Skip to content
Part 21 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Kamar jira ake ya rage gudun motar wayarsa ta fara ƙara, a lalace ya mayar da idanunsa kan wayar. Alh Lukhman ne, mahaifin Firdausi. Ƙirjinsa ne ya buga daram, a tsorace ya ɗaga wayar zuciyarsa cike da tunanin Allah yasa dai lafiya?

“Lafiya ƙalau Yusuf. Fatan ka isa gida lafiya?”
Daga can ɓangaren Alh ya tambaye shi da kulawa.

“Lfy kalau Alh. Ban ma isa gidan ba…”

“Yauwa… faɗuwa ta zo daidai da zama. Bayan fitarku sai muka yanke shawarar kiran Jami’i Labaran don sanar da shi halin da ake ciki. Ka san ta inda aka hau ta nan ake sauka, to bayan dogon tattaunawa dai ya bamu shawarar tunda al’amarin ya zo da sauƙi fiye da yanda muka zata yana ganin gara mu janye case ɗin daga gaban hukuma. Ya faɗa min jiya Khamis ya tura da kuɗi an karɓo mishi motarshi ko?”

Duk da bai san an karɓo motar ba, sai kawai ya amsa da,

“Eh”

“To yanzu abinda za’ayi, ku wuce kai tsaye State CID ɗin ga mu nan zuwa…”

“Alhaji kayi haƙuri. Wlh yanzu haka kaina ciwo yake min sosai, ba abinda nake buƙata sai in ƙarasa gida in sha magani. Idan babu matsala zan tura Khamis ɗin shi kaɗai. Zai bada ragowar kuɗin neman maganin da ta kashe da duk wasu abubuwan da ake buƙata don a kashe maganar gaba ɗaya.”

“To shi kenan, babu laifi. Amma dai na so ace kun je ku biyun don a sake jaddada batun auren a rubuce bayan ta gama istibra’i.”

“Ba matsala Alhaji. Maganar aure in dai muna raye tabbatacciya ce in Allah ya yarda. Ko Khamis yana gargarar mutuwa za’a ɗaura in yaso tayi masa takaba. Ka kwantar da hankalinka.”

Ko da suka gama waya kai tsaye wayar Khamis ya kira, a taƙaice ya sanar da shi halin da ake ciki, da kakkausar murya ya ƙara da yi mishi umarnin lallai ya tabbatar duk kuɗaɗen da aka buƙata ya bayar wanda yarinya ta kashe wajen neman magani ya tabbatar ya biya a take ba tare da ɓata lokaci ba. Bai saurari me zai ce tsakanin ƙorafi da amsawa ba ya kashe wayarsa bayan yaja tsaki ƙasa-ƙasa.

A lokacin da kiran Yaya Yusuf ya shigo wayarsa, yana tsaye qne a gefen titi yana gwada kiran lambar Uwar ruwa da ta kira wayar na hannun Yaya, wani abin mamaki a gare shi shi ne sam lambar bata shiga, ita da ba kasafai ta cika barin waya a kashe ba.

Ya saka hannu yana tare ɗan sahu da niyyar zuwa gidansu don yaji ba’asin kiran sai kiran Yaya ya shigo masa. Ko da yaji dalilin kiran kai tsaye ya tare keke ya nufi State CID.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gurin, saboda sanin da yayi a tafiyarsu an kawo iyaka babu wani taurin kai da ya nuna musu. Bakin aljihunsa ya buɗe sosai ya biya duk abinda suka buƙata. Hatta jami’an bai barsu haka ba, daidai gwargwado yayi musu ihsani kafin ya gama ciccike duk wasu takardu da ake buƙatar saka hannunsa sannan ya bar gurin.

Ya fita daga gurin kenan muhimmin kira ya shigo wayarsa daga Babbar Harka 1. Tsawon kwanaki biyunnan ya shafe su ne wajen jiran kira daga lambar, tunda ya ji shiru, jikinsa ya bashi tabbacin kaya sunyi yadda ake buƙata.

Shi daman babbar harka haka tsarinsa yake, idan aka ji shiru kaya sunyi, idan basu yi ba tun a lokacin da yayi arba da su zai kira a kwashe su da gaggawa.
“Khamis! Ka saurareni da kyau! A tsawon harƙallarmu ina so ka kiyaye wannan, duk kayan da bai kwanta min arai ba bana taɓa iya juriyar daɗewa ina kallonshi ko da idanu balle har in iya danne zuciyata wajen yin maneji da shi, ko da kuwa ina da tabbacin baza’a musanya min ba.”
Amsar da ya taɓa ba Khamis wani lokaci can baya da ya taɓa roƙonshi yayi maneji da waɗanda suka samu don babu wadatattun kaya a ƙasa.

Jikinsa na rawa ya raɓe gefe guda ya danna amsa kiran, bayan ya gama waige-waige ya tabbatar babu mai kallonsa.

“Khamis!”
Aka kira sunansa cikin ƙasaita daga can ɓangaren.

“Na’am! Allah ya taya ma Ranka ya daɗe. Ka daɗe kayi ƙarko kana damawa Ranka ya daɗe, Allah yaja kwana, ya ƙara ɗaukaka, ya kare ka daga sharrin ƴan sa’ido, maƙiya, mahassada.”
Ya jero kirarin a tausashe har yana ɗan duƙawa hannunshi a dunƙule babbar yatsarsa a ɗage alamar sarawa, kamar yana gabanshi.

“Amin, na gode Khamis”
Daga can ɓangaren aka sake amsawa a ginshire. Kafin ya ce komai aka cigaba da cewa
“Kaya sunyi sosai Khamis, kuma na ji daɗi da aka kawo min sabbin hannu masu sauƙin kai da daɗin sha’ani. Lallai ka cancanci sallama ta musamman”

Sai da ya daka tsalle saboda tsananin murna kafin ya amsa da
“Girmanka ne Ranka ya daɗe. Ka ma wuce haka Ranka ya daɗe. Allah ya bar mana kai…”

“Ka saurare ni da kyau. Muhimmiyar tafiya ce ta taso min, yanzu haka na gama shiri tsaf zan bar kaduna. Duk inda kake kayi saurin zuwa ka kwashi kayannan. Akwai saƙo na bar maka a hannun Idris (Mai kula da al’amuran gidan baƙin) Idan Allah ya dawo da ni zan neme ka.”

Ko kafin ya amsa har an katse wayar. Ko da yaga tare mai keke napep bazai yiwu mishi ba, ga kuma motarshi tana gida, komawa ɗauko motar sannan ya wuce gidan baƙin Arewaci na Babbar Harka 1 zai ɓata mishi lokaci sai ya kira ɗaya daga cikin abokan harƙallarsa.

Da gaggawa ya ƙaraso, don lokacin da kiran ya iske shi ba’a nesa yake ba. Bayan caf-cafkewa da shaƙiyanci irinna abokan da basu sa komai a gaba ba sai iskanci. Gaban motar ya shige abokin mai suna Ibrahim amma suna kiranshi Maliyans ya ɗan waiga yana tambayar Khamis
“Shegen gora ina muka nufa ne?”

“Cigaba da tafiya kawai Maliyans, can wajen gari muka nufa. Wasu sabbin kaya ne da na bayar da hayarsu shekaran jiya zan je in kwaso…”

“Ah kar dai ka ce min kwantai suka yi?”
Maliyans ya katse shi da tambayar yana ƙyalƙyala dariyar shegantaka.

“Haba… Wuce nan wallahi. Sai ka ce wani kai? Kai da kanka ka sani ƙarya ne inyi zaɓi in tura a dawon da su da cewar basu yi kala ba. Muhimmiyar tafiya ce ta kama wanda ya hayi kayan, albishirin kyakkyawan sallama yayi min yanzunnan shi yasa kaga ina ta tsuma…”

“Ka ce nima zan samu kaso na…?”

“Wannan dole ne. Ci muci ai bai hana arziki.”

A tare suka ƙyalƙyale da dariya kafin suka cigaba da hirar da ta shafe su. Ko da suka isa, Khamis shi kaɗai ya shige gidan yabar Maliyans a waje. Kafin ya shiga babban falo inda ya saba tarar da ƴanmatan da ya kai gidan sai da ya nemi Idris, ya karɓi saƙon da aka bar mishi.

Miliyan ɗaya da rabi cif ya gani a cikin babban envelope ɗin, kamar wani sauna shi kaɗai ya riƙe baki yana ƙyalƙyala dariyar farin ciki. Maƙurar sallamar da Babbar harka yake mishi 1m ne, amma yau an ƙara zuwa 1.5, lallai wannan babban abin farin ciki ne.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya zare ɗauri biyar na bandir ɗin kuɗaɗen, cikin ƙwarewa ya maƙala stepler ɗin da aka danne bakin envelope ɗin kamar bai taɓa wani abu a cikin kuɗin ba. Sannan ya tafi gurin ƴanmatan.

Arba da su da yayi yasa shi sauke ajiyar zuciya uku a jejjere. Lallai sun cancanci wannan gwaggwaɓar sallama. Zuƙa-zuƙan ƴanmata ne kuma kyawawa na gasken gaske. Ga su farare tas, cikakku ta ko wane ɓangare.

Ko da ya gabatar musu da shi ɗin wanene a ladabce suka gaisar da shi. Domin Big Aunty ta faɗa musu ko shi ɗin wanene a cikin harkarta. Ta faɗa musu da shi ne kawai za ta fara haɗa su ya zama kamar mabuɗin haske na wannan harka da suke sabbi a ciki.

Sai wani gwalli suke mishi da ƙwainane domin an faɗa musu shi ɗin ma ɗan hannu ne ƙwarai. Kuma Big Aunty ta faɗa musu matuƙar suka bi da shi hanya a killace zai basu duk kuɗin da aka sallame su da shi ba tare da ya taɓa ko kwabo ba.

Don haka tun daga nan suka fara hillatarsa. Khamis kuwa ba dama ne, idonshi idon kyakkyawar mace in dai ya haɗiye miyau tabbas sai ya mayar da kwaɗayinshi, balle irin waɗannan da suka kai har suka nemi zarce irin waɗanda yake marari. Suna maƙalƙale da shi daƙyar ya iya jansu suka fice zuwa gurin motar Maliyans.

Daga nan, maimakon su wuce gidan Big Aunty kai tsaye hotel suka wuce. Duk yadda Big Aunty take kiransu a waya shi da ƴanmatan ƙin ɗagawa suka yi.

Sai da suka gama sheƙe ayarsu can da daddare misalin goma da rabi Maliyans ya kwashe su a gajiye zuwa gidan Big Aunty.

‘Babban gida ne mai ɗauke da ƙatoton get na gani a faɗa. Big Aunty, wacce asalin sunanta na yanka shi ne Karimatu. Babbar mace mai shekaru arba’in da takwas. Amma saboda yanga, gwalli, da sanin sirrin gyaran jiki irinna mai da tsohuwa yarinya babu wanda zai ganta ya ce ta kai wannan shekarun.

Ƴar siyasa ce da ta san manya sosai a garin Kaduna da kewaye. A bayan siyasar kuma tana fakewa ne da harkar kano to Jiddah tana cin karenta babu babbaka. Asalinta ba ƴar cikin garin kaduna bane, iyaye da ƴan’uwanta gaba ɗaya suna can Igabi Local Govt. Tun tana ƙanƙanuwa ita macece mai son rayuwa irinta ƴanci da fantamawa.

Da wannan babban burin ta taso a cikin ranta, shi yasa take yiwa ƙauyen da mazauna cikinsa gani-gani, a fili take faɗin an ƙaddari samuwarta a ƙauyen ne kawai amma ita ba kalar garin da ƴan garin bane. Duba da irin halayenta lokaci ɗaya mahaifinta ya katse mata hanzari ta hanyar aurar da ita da ƙananun shekaru sosai, ga abokinsa Dattijo mai shekaru hamsin da biyar.
Sannan ba tare da sanin kowa ba yabi hanyoyi na asiri irin nasu na mutanen da ta yadda in dai ba mutuwa ba, babu abinda zai fitar da ita daga gidan Alh Inusa.

Duk da wannan ƙullin da babu wanda yasan da shi kasancewarta mace mai kafiya da dagewa kan abinda take so bata bari burinta ya mutu murus ba. Waje na musamman ta nema a can saƙon zuciyarta ta adana wannan burin. A haka har ta haifi yara biyu. Kwatsam sai Allah ya aiko ma Alhaji Inusa sanadiyyar ciwon ciki na farat ɗaya, wannan shi ne sanadiyyar ficewarta daga gidan miji. Bayan wata biyu kuma shi ma mahaifinta da take jin tsoro Allah ya karɓi rayuwarsa sanadiyyar hatsarin mota.

Ta fito daga ƙauyensu dalilin wata mata ce mai ɗiban yara aikatau zuwa cikin birni, ba tare da duba yaya rayuwar ƴaƴanta biyu mata zai kasance bayan tafiyarta ba, ba tare da duba ya rayuwar mahaifiyarsu zai kasance ba. Ita dai babban burinta ta samu rayuwar fantamawa irin wanda ta daɗe tana burin samu a rayuwarta.

Sannu a hankali bayan dogon faɗi tashi da bin hanya irinta ya ki haram ya ki halas ta samu cikar burinta. Tayi kuɗi sosai fiye da yadda take tsammani, ta mallaki tanƙamemen gida ta hannun wani ɗan siyasa da tayi ma wahala har zuwa sa’adda ya samu cikar burinsa na ɗarewa kujerar Gwamna.

A wani zuwa Umara da tayi don sarin gumamar jallabiyoyi da ta fara harkarsu kuma Allah ya tarfawa garinta nono ta haɗu da Ogansu Khamis, Alh Bashir mai ɗan kuɗi. Cikin ƙanƙanun lokaci suka ƙulla harƙalla har ta tashi daga hotel ɗin da take zaune ta koma gidanshi na Jiddah. Bayan ta shafe wata guda cif suna gudanar da mummunar mu’amala sannan ta shirya komawa gida Nigeria. Ba tare da wani ɓoye-ɓoye ba yayi mata tayin munanan harkokinsa ita kuma ta karɓa da hannu bibiyu.

Kasancewar a komai zaɓi yake bayarwa, itama dai kamar Khamis, sai ta zaɓi harkar haɗa waya tsakanin ƴanmata da manyan ƙusoshin ƙasar a maimakon harkar neman jinsi. Da wannan dalilin yasa shi haɗa ta da yaran da ke mishi aiki a jihar kaduna. Wannan shi ne asalin dalilin da ya haɗa Big Aunty da Khamis.

Duk girman gidanta da ƴanmata suke tururuwar zuwa suna fakewa da sarin Abaya kaso tamanin cikin ɗari harkar banza ce take kai su. Gidan yayi kama da gidan karuwai, amma ba gidan karuwai bane, saboda duk masu zuwa gidan kusan duk ƴan gari ne mazauna gaban iyayensu. Suna gidan ne don a haɗa su da manyan gari suyi musayar gishiri da manda. Duk yawan ƴan matan da suke shige da fice waɗanda suke zaune din-din-din a gidan su takwas ne. Sauran duk masu zuwa su kwana uku, huɗu, biyar, zuwa sati ɗaya ko biyu ne idan sun samu abinda suke nema su koma gidajen iyayensu.’

Saboda gayyar ta mutanen banza ce har cikin ɗakin barcin Big Aunty Khamis ya bi Zuly, Ruky, Amina wacce suke kira Ami Baby.
Envelope ɗin gaba ɗaya ya miƙa mata, bai nemi ta bashi ko sisi ba, illa jaddada mata da yayi lallai ta tabbatar ta yi ma su Zuly kyakkyawar sallama.

Ba tare da kunyar idanun Big Aunty ba ya ruƙunƙumesu ɗaya bayan ɗaya ya sumbacesu a laɓɓa. Da alƙawarin gobe yana nan tafe.

A gaggauce ya fice daga gidan yana jin yadda gaɓoɓin jikinshi ke amsawa, daman da sauran ciwon jikin dukan da aka yi mishi kwanaki biyu da suka wuce, ga shi ya sake tara ma kansa wata gajiyar ta hanyar mu’amalar banza da wofi.

A maimakon ya koma gida daga nan, Hotel ɗin da suka baro Maliyans ya sake mayar da shi. Wanka yayi da ruwa mai zafi-zafi ya gargasa jiki, ko kafin ya fito daga wankan Maliyans ya dawo mishi da saƙon da ya aike shi na kayan sakawa da duk wasu ƙananun abubuwa da yasan zai buƙata na kwanaki uku. Ya sallami Maliyans da naira dubu ɗari cif. Suka rabu da cewar gobe da yamma zai zo ya ɗauke shi su zaga gari.

Har ya kwanta ya tuno da Ziyada da yaransa, a kasalance ya ɗauki wayarsa ya lalubo lambarta ya danna mata kira. Amma har ta ƙaraci ringin bata ɗauka ba, wasa-wasa sai da ya kira sau uku bata ɗauka ba.

Taɓe baki yayi, a jikinsa yaji tana kallon kiranshi taƙi ɗagawa. Yasan fushi tayi na rashin komawarshi gida akan lokaci. Ya gaji matuƙa gaya, hutu sosai yake buƙata, ko ya koma gidan babu abinda zai iya tsinanawa, ga hayaniyar yara da matsalolin Ziyada da basa ƙarewa matuƙar taga yana waya don gabatar da harkokin sana’arshi ko kuma ƴanmatanshi suka kira a waya.

Gajeren saƙon kar ta kwana ya tura mata da cewar ya tafi Kano, zai kwana uku kafin ya dawo. Bai saurari amsar da za ta bashi ba ko tunanin za ta iya biyo bayan kiranshi ya saka wayar a silent. Ya gyara kwanciya haɗe da ruƙunƙume filo ya fara karanto addu’ar kwanciya barci a zuciyarsa.

******

“Aunty Samira wai inji Baba ya ce ki bashi alƙawarin da kika yi mish…”

“Tasss!”
Saukar wani ƙaƙƙarfan mari a kumatun ɗan ƙaramin yaron da bai wuce shekaru tara a duniya ba yasa shi kasa ƙarasa maganar da yake yi. A gigice ya ƙwalla ihu saboda tsananin zafi da raɗaɗin da ya mamaye kuncinsa har zuwa kunne lokaci ɗaya kamar an watsa mishi tafasasshen ruwa.

Ya kasa tsayuwa guri ɗaya, yayi gabas, yayi yamma kudu da arewa sai ya fice a guje daga cikin ɗakin yana zambarma yana ƙwalla ihu. Hannunsa dafe da kumatunsa. A guje ya nufi ɗan ƙaramin ƙofar fita daga gidan zai nufi waje da sauri uban ya riƙo shi hankalinsa a tashe.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 20Lokaci 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×