Skip to content
Part 20 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Ɗif! Ya ɗauke wuta kamar mutum-mutumi saboda rashin amsar bayarwa. Har sai da daga can ɓangaren Alhaji Lukhman ya sake cewa
“Hello? Alhaji Yusuf kana ji na?”

Daƙyar ya iya buɗe bakinsa ya amsa da
“Ina jin ka Alhaji.”
Shirun ne ya sake ratsa tsakaninsu na daƙiƙu biyar.

Daga can ɓangaren Alh Lukhman ya buɗe baki zaiyi magana Yaya Yusuf ya riga shi da cewa
“Kayi haƙuri da duk abinda za ka ji ya fito daga bakina Alhaji. Ban saba ƙarya ba, don haka bazan yi ta don in kwantar maka da hankali ba. A yanzu haka da ka kira wayar nan ina tare da Khamis ne, kuma wayar a amsa kuwwa take duk maganar da kake yi yana jin ka.

Kwanaki biyun da suka gabata ban ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki bane saboda Khamis ɗin bashi da lafiya. Amma yanzu haka maganar zuwa gurin malamin da yayi asirin muke yi. Kayi haƙuri, Allah ya huci zuciyarka. Ka bani daga yanzu ƙarfe tara na safiyar nan zuwa Azahar, duk yadda ake ciki za ka ji ni da ƙwaƙƙwaran magana.”

Daga can ɓangaren Alhaji Lukhman shiru yayi, kamar dai ba iya kalmomin da yaso ji ba kenan.

“Kayi haƙuri Alhaji.”
Yaya Yusuf ya sake faɗa a tausashe.

“Shi kenan! Babu damuwa. Allah ya kaimu yammacin lafiya.”
Ƙit ya katse wayar ba tare da ya jira ko Alh Yusuf zai sake magana ba.

A tare Yaya Yusuf da Khamis suka sauke wani nannauyan ajiyar zuciya. Wani mugun kallo da Yaya Yusuf ya aika mishi haɗe da miƙo hannu a zabure kamar zai kai mishi naushi yasa shi matsawa baya da sauri, ƙasa-ƙasa ya fara gunguni amma Yayan yana jin abinda yake cewa.

“Haba Yaya, me kake ƙoƙarin yi? kan wannan abun da bai kai ya kawo ba karo na biyu kenan fa kana ƙoƙarin ɗora hannu a kaina kamar ba magidanci ba? Kayi haƙ…”

“Magidanci?”
Yaya Yusuf ya katse shi da tambayar cikin matsanancin ɓacin rai.
Ya jinjina kai. Bai jira amsawar Khamis ɗin ba ya sake jefa mishi tambayar
“Ka san me kalmar magidanci take nufi Khamis?”
Nan ma shiru ne ya biyo baya.

Da fushi sosai a fuska da muryarsa ya cigaba da cewa
“Allah ya kyauta wannan magidancin da nauyin da ya hau kansa na iyali bai hana shi aikata miyagun ayyuka na assha ba. Wlh tallahi gara zaman gwaurantaka da zama Magidanci irinka Khamis. Kai yanzu ko kunyar kiran kanka magidanci baka ji ba.? Mutumin da…”

“Ya isa haka Yaya ! Ya isa!! Allah ya huci zuciyarka. Tashi mu tafi gurin Malamin.”
Khamis ya katse baƙaƙen maganganun da Yayan yake ta caɓa mishi a fusace ya miƙe tsaye.

Da alamun maganganun ba ƙaramin ƙona masa rai suka yi ba, don bai jira miƙewar Yayan ba ya nufi hanyar ficewa daga falon da sassarfa.

“Ah-Ah! Mai gidan ficewa kake niyyar yi ba ko sallama? To Allah ya kama ka, ina alƙawarin da kayi min?”
Ta ƙarasa maganar tana dariya haɗe da tare masa hanyar wucewa.

“Aunty Zainab pls bani guri in wuce. Bana cikin yanayin.”

Sau ɗaya ta kalli fuskarsa da saurin gaske ta raɓe gefe guda ta bashi hanyar wucewa, a tare suka raka shi da idanu ita da maigidanta.

“Malam a lalata aikin gaba ɗaya kawai tunda baza su bari abi a hankali ba. Ko ma me zai biyo baya ba abinda ya dame ni bane.”

Kalmomin da suka sauka karaf a kunnen Yaya Yusuf kenan, a daidai lokacin da ya fito daga cikin gidan. Tsayawa yayi guri ɗaya ya ƙure Khamis da kallo, wani irin tsoronsa na ƙara cika zuciyarsa. Me yake nufi da cewar ko ma me zai biyo baya ba damuwarsa bane? Kar dai ace wani mugun abun yake niyyar sake aikatawa ga ƴar mutane?

Ƙara harhaɗe fuskarsa yayi tamau ya taka zuwa kusa sosai da Khamis ɗin. Duk abinda Yayan yake yi yana ankare da shi, amma sai ya nuna kamar bai gani ba, ya cigaba da wayarsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

“Nan da awa biyu ko? To shi kenan, na gode Mal…”
Bai ƙarasa godiyar ba a sanadiyyar zare wayar da Yaya Yusuf yayi daga kunnensa.

Kallon kallo sukai ma junansu na daƙiƙu uku, Yaya Yusuf ne ya fara saukar da idanunsa ƙasa ya mayar kan wayar Khamis da take riƙe a hannunsa. Hannu yasa ya latsa gefen wayar, sai yaga ashe an katse kiran daga can ɓangaren, kuma wayar ta shiga key.
“Menene mabuɗan sirrin buɗe wayar?”

Khamis da tambayar da dira kunnuwanshi a bazata baisan sa’adda ya gwalalo idanunsa waje ba, ya kasa cewa komai, har sai da Ya Yusuf ya maimaita tambayar da yayi masa.

“Yyyyyyaaaayaaaaa mmmmme ya haɗaka da key ɗin wayata kuma? Ca nake dai matsalar kan asirin da aka yiwa yarinyar can ne? To duk ku kwantar da hankalinku, nan da awa biyu za’a karya duk wani asiri da yake jikinta…”

“Me kuke shiryawa bayan haka?”

Hannaye biyu ya ɗaga alamar sallamawa kafin ya amsa da
“Me kuwa za mu shirya Yaya? Ba komai, babu komai Wallahi. Ni fa daman na daɗe ina neman maraba tsakanina da mayyar yarinyar nan, sara ne yazo daidai kan gaɓa…”

Ƙarar kiran wayarsa ya katse maganganun da yake yi. Da saurin gaske ya matso haɗe da miƙa hannu a bazata da niyyar karɓe wayar daga hannun Ya Yusuf.

Yana ankare da shi, don haka ya janye hannunsa da sauri, ya aika masa da wani mugun kallo.
“Me kake niyyar yi?”

Marairaicewa yayi kafin ya amsa da
“Yaya, kira na ake yi fa…”

“Na gani ai.”
Ya amsa cikin rashin damuwa. Sai kuma ya mayar da idanunsa kan wayar yana kallon sunan mai kiran wayar.
“Uwar ruwa.”
Ya karanto a fili. Ya sake mayar da idanunsa kan Khamis ya ce
“Wacece haka?”
“Wani irin suna ne haka?”
Ya jefa mishi tambayoyi biyun a jere ba tare da jinkirtawa ba.

“Yaya! An ce dai Wala tajassasu. Sanin wacece ko wane irin suna ne duk babu abinda zai amfana maka Yaya, don Allah ka bani wayata mu wuce zuwa inda muka nufa. Idan kuma za mu koma ciki mu jira nan da awa biyu ne sai mu koma, ni daman barci bai ishe ni ba.”
Ya ƙarasa maganar da dariyar da ke bayyana rainin wayau ƙarara.

“Uhmmm! Allah ya shiryeka Khamis”
Yaya Yusuf ya faɗa cikin rauni da sallamawa ƙanin nasa.

“Ameen Yaya! Kayi haƙuri, wata rana zan daina duk abubuwan nan da baka so.”

“Sai Yaushe?”
Ya tambaye shi lokacin da ya juya zuwa gurin motarsa.

“Nan gaba kaɗan, kafin mu kai gargara.”
Ya amsa da dukkan gaskiyarsa.

“Hmmm! Lokaci ba ya jira Khamis. Ina yi maka kwaɗayin ka tuba tun kafin lokaci ya ƙure maka, ka tuba tun kana tsaka da jin daɗin saɓon da kake aikatawa. Irin wannan tuban ne cikakken tuba wanda Allah da Manzonsa suke so.”

“Hmmm! In Allah ya yarda”
Amsar da ya bada kenan yaja bakinsa ya tsuke. Hankalinsa na kan wayarsa da har lokacin take hannun Yayansa.

Shi ma Yaya Yusuf daga haka bai sake cewa komai ba. Suna ƙarasawa gurin motarsa mazaunin direba ya shiga Khamis ya zauna a ɗaya ɓangaren, a maimakon ya miƙa mishi wayar, sai ya buɗe aljihun gaban mota ya jefa wayar a ciki ya kulle.

Baki da hanci buɗe Khamis ya bishi da kallo, kallo ɗaya za’a yi masa a fahimci tashin hankali ƙarara a fuskarsa. Yaya Yusuf yayi kamar bai gani ba, bismillah yai ya tayar da motar, bayan wasu daƙiƙu yaja motar cikin nutsuwa suka fice daga gidan.

Kai tsaye gurin aikinshi ya wuce, shi dai Khamis yana zaune kamar mutum-mutumi, tashin hankalin wayarsa da aka karɓe ya fiye mishi komai. Ko da Yaya ya ce su shiga Ofis ɗinshi daƙyar ya iya jan ƙafafunshi ya fito daga motar, kamar wanda ya kwana yana amai da gudawa. Gwuiyawunshi sanyi ƙalau.

Fiye da awa biyu da rabi Ya Yusuf ya ɓata yana cike ciken takardu da aiki a na’ura mai ƙwaƙwalwa kafin ya tattara komai ya aje a mazauninsa.

“Baza ka ci ko kasha komai ba?”
Ya tambayi Khamis.

“Ba na buƙata.”
Ya amsa a cije kafin ya miƙe daga kan kujerar da yake zaune ya fita waje. Zuciyarsa sai ƙuna take yi, kamar ya ɗora hannu biyu akai ya fashe da ihun kuka.
‘Uwar ruwa ba ta kiranshi a banza. Tunda ta kira, ya tabbatar wata harƙalla ce ta taso mai tafe da guguwar alkhairai. Amma Yayansa yana neman toshe masa hanyar samu.’

Daga nan kai tsaye gidansu Firdausi suka wuce. Kasancewar Ya Yusuf bai san gidan ba, sai Khamis ɗin ne ya buɗe baki daƙyar yayi mishi kwatancen gidan, har Allah yasa suka ƙarasa.

Ba yabo ba fallasa, shi ne irin tarban da suka samu daga iyaye da yayyin Firdausi. Bayan musayar gaisuwa sama-sama a tsakaninsu da Ya Yusuf zuru suka yi mishi suna jira suji inda aka kwana. Domin darajarsa ce ta hana Yayyin Firdausi rufe Khamis da duka saboda bala’in haushi da tsanarsa da suke ji cike da zukatansu, abinda suka ƙudurta a tsakaninsu shi ne matuƙar basu ji gamsasshiyar magana daga bakin Ya Yusuf ba tabbas Khamis bazai fita daga gidan da ƙafafunsa biyu lafiya ƙalau ba.

“Alhaji, ku kwantar da hankalinku. An karya asirin…”

“Alhamdulillahi”
Suka haɗa baki gurin faɗin haka gaba ɗayansu.

Irin farin ciki da walwalar da ya mamaye fuskokinsu lokaci ɗaya yasa Ya Yusuf jin idanunsa sun cicciko da hawaye, a fakaice ya kawar da fuskarsa ya ɗauke ƙwallah da babbar ƴar yatsarsa.

“Da gaske kake yi? Yusuf da gaske kake yi an karya asirin cikin ƙanƙanin lokaci haka?”
Alh Lukhman ya tambaya da ɗan rawa-rawa a muryarsa.

“In sha Allahu! Ƙwarai kuwa! Domin abinda ya janyo ɗan daɗewarmu kenan. Awa biyu Malamin da yayi asirin ya buƙaci a bashi domin ya lalata komai, a yanzu awa uku har da ƴan mintuna. In Allah ya yarda komai ya zama tarihi.”

“Madallah! Allah na gode maka. Ka ga yanzu sai batun auren kenan ko? Tunda asirin ya karye cikin ƙanƙanin lokaci haka ai ina ganin ko yanzu idan muka idar da sallar azahar sai a ɗaura aurensu…”

“Aure kuma?”
Khamis yayi saurin katse Alhaji Lukhman da wannan tambayar. Ganin yadda fusatattun idanuwan Yayyin Firdausi ya dawo kanshi ya sa shi saurin gyara zancenshi da cewa
“Ina nufin Ɗaura auren a wannan ɗan tsukun lokacin ai anyi gaggawa. Kar ku manta da hukuncin addininmu akan irin wannan al’amarin, kafin ƙulluwar aure a tsakaninmu dole sai ta yi Istibra’i, don tsarkake auren da samun tsaftatacciyar zuri’a a tsakani.”

Wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Gaba ɗayansu sai suka yi laƙwas, har Ya Yusuf. Sun san gaskiya Khamis ya faɗa, gaba ɗaya sun sha’afa da batun istibra’i. Babban burinsu a ɗaura auren don tabbatuwar rufin asiri ga Firdausi har abada.

Matsanancin farin ciki ne ya lulluɓe zuciyar Khamis ganin haƙarsa na gab da cimma ruwa. Don ƙara gyara hanyarsa sai ya lanƙwashe murya ya cigaba da cewa
“Amma idan kuna ganin da kuskure a maganata sai a tambayi malamai. Idan kuma kuna ganin a ɗaura auren a hakan to shi kenan, ni dai na tunatar da ku ne abinda duk idanunku suke ƙoƙarin rufewa akai.”

Tsawon mintuna uku shiru ne ya ratsa tsakaninsu, basu isa suja da hukuncin Allah da Manzonsa ba. Amma sun rasa dalilin da yasa a zukatansu suke kokwanto, gani suke kamar neman hanyar zulle ma auren Firdausi yake yi.

Saboda rashin ƙwaƙƙwaran hujja da kuma sanin hukuncin Allah gaba yake da komai, sai suka bar kokwanton a zukatansu. Batun auren dole aka ɗage sai bayan Firdausi ta yi istibra’i.

Ɗan muskutawa Ya Yusuf yayi ya kalli Alh Lukman a tausashe ya ce
“Kayi haƙuri Alhaji. Kamar gobe ne za kaga lokacin ya zo har ya wuce. Abu ɗaya da zan ƙara tabbatar maka shi ne in dai ina raye, babu abinda zai hana ƙulluwar aure tsakanin Firdausi da Khamis, in Allah ya yarda.”

“Na gode Yusuf, babu komai. Allah yasa muna da rabon ganin lokacin.”

“Ameen thumma Ameen.”
Suka amsa gaba ɗaya, banda Khamis.

Har sun miƙe za su tafi ɗaya daga cikin Yayyin Firdausi ya damƙo gefen rigar Khamis ya janyo shi baya da ƙarfi. Taga – taga yayi kamar zai faɗi Allah ya bashi sa’ar tsayuwa kan ƙafafunsa. Har ya buɗe baki a fusace zai lailayo ƙatotuwar ashariya ya maka mishi sai yayi saurin dannar kansa bayan ya tuna neman hanyar rabuwa da su har abada yake yi.

“Idris? Menene haka kake yi?”
Alhaji Lukhman ya tambaya idanunsa na kan wanda ya ja rigar Khamis ɗin.

“Abba, ya kamata ya bamu tabbacin karyewar asirin jikin Fido, kar sai sun tafi ita kuma ta farka daga barci mu fahimci tsantsar rainin hankali suka zo mana da shi…”

“Eh to kuma haka ne. Kai Hamisu wane tabbaci za ka bamu? Don batun karya asirin a bakin ɗan’uwanka muka ji. Ta wace hanya za mu tabbatar yarinya ta samu lafiya?”

A wannan karon duk yadda yaso dannar zuciyarsa ya kasa. Bai fahimci komai a maganar Yayan Firdausi ba sai son ya tozarta shi a cikin jama’a. Shi kuma mahaifin da yake raƙumi da akala ne sai ya biye mishi har yana wani tambayarsa. Da zafin rai ya amsa da
“Ta hanyar da kuka tabbatar ba ta da lafiya.”

“Fitsara za ka zo mana da shi? Duk ɗanyan kanka daidai nake da kai Wallahi”
Idris ya faɗa cikin fushi yana nannaɗe hannayen rigarsa.

“Idris, zauna.”
Alh Lukhman ya bashi umarni.

Cikin fushi ya zauna yana sauke numfashi sauri-sauri alamar zafin zuciya.

“Ka kwantar da hankalinka. Idan ma ƙarya suka faɗa mana, za mu tabbatar sannu a hankali.”

Ya mayar da hankalinsa kan Ya Yusuf da yake tsaye kamar mutum mutumi, fuskarsa a damalmale da damuwa. Ɗan murmushi kaɗan yayi masa kafin ya ce
“Yusuf kuna iya tafiya, duk abinda ya biyo baya za muyi magana a waya. Allah yasa muga alkhairi.”

“Ameen.”
Ya amsa daƙyar kamar mai ciwon haƙori. A kasalance ya riƙo hannun Khamis da yake tsaye yana hura hanci cikin jiran ko ta kwana suka fice daga falon.

Har suka shige mota babu wanda ya cewa wani uhummm! A guje Ya Yusuf yaja motar suka fice daga layin, bai tsagaita daga gudun da yake yi ba sai da suka bar Kadaure, suka shiga unguwar rimi, gefen hanya ya gangara ya faka motar.
“Sauka!”

“Yaya…”

“Khamis ka tare Napep ya ƙarasa da kai duk inda za kaje, na rantse da Allah haushinka nake ji, ba na ko ƙaunar ganin fuskarka a yanzu. Don Allah ka bani iska ko zuciyata za ta sassauta daga zafin da take min.”

Da jin waɗannan kalaman ya kasa cewa komai, lallai ya kai Yayansa bango a wannan karon. Kalamai makamancin waɗannan bai taɓa shiga tsakaninsu ba duk da irin ababen tsiyar da yasha aikatawa a baya. Da sauri ya buɗe ƙofar motar ya fita waje
“Yaya wayata…”

Tun kafin ya aje numfashi ya ɗakko wayar ya miƙa mishi.

“Kuma ka tabbatar an warware asirinnan. Idan ba haka ba ni kaina bazan ce ga abinda zai biyo baya tsakanina da kai ba Khamis. Lokaci ne kawai zai nuna. Rufe min ƙofa”

Bai ƙara minti ɗaya a gurin ba ya figi motarsa a guje ya harba kan titi. Da gaske ba ya ko ƙaunar ganin fuskar ƙanin nasa, wani abu da bai taɓa ji kan Khamis ɗin ba shi ne, tsana ce take neman samun matsuguni a zuciyarsa. Tsaki mai ƙarfi yaja, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Kwaƙwalwarsa sai zafi take yi saboda tunanin yadda zaiyi da Khamis da munanan halayensa, irin yadda hankalinsa ke tashe a lokacin ya tabbata da za’a auna jininsa a yanzu ba abinda zai hana aga yayi mugun hauhawa.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”
Kalaman da ya fara maimaitawa kenan a fili, bayan ya sassauta gudun da yake yi da motar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 19Lokaci 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×