Skip to content
Part 15 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Baza ta ce ga irin tafiyar da mai adaidaita yayi sauri ko akasin haka ba saboda nisan da tayi a tunani. Ta dawo cikin hayyacinta ne saboda kalmomin da suka fito daga bakin Khamis zuwa ga matashin mai adaidaita sahun.

“Abokina don Allah ka zagaya ka shiga da mu cikin gareji. Motar Kano za mu hau.”

Kalmomin da suka sauka a kunnuwanta kamar saukar mari don dawo da ita cikin hayyacinta. A zabure ta ɗago idanu ta kalle shi, sai taga sam hankalinshi ba ya kanta. Hannun damanta ta fitar daga cikin hijabinta ta damƙi nashi na hagu, ta matsa da ɗan ƙarfi don dawo da hankalinshi zuwa gare ta.

“Menene? Kina jin yunwa ko?”
Ya aika mata tambayoyi biyun kamar bai ga firgicin da ke kwance a fuskarta ba.

“Kano? Da yamman nan? Ka ga fa sallar magrib ake kira a masallaci? Me yake faruwa? Don Allah…”

“Ziyada, a matsayina na mijinki ina umartarki kiyi min shiru akan duk abinda kika ga na aikata ko zan aikata nan gaba. Har zuwa sa’adda zan samu nutsuwar yi miki bayanin duk abinda yake faruwa.”

A dole taja baki ta tsuke. Tana kallo ya sallami mai adaidaita sahu da yake ta bin su da wani irin kallo tun bayan da ya ji abinda Khamis ya ce, yaja hannunta har zuwa cikin motar da suka tarar saura fasinjoji uku ta cika. Suna zama kuwa aka samu cikon fasinja ɗaya, kwandasta na harhaɗa kuɗin mota sai ga wani mai tallen balangu da gurasa ya ƙaraso kusa da motar yana tallatawa fasinjoji.

“Kina jin yunwa?”
Ya tambayeta da kulawa.

Fuskewa tayi ta ƙara duƙar da kai kamar ba da ita yake magana ba. Shi ma bai ƙara saurarenta ba ya sayi balangu da gurasar mai ɗan dama, ana niyyar tayar da mota sai ga mai sayar da ruwan leda, har ya sayi guda biyu, sai ya ƙara biyu suka zama huɗu saboda yawan shan ruwan da Ziyada take yi tun da cikin jikinta ya tsufa.

Tafiya mai nisa irin wannan a halin da take ciki abu ne da ko a mafarki bata taɓa tsammani ba. Tun ba’a yi rabin tafiya ba ƙafafunta suka yi tsami, ba kasafai take jure zama mai tsawo a guri ɗaya ba. Duƙar da kanta tayi, zuciyarta babu abinda take yi sai suya da tafarfasa, ga matsananciyar yunwar da take saɗakarta. A ƙarshe dole ba don ranta na so ba ta fusgi ledar hannun Khamis ta buɗe ta fara cusa gurasa hannu baka hannu ƙwarya.

Aka ce tafiya mabuɗin ilimi, ita kam a wannan tafiyar babu abinda ta ƙaru da shi sai matsanancin wahala. Bayan shafe awoyi uku cif suna tafiya kafin suka shiga garin kano, haka suka sake shafe mintuna talatin cif a cikin adaidaita sahu kafin suka isa ƙofar gidan Alhaji Bashir.

Wani babban sa’a da suka taka shi ne suna isa suka tarar da Alhajin dawowarsa kenan daga wajen dubiyar mare lafiya, ana buɗe mishi get zai shiga da mota suka isa ƙofar gidan, don haka ba tare da ɓata lokaci ba yaja hannun Ziyada da take ɗaga ƙafa daƙyar tana matsar ƙwallah zuwa cikin harabar gidan.

Haske ne tar a tsakar gidan, mai gadi da bai gane ko su waye ba yana niyyar balbale su da masifa Alhaji Bashir ya dakatar da shi. Da mamaki sosai a fuskarsa yake kallon Khamis, yana kuma kallon Ziyada da a fili yake ganin tsananin galabaita da jigatar da tayi.

“Khamis ka yi hauka ne? Ka ɗauko mace da tsohon ciki kuyi irin wannan doguwar tafiyar kuma a cikin dare? Me yake faruwa da ya zama dolen dole sai ka taho da ita baza ka iya zuwa kai kaɗai ba?”
Kalaman da ya fara faɗe kenan cikin faɗa-faɗa. Sai kuma ya bashi umarnin yayi saurin shiga da Ziyada cikin gida gurin Hajiya, shi kuma idan ya ci abinci ya same shi a falon shi.

Hajiya Rahina mace mai faran-faran da iya tarbar jama’a, haka ta tarairayi Ziyada kamar ƴarta ta cikinta. Da kanta ta shiga cikin bayi ta haɗa mata ruwan wanka, ta taimaka mata zuwa bayi, ko kafin ta fito har an ajiye mata yalwataccen doguwar riga wanda za ta ji daɗin sakawa sosai a irin yanayin da take ciki. A zaune ta rama sallolin da suke kanta saboda kumburin da ƙafafunta suka yi, kafin ta idar har an jera mata abinci mai rai da lafiya a gefenta.

Ɗakin da Khamis ya zauna sa’adda yake makaranta nan aka umarceshi ya shiga bayan mai aiki ta gyara ɗakin. Shi ma wankan ya fara yi, kasancewar shi tafiyarsa da shirinsa jakar da take goye a bayansa shaƙe take taf da suturunsa. Ƙananun kaya ya saka ya fice zuwa gurin Hajiya Rahina, akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu, zamanin da yai zaman karatunsa duk miskilancin da yai ta gwadawa a farkon zuwansa haka tai ta haƙuri da shi tana bin shi da yadda yake so har zuwa sa’adda ya saki zuciyarsa ya rungumeta a matsayin uwa. Sosai shaƙuwa ke tsakaninsu, ko kaɗan ba ya ɓoye mata duk wani abu da ke cikin zuciyarsa.

“Hajiya.”
Ya faɗa a kasalance yana zama a kusa da ita.

“Na’am, Ɗan Hajiya barka da fitowa. Ya gajiyar tafiya? Ita dai Ziyada saboda gajiya har ta yi barci, Baiwar Allah…”

“Daman barcin wuri take yi, ko babu tafiya.”
Ya katse ta da sauri don gudun sake ɗora mishi laifin yin doguwar tafiya da ita ga tsohon ciki a jikinta.

“To madallah! Ga abincinka can kan tebur”

Har ya tashi zai wuce sai ta sake cewa
“Ni kam ya jikin Hajiya Hauwa’u? kwana biyu ba na samunta a waya. Bani lambarta in gwada kira yanzu in ji ko zan same ta.”

Tsam yayi a guri ɗaya, wayarsa yake tunawa da ya baro ta can cikin ɗakinsa. Tunda ya kashe ta buɗe wata ƴar ƙaramar loka yayi ya jefata a ciki, duk yadda wayar take da matuƙar amfani a gurinsa yasan ita ce hanya ta farko kuma mafi sauƙi da za’ayi amfani da ita wajen gano inda yake.

A hankali ya juyo ya fuskanceta, murmushin yaƙe ya maƙala a fuskarshi yana sosa ƙeya.
“Hajiya, wannan tafiyar ba ta shiri bace..”

“Na yi tunanin haka Khamis. Me ya faru?”
Ta katse shi da tambayar, fuskarta cike taf da yanayin alhini.

“Yi haƙuri Hajiyata in ci abinci. Alhaji na can yana jira na da nashi tulin tambayoyin, can falonshi za mu tafi in warware muku zare da abawa.”

*****

“Ummee? Sannu Ummee, ya jikin naki?”
Ya tambayeta a tausashe, idanunsa cike taf da hawayen damuwa da tausayin matsanancin halin da take ciki tun bayan faruwar al’amarin.

Sau uku tana ƙoƙarta buɗe idanu tana rufewa, daga bisani daƙyar ta samu nasarar buɗewa ta zuba ƙwayoyin idanun akan shi.
“Khaaaa..mis..”
Ta ambata cikin rawan murya.
“An samu labarin inda yake?”
Ta sake ambata daƙyar tana matse matsen fuska, yanayin da ke nuna ita kaɗai ta san halin da take ciki.

Sau biyu yaja hanci kafin ya laluba a hankali ya riƙo hannayenta cikin nashi. Muryarsa a tausashe ya fara magana
“Eh, an samu Ummee. Ɗazu Baba Bashir ya kira ni yana jajanta min abinda yake faruwa. Kuma ya tabbatar min Khamis ɗin gurinshi ya tafi, shekaran jiya misalin ƙarfe goma na dare suka isa gidanshi shi da Ziyada. Ya faɗa min gobe in sha Allahu yana nan zuwa, zai zo da wuri ya samu iyayen ita wancan yarinyar ya basu haƙuri kan abinda ya faru, zai kuma alƙawarta musu in Allah ya yarda Khamis ya rabu da ɗiyarsu har abada.”

“Alhamdulillah!”
Ummee ta faɗa a hankali haɗe da lumshe idanunta, nutsuwa take ji yana kwaranya a cikin jikinta. Daman rashin samun labarin inda Khamis da matarsa suke shi ya taka muhimmiyar rawa gurin ƙara hauhawar halin da take ciki na matsanancin hawan jini da ciwon suger, ciwuka biyun da ko alamu basu taɓa bayyana kansu a jikinta ba sai bayan rasuwar Abba.

Yau kwananta biyu a asibiti, duk ƙoƙarin likitoci a kanta jininta ya ƙi sauka. Hankalin Yaya Yusuf a ɗugunzume yake sosai da halin da take ciki, shi kanshi da za’a bashi gado a asibitin kwanciya zaiyi, amma ya ƙi yaddar ma kanshi ma baida lafiya balle har ya nemi magani. Kusan raba dare yake yana addu’ar Allah ya baiyana Khamis da Ziyada, domin duk iya binciken da yayi a ɗakin Khamis bai ga wata shaida da zai alamta mishi ga inda Khamis ya tafi ba. Kuma saboda yawan suturun da yake da ko kusa bai fahimci an ɗebi kaya daga cikin kayan sakawarshi ba. Ganin wayarshi a cikin durowa shi ne abinda yasa shi yake ta tsananta addu’a kan Allah yasa su Ibbu basu samu nasarar kama Khamis ba.

Kallon Ummee ya sake yi, sai yaga tana sauke numfashi cikin nutsuwa, barci ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke, zuciyarsa cike da fatan Allah yasa idan ta tashi farkawa a samu gwaggwaɓar cigaba a yanayin lafiyarta.

*****

“Wa nake gani haka kamar Kham? Duwan duba wancan matashin dakyau ka gani, ba Kham bane?”

A hankali ya ɗaga idanunshi daga kan wayar hannunsa zuwa inda yatsar abokinsa yake nunawa. Ware idanu yayi sosai yana kallon matashin da ke riƙe da babban jarka a hannunshi yana jiran a sallami mai adaidaita sahu a zuba mishi mai a cikin jarkar.

“Ƙwarai kuwa, Kham ne, ko shekaru nawa aka ɗauka kamanninsa bazai taɓa ɓace min ba. Amma shi ba ɗan kaduna bane? Hadi me ya kawo Kham Kano a daidai wannan lokacin?”

Wanda aka kira Hadi kafaɗa ya ɗaga alamun bai sani ba. Sai kuma ya ce
“Kila kuma ya zo gurin Mugun Principal ɗinnan ne, kasan an ce Aminin Dagus ɗinshi ne na ƙud da ƙud. Kawai dai domin share duk wata tantama muje muji daga bakinsa.”

Gyaɗa kai Duwan yayi, a ƙasaice suka buɗe ƙofofin ƙatuwar motar da tun tsayuwarta a gidan man ɗai-ɗai waɗanda basu ɗaga idanu sun kalleta ba. Da ganin motar sabuwa ce dal, sannan irin motar nan ce da a ido kawai za’a gane tana da tsadar da mallakarta sai wane ko ɗan wane.

*****

Duwan wanda asalin sunashi Ridwan da Hadi wanda asalin sunanshi Abdul-Hadi aminai ne na ƙud da ƙud, sun taso tun suna ƙanana a unguwa ɗaya ne anan cikin garin kano. Irin taƙadiran yarannan ne da tun a makarantar primary sukayi fice ba don komai ba sai don bala’in tsokana da rashin ji, haka a unguwarsu babu wanda bai sansu ba, sun gallabi iyayensu sun gallabi mazauna unguwa.

A haka har suka tafi Sakandire bata canza zani ba. Kuma wani ikon Allah shi ne ga shi dai a zaman aji ba su da ƙoƙari, amma duk sa’adda jarabawa tazo suna iyakar ƙoƙarinsu wurin ciwo making ɗin da zai sa su shallake zuwa ajin gaba.

Khamis yaro ne mai farin jini duk inda ya shiga, tun ganin Khamis da suka yi kwatsam a aji ɗaya na babbar sakandire ƙaunarsa ta shiga cikin zuciyarsu. Wani abu da yake baƙo a cikin halayen abokan biyu shi ne janyo wasu yaran cikinsu, duk rashin ji da fice a taƙadirancin da yaro zaiyi sai dai a gaisa hy-hy, sun kasa shaƙuwa da sauran yara sa’anninsu balle har su haɗa gungun taƙadirai.

Amma wani ikon Allah shi ne duk su biyun da gaske suka so janyo Khamis cikinsu su zama su uku. Sai dai duk yadda suka so janyo shi sam Alh Bashir ya hana damar haka, sosai yasa ake kula mishi da lamarin Khamis a cikin aji da harabar makarantar, balle kuma a gida da unguwa, tsaron ya fi ƙamari.

A haka dai har suka gama karatun tsakaninsu babu wata shaƙuwa ta azo a gani, sai dai gaisuwa itama ba irin can-can ɗinnan ba.

Inji Mal Bahaushe dare ɗaya Allah kanyi bature. To irin haka ce ta kasance ga Hadi da Duwan, da kammala karatunsu babu daɗewa lokaci ɗaya aka ga sun fara fantamawa cikin manyan kuɗaɗe ba tare da sanin takamaimai sana’arsu ba.
“Kakarmu ce ta yanke saƙa, Allah yayi mana gyaɗan dogo ta hanyar samun babban aiki a Abuja.”
Wannan ita ce amsar da suke ba duk wanda ya tuhumesu da zancen ina suke samun kuɗi.

Kasancewar an daɗe muna cikin wani irin yanayi da ba kasafai iyaye suka cika saka idanu a al’amuran ƴaƴansu ba, ba ma kamar ƴaƴan da suka kasance kamar na Allah bani, fitinannu irinsu Ridwan da Hadi da tuntuni aka rasa yadda za’ayi da su, da wannan6 dalilin yasa tuni aka shashantar da zancen, aka rungume su cikin ƙauna da tarairaya, har wata girmamawa ta musamman ake musu a cikin unguwa.

Tun da suka fara samun kuɗi sai suka zama wasu ababen so a gurin iyayensu da cikin unguwa, saboda yadda suke taimakawa mahaifansu da ƴan’unguwa. Duk wani abu da zai taso na buƙatar unguwa suna gaba-gaba wajen taimakawa da ƙarfin aljihunsu, har ma fiye da asalin masu kuɗin da suke cikin unguwar. Tuni suka sa aka rushe gidajen iyayensu aka ƙera sabon gini na zamani bulo da bulo. Ƙaramin masallacin unguwar da Khamsu salawati kawai ake yi tuni suka siye gidaje da filayen da suke maƙwaftaka da shi aka ƙera babban masallaci na gani a faɗa.

“Uhmmm! Ku dubi ikon Allah Almusawwiru, maiyin yadda yaso a lokacin da yaso. Yarannan da muke musu kallon fitinannu ba tare da saninmu ba ashe su ne maɗaukaka a cikinmu masu taimaka mana. Allah ya musu albarka ya ƙara shirya mana su.”
Ire-iren maganganun da ke fita daga bakunan da yawa daga cikin mazauna unguwarsu kenan.

****

“Khamis? Kai nake gani ko idona ke min gizo?”
Duwan ya faɗa da fara’a sosai a fuskarsa lokacin da suka ƙarasa kusa da Khamis ɗin.

Da fari kallon rashin sani ya bisu da shi, sai da Hadi ya ƙara mishi bayanin ko su ɗin su waye sannan ya saki fuskarshi kaɗan suka gaisa. Ko dama can su suke bin shi, shi bawai ya damu da al’amarinsu bane.

“Me kake yi yanzu ne Kham? ko ka samu aiki anan kano ne?”
Duwan ya tambaye shi.

“Aiki? A’a, ina aiki dai a Kaduna hukumar alhazai. Na zo ziyara ne kwanaki huɗu da suka wuce. Ku fa?”
Ya tambayesu a lokaci ɗaya kuma yana faɗan yawan man da za’a zuba mishi.

Gefe suka tsaya har aka gama zuba mishi mai, Hadi ya taso zai biya kuɗin da sauri ya dakatar da shi.
“Bari in biya, nima saƙo aka bani, kuma an bani wadatattun kuɗaɗen da duk tsadar man zan biya in mayar da canji.”

Har zaiyi magana Duwan ya dakatar da shi ta hanyar riƙe mishi hannu, ya biya kuɗin. Sallama yayi musu zai wuce sai suka roƙi alfarmar ya bari su rage mishi hanya, bai ja da nisa ba, ganin ranar da ake kwantsamawa zai so isa gida akan lokaci.

Tunda suka ambaci za su rage mishi hanya ya san da mota suke tafe, amma bai taɓa tsammanin mota mai numfashi irin wannan suke tafe a cikinta ba. Duk da kaɗawar da hantar cikinsa tayi ko kaɗan bai nuna a fuskarsa ba.

Bayan saka jarkar man a booth ɗin mota har zai shiga kujerar baya Duwan ya dakatar da shi.
“Khamis shigo gaba, akwai maganar da nake so mu tattauna kafin mu sauke ka a gida.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 14Lokaci 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.