Skip to content
Part 12 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Rukayya da Kareema ruƙunƙume junansu suka yi suna rusa kuka cikin tashin hankali, jin halin da ƙanwarsu take ciki wacce a kullum da tunaninta suke kwana suke tashi ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba.

Ummanmu mahaifiyarsu ce, ba su da ikon tilastata yin abinda bata yi niyya ba, tana da haƙuri ƙwarai, amma duk sa’adda aka fusatata bata iya fushi ba.

A al’amarin Ziyada nasu ido ne kawai, tun da ta shata musu Allah ya isa kan ko da wasa suka tafi gurin Ziyada babu wacce ta taɓa taka ko ƙofar gidansu Khamis, a taƙaice ma idan za su wuce ta gurin gidan da saurin gaske suke wucewa don kar Allah ya isa ya shafe su.

Dangi da ƴan’uwa babu irin magiya da roƙon da basu yi ma Ummanmu kan tayi haƙuri Ziyada ta dawo gidanta ko kuma gidan ɗaya daga cikinsu ba. Amma tasa auduga ta toshe kunnuwanta, tayi kunnen uwar shegu ga kowa. Da aka matsanta mata ma sai ta shata kalmar tsinema Ziyada za tayi muddin wani daga cikin dangi ya ɗauketa daga gidansu Khamis.

A dole kowa ya kawo ido ya zuba ma al’amarin. Daman iyayen Ummanmu da na mahaifinsu sun daɗe da rasuwa. Babu wani shaƙiƙi da zai iya tilastata yin abinda bata yi niyya ba. Abu ɗaya da basu taɓa fashin yi duk sallah ba shi ne roƙon Allah ya sassauta zuciyar Ummanmu kan Ziyada, Allah ya kawo sauƙi da rangwame a cikin fushin da take yi da ita. Allah ya nuna musu ranar da Ummanmu za ta furta kalmar yafiya ga shalelen ƙanwarsu. Suna cikin kukan kwatsam suka tsinkayi muryar Ummanmu tana cewa

“A faɗa mata, na yafe mata.”
Ta faɗa cikin sanyin murya. Daman jikinta a sanyaye yake, jin irin halin da Ziyada take ciki sai ya ƙara sanyayar mata da jiki sosai. A kasalance ta miƙa ma Hajiya Hauwa hannayenta ta kama ta miƙe tsaye.

Ta ɗaga ƙwayoyin idanunta da suke ta maiƙo a cikin hasken lantarki da na farin wata ta ce
“Ya Allah ka shaida, ni Khadeeja na yafe ma Ƴata Ziyada laifukan da ta aikata min tun daga haihuwarta har zuwa yanzu. Ina roƙon kayi mata albarka, ka sauketa lafiya don darajar sunayenka tsarkaka kyawawa.”

Tsananin farin ciki da jin daɗi yasa Ummee ruƙunƙume Ummanmu tana sambatun murna. Abba da Yaa Yusuf kuwa hannu bibiyu suka ɗaga sama suna godiya ga Allah, fuskokinsu cike da yalwataccen fara’a.

Tunawa da halin da ta baro Ziyada a ciki yasa ta janye jikinta daga na Ummanmu da sauri.
“Na gode Hajiya. Bari in koma in duba ƴar Amanata. Ki cigaba da taya mu addu’a Allah ya sauketa lafiya.”

“Mun gode Hajiya. Mun gode ƙwarai. A madadin Khamis shi ma ina nema mishi afuwa…”

“Na yafe mishi.”

Ummanmu ta katse Abba tun kafin ya ƙarasa abinda yayi niyyar faɗa.

“Allah ya yafe mana gaba ɗaya.”
Ta ƙara da faɗin haka.

“Ameen ya Allah”
Suka amsa gaba ɗaya.

Ummee dai tuni ta daɗe da barin gurin da sauri. Su Abba har sun juya za su tafi Rukayya da Kareema suka kalli Ummanmu, fuskarsu a shagwargwaɓe,

“Ummanmu, don Allah mu ma ki janye Allah ya isar…”

“Na janye, ku je ku dubo ta. Allah ya raba lafiya.”

Ihun murna suka saki kamar ba dare ba, sannan suka rungumeta suna godiya. Daman da hijabi a jikinsu, da saurin gaske suka bi bayansu Abba don duba jikin ƴar’uwarsu.

Bata koma cikin gida ba sai da suka ɓace ma ganinta. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke. Ta haɗiye wani dunƙulallen abu da ya tsaya mata a maƙoshi tana rayuwa cikin ƙunci tun bayyanar ciki a jikin Ziyada. A yanzu sai taji wannan abu ya faɗa mata, nauyin da zuciyarta tayi na tsawon wata watanni a hankali yana raguwa.
“Subhanallahi Alhamdulillah”
Ta faɗa a fili. Sai kuma wasu siraran hawaye masu sanyi suka gangaro daga cikin idanuwanta.

Babbar yatsarta ta sanya ta ɗauke hawayen. Ta mayar da ƙofar gidan ta rufe, ta juya zuwa cikin gida. Ko da ta shiga ɗakinta bata ɓata lokaci gurin tunanin abinda yake faruwa ko wanda zai faru nan gaba ba. Bayi ta shige ta ɗauro kyakkyawan alwala, ta saka hijabi ta fuskanci gabas, ta fara jero nafilfili tana roƙon Allah ya sauƙaƙa ma Ziyada ya sauketa lafiya.

****** ******

“Ziya, Ziya, Autar Ummanmu kinga, buɗe idanunki ki gani ƴan’uwanki ne. Kin ganni Kareema, ga Rukayya ma a kusa da ke. Kuma Ummanmu ta ce a faɗa miki ta yafe miki duniya da lahira.”
Cikin hukuncin Allah da saukar maganganun a kunnuwanta kawai sai taja wani nannauyan ajiyar zuciya.

Sai kuma ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta don ganin shin da gaske ne abinda taji ko kuwa mafarki ne tayi a cikin nannauyan barcin da ya ɗauketa.

“Alhamdulillahi Allah mun gode maka. Hajiya matso ki gani ta farfaɗo.”
Nurse Halima ta faɗi haka a ruɗe sannan ta matsa kusa da Ziyada don tabbatar da ita ɗin da suka yi tsammanin ta rasu ne ta farfaɗo daga jin kalaman bakin ƴar’uwarta.

Itama Ummee da ta haɗe kai da bango tana sharɓen hawaye jin abinda Nurse ta ce da saurin gaske ta matsa inda Ziyadar ke kwance don tabbatarwa. Jikinta babu inda ba ya rawa.

Ziyada tana samun nasarar buɗe idanunta ta zuba akan Rukayya da Kareema da suke rirriƙe da hannayenta suna hawaye sai ciwon naƙuda ya sake taso mata gadan-gadan. Nan take ma’aikaciyar jinya ta fara aikinta cikin ƙwarewa Ummee na taimaka mata, cikin hukuncin Allah a wannan karon babu wani haɗe ƙafa da Ziyada take yi. Ko da kan ɗa ya taho wani nishi mai ƙarfi tayi nan take kan ya fito gaba ɗaya, Nurse Halima tasa hannayenta biyu da suke ɗauke da safar hannu ta taimaka gurin ƙarasa janyo shi. Yaron ya galabaita gaba ɗaya, minti ɗaya tsakanin haihuwar na farko ƴar’uwarsa ta biyo bayansa da mahaifa gaba ɗaya.

Ita kam jaririyar da kuzarinta ta faɗo duniya, tana fitowa ta fara callara kuka inyaaa, inyaaaa. Kukanta shi ya ankarar da su Abba lallai an sauka. Tsananin farin ciki yasa su saka goshinsu a ƙasa suka yi sujadar godiya ga Allah.

Bayan yanke ma jariran cibiya, Nurse Halima ta miƙa ma Ummee ƴar babyn mace ta mayar da hankalin kan namijin da ya fara fitowa. Tunda aka haife shi ko kuka baiyi ba, sai take mishi ƴan dabaru irin nasu na ma’aikatan jinya.

Duk yadda tayi iya ƙoƙarita Allah bai sa mai nisan kwana bane. A galabaice yayi kuka sau ɗaya Allah ya karɓi rayuwarsa. Jikinta a sanyaye ta kwantar da shi gefen gadon bayan ta lulluɓe shi da zani.

“Hajiya sai dai fa muyi haƙuri. Hassan ya koma ga mahaliccinsa.”

Ta faɗa idanunta na kan Ummee da take goge jikin jaririyar da man Zaitun.

Allahu akhbar! Duk da jariri ne da basu saba da shi ba ko misƙala zarratin ahalin gidan sun ji rasuwarsa. Ummee da su Rukayya har da kuka. Abba ne yayi mishi wanka da taimakawar Yusuf, aka naɗe shi cikin farin likkafanin da Abba ba ya rabo da shi a cikin ɗakinsa.

Cikin awa ɗaya da ƴan mintuna mai jego da ƙatuwar jaririyarta sun fito tsaf, an shirya su cikin sababbin sutura. Duk yadda taso yin hira da yayyinta da suke ta tsokanarta bai samu ba, saboda wani irin nannauyan barci da ke fisgarta. Daƙyar ta iya shanye kakkauran tea ɗin da Ummee ta haɗa mata cikin kofi ta bi lafiyar gado. Bayan anyi mata allura, ta sha magungunan da Nurse Halima ta taho da su musamman don amfanin bayan haihuwa.

Ana idar da sallar asubahi kafin a watse a masallaci jama’a suka shaida ɗaurin auren Ziyada da Khamis. Bayan kammala ɗaurin aure jana’izar Hassan ya biyo baya.

Ko da Rukayya ta koma gida Ummanmu mayar da ita tayi da saƙon a faɗa ma Ummee za ta dawo da Ziyada gidanta don yi mata wankan jego. In yaso bayan tayi arba’in sai ta tare a gidan mijinta. Duk da ba haka Ummee taso ba sai bata ja zancen da nisa ba, shi ma Abba bai ja zancen ba ya ce Allah ya kaimu sadda za ta gama wankan, ai kamar gobe ne in da rai da lafiya.

A haka kwanakin suka cigaba da tafiya cikin farin ciki da godiya ga Allah a duk ɓangarorin biyu. Toshe kunnuwansu suka yi wajen sauraren irin maganganu na assha da tir da yake zagayawa a unguwar. Rukuni-rukuni na mata ke ta tururuwar shiga gidajen da sunan barka da arziki, an rabu lafiya. Amma da yawansu tsegumi da gulma ke kai su, sai sun fito suyi ta mamaki suna hum-hum-hum.

“Ke kin ga ƴa jajur da ita ƙatuwa, kamar Khamis yayi kaki ya tofar. Lallai wannan shi ne ga doki har doki amma ƙafar na sakaina.”
Kalaman da suka fito daga bakin aminiyar Hajiya Hauwa ta ƙud da ƙud kenan bayan ta je gidansu Ziyada ta gano jaririya.

Kasancewar ruwa ya daki babban zakara. Tun da wannan ƙaddarar ta afka ma Hajiya Hauwa tayi wani irin sanyi. Kamar ba ita ce wacce a baya idan aka nuna mata yatsa a take za ta karya ba. Duk da kalaman sun sosa zuciyarta bata iya cewa komai ba, sai ɗan murmushin yaƙe da tayi wanda bahaushe ya ce ya fi kuka ciwo.

“Ki ƙyale su Hajiya, za suyi su gama ne. Aduk sa’adda bawa ya zama ba shi da aikinyi sai damuwa da abinda mutane ke cewa a kansa ko iyalinsa lallai ya ɓata ma kan sa lokaci. Muyi ƙoƙarin gyara tsakaninmu da Ubangiji kawai, mu cigaba da istigfari kan laifukan da muka aikata. Mu nusar da ƴaƴayenmu kiyaye sake aikata kuskure makamancin wanda ya faru a baya. Duk abinda jama’a za su ce sun daɗe basu ce ba, farkon fitan zancen cikin sunyi maganar da ya fi wannan, kuma ya wuce kamar ba’a yi ba. To a yanzu ma za suyi su gama ne.”
Abinda Ummanmu ta faɗa ma Ummee kenan lokacin da ta shiga gidan da damuwarta kan irin maganganun da ake faɗa a gaban idanunta da bayan idanunta.

Ummanmu kam ko a jikinta. Daman babban damuwarta rashin aure tsakanin Ziyada da Khamis ne, to a yanzu tunda an ɗaura musu aure ba ta da sauran damuwa. Tasu ƙaddarar kenan fara haihuwa a waje kafin zamowarsu ma’aurata. Hannu bibiyu tasa ta rungumi ƴarta da jikarta. Kula sosai take ba Ziyada da ƴar jaririyarta wacce aka raɗa ma suna Hauwa’u, su Rukayya suna yi mata inkiya da Nauwara.

******

“Aboki? Wai da gaske kake yi?”
Alhaji Abubakar yayi tambayar da mamaki sosai a fuskarsa.

Daga can ɓangaren Alh Idris dariya yayi, ya juya ya kalli Khamis da yake zaune a bayan mota yana ta kalle-kalle ta jikin tagar motar. A fuskarsa kawai za’a fahimci matsanancin doki da farin cikin da zuciyarsa take ciki.

“Da gaske nake Aboki. Haba don Allah, kai ko tausayin yaron nawa ba ka ji? Shekararsa ɗaya da wata biyu rabon da ya saka ku a idanuwansa. Kawai gani nayi tunda kwalliya tana biyan kuɗin sabulu sai nayi amfani da wannan damar na saka shi cikin masu rubuta jarabawa wannan shekarar. Na ƙi sanar da kai ne don na san sai ka kawo min wasu ƙabli da ba’adi, satin da ya wuce suka gama rubuta jarabawa. A hankali na cigaba da shiri ba tare da shi kanshi ya sani ba sai shekaran jiya da daddare. Yanzu haka dai ga mu mun iso jaji, a shirya mana kyakkyawan tarban da zai tabbatar min lallai anyi kewar yaro na.”

Ƙit ya katse wayar, ba tare da ya saurari abinda Abba zai ce ba.

Bai san yayi kewar Khamis ba sai da ya ji sun kusa shigowa kaduna. Da rawar jiki sosai ya fara ƙwalla ma Ummee kira yana faɗin autarta na hanya, me za ta tanadar musu a gaggauce don sun kusa isowa.

Da murna sosai a fuskarta take ƙara tambayarsa da gaske yake ko dai yana zolayarta ne don ta ajiye masa sabuwar amaryarsa a gefensa.

Ƙaƙƙarfan dariya ya fashe da ita. Ya juya ya kalli Nauwara da take barci a cikin ɗan gadonta nan gefensa. Kasancewar yarinyar tana samun wadataccen ruwan nono kuma lafiyayye sai ta ƙara zama ƙatuwa, watanta uku da ƴan kwanaki a duniya, amma wanda bai sani ba sai yai tsammanin tayi wata biyar.

Ajiyar zuciya ya sauke, zuciyarsa cike da ƙaunar jikar tasa. Ya mayar da hankalinsa kan Ummee da murmushi sosai a fuskarsa ya ce,

“Na taɓa miki irin wannan wasan? Da gaske nake yi. Ni ma sai yanzu Babanshi Idris ya kira ni a waya ya faɗa min. Sun kusa isowa fa, yanzu haka suna Jaji.”

Kamar ƙaramar yarinya haka ta daka ɗan ƙaramin tsalle saboda murna.

“Amma na ji daɗi wallahi, Idris bai taɓa faranta min rai irin na wannan lokacin ba. Allah ya kawo su lafiya.”

Ta faɗa fuskarta bayyane da matsanancin farin ciki. Jiki na rawa ta wuce kicin zuciyarta cike da tunanin me ya kamata ta ƙara tanadar musu bayan sinasir ɗin da tayi?

Tana da tafasasshen naman rago a frig. Don haka shi ta ɗakko cikin sauri ta haɗa mishi kayan ƙamshi da kayan yaji da na ɗanɗano ta ɗora akan wuta. Ba ta rabo da zoɓo da jinger a cikin ƙaramin frig ɗinta na kicin, ko da ta duba sai taga wanda ya rage zai ishe su a wadace. Hamdala tayi ta faɗa banɗaki don yin wankan tarban Auta.
‘Ko ya Auta zai ji idan ya dawo ya tarar da labarin Ziyada matarsa ce ga kuma kyakkyawar ƴar da ta haifa masa?’

Dayin wannan tunanin ita kaɗai ta saki lallausan murmushi tana hango fuskar Khamis a cikin idanuwanta.

Awa ɗaya bayan nan su Khamis suka isa gidan. Kamar ƙaramin yaro haka ya rungume iyayen yana sharɓen hawaye, su kuwa me za suyi ba dariya ba. Sai tsokanarsa suke yi shi dai yayi musu shiru yana sauke ajiyar zuciya, kansa yana cinyar Ummee ƙafafunsa na jikin Abbansa.

“Kai dan Allah ɗaga ni mu gaisa da Aboki na. Kai baka san ka girma bane? Kalli can kaga”
Ya nuna masa ɗan gadon da Nauwara ke kwance tana barci.

“Ajiyar da ka tafi ka bari kenan, biyu ne ma Allah ya karɓi ran Hassan tun sa’adda aka haife shi. Da wannan dalilin ka ga hawa jiki sai dai ka bar ma ƴaƴanka.”

“Ma sha Allah, Alhamdulillah! Allah ya raya yayi mata albarka.”

Alh Idris ya fada cikin farin ciki, idanunsa na kan yarinyar da lokaci daya ya ji ta kwanta mishi arai.

Shi kuwa Khamis tsananin firgita da ganin abinda ko a waya ba’a sanar mishi da samuwarta ba yasa shi yin wani wawan juyi sai ga shi a kasa tim. Bai damu da kwaluwar da kansa yayi akan tiles ba ya mike ya rarrafa da sauri zuwa inda ‘yar take kwance.

Rawa sosai hannayensa ke yi sa’adda ya dauko ta daga cikin gadon. Ya kura mata idanu na wasu yan dakiku yana kallon photo copynsa sak!

“Yanzu wannan ‘yata ce?”
Yai tambayar muryarsa na rawa, idanunsa akan Mahaifiyarsa.

“Yarka ce mana Auta. kalleta dakyau ka gani, da wa take tsananin kama a gidannan?”
Ta amsa tana mishi dariya.

Idanunsa ya sake mayarwa kan ‘yar yayi shiru. Can bayan dak’iku sai suka ji shesshekan kukansa.

“Ikon Allah! Dan naka dai ya zama ragon maza Aboki. Minti daya biyu sai kuka? Anya ya cancanci zama uba har da matar da ta shafe watanni tana jiran dawowarsa?”

A firgice ya d’ago kai yana kallon mahaifinsa. Bai manta da ita ba, sai dai ganin tafiyar Lokaci ba tare da sanin yaushe za’a bashi damar dawowa gare ta ba yasa shi neman can wani lungu cikin sakon zuciyarsa ya adanata da matsananciyar soyayyarta.

“Ziyaadaaa”

Ya furta sunan a hankali sosai da wani irin salo mai bayyana shauki a fili.

<< Lokaci 11Lokaci 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.