Skip to content
Part 23 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Ko da suka ƙarasa asibitin, kai tsaye wajen biyan kuɗi suka nufa. Ba tare da fargaba ko tsoron komai ba Khamis ya biya kuɗaɗen da ake buƙata gaba ɗaya, har ƙarin dubu hamsin ya bada akan kuɗin ko za’a nemi wani abu daga baya.

Samira sai kallonshi take yi tana jinjina kasada da ƙarfin hali irinna Khamis, amma ta san shi ɗin ne baka asara ne, duk abinda yake yi yana sane, kowa ya ci ladan kuturu dole yayi masa aski.

Shi kuwa ko ɗar bai ji ba a zuciyarsa sa’adda yake biyan kuɗaɗen, da kallon Rahma kawai ya san zai fanshe kuɗinsa har da riba mai tsananin yawa. Shi yasa babu fargaba ya buɗe bakin aljihu, har siyayyan kayan shayi da fruits yayi musu mai yawan gaske, ya bata dubu ashirin ta riƙe a hannunta kafin suka yi mata sallama suka bar asibitin.

Daga nan kai tsaye hotel ɗin da yayi masauki Uwar ruwa ta wuce da shi. Yini guda har dare suna maƙale da juna, tsohon tsumin soyayyar da ke tsakaninsu sai da aka tado ta, hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba sadda ta ce mishi za ta tafi.

Samira wata iriyar mace ce mai baiwa da ni’ima sosai a cikin mata. Idan yana tare da ita ko kaɗan ba ya so wani abu ya raba shi da ita. A lokutan baya da gaske ya so aurenta ita kuma ta ce ba aure ne a gabanta ba. Shi da kanshi ya raɗa mata sunan Kankana Uwar ruwa, kuma sunan ya bi ta. Tana daga cikin matan da yake baƙin ciki da kishi sosai idan zai haɗa su da wasu mazan, daga ƙarshe ita da kanta ba gujeshi ba don ransa ya so ba.

Ko a yanzu babu yadda baiyi da ita ta kwana a gurinshi ba ta ce baza ta kwana ba.
Da ɗan haushi-haushi a muryarsa ya ce
“Wato ba ni da arzikin da zan biya ki kwana a gurina ko Kankana? Ni kike yi ma haka ko?”

Tsayawa tayi daga shafa hodar da take yi a fuskarta ta ƙarasa gare shi ta riƙe fuskarshi ta sumbace shi a laɓɓa, kwantar da kanshi tayi a ƙirjinta tana shafa bayanshi alamun rarrashi, da kwantacciyar murya ta ce.
“Ba haka bane, kayi haƙuri Kham! Wallahi yanzu in dai ba gari na bari ba komai dare ina ƙoƙarin komawa gida in kwana. Sosai Momcy take ƙara ɗaukar fushi da ni idan ban kwana gida ba.”

Idanunta ta mayar kan agogon bango sai taga sha ɗaya saura minti biyar. Da sauri ta saki kanshi
“Lokaci na ƙara tafiya, bari in wuce kawai. Ka kwantar da hankalinka, gobe ma rana ce…”

“Dama wata wainar ba ta wake ba Kankanata. Ke ɗin ce za ki ce gobe ma rana ce? Na san ni da in sake ganinki sai ranar da buƙatar kanki da kanki ta taso miki…”

Dariya tayi sosai, bata nemi kare kanta ba don ta san gaskiya ya faɗa. A gurguje ta ƙarasa shafa hodar, ta harhaɗa ƴan kayayyakinta cikin jaka ta ɗaga mishi hannu alamun bye.

“Shi kenan, Allah ya tashe mu lafiya. Kiyi haƙuri babu kuɗi a hannuna. Amma zan tura miki ta account ɗin ki yanzu.”

“Ba ka da case”
Da saurin gaske ta fice daga cikin ɗakin Otal ɗin.

*******

Khamis bai koma gida ba sai da ya kwana uku yana hutawa kamar yadda ya faɗa ma Ziyada. A rana na ukun tun da wuri ya haɗa ƴan kayayyakinsa ya bar hotel ɗin, bayan ya kira wani abokinshi ya daukeshi a motarshi suka shiga gari.

Ba su nan matattarar yan iskan, ba su gidan waccan magajiyar. Khamis idon gari ne, zai iya rantsewa kaf fadin garin Kaduna, ciki da wajenta babu wani wajen ‘ya’yan iska dama na guguwa shahararre da ƙasƙantacce wanda bai sani ba. Duk wani titi da ƴanmatan Good evining ke tsayawa da yamma babu inda bai sani ba, kama daga matattarar yaran musulmi zuwa na sauran ƙabilu.

Shi yasa idan aka tashi neman ƴanmata na hausawa ko ƙabila, waɗanda suka san shi ba sa shakkar tuntuɓarshi. Domin sun san duk kalar macen da suke buƙata zai kawo musu, budurwa ko bazawara.

Bai koma gida ba sai Magriba Abokinshi ya sauke shi a kofar gida ya ƙara gaba, suka rabu suna ma juna shaƙiyanci.

Sai da yaji ana sallar magrib a masallacin unguwa sannan ya tuna ko sallar la’asar bai yi ba. Suna can suna duba sababbin kayan da suka shigo gari bai damu da duba tafiyar lokaci ba. Kamar zai wuce masallacin kai tsaye, sai kuma ya girgiza kai kawai ya shige gida cikin gida, a kafaɗarsa rataye da ƴar madaidaiciyar jaka ta matafiya.

Babu wuta a unguwar, amma da yake suna da wutar solar a gidan ya sa koda ya shiga tsakar gidan haske tar har cikin falonsu.

Yaran gaba ɗaya da Ziyada suna falon. Ita da ƙananun ƴaƴan suna kan sallaya suna karatun Al-Qur’ani Mai Girma, manyan biyu suna zaune kan kafet suna aikin gida da aka basu na makarantar islamiya.

Da ganin shigowarshi bakinshi ɗauke da sallama yaran suka tashi da gudunsu suna mishi oyoyo, ya tare su shi ma da tashi fara’ar sosai a fuskarsa, kamar yayi wata guda bai gansu ba.

Hisham, ɗanshi namiji kuma ƙaramin, mai kimanin shekaru huɗu ne ya riƙe hannunshi yana tambayar ina tsarabar daya siyo mishi? Mutum ne shi mai matukar ƙaunar ƴaƴanshi, shi ya sabar musu da tsarabar ciye-ciye mabanbanta. In dai halin lafiya yake mawuyacine ya shiga gidan ba tare daya rike wani abu na tsaraba ya kai ma yaran ba.

Ya ɗauki ɗan yana shafa kanshi cike da kulawa,
“Kayi hakuri sojana, na gaji ne sosai a hanyar dawowa. Amma in Allah ya yarda gobe zan taho maka da shi, kowa a cikinku ya faɗi abinda yake so zan siyo muku. Kai me kake so in kawo maka?”

Da tsananin murna sosai a fuskar yaron ya fara zano sunayen cakuleti kala-kala da ice cream. Sai da ya gama faɗin abinda yake so sannan sauran suka rufa mishi baya suna zana abubuwan da suke so dangin kayan ƙwalam da maƙwalashe.

Mommynsu tana gefe zaune, izuwa lokacin ta ajiye Alƙur’ani, littafin Hisnul Muslim ne a hannunta tana dubawa, ko kallon tsiya bata jefa musu ba su duka balle na arziki. Ko rububin sannu da zuwa da ƴaƴan suka yi mishi ita bata tanka ba, fuskarta ɗaure tamau.

Sai da ya ɓata lokaci a gurinsu kafin ya sauke Hisham ya wuce daki a gaggauce. Wanka ya fara yi, kafin ya biya bashin sallolin da suke kanshi. Kafin ya gama anyi isha’i, don haka yayi sallar kafin ya sake fita falo, kayan shan iska ne sanye a jikinsa.

Lokacin yaran sun gama abinda suke yi, suna zazzaune a tsakiyar falon akan ledar abinci da aka shimfida suna ci.
Nauwara ta tashi da sauri tana kokarin gyara mishi wajen da zai zauna a kusa da Mommy, lokaci ɗaya tana faɗin
“Daddy sannu da fitowa.”

Hannu ya ɗaga mata alamar dakatar da ita don cikinshi a cike yake, sannan ya amsa sannun da take mishi.

Kusa da Ziyada ya ƙarasa a bazata cikin salon tsokana yasa hannu ya cakuleta a kwuiɓinta, lokaci ɗaya ta zaburo a tsorace, tana ganin shi ne yayi mata haka ta galla mishi wata ƙatuwar harara, a maimakon ta saki fuska kamar yadda yake so sai ta ƙara haɗe gabas da yamma, taja tsaki ƙasa-ƙasa.

Tana niyyar kawar da fuska daga gare shi ya ƙale mata ido ɗaya.
“Madam me yake faruwa ne? Tun da na shigo ke kaɗai sai cika kike kina batsewa. Wa ya taɓo min ƴar kyakkyawar matata?”
Ya ƙarasa tambayar haɗe da miƙa hannunsa da niyyar shafa kumatunta.

Kamar wanda ya nufe ta da wuta, da saurin gaske ta janye fuskarta baya. A fusace tasa hannunta na dama ta make hannunsa da ƙarfi. Cikin masifa da ɗaga murya ta fara magana
“Miye haka kake min? In dai kana son kanka da arziki ka ƙyale ni Khamis. Kayi harkarka inyi tawa, ban kasa da kai ba kar kayi kuskuren kwashewa.”

Daƙiƙu talatin ya kwashe yana kallonta, sai kuma ya taɓe baki, ya wuce kan kujera ya zauna ya dauki remote ya canza tasha daga inda suke kallo. Ko kaɗan kallon ba shi ne a gabanshi ba, haka zalika hargagin Ziyada ko kaɗan bai dame shi ba. Wayarshi ya ɗauka ya buɗe data ya shiga kafafen sada zumunta yana mayar da martanin saƙonnin da aka tura mishi.

Ba yau ne farko da suka ga irin haka tsakanin iyayen ba, amma duk sa’adda lamarin ya faru sai sun ji babu daɗi kaɗan a zukatansu. Ko a yanzu tsuru-tsuru suka yi suna kallon uwar da a bayyane a idanuwansu dai ita ce ba ta da gaskiya.

Sun kasa ci gaba da cin abincin har sai da ta daka musu wani gigitaccen tsawa da ya sa su shiga taitayinsu. Suka mayar da hankali kan cin abincin amma a kasalance, ba kamar da farko da suke ci cikin zakwaɗi da marmarin dambum cous-cous da yasha haɗin ganyayyaki da ƙananun hanta da aka yayyaka a ciki.

Suna gama cin abincin Mannira ta kwashe kayan, Nauwara kuma ta gyara gurin tsaf ta goge kamar basu ci abinci ba.

Hankalinsa na kan waya yana latsawa fuskarsa cike fal da murmushi bai ma san sun gama cin abincin ba sai da Nauwara ta zauna a kusa da shi ta ce
“Daddy, anyi mana hutun makaranta. Ka ga report card ɗina.”
Ta miƙa mishi takardar fuskarta ɗauke da fara’a sosai.

Sai a lokacin ya aje wayar ya mayar da hankalinshi kan Yarinyar da duk cikin ƴaƴan ta fi ƙwaƙwarshi da shige mishi, a fili take nuna tana tsananin ƙaunarshi, da wannan dalilin yasa shi ma akwai ƙauna ta musamman da yake mata fiye da sauran ƴaƴan.

Takardar da take miƙa mishi ya amsa da dan murmushi a fuskarshi yana kallonta cikin sigar tsokana ya ce
“Nauwara Allah dai yasa ba na ƙarshen aka sake kwaso mana ba wannan karon”

Sosai ta kwaɓe fuska cike da shagwaɓa a muryarta ta ce
“Daddy ai kasan dai ban taɓa yin na ƙarshe ba sai dai na uku, huɗu ko na biyar. To a wannan karon ma na ɗaya nayi!”

Cikin fara’a sosai ya ɗaga takardar yana dubawa,
“Alhamdulillah! Lallai Nauwara kinyi ƙoƙari sosai. Wacce take cin na uku wannan karon ta ɗakko kambun na ɗaya abin a jinjina miki ne Ummina. Gaskiya dole ne ma in miki babbar kyauta kamar yadda na miki alƙawari. Yanzu faɗa min, kyautar me kike so in miki?”

Tayi ɗan jim kamar mai nazari fuskarta cike da murmushi, sai ɗan jujjuya kai take yi irinna jin daɗin ana yabonta. Can ta muskuta ta ce,
“Daddy ka siya min waya, ita nake so”

Kai ya gyaɗa yana cewa
“In dai waya ce baki da matsala Ummina, zan saya miki in Allah Ya yarda”

A fusace Ziyada ta ɗago fuska a cune da fushi sosai a muryarta ta ce
“Wani irin ba ta da matsala? Ka ji me ta ce kuwa? Waya fa ta ce. Gaskiya ban yarda ba a siya mata waya ba. Ta yaya ma za ayi ace yarinya karama kamar Nauwara wadda ko karamar sakandare bata gama ba za a dauki waya a mallaka mata? Tayi hakuri ta bari sai ta kara girma ba dai yanzu ba.”

Ya kalleta a kaikaice,
“To in banda abinki Ziya menene matsala a cikin mallaka mata waya? Yanzu ai abinda ake yayi kenan, Lokacin ya daɗe da canzawa ba irin naku lokacin bane. Yara ƙanana waɗanda basu kai shekarunta ba suna riƙe waya balle ita. Kuma ma ai ba wata babba ce za a siya mata, ƙarama ce wacce za ta dinga tayata home work ba sai ta dinga ɗaukar taki ba. Kuma za a dinga bibiyar abinda take yi da wayar lokaci bayan lokaci. Ki kwantar da hankalinki, babu wata matsala in Allah Ya yarda”

Ta ɗaga baki da niyyar sake musawa, sai wayarshi ta katse mata hanzari ta hanyar fara ringing, alamun ana kiranshi.

Idanunshi ya kai kan wayar, yana ganin sunan mai kiran da saurin gaske yayi zumbur ya tashi ya faɗa ɗaki, saboda tsaro ba don tsoro ba har da haɗawa da kulle ƙofar ɗakin.

Ziyada ta bi bayanshi da kallo cike da takaici da baƙin cikin wannan hali na Khamis. A ce mutum ba shi da wani lokacin kanshi ko na iyalanshi sai na wasu? Kullum cikin waya sai kace wani customer care na MTN?

A hankali ta dawo da kallonta ta mayar ga Nauwara cikin harara ta fara sauke mata bala’i
“Watau Nauwara saboda kin raina ni da na ce kada ki faɗawa Daddynku zancen wayar nan sai da kika mishi maganar ko? Ni ban isa in faɗi magana ba sai kin musa kin aikata abinda ranki yake so ko? To ki kuskura ya kawo miki wayar ki amsa ki ga irin ɓacin ran da za ki haɗu da shi…”

A marairaice ta katse uwar tana magiya
“Mommy don Allah don Annabi kiyi hakuri, Allah wayar nake so. Kin ga fa ƙawayena da yawa duk suna da ita. Kuma kinga yanzu wayar tana sauƙaƙawa mutane abubuwa da yawa, kinga ko ta fannin yin assignment da karatu zan iya amfani da wayar inyi ba tare da wata wahala ba”

“Humm! Ai sai kiyi. Duk inda aka je aka zo babu wani amfanin mallaka miki waya a wannan matakin da kike kai Nauwara. Na faɗa miki, matuƙar kika karɓi wayar nan ni kuma zan karɓe ta har zuwa sadda zan gamsu a karan kaina kin kai ki riƙe wayar.”

Saboda baƙin ciki Nauwara duƙar da kai ƙasa tayi tana hawaye. Allah ya sani tana matuƙar son waya a rayuwarta, amma ga shi rijiya ta bada ruwa guga na neman hanawa.

****

A gefen gado ya zauna, cikin sauri ya ɗaga wayar da sunan Ogansu yake yawo akai. Ya san ba ƙaramin abu bane zai sa ya kira shi da kan shi, domin mafiyawancin lokuta sai dai ya bada saƙo a faɗa mishi.

“Barka da dare ranka ya daɗe”
Ya furta cikin girmamawa da ƙanƙan da kai.

Daga can ya amsa mishi cikin muryar girma
“Yauwa! Khamis kana jina ko? Akwai babbar tawaga da za ta shigo garin Kaduna gobe da hantsi. Ka kula sosai domin ba na son shirme ko kuskure a cikin wannan harka. Nunannun yan shiloli muke so, nasan kasan ko wasu iri ba sai na maka gwari-gwari ba. A shirya su da kyau sosai fiye da yadda muke tsammani, na san baza ka bani matsala ba. Abinda nake so komai ya zama a ƙasa kama daga masaukinsu a masaukinsu zuwa duk wani abu da ka san zai nishaɗantar da su. Ba sa harkar wasa da ƙaranta, kana ga za mu samu yadda ake so cikin ƙanƙanin lokacinnan?”

Tun ma kafin ya gama rattaba bayaninshi tuni har ya gama ware wadanda zai yi wannan kwangilar da su. Ya gyada kai da sauri ya ce

“kwarai kuwa Oga, ai an ma same su an gama!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 22Lokaci 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×