Kamar jira ake ya rage gudun motar wayarsa ta fara ƙara, a lalace ya mayar da idanunsa kan wayar. Alh Lukhman ne, mahaifin Firdausi. Ƙirjinsa ne ya buga daram, a tsorace ya ɗaga wayar zuciyarsa cike da tunanin Allah yasa dai lafiya?
"Lafiya ƙalau Yusuf. Fatan ka isa gida lafiya?"Daga can ɓangaren Alh ya tambaye shi da kulawa.
"Lfy kalau Alh. Ban ma isa gidan ba..."
"Yauwa... faɗuwa ta zo daidai da zama. Bayan fitarku sai muka yanke shawarar kiran Jami'i Labaran don sanar da shi halin da ake ciki. Ka san ta inda aka hau ta. . .