Skip to content
Part 25 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Tunda suka rabu akan hanya shi da Yaya rana ta ƙarshe da suka baro gidansu Firdausi, bai sake neman Yayan ba shi ma bai neme shi ba. Tsakani da Allah ma ya ɗan manta da babin ɗan’uwan nasa, daman dai yana nacin nemansa ne idan matsalar da tasha ƙarfin magancewarsa ta taso.

Tunda an gama Case ɗin Firdausi, don haka ya aje Yayan da al’amuran da suka shafi Yayan a gefe ɗaya. A yanzu ganin sunan Yaya dole hankalinsa ya ɗaga, ko rantsuwa yayi ba kaffara yana da tabbacin yadda suka rabu rannan da Yaya akan titi har yanzu bai huce daga ɓacin ran da yake ciki ba.

“Wannan kiran ba na alkhairi bane.”

Ya faɗa a fili yana ƙanƙance idanu cikin ɓacin rai.

Gefen titi ya faka motar, ganin kiran farko har ya tsinke na biyu ya shigo yasa shi ɗaga wayar a gaggauce. Da nutsattsiya kuma kamilalliyar murya kiran da cikakkiyar sallama

“Assalamu alaikum, Yaya barka da dar…”

Acan ɓangaren Yaya Yusuf bai bari ya ƙarasa ba saboda kwata-kwata baya da lokacin zama wani musayar gaisuwa da ƙanin nasa ya katse shi da cewa,

“Wa’alaikumussalam. Ya maganar mu ta kwana ne da kai Khamis?”

Ɗan zaro idanu yayi a tsorace kamar yana gaban Yayan, da in’ina a muryarsa ya ce.

“Maga…magana kuma Yaya? Wa…wace magana kenan?”

Cikin yanayin gajen haƙuri da ɓacin rai Yaya ya mayar mishi da martani

“Akwai wata magana da ke tsakaninmu ne a yanzu wadda ta wuce ta aurenka da Firdausi?”

Kici-kicin yayi da fuska kamar wanda aka ambata mishi sunan mala’ikan ɗaukar rai. Da ɗan hasala a muryarsa ya ce,

“To Yaya me ya rage ne yanzu tsakaninmu da su? Asiri ne muhimmin abu kuma na faɗa muku an karya, to me yayi saura kuma? Auren nan fa ba dole bane…”

“Aure kuwa dolen-dole ne tsakaninku Khamis, ko da kuwa auren yarinyar nan shi zai zama ajalinka Wallahi sai ka aure ta.”

Ya katse shi cikin masifa. Yayi ƙwafa mai ƙarfi, zuciyarsa cike da takaicin halin Khamis ɗin ya ƙara da cewa,

“Kuma da kake ta wani ikirarin an karya asiri ai muna jira Lokaci ne ya nuna mana idan da gaske an karya ɗin! Aure kuwa ina tabbatar maka babu abinda zai hana shi matuƙar ina numfashi kai ma kana numfashi. Ba dai ka ce sai ta yi istibra’i ba? Za mu ga ƙurewar ƙaryarka Khamis.”

Gefen motar ya maka ma harara kamar Yayan ne a gurin, ciki-ciki ya amsa da,

“Ba fa wani batun ƙurewar ƙarya anan Yaya. Allah ya kaimu ta kammala istibra’i ɗin, aure dai ina sane da batunshi. Kuma ai ba ji aka yi nayi wata magana ta daban game da hakan ba ko?”

“Sanin hali ya fi sanin kama Khamis, na san halinka kamar yunwar cikina. Tun rannan da ka kawo batun tayi istibra’i na san ba wani babban aiki bane a gurinka ka nemi zamewa daga baya. Don haka ne a yanzu na amincewa buƙatar Alhaji Lukman kan cewa gobe in Allah Ya kaimu zamu je can caji ofis a sake rubuta yarjejeniyar auren a gaban hukuma!”

Wata irin zabura yayi hankalinshi a tashe, hannunshi ɗaya dafe da kirjinshi yana zare ido ya ce,

“Yaya ofis din yan sanda fa?”

“Ƙwarai kuwa! State CID ma za mu koma don ka san ba da wasa muke ba.”
Yayan ya amsa mishi da murya mai ƙara tabbatar mishi da gasken gaske yake yi.

Marairaice murya yayi sosai, a idanunshi babu abinda yake hangowa sai mugun dukan da ya ci a hannun jami’an gurin sa’adda ya ce bazai auri Firdausi ba.

“Haba Yaya don Allah! Wai me yasa kake yi mun haka ne? Ba ka ko duba girmana da mutuncina saboda Allah da Annabi kai da kanka za ka dinga haɗani da mugayen jami’an gurinnan!”

Yaya Yusuf shiru yayi cikin ɓacin rai yana jujjuya kalaman Khamis ɗin a zuciyarsa. A hankali ya tambayi Khamis ɗin.

“Mutunci da girma kake magana akai Khamis? Wai daman kana da su?”

Shiru yayi bai amsa ba, sai Yayan ya cigaba da cewa,

“Kai yanzu nan har wani sauran mutunci da girma ya rage maka bayan irin abubuwan da kake aikatawa ba na mutane masu mutunci da girma bane?”

Nan ma dai bai ce komai ba. A hassale Yaya ya cigaba da cewa,

“To bari kaji in sake tabbatar maka, ko ka ƙi, ko ka so, sai mun je anyi wannan yarjejeniya gobe. Don Allah kar ka zo goben kaga abinda zai faru, mutumin banza mutumin wofi kawai!”

Ya kashe wayar bayan ya ja dogon tsaki.

Shi kuwa Khamis wayar ya bi da kallo, zuciyarsa cike da tu’ajjibin Yayan nasa. Shi fa gaba ɗaya ma mamakin yadda Yayan ya ɗauki lamarin da wani bala’in zafi yake yi, ina ruwansa? Yarinyar nan dai da danginta shi ya jangwalo su, to a ƙyaleshi mana ya nuna musu shi ma fa ɗan garinnan ne. Dogon tsaki yaja ya fara ƙoƙarin tayar da motarshi.

A fili yake faɗin,

“Lallai Firdausi nema take yi ta zame min ƙarfen ƙafa. Ni kuwa ba sam bazan lamunci haka ba. Ba a kanki na fara lalatawa in yasar ba don haka a kanki bazan fara auren lalataccen abu ba. Ya zama dole in ɗauki ƙwaƙƙwaran matakin da zai kai mu ga rabuwa ta har abada.”

A guje ya harba titi ganin ƙarfe takwas na dare har da ƴan mintuna. Kai tsaye shagon sayar da wayoyi ya nufa, ya tsaya aka bashi waya mai kyau wadda ake yayi Android ƙarama. Sai da aka haɗata da sabon layi da komai sannan ya biya kuɗin aka sanya mishi a leda ya wuce.

Kafin ya ƙarasa gidan sai da ya tsaya a hanya ya samu gyararrun kaji gasassu guda biyu manya ya saya da tarin lemuka da kayan tanɗe-tanɗe da lashe-lashe.

Ganin waya a hannunsa a daidai wannan lokacin ba ƙaramin farin ciki matsananci ya jefa Nauwara a ciki ba. Ta ma manta da wani kashaidi da uwar tayi mata, ruƙunƙume uban tayi tana ihun murna da sambatun ta gode Allah ya ƙara buɗi.

Ita kuwa Ziyada sosai ta tayar da ballin bata yarda ba, bazai taɓa yiwuwa ya mallaka ma Ziyada waya a yanzu ba.

Daman ya tsammaci haka daga gare ta, Don haka shi ma ya kafe har da rantsuwarsa kan cewa tunda har ya saya, bai ga wanda zai hana Nauwara amfani da wayar nan ba. Gara ma tayi haƙuri kawai.

A gaban yaran suka hau sama suka faɗo, daman wannan ba sabon abu bane a gurinsu. Abin dai har sai da ya kai ga ya zare mata ido akan cewa daga ita fa har Nauwara ɗin shi yake da iko da su. Da wannan dalilin kuwa abinda yace shi ne doka da oda a gidanshi dole ta bi, ko tana so, ko bata so.

Ƙaƙƙarfan kuka ta fashe da shi ta shige ɗakinta da gudu ba tare da ta ko kalli ledar kajin da tunda ya aje akan teburin cin abinci ƙamshinsu ya cika falon ba.

Kafaɗunsa ya ɗaga alamun ko a jikinshi, ya ƙara da taɓe baki. Sannan ya umarci Nauwara da tsabar murnar sabuwar wayar da tayi yasa ta ma kasa maida hankalinta kan sa’in’sar da iyayen suke yi. Umarni ya mata cewa ta ɗauki rabin kaza ɗaya ta ajiyewa Ziya inda bazai lalace ba zuwa lokacin da za ta sauka daga dokin fushin da ta hau.

Sauran kuma ya zauna cikin yaran suka ci kayansu anan. Shi ɗan kaɗan ma ya ci saboda yini suka yi suna ciye-ciye shi da Ƴar madara.

Suna gamawa ya umarce su da suje su kwanta haka nan. Shima ɗakinshi ya wuce ba tare da ya ko kalli ɗakin da Ziyada ke ciki ba. Wanka ya fara yi, sannan shirin kwanciya ya biyo baya.

****

Washe gari a dole ba don ranshi yana so ba ya shirya da misalin ƙarfe goma zuwa gidan Yaya, ko shiga ciki baiyi ba Yayan ya fito suka hau mota kowa fuska a tamke zuwa caji ofis kamar yadda aka tsara.

Yana ji yana gani aka rubuta yarjejeniyar aure babu fashi tsakaninshi da Firdausi idan ta kammala istibra’i. Bin su kawai yake yi da kallo, don har ga Allah shi a ranshi ba shi da wannan niyyar ko misƙala zarrah. Yana da tabbacin kafin lokacin ya cika zai nemawa kanshi mafita wacce za ta fisshe shi.

Bayan gama rubuta yarjejeniyar aka ba Alh Lukhman da Yayan Firdausi Idrees suka sa hannu, shi ma da Yaya Yusuf suka sa hannu.

******

Sosai tayi nisa cikin tunanin da ta tsunduma har bata ji irin kiran da mahaifiyarta take kwaɗa mata ba sai da ta kai hannu ta jijjigata sannan tayi firgigit! A tsorace ta kalli uwar haɗe da cewa,

“Na’am! Magana kike yi? Me kika ce Iyallu?”

“Wannan wane irin tunani ne kike yi haka Rahama? Na fi minti biyu ina kiran sunanki fa amma baki san ina yi ba. Tunanin me kike yi?”

Kai ta girgiza a hankali, cikin ƙarfin hali ta fara ƙoƙarin sakin fuskarta haɗe da kalaman kare kai,

“Kiyi hakuri Iyallu (sunan da suke kiran mahaifiyar tasu) Wallahi sam ban ji ki bane. Akwai wani abu da kike bukata ne?”

Ta ƙarasa da tambayar muryarta a tausashe.

“Tunanin me kike yi?”

Iyallu ta sake tambayarta da kallon tuhuma.

Ta san halin Iyallu sarai, matuƙar ba amsa ta bata ba baza ta sarara mata da tambayar mecece damuwarta da har take irin wannan zurfin tunanin ba. Don haka ta ƙirƙiro ƙarya ta gilla mata.

“Iyallu kin san satin da ya wuce munyi jarabawa a islamiya. Rashin lafiyarki yasa asha ruwan tsuntsaye nai ta yi ma rubutun jarabawar, sai yanzu da hankalina ya fara dawowa nake tunanin lamarin, addu’a nake ma Allah yasa ba na cikin waɗanda za su maimaita aji…”

“In Allah ya yarda bakya cikinsu. Ki daina damuwa kin ji? Zan taya ki addu’a.”

“Na gode Iyallu. Allah ya ƙara miki lafiya.”

‘Cikin hukuncin Allah anyi aikin mahaifiyarta cike da nasara, ga shi yanzu har tana iya zama ta ci abinci kuma suyi hira, abinda ya gagara a da. Alhamdulillah’

“Amin. Dama magana nake miki akan wannan bawan Allah da ya taimaka mana gurin biyan kuɗin aikin da aka yi min. Allah ya saka mishi da alkhairi, mutumin kirki. Bayin Allah irinsu sunyi ƙaranci a wannan lokacin”

Ba ƙaramin namijin ƙoƙari tayi ba wajen danne faɗuwar gaba da firgicin da ya lulluɓets lokaci ɗaya da ambato mutumin da take kwana take yini da tunaninshi. Daƙyar ta iya buɗe bakinta da lokaci ɗaya ya mata nauyi kamar mai ciwon haƙori ta ce,

“Gaskiya ne Iyallu, Bawan Allahn nan ya taimaka mana ƙwarai da gaske. Babu abinda zamu ce dashi sai dai fatan alkhairi.”

“Amin thumma Amin. Ba don shi ba da yanzu kila wani labarin ake yi ba wannan ba. Idan jiki na ya warware sai muje ki rakani har inda yake harkokinsa inyi mishi godiya”

Bata da wani abin cewa a lokacin wanda ya wuce ta gyaɗa mata kai ta kuma bita da

“To”

Hira suke yi, amma rabin hankalinta ba a kan hirar yake ba, yana wani ɓangaren.

Yau ɗin ranar laraba ce, ranar da Khamis zai karɓi la’adar taimakon da yayi mata. Duk wani bugawar sakan da kuma ƙaratowar lokaci zuwa yammaci, ƙirjinta bugawa yake yi da karfi, zuciyarta tana tsere da daka kamar zata fasa kirjinta ta fita.

‘Da na sani aka ce ƙeya. Ji take a ranta ina ma bata yi gaggawar amince ma tayin da Samira tayi mata ba? Mai yasa ta kasa haƙurin yin amfani da karin maganar nan ta malam bahaushe da ya ce mai rabon ganin baɗi zai gani ko yana bakin kura? me yasa ta kasa haƙuri ta cigaba da addu’a ga mahaifiyarta har Allah ya yanke musu wahala? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! ita yanzu ina za ta sa kanta? Taya za’ace tattalin da ta kwashe shakaru ashirin da biyu tana yi a lokaci ɗaya wani can da bai san darajarta ba ya wulaƙanta wannan tanadi nata akan ƴan kuɗaɗen da basu taka kara sun karya ba?’

Rahma da Samira abokai ne tun na yarinta. Ƙawancen tasu ta fara ne tun daga makarantar firamare ta gwamnati da suka yi, sai kuma ta ƙara ɗorewa zuwa lokacin da suka sake haɗewa a karamar sakandare ta gwamnati. Nan suka zama kamar tif da taya, duk inda ɗaya take, to zaka samu ɗayar a maƙale da ita, saboda duk su biyun yara ne masu nacin karatu.

Su duka iyayensu masu ƙaramin ƙarfine. Dama-dama ma gidansu Samira wani lokacin da ɗan abin arziki, Rahma kuwa da ta kasance marainiya, mahaifiyarta kaɗai gareta. Ita take ta ƙaƙa-ni-kayin kulawa da ita, gashi ba wata takamaimiyar sana’a take da ita ba, wankau ne take yi ma maƙwafta kuma ba kullum take samu ba. Ba kamar mahaifiyar Samira ba da ta kasance mace mai zuciyar nema, ga wadatar lafiyar jiki da Allah ya huwace mata, shi yasa sana’o’in da take yi sun fi kala goma.

Su dukansu basu samu sun wuce makarantar gaba da sakandare ba duk da kyawun sakamakonsu. Suna gida a zaune ne kawai, ba aikin fari babu na baƙi.

Daga baya ne dai Rahma ta samu da ƙyar ta lalubi jari, ta fara sana’ar suyar ƙosai da safe, dankali da doya da rana, anan kofar gidansu, kuma babu laifi tana samun alkhairi gwargwado.

Samira dai tana daga gefe ta zama ƴar cima zaune, amma duk da rashin sana’arta sai take nema tafi Rahmar walwala kashe kuɗi. Kullum za ka sameta da sabbin kaya da na ƙawa masu tsada waɗanda samarinta suke bata.

Da alfahari da ɗagawa take cewa Rahma ita fa jikinta na hutune ba na wahala ba, don haka ita dai ba zata iya wata sana’ar wahala ba balle har ta kai ta ga yin suyan ƙosai, dankali da doya.

A hankali a hankali yau da gobe da taka rawar shaiɗan la’ananne yanayin fantamawar da Samira take yi ya fara taɓa Rahma. Ita ma ta fara kwaɗayin samun wanda zai dinga mata da irin wannan hidima. Ga shi a lokacin da kaɗan-kaɗan ciwo ya fara tasarma Iyallu.

Don samari tana da su, har ma taso tafi Samira samun samari, saboda ta fi Samira farar fata da dirin halitta. Amma sai ta kula duk wanda zai mata hidima to akwai abinda yake buƙata a tare da ita. Don haka sai take yin baya-baya da su tana kame kanta saboda tsare mutuncinta da a kullum mahaifiyarta ba ta gajiya da yi mata nasihar ta tattala mutuncinta.

Kwatsam, rana guda sai ga Samirar tayi wani arziki na ban mamaki. Lokaci guda sai gata da tamfatsetsiyar waya iPhone 12pro. Ta gyara ɗakinta guda a cikin gidansu kamar wata mai aure, wai har ma da mota Samirar take tuƙawa.

Abin ya ɗaurewa Rahma kai sosai. Ta daɗe cikin shiru tana tunani, anan ta yarda da kalmar nan ta lallai zafin nema ba ya kawo samu. Dubi dai duk yadda take dagewa da neman kuɗi buga nan buga can da irin tattalin da take yi har yanzu ko waya ƴar shafa mai ƙaramin kuɗi ta kasa saya, sai mai madannai take fama da ita.

Ranar nan dai da gumu tayi gumu, jinyar mahaifiyarta ya ƙarasa cinye duk ɗan abinda take tarawa ta samu Samirar ta rutseta a ɗaki, tace ta gaya mata sirrin sana’ar da take yi itama ta gwada sa’arta ko Allah zai sa tana da rabon shan kwana lokaci guda.

Sosai Samira ta dinga ƙyalƙyala ma Rahma dariya saboda yadda ta haƙiƙance tana maganar. Daga bisani tace mata babu wata sana’a da take yi, kawai dai buɗi ne daga rabbil izzati.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 24Lokaci 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×