A karo na biyu Hajiya Ladidi ta sake kwashewa da dariya, tana kallon yadda jikin Rahma ke rawar da ya gaza ɓoyuwa.
Idanunta ta mayar kan Samira tana cewa.
"Eh lallai na yarda, ɗanya ce shataf a wannan harka. Amma ba wani abin damuwa a ciki.
Da sannu za ta fahimci komai, za'ayi mata regista da Ƙungiya bayan anyi mata wankan dafa'i da jalabi. Yanzu dai ki shiga da ita ciki ta huta, ki bata duk abinda za ta buƙata. Ko jibi haka za'a haɗa taron ƙungiya taga membobin ƙungiya su ma ganta matsayin sabuwar. . .