"Ahhhhhh! Wayyoh Allah naa!" Kamar a mafarki Ziyada ta jiyo ihun Khamis a cikin ɗaki.
Tsam tayi guri ɗaya tana saurare, izuwa wannan lokacin hawayen idanunta sun ƙafe ƙaf, sai sauke ajiyar zuciya da take yi lokaci bayan lokaci. Kuka a cikin labarin rayuwarta ba sabon abu bane, baƙin ciki ne da ako wane lokaci ake yi ana sake maimaitawa. In bacin ma ɗan adam da ba ya sabo da mugun abu, ai da tuni ta daɗe da haddace salo-salo samfur-samfur na baƙin cikin da Khamis yake cusa mata ko wane lokaci babu ƙaƙƙautawa. . .
Amma khamis de anyi Dan kwal ..