Baza ta ce ga irin tafiyar da mai adaidaita yayi sauri ko akasin haka ba saboda nisan da tayi a tunani. Ta dawo cikin hayyacinta ne saboda kalmomin da suka fito daga bakin Khamis zuwa ga matashin mai adaidaita sahun.
"Abokina don Allah ka zagaya ka shiga da mu cikin gareji. Motar Kano za mu hau."
Kalmomin da suka sauka a kunnuwanta kamar saukar mari don dawo da ita cikin hayyacinta. A zabure ta ɗago idanu ta kalle shi, sai taga sam hankalinshi ba ya kanta. Hannun damanta ta fitar daga cikin hijabinta ta damƙi nashi na hagu, ta. . .