Ya ƙura ma guri ɗaya idanu yayi shiru. Kalaman da Ummanmu ta umarceshi da maimaitawa sun taimaka masa ƙwarai gurin rage ƙunci da baƙin cikin da ke danƙare a zuciyarsa. Ummee dai ta riga ta tafi, wanda ya fi shi son ta ya karɓi abarsa, sai addu'ar Allah ya gafarta mata yakai haske cikin kabarinta. Ya zama dole a gare shi ya rungumi wannan ƙatotuwar ƙaddara da ta afko masa, sai kuma tunanin yadda zai iya fuskantar rayuwar duniya ba uwa ba uba, ga yadda zumunta ya zama a wannan zamani da muke ciki.
"Yusuf? Na. . .
Masha Allah