗabi’ar kulle gidan da rana gatse-gatse, abinda sam ba sabonsu bane. Suna ji za’a yi ta ƙwanƙwasawa sam baza su buɗe ba, sai dai in sun tabbatar ɗaya daga cikin ahalin gidan ne.
Ziyada wani irin mawuyacin hali ne ta shiga a sanadiyyar baragurbin ƙwan da ya a rayuwarta. Ga tsananin damuwar da take ciki na fushin mahaifiyarta gare ta, ga damuwa da tashin hankali na tunanin wai ita ce da ciki a jikinta. Zama a gidansu Khamis wani irin zama ne kamar na kurkuri a gare ta. Duk da ba tsana, ba harara, ba hantara, amma ko kaɗan babu fuska daga mutanen gidan. Khamis da take mutuwar so har ta ƙetare umarnin mahaifiyarta akanshi ba ganinshi take yi ba. Abinda bata sani ba tun washe garin faruwar al’amarin iyayen suka yi mishi kaca-kaca sannan suka kora shi makaranta. Duk yadda suka tutsiye shi da tambayar yadda lamarin ya faru shiru yayi musu, sun juya shi dambu da taliya ya ƙi tankawa.
A zuciye Yusuf ya taso yana masifar a barshi ya nakaɗa ma Khamis ɗin tsinannen duka, iyayen suka dakatar da shi.
“To ya za’ayi? Sai haƙuri kawai. Aikin gama ya riga ya gama, duka babu abinda zai haifar sai ƙarin ɓacin rai.”
Cewar Alhaji Abubakar.
Da damuwa sosai a fuskar Hajiya Hauwa ta kalle shi ta ce
“Ni duk ba ma wannan ba. Ya za ayi da cikin jikin yarinyar nan?”
A tare Uban da ƴaƴan suka aika mata wani irin kallo mai wuyar fassarawa.
“Ban gane ba Hajiya. Me kike nufi? Cikin jikin yarinya kam dole ta haife shi tunda dai na ɗanki ne. Kinga, kar ma ki sake kawo wata magana saɓanin ta arziki kan cikin nan. Kina gani dai daman ba wani yawa ne damu ba, lallaɓawa za’ayi idan ta haihu sai a ɗaura musu aure…”
“Aure kuma Alhaji? Taɓɗijan!!! Yarinyar ta haihu a gida sannan a aura ma Auta ita…?”
“Hauwa’u!!!”
Ya kira ta da ainahin sunanta cikin tsawa, fuskarsa bayyane da ɓacin rai ƙarara.
“Idan kika nemi kawo min maganar banza akan abinda yake faruwa zan baki mamaki. Ki kiyaye ni fa! Tun farkon sadda Khamis ya fara zancen yana so a aura masa ita wacece tayi uwa tayi makarɓiya ta kore maganar? Da tun farko kin bari an ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki da za mu kai kan wannan matakin? Ko za ki mutu aure tsakanin Auta da Ziyada kamar anyi an gama, in dai ina raye, kuma in Allah ya yarda.”
Ƙus tayi, ta san ya fi ta gaskiya. Sunkuyar da kanta ƙasa tayi ya gama bambamin faɗansa ya fice. Bayan ya jaddada ma Khamis awa biyu kacal ya bashi ya shirya zai mayar da shi makaranta.
Wani irin mawuyacin rayuwa ta cigaba da yi mai cike da ƙunci da raɗaɗin zuciya. Babu rashin ci ko sha, kusan ko wane lokaci abubuwa na kwaɗayi da marmari Hajiya Hauwa take mata.
Aka ce abin cikin ƙwai ya fi ƙwan daɗi. Duk da cikin jikinta ba na halal bane kakannin ɗan suna son jikansu, balle ma da a hankali kwanaki suna turawa watanni suka fara shuɗewa cikin nata ya fara bayyana a sarari.
“Ziyada, a lissafina yanzu kin shiga wata na biyar. Ya kamata ki fara zuwa asibiti…”
“Asibiti kuma Ummee?”
Ta katse ta cikin rawar murya hankalinta a tashe. Sai kuma tayi rau-rau da idanunta, lokaci ɗaya ta fara tsiyayar hawaye.”
“To miye kuma abin kuka daga maganar gaskiya? Kin san dai bazai yiwu mu barki zaune a gida ba tare da sanin matakin lafiyarki da na abinda ke cikinki ba. Alhaji shi ya fara tunkarata da maganar, ni ma kuma naga gaskiyarsa. Ki kwantar da hankalinki kin ji?”