Ko da suka ƙarasa asibitin, kai tsaye wajen biyan kuɗi suka nufa. Ba tare da fargaba ko tsoron komai ba Khamis ya biya kuɗaɗen da ake buƙata gaba ɗaya, har ƙarin dubu hamsin ya bada akan kuɗin ko za'a nemi wani abu daga baya.
Samira sai kallonshi take yi tana jinjina kasada da ƙarfin hali irinna Khamis, amma ta san shi ɗin ne baka asara ne, duk abinda yake yi yana sane, kowa ya ci ladan kuturu dole yayi masa aski.
Shi kuwa ko ɗar bai ji ba a zuciyarsa sa'adda yake biyan. . .