Rukayya da Kareema ruƙunƙume junansu suka yi suna rusa kuka cikin tashin hankali, jin halin da ƙanwarsu take ciki wacce a kullum da tunaninta suke kwana suke tashi ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba.
Ummanmu mahaifiyarsu ce, ba su da ikon tilastata yin abinda bata yi niyya ba, tana da haƙuri ƙwarai, amma duk sa'adda aka fusatata bata iya fushi ba.
A al'amarin Ziyada nasu ido ne kawai, tun da ta shata musu Allah ya isa kan ko da wasa suka tafi gurin Ziyada babu wacce ta taɓa taka ko ƙofar gidansu Khamis. . .